Showing 138001 words to 141000 words out of 186291 words
zuciya da ma gangar jikin ki gaba'daya".
Ta gyara zama ta ce " Ai kuwa kana da Babban goro fari kal Baffan Iyah".
Da murmushi ya ce "Abin da muka Dade muna addu'a da fatan ya kasance ne zai tabbata bayan mun debe kauna da samunsa".
Zuciyar Innah ta sake takura amma sai ta shanye ta ce "Al'amarin ubangiji ya wuce hakan, yana zartar da komai a sadda ya nufa".
"Baffa ya ce "kwarai kuwa komai nufin Allah ne, bana dai kukanmu ya kare domin ubangiji ya nufa zaman Iyah yana daf da karewa a gabanmu, dazun nan Mutari ya zo mini da wannan albishir din, tun yamman na so na fa'da miki, ganin ki wani iri yasa na ce wannan maganar mai dadice bari na bari sai mun zauna".
Yana rufe baki ta fashe masa da kuka sosai fiye da wadda ta yi akan auren da Mk ya yi. Kuka sosai ta dinga yi, tana ambaton raini ne zaisa Mukhtar ya iya zuwa gabansa ya ce zai mayar da Iyah a yanzu, bayan ya gama wulakanta ta, ya gama cusa musu ba'kin ciki. Ba dan karfin imani ba da yanzu barin jikinta ba ya aiki saboda tsananin tozarcin da Muutar ya yiwa Iyah har da su, shine yanzu da aka samota da kyar zai dawo ya ce zai mayar da ita, saboda yana ganin komai ya ce maka haka zaka yi masa?"
Baffa ya yi shiru yana sauraronta, wannan ne karon farko tun aurensu da ta zauna take fa'da masa magana cikin kara'di da daga murya, kullum harshenta a kasa yake dan haka ya mata uzziri domin ba dabi'arta ba ce.
Ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka sosai tamkar yarinya karama.
Ya ce "Yanzu wannan kukan na menene Salamatu?"
Kai tsaye ta ce "Na ba'kin ciki ne, saboda wallahi na tsani duk abin da zai hada Iyah da Muutar, Jawad ne a tsakanin su ubangiji ya raya shi, amma ni kam na rufe babin wannan yaron mai kafirin ri'ko, da 'Kullaci da kuma rashin ragayya".
"To kuma idan ubangiji bai rufe babinsa da Iyah ba fa? Ya ya zaki yi ne?"
Kafin ta yi magana ya sake cewa na bashi dama ya nemi amincewarta, zan kuma ta ya shi neman yardarta".
Ta kuwa sake fasa kuka tamkar wata sa'ar Iyah.
Ya hassalo ya ce "lallai kin bani Babban goro fari kal Salamatu! na gode miki, amma abin da zan fa'da miki, 'daya ne, Ni ne na haifi Iyah kuma nine wakilinta, ko da shari'a ta bata damar ta zabi wadda ta aminta da shi, a matsayinta na bazawara, Nima kuma shari'ar bata ba ta bata damar yi mini kwangen biyayya ba, dan haka ba zance miki komai a yau ba, sai ta zo gidan nan a gaban ki zan tambayeta ra'ayinta. Da ra'ayin ta zaku ga matsayata".
Haka tsofaffin masoyan suka kwana zuciyoyinsu ba da'di amma Inna ta ta nan kan ba'kanta tana fatan ko zaman mota kar Allah ya sake hada su bare zaman aure, shekaru bakwai yarinya na zaune, sai yanzu tana shirin tsayar da miji zai lallabo ya watsa maneman, kai Muutar ya cika tabbataccen marar kunya, kuma marar mutunci, ta tabbatar zai iya aikata abin da ta gani a mafarkinta sai dai da ikon ubangiji ba da Iyanta ba.
A bangaren Sa'adah kuwa ta shanye murnar dawowar Mk, domin sai da suka zauna da Suamayyah ta sake gane ba 'karamin wauta ta yi ba da ta bari ta ji da'din dawowarsa cikin rayuwarta, domin washagari da zata fita zuwa kotu hawaye Sumayya ta dinga yi tana cewa "Iyah yanzu dai da kike da shekaru talatin da biyu ai ya kamata ace kin fahimci ba abin da mace zata ri'ke a duniya sama da martabarta da 'kimarta. Domin kyau da arziki duk suna samun tawaya, amma idan mace ta ri'ke darajarta to ko da tsufa ya yi wa kyakkawar surarta tawaye wannan 'kimarta da ta ri'ke zata bata kariya. Kar ki bari matsananciyar soyayyar da kike yiwa Mukhtar tasa ki kasa gane a yanzu kinfi bu'katar ki yi daraja a maimakon samun son zuciyar ki.
Sa'adah da take jin magaganun Sumayya har cikin kanta ta dago ta kalleta, sai ta ji a yau tausayin Sumayya ne ya kamata saboda yadda take ganin rauni da wata irin fargaba a kwayar idanuwanta, tana kuma ganin wata irin soyayya da jini kawai ke samar da ita saboda tsananin karfinta da amincinta.
Ta matsa ta rungumeta cikin rawar murya ta ce "Na gode Anti! Ko yau Baffah da Inna suka barmu na san Zan yi kukan rashin ganinsu ne, da kuma adduionsu gare ni, Amma ba na rashin gata ko rashin samun wani abu ba, na tabbatar ubangiji ya zaba mini ke ki zame mini Yar uwa kuma garkuwa domin ya san idan ban samu irin wannan katangar ba zuciya ta tana iya tarwatsewa adalilin jarbawar rayuwata mai zafi ce, Ina tabbatar miki Anty ke ka'dai idan na kalle ki na ga tarin kaunar da kike mini fiye da ta ya'yan cikin sai na yi ta godewa ubangiji domin gatan da ya yi mini mai girma ne".
Suka dinga kuka tamkar anyi musu Rashi ne.
Da kyar suka rabu Sumaayya ta bita har hanyar waje tana fa'din ki rufe dukkan kofofin da kika san Mukhtar zai gan ki, idan kuma kaddara ta sake hada ku, to ki rufe dukkan kofofin da zai ji kayyawan kalmomin bakin ki domin shi din bai cancanta ba, bai dace da ke ba, shekaru bakwai da Kika yi, ba shi kika tsaya jira ya zo ya miki alfarmar mayar da aurenku ba. kin yi wadannan shekarun ne kawai dan gina Goben ki, da samarwa kai nutsuwa.
Sa'adah ta kasa bu'de baki ta yi magana domin kuka ne zai kwace mata mai karfi, saboda kalaman Sumayya tausayi su ke baata.
Tana tafe tana yiwa Sumayya addu'a da dukkan ahalinta tana fatan shakuwa da soyayyar da Jawad da Khairat suke yiwa juna ta bisu har girmansu dan su sake hada zuri'arsu ta zama dunkulalliya.
Tana isa kotun sai ta sake tarar da shari'ar da ta bata mamaki, mahifin Khalil hukumar ya'ki da yiwa kasa zagon kasa da ta'annati wato (E.F.C.C) ta gurfanar domin tuhumarsa da take yi da sama da fa'di da ma'kudan kudaden da ya wawure a lalitar gwamnati a laokcin da yake shugaban maaikatan gwamnati (Head of service).
Ido biyu suka yi da Khali cikin jerin mutanan da suke zaune suna dakon yadda shari'ar zata kaya. Rabon da ta su yi ido da ido idan har lissafinta dai dai ne, shekaru kusan goma sha hudu, tun ranar da suka je partin kammala sakandire a Hang out, ta tuno jidalin da Mk ya yi mata a lokacin. sai dai ta ganshi a hoto, sosai ya girma ya zama zabgegen saurayi na kece raini.
Wani irin abu ya dinga ta so musu dukkansu. Da sauri Sa'a ta wuce gaba inda tawagar lauyoyi suke zaune. Shi kuma ya bita da kallo yana fata iri iri akanta ya kasa daurewa a fili ya ce "Ba zai zama illah dan na auri age mate dina ba, domin har yau din nan da yake da yanmata daban daban yana jin son Gogel din sa, yana tuno moment dinsu kafin kutsen Mk Bichi cikin soyayyar su mai cike da kuruciya da Sanya nisha'di.
Sosai ta yi masa kyau, tafi Halima da ta ke budurwa komai da komai, domin ko a jiya sun hadu tunda basu da nisa . Hula da rigar lauyoyin nan ba karamin kyau da kwarjini suka kara mata ba, ga wani siririn farin glass a Idonta , kamshin ta na turaran Escada sentiment da ya santa da shi tun cikin kuruciya wadda a lokacin na Sumayya take daukowa bata san ma mai daraja bane, yauma kamshin ya shaka, tabbacin har yau da shi take tu'amalli.
A yanzu mahaifin Khalil Sanata ne mai ci, Dan haka yan adawa suka dinga rubuce rubuce akansa har sai da suka ja hankalin hukimar E.F.C.C ta damke shi, wata biyu ana ta dauki ba da'di tunda shi ya kafe ya'ki daukar lauya, ya kuma hana a daukar masa, da yake yana da kyakkawan alaka da gwamnatin jahar Kano sai ta bashi lauyoyi har guda biyar dan su tsaya masa, tunda mai girma gwamna da kansa ya gamsu Hon Ibrahim Hassan bai ci wannan kudaden da ake ambatonsu ba.
Manyan kwarrarun lauyoyi har guda uku masu mukamin (S.A.N.) sai guda biyu 'kananu amma hazi'kai, Bar Sa'adatu Bashir Gogel da Bar Mustafa Isa Gwaram.
Kotu ta 'dage sauraren shari'ar Alh Ibrahim Hassan zuwa 28/6 a shekarar da muke ciki, wattanni biyu masu zuwa.
Duk da adalilin Khalil ta rasa aurenta ta kudiri aniyar tsayawa mahaifinsa da dukkan iyawarta ko dan ta nunawa Khalil martanin kaunar da ya da'de yana yi mata da tarin hidimar da ya mata a rayuwa, ta tuno sadda suke FGC Kano ku'din break din Khalil akanta yake karewa, ta sake tuno sadda zai kwaso abaya da lace tsadaddu da mahaifiyarsa take siyarwa ya kawo mata.
Har gate ta bisu ta gaisa da iyayensa tana jaddada musu su kwantar da hankalin su zasu yi aiki tukuru har komai ya zama tarihi.
Suka yi musayen lamba da Khalil.
A gajiye ta isa gidan Sumayya, amma haka ta yi wanka ta Fara shirin tarbar Anwar da zai kawo mata ziyara.
Anwar bashi da mace amma ba saurayi bane, ya yi aure wata sha'daya da auren matar ta zo haihuwa ta rasu ta bar yaro yana hannun kakarsa wadda ta haifi marigayiya. Shekaru hudu kenan, tun akanta kuma bai sake kula kowacce mace ba, sai
SA'ADAH da yake sonta sosai, duk da dai har yanzu bai samu cikakken hadin kai daga gareta ba, amma dai yana ganin cigaba.
Anwar Ma'aikacine a ma'aikatar zabe(INEC).
*Bayan wata Daya*
Zuwa wannan lokacin Mk ya kasa gane manufar Sa'adah domin tun ranar da Baffah ya sa ya kaita gidan, Sumayya bai sake ganinta ba, a rana yana kiran layinta kamar sau biyar amma bata 'dagawa wani lokacin ma zai kira ya ji tana waya, amma da za'a jima ya sake kiran
sai dai ta gama ringing ta katse, tun baya jin damuwa sosai har ya fara ji har cikin ransa.
Ranar Talata yana zaune a bakin shagonsa kawai ya hango wata dalleliyar mota ba zato yaga Iyah ta fito sanye cikin shigar lauyoyi, kyau iya kyau ta yi daga nesa ya hangota amma ba karamin kwarjini ta yi masa ba.
Bai gama hasashen da wa suke tafe ba, kawai sai ya ganin wani matashin namiji y fito cikin fararen kaya kal, ba shi da gajarta amma sa Mk zai jera da shi sai aga gajartar tasa tunda Mk dogone mai cikakken jiki.
Ganin da ya yi matashin yana nuku nukun shiga gidan sai ya gane bazawarinta ne, domin sai da ta Fara shigewa sannan ya bita a baya, Mk bai san ya akayi ba sai ganin sa ya yi, ya tsallako titi yana leka gidan su Iyah, Bai gansu a zaure ba, kenan ciki suka shiga wani irin azabben kishi ya mamaye masa kalbinsa, ya matsa ya zauna a shagon faci na jikin gidansu, jikinsa ya dinga shaking wato har fa'da masa ta yi tana son namiji cikin fararen kaya? Shiyasa ya mata kwalliya da su. Duk addu'ar da ta zo bakinsa sai ya yi amma baya iya yinta cikakkiya, Karin tashin hankalinsa da Baffa ba ya nan yana Gogel, tunda daminace, shiyasa garin yake da dan sanyi, amma Mk sai zufa yake yi.
Mintina goma ya ji fitowarsu ya yi maza ya juya gefe daya, yana kallon kyakkawan matashin da ba zai nuna masa komai ba sai tsayi da shekaru, a kiyasin Mk zai iya bawa Anwar shekaru talatin da bakwai, shikuwa shekaransu arbain har da biyu kawai dan yana yawan motsa jiki ne ake ganinsa tamkar Yana cikin early 30th ne.
Ba bata lokaci Anwar ya ja motarsa ya tafi, Mk ya na zaune yana jin tamkar ya bi wannan matashi ya masa dukan kawo wuka, Sai ya ga wani saurayi da ba zai wuce sa'an Ahamad ba, ya zo akan mashin.
Ya kafe mashin din ya fito da wayarsa Jim kadan ya Kara a kunne, ya ce "na iso".
Ba jimawa ya ga Sa'adah ta fito cikin dogon hijab har kasa, ta karbi ledar ta mi'ka masa kudi, kafin ta juyo Mk ya yi wuf ya mi'ke ya isa kofar zauren nasu, tana juyawa ta ganshi, zuciyarta ta buga ta rasa gane wanne irin abu ne duk sadda zata ganshi sai ta ji wannan bugun zuciyar. Kai tsaye zata shige ba tare da ta nuna ta ganshi ba, ya jah Hijabinta tare da cewa " kina nufin Baki ganni bane?"
Ranta ya baci sosai ta fincike, cikin gatsali ta ce " Mukhtar bana son wula'kanci ko da nake bin maza nake Ballagazaci, ai ba cikin gidan da ubana ya samar da ni nake yinsa ba, kar kuma ta'ba ni, iskancin da nake yi ba da irin ka bane, da yara ne sa'anina wato matasa irin Ahamad dinka".
Ya kai mata wani irin bahagon mari, ta yi maza ta goce ta bar shi da marin iska, a kufule ta daga ido ta zuba masa nata, ta tsorata da yaddda ta ga idonsa ya yi jawur, zuciyarta ta sake bugawa Amma duk da hakan sai da ta yi jarumtar cewa "A da ne ka dake ni ka kwana kalau Mukhtar amma a yau ina rantse maka da Allah da ka mare ni da ka ga 'kwanjina domin kuwa sai na gurfanar da kai gaban Human Right".
Ya juya tamkar tafiya zai yi, sai kuwa ya juyo ya kaiwa bakinta damka ya murde da iyakacin karfinsa, yana fa'din ai tunda kin riga kin tsufa ba zai yiwu ki dinga mini kaifin harshe ba, jikin ki ne zai fa'da miki. Cikin kishi mai yawa ya ce "ki je ki kai ni court of appeal, ko kuma ki sakaye ni a gidan gyaran hali na muddin Rai karshe dai na san ba komai ya saki hakan ba sai kishin na auri first love Dina".
Hawaye ya goce mata ta ce "Me zan yi wa kishin, ina abin kishin ya ke?"
Ya make kafada ya ce "kin fi kowa sanin inda abin kishin ya ke? wato har kin yi ilimin da za ki kai ni Human Right ko? Ina rantse miki da Allah sai na raba ki da wannan damar".
Ta yi tsaki ta ce "Bismillah".
Gaba'daya ya damkota ya jijigata idonsa ya ka'da da wani irin karfi saboda yadda taga idonsa ya juye nan kuwa wani irin tsumin kishi ke huda masa zuciya.
Ya ce " Ni Kika yiwa tsaki? ta yi kasa da kanta ta kasa magana saboda yadda ta razana, ta san baya son tsaki.
Ganin da ya yi ta dan risina sai ya saketa ya ce "Wa ye wannan da ya kawo ki a mota? Anya Sa'adatu ba zaki bar zuciyata ta huta ba? Na fa'da miki ban son na gan ki da kowa shine kika dauko wani gajeran yaro kika zo da shi, kuma kin san zan iya ganin ku?"
Nan ma shiru ta masa tana jin haushin yadda ta kasa tafiya ta barshi, zuciyarta tana bada ita da yawa.
Zuciyarsa ta dinga zogi tamkar ya curo ta, ya daure ya ce "Baffah na dawowa zance a daura auren nan tun ban janye komen da zan yi da ke ba, na san dai sadaki kawai za'a ce na kawo, ko yanzu na ruga shago zan hado dubu ashirin dan baki wuce hakan ba".
Hawaye ya balle mata ta ce "Dan Allah ka janye komen dan kuwa ba sonka nake yi ba, maganar ban wuce dubu ashirin ba kuma, idan ka so ka ce sadaka ce ta dace da Ni, ina ce kai kana da wadda ta cancanci kudade masu nauyi?"
Ya saki murmushin da Babu nisha'di ya ce "kwarai kuwa, kin san dai fari da tsayin amaryata kadai ya isa namiji ya biya kowanne irin farashi domin irin sune na shiga gaban mota, idan kuma kana gida a maka kwalliya da gashi yala yala kana jin ka tamkar kana tare da balarabiyar Yemen".
Hawaye ya balle mata, har da shesshekar kukanta, shi kuma ya dinga jin dadi, domin ya san har abada shi da Sa'a suna son juna dan haka dole su ji kishin junansu, akan dole yake yin hakan dan sai yafi samun lagonta a maimakon ya yi ta rarrashi tunda ya san bata biyuwa ta da'din rai.
Kafin ya yi magana ta ce "idan ma Balarabiyar Saudiya ce ina ruwana, sai dai kuma na san banbancin jikinta da zagarniyar dabino kawai numfashi ne, ta fa'da hawaye ya na sake zuba".
Jikinsa ya yi sanyi ya ce "very sorry my sweet Sa'adah".
Haka kawai ya fa'da kukan ya zo mata gaba'daya ta dinga yinsa saboda yadda ta ji kishin maganganun da ya yaba mata
"Yi hakuri mana tunda na bata miki Rai ki yi ha'kuri, shiga ki dauko mani abin zama, zance na zo, ai ba maganar kuka tunda dai kin san nafi son ina kamo halittu suna cika mini hannu, zangarniyar dabino ai kawai ta fashion ce".
Ta goge fuskarta ta ce "da wa zaka yi zancen?".
Kai tsaye ya ce "Sa'ade".
Ta ce "bani da muradin ka, je ka dauwama da ta shiga mota, ni ma ubangiji ya bani rabona".
Da sauri ya ce " zuciyata ta gama yarda tunda kika shafe wannan lokacin wani bai yi mini shigar sauri ba, to kuwa tabbas ni ka'dai ne zai mallake ki, ada na kudire idan na dawo na tarar kin yi aure zan nemo Safina na aureta, amma tunda kin cigaba da jirana to na fasa da Safina, dan haka ki ajiye duk wani borin da kike da nufin yi mini yanzu da sunan jana a kasa, ki adana idan an shafa fatiha sai ki ta yin su ni kuma zan ta lallashinki da allurorin kauna kala kala".
Kawai sai ganin ta ya yi ta zube a kasa tana kuka sosai tana tirza kafa ya dinga kallon ta yana murmushin ashe dai har yanzu bata girma ba, zai mata komai ta shanye amma idan ya jingina kansa da wasu matan sai yaga gazawarta da rauninta, bata iya