Showing 150001 words to 153000 words out of 186291 words
miyar ganye da yake santi, haka nan ya yi kewar dambunta, ya yi kewar farfesu mai daddawa, ya yi kewar kunun danyar gyada da shinkafa, da alkubus. Traditional dishes da ya yi kewar su ba za su lissafu ba, hatta shinkafa da wake har yau bai sake cin mai gardin ta Sa'adah ba. Haka nan kwa'don zogale da Rama. Yana matu'kar jinjinawa Inna yadda ta horar da Sa'adah nau'in abinci kala, kala masu dan karen 'dan'dano da kashe kowacce irin yunwa, ga kara lafiya.
Sa'a tana jinsu ta rakube, ko kwakkwaran motsi ta ki yi dan kar a hangota.
Baffa ya fito yana marabatarsu, yayin da hankalin uba da 'da ya karkata a son ganin Iyah.
Lura da hakan da Baffah ya yi yasa ya kirata, ta fito sanye da doguwar riga ta atamfa, dinkin free ne amma ya matu'kar yin kyau.
Da sauri Jawad ya ruga ya rungumeta yana fa'din "Daure ki gwada daga ni sama Mami".
Baffah ya yi saurin cewa "wannan shine gangan Jawad, a gabana ka ke son ka kayar mini da uwa?"
Mk ya murmusa ba tare da ya ce komai ba, bagarar da shi da Inna ta tsiri yi masa na matu'kar damunsa.
Duk yadda Inna take jin haushin Mk bai hana ta zuba masa waina ba, ta zuba masa masar a ledar ta sake kara wata ledar, ta mike ta dauko flask ta shiga kicin ta zubo miya, ta kawo ta ajiye masa a gabansa, a hankali ta ce ga waina, ta koma ta cigaba da aikinta.
Baffah kuwa fa'di yake "wannan tafiya zai yi da shi zubo masa wadda zai ci yanzu"
Da sauri Mk ya ce "Na riga da na karya, na gode, a ransa kuma fa'di yake yaushe zan iya cin abinci a gaban ku?"
Idon Baffa ya sa Sa'adah cewa Mk "Ina kwana".
Ya amsa da sauri, cike da walwala.
Ta shige dakinta Jawad ya bita, ya kwanta a shimfidarta, yana cewa "I miss your scent, I missed everything about you my Iyah".
Ta ce "Ashe ban hanaka fa'dar Iyan nan ba?"
Ya turo baki irin yadda ta ke yi ya ce "Iyah means mother, means uwa, Mami da Iyah all the same".
Ta ce "To dai ban son sunan a bakinka barwa Baffa da Innah kawai".
Mk suka fita tare da Baffah! Jawad ya fito da sauri ya bisu, daga kofar gida Baffa ya wuce inda za shi, yayin da su kuma suka tsallaka zuwa shagon Mk .
Jawad ya yi mamakin yadda aka sake kawata shagon, komai na wurin na zamani ne, ya zauna yana cewa " Azo a wanke mini kafata".
Harara Mk ya galla masa ya ce " Saminu ba ya nan, ina fatan ba Uncle Akil kake nufi ya wanke maka kafar ba?".
Jawad ya yi shiru! Yayin da Mk ya zarce da fa'din, kullum ana idar da Sallar la'asar ka tabbatar ka zo nan kana koyon aiki, zan fa'dawa Akil duk ranar da baka zo ba, ya yi dealing dinka well well, kasan dai shi no nonsense ne baya wasa da yara, ba kamar Uncle Abbas bane da yake yi muku yadda kuke so".
Jawad ya nisa ya ce"Malam ni bazan iya yiwa mutum aski ko wanke kafa ba, zan bata jikina ne kawai".
Mk ya zuba masa ido yana kare masa kallo, a zahiri dai yaron kamarsa ya yi, amma dabi'unsa sak na uwarsa ne, gayu da pride dinsa na Sa'adah ne.
Ya daure fuska sosai ya ce "Jawad ai baka kai a baka yin aski ko wankin kafa bama tukun, share wurin zaka dinga yi, kana wanke towels din da aka yi amfani da su, sannan ka dinga ganin yadda ake gudanar da aikin".
Ya shagwabe fuska ya ce"Haba mana Malam a shagonka zan dinga irin wannan wahalar?"
Mamaki ya kama Mk amma da yake yasan a iya shekarun Jawad da iya tunaninsa shi hakan abin kunya ne, a gurinsa.
Sai ya sassauta ya ce, "Jawad Ni dai a tarihin Nigeria ban taba ganin wadda ya yi karatu mai zurfi ya mallaki jirgin sama ba, Amma na san yan kasuwa da suka fara da kananun business, a hankali business din y tunbatsa har suka sayi jirgin sama. Na san kai kuma burinka ka samu damar siyan jirgi, fa'da mini idan ba ka koyi business ba, how ur dreams will be reality one day?"
"To zan dinga zuwa, amma plz Malam! tell Uncle Akil to be gentle, I really dislike his hershness"
Mk ya sake daure fuska sosai ya kafe shi da Ido, har sai da Jawad ya dinga jin wani irin abu na ratsa shi, ya sunkuyar da idonsa kasa ya ce " very sorry Malam".
Mk ya nisa ya ce "Akil din ka ke fa'din haka akansa? Kanina, kanina Jawad? ashe kuwa nima na shirya, domin Ni da shi ai daya ne a gunka! Ko Ahamad da yake karamin mu ban za ci zaka iya fa'dar wani abu da bai maka a tare da shi ba".
Ya ru'ko hannun Mk ya ce "ba zan sake ba Malam! Plz forgive and forgot".
Ya na fada yana leka waje, yana fatan Akil din bai iso ya ji me ya ce ba".
Mk ya ce daina ma wani lekawa dan kuwa zan fada masa.
Nan da nan kuwa ya fara kuka yana fa'din sorry Malam, ya tsorata sosai, domin Akil mala'ikan Yara ne, baya musu ta Dadi shine discipline master a family din nasu.
"Ok stop crying! Ba zan fa'da ba, amma idan ka sake, ko idan ka zo ka ga baya shago ka ce zaka dinga yiwa su Saminu rudeness to ka tabbatar zai ji komai".
Ya goge fuskar sa yana fa'din " Thank you! Komai suka ce na yi, yi kawai zan yi".
Mk ya ru'ko shi yana fa'din "good boy! Sannan islamiyar nan ta safe zaka dinga zuwa. 9 ake faraawa, a tashi 1pm.
*A samarwa Yara lokacin da zasu dinga zuwa wurin koyon sana'a domin hakan zaisa su taso da burin tsayuwa akan kafafuwansu, zai rage musu burin su kammala digirin farko su zauna zaman jiran gwamnati ta basu abin yi, lokaci ya yi da zamu daina yaudarar kanmu cewa gwamnati zata iya WADATAR da kowa*.
Haka kwanaki suka dinga shudewa, har shari'ar mahaifin Khalil ta zagayo, aka yi ta cakudawa bisa taimakon lauyoyinsa mussaman Sa'adah suka samu kotu ta bada belinsa, bayan sun kawo wadda kotu ta bu'kata a matsayin sharudda.
Kotu ta sake zabar ranar 28/08 a matsayin ranar yanke hukunci na karshe.
Wannan shari'a ta matu'kar Jan hankalin yan siya domin gaba'daya al'amarin siyasa ne, belin da ya samu ya matu'kar daga darajar lauyoyinsa mussaman Sa'adah da ta kasance mace tilo, duka shafin jaridun kasar nan shafin farko sai ka tsinci hoton Sanata Ibrahim Hassan da lauyoyinsa.
Mk da ya tsinci hoton Sa'adah a tsakanin manyan lauyoyi gefe kuma ga mahaifin Khalil sai ya ji tamkar ya shide dan tsananin takaici.
Ya sani tabbas burinta ne tun tana secondary ta zama lauya, shiyasa a lokacin da zai samo mata gurbin karatu ya yi iyakacin kokarinsa ta samu fannin shari'a, Dan ta sami sau'kin halin da take ciki a wanccan lokacin.
Sai gashi duk irin fa'di tashin da yayi akan karatun nata, ashe a mahaifin wannan Dan isakan yaron da ya tsana, zai fara yi wa rana? Ya sake zubawa hoton idon suna kallon juna ita da Bar. Mustapha, da ya kasance saurayi, wani irin al'amari mai nauyi ya danne masa zuciya, idan ba Sa'a ba kishin Sa'adah ne sanadin mutuwar sa domin zuciyar sa zata iya bugawa.
A fili ya dinga ambaton "wallahi ba zan iya ba, ba zan jure ba, dole ki ajiye aikin nan, inko ba haka ba rana daya za'a tarar na zama gawa".
Karfin addua ne kawai ya daidaita Mk.
A yammacin ranar ya shirya ya nufi gidansu yana jin yau kam dole sai ya ganta.
Yana zuwa ya tarar da wani bacin ran domin tarar da ita ya yi tana zance da Anwar da ta ganshi kuma ko dar bata ji ba, bare ta sallami bakon ta saurare shi.
A sanyaye ya juya ya tafi, cikin sanyin jiki.
Hankalin Mk ya yi matu'kar tashi domin ya fara gasgata Sa'a cewa da gaske take zata dora ikon da Sharia ta bata akan ikon Baffa.
Ya kasa jurewa, washagari da yamma ya bita gidan Sumayya, da kyar ta saurare shi adalilin Idris din Sumayya na gidan ya masa masauki a katafaren falonsa na kasa.
Sumayya tana ta fishin akan me zai saurare shi, bayan ya san duk irin ba'kin cikin da suka sha adalilin sa.
Haka dai ya lallaba su tare da fa'din ai mahaifin Jawad ne, dole kuwa ayi taka tsantsan.
A rikice Mk yake fa'din "ya kike so na yi miki ne Sa'adatu? Ke fa kika mini laifi, ke kika zalunce ni, yanzu na samu, na farfado daga gashin Kumar da kika mini, shine kike son sai kin Kai ni kasa, wai me na miki ne da ban cancanci na sami nutsuwa da ke ba?".
Ya nuna kansa da yatsa ni kike cewa ba Kya so? A akan idona kike hira da wani namijin, kika wulakantani a gabansa? Ashe ba ni da wata alfarma a gurinki komin kankatarta, sai na fa'di na mutu ko sai na hadu da mummunar jinya sannan zaki gane ina son ki?"
"Ki na fadawa mutane ba Kya so na ko?"
Ya fa'da da wata irin murya mai nuna sarewa kwarai da gaske.
Ya mike shikenan Sa'adatu, shikenan, na yafe miki komai, ko na mutu ma, na yafe miki".
Ya tafi ko waiwaye bai yi ba.
Kwana ta yi tana jin fargabar ko ya tafi kenan?
Washagari Jawad ya biyota gidan Sumayya ya tarar da ita a compound din gidan tsaye da Alh Mamman da alamu rako shi ta yi zai tafi.
Wani iri Jawad ya ji, ya zo zai wuce su, ba tare da ya musu magana ba.
Alh Mamman ya ce" zo mana tare da yafito shi. Jawad akan dole ya karasa ya ce "ina yini a tsaye kerere, sannan fuskar nan a hade tamkar bai san murmushi ba, bare dariya.
Alh ya ce " da gani wannan shine 'Dan nawa ga shi nan sak Babansa".
Ya zura hannu ya dauko bandir din Yan dari biyu sabbi ya mikawa Jawad yana fa'din ka sha Ice-cream".
Jawad ya sake daure fuska fiye da dazu "Ya ce Babana zai mini fa'da ka ajiye' ka bawa masu bara".
Ya juya ya bar Alh Mamman da kudi sororo yayin da kunyar duniya ta kama Sa'adah, ta kasa cewa komai, mussaman yadda take bashi labarin hankalin Jawad da yadda yake sonta yake tausayin ta.
Haka Suka rabu ita a kunyace, shi Kuma jikinsa a sanyaye na mamakin iskancin karamin yaro irin wannan wato ya san kishin uban sa?
Sai da ta bari sun kwanta ta dinga yiwa Jawad nasiha da nuna masa rashin tarbiyar da ya yi ka iya ta'ba cigabaansa. Ya amsa da ya daina.
Bayan kwana biyu ta je kotu Anwar ya dawo da ita.
Jawad na compound din suna ball da su Ayman da Anis har ma da Khairat, suka ga shigowar motar Su Sa'adah.
Dukkansu yaran suka ruga wajen Yi mata oyoyo tare da gaida Uncle Anwar, soasai suke sonsa saboda yadda yake ciko musu leda da kayan ciye ciye.
Jawad ne kawai bai doshi inda suke ba sai kawai ya ja ya tsaya ya rungume hannunsa a kirjinsa.
Sa'a ta yafito shi da hannu, ya karaso ya tsaya bai ko kalli inda Anwar yake ba.
Ta ce Jawad ga Uncle kullum na tambayar ka".
Ya sake dauke kai ya ce "na ganshi sannunsa".
Ba'kin ciki tamkar ta hadiye zuciya.
Ta ce "ba zaka gaishe shi ba?"
Ba kunya ko shakka ya ce "Ai ba ubana bane" a hankali, sai dai dukkansu sun ji shi.
Ya juya ya barsu.
Anwar da ransa ya baci sosai, dole ya mata sallama ya tafi.
Ta shiga gidan a fusace tana neman Jawad tana jin tamkar zuciyar ta ta Fado dan tsananin bacin rai.
Ta nemi shi ta rasa amma ta kudiri aniyar yau sai ta masa dukan kawo wuka, gobe idan akace ya sake wulakanta ba'kinta zai ji shakka. Ta rasa irin wannan rashin tarbiyar da ya tsira a yan kwanakin nan.
Shikuma yana can ya buya a boys quarters.
Sai yamma lis ya fito, ai kuwa ta hango shi ta windo ta dauki wayar wuta ta fita domin ta san bata isa dukansa a gaban Sumayya ba, cewa zata yi rainata ta yi shiyasa zata doke shi akan idonta.
Cikin Sa'a Jawad ya ankara da
yadda ta tunkare shi a fusace, ai kuwa ya kwasa ya yi gate a guje, ba'kin ciki yasa ta bishi itama.
Suna fita suka yi kicibus da Mk a waje zuwan sa kenan parking ya gama yi.
Ai kuwa ya ruga ya buya bayan Babansa.
Mk ya ri'ke shi yana fa'din "menene?"
Ya kalli Sa'adah da take hawayen takaici, tana rantsuwar sai ta dake shi.
Jawad ya ce " yau zan bika mu tafi Malam kar bar ni anan duka na zata yi"
Mk ya daure fuska ya ce " me ka yi mata?"
Jawad ya turo baki gaba irin na gado ya ce " wani gajeran mutum ta ce na gaisar shine na ce ai ba uba na bane.
Shikenan zata doke ni, Ni kuma bana sonsa ne, haushi yake bani, I hate him so much".
Ya fa'da da karfi tare da buga kafa.
"Kar ka bari ta doke ni Malam domin ni sonsa ne bana yi, ba laifi na yi mata ba".
Surayya Dahiru.
✍️✍️
🌺 *HALIN YAU*! 🌺
NA
*SURAYYA DAHIRU*.
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai dai da satar Dukiya._*
_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_
*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.
100_101.
Cikin mintina kadan Mk ya fahimci dalilin wannan takaddamar tsakanin Jawad da uwar da yake mata wani irin so marar misaltuwa.
Kishin Babansa da yake yi ne sanadin da zai iya yin fito na fito da ita.
Da'di ya yi matu'kar kama Mk ashe dai soasai Jawad ke sonsa, ba uwarsa yake so ba kawai, ya lura bai son kowa ya ratsa tsakanin su, ya fi son ya gansu a tare muddin rai.
Ya ja numfashi ya kalli Sa'adah da idonta ya kuje dan tsananin bacin rai, ya yi jah tabbacin ba yanzu kawai ta yi kukan ba.
Cikin rarrashi ya ce "Wai sai yaushe zaki girma ne? Yau kuma a koke koken na ki har Jawad zaki yiwa?"
Da kuka sosai ta ce "Ai kaine ka ke hure masa kunne ka ke so ya raina Ni. Dama na san da biyu ka tattaro mini shi, to burinka ya cika. Sai dai duk abin da ya mini har zuciyata ta baci, na yafe masa, in Sha Allah ba abin da zai same shi, amma tabbas sai na zane shi, domin ai wannan ba tarbiyar kwarai ya dauka ba, ya dinga yiwa manya rashin mutunci".
Kafin Mk ya yi magana Jawad dake ri'ke da Babansa ya ce "Ni bana raina manya, ba haka kawai na ki gaishe shi ba, sonsa ne bana yi, bakon jiya da na ga mai farin gemu ne ai na gaishe shi saboda ana yawan fa'da mana mu girmama tsofaffi masu farin gashi".
Sa'a ta kai masa wawura amma ya zille, da taimkon Mk.
Mk ya shanye dukkan dariyarsa ya ce yanzu a gabana sai ki doke shi? Kin san dai bana so ko?".
Cike da shagwabar da ba ta yi zaton zata sake yiwa Mk ba ta ce " Billahillazi sai na doke shi, zaman ka lafiya ka miko mini shi".
Ta fa'da cikin dire 'kafa da goge hawayen idonta.
Ta sake cewa "Baka son na dake shi. Amma ka 'ki yi masa fa'da".
Ya ce "cool down Ummu Jawad"!
Ta katse shi da cewa "kar ka kuma ambata mini wannan sunan, ka 'Kira wadda take maka alkunya da shi".
Ya ce "To Na ji".
Amma abin da nake so da ke, ki yi hakuri, yaro ne ai, tunda dai kin rantse, to zan kubutar da ke daga yin kaffara, zaki doke shi, amma ba da wannan wayar ba".
"Ni kuwa da ita zan dake shi" ta fada da sauri.
Mk Yana so ya ce to shi ta dake shi da ita, Yana jin tsoron kar ta zabga masa ta rashin tausayi tamkar ta 'KARFI.
Ya ce "A a Sa'adah kin so ki yi rikici ne kawai, yaushe zaki dake shi da wannan uwar wayar da alamun ta suka nuna ta A.c ce. Zo ki ga yadda za'ayi".
Bata san ya akayi ba, shauki ya kwashe ta, ta isa kusa da su, domin ganin da ta yi Jawad na rungume da shi, sai ta ji tamkar ta tabbata tana ganin su a haka, sune cikon farin cikin ta, ta yarda.
Mk ya rungume Jawad sosai ya ce "Dan yi masa dundu amma ba wadda ya zarta 'kwarin 'kashinsa ba, duka duka ma yaushe kika haifo mana shine?"
Ai kuwa kamar sokuwa ta yar da bulalar ta yi masa dundu har uku, za ta yi na hudu ya ce " oh sorry ya isa haka nan, ni ma zan yi masa fa'da ai".
Ta koma gefe tana harara tamkar idon zai fa'do.
Mk ya saki Jawad da suka kankame juna tamkar zasu zama halitta guda, ya ce " shiga ciki muna zuwa".
Ai kuwa ya tafi da gudu ya na dariya. Abin da ya sake kular da Sa'adah.
Ya kalleta ya ce "wannan ka'dai ya isa ki gane shima yana dandanar azabar da nake sha idan na ganki da wani".
Ta tabe baki ta ce "Allah ya bawa wadanda aka 'ki su, ake zaune da makiyansu ha'kuri".
Ya kasa cewa komai.
Ya saki maganar da cewa "ina son azo nema mini auren ki, jiya Baffa ya ce mini wai Gogel za'a je domin Yayansa dan wan Babansa ya ce wannan karon can za'a je".
Ta murmusa sosai ta ce "Ashe duk wasa ka dauki maganata? Wallahi bana fatan zaman aure ya sake hadamu, na riga da na yarda kaddarar haihuwar Jawad da kanwarsa ya sanya na yi muku kutse cikin soyayyarka da Yar mutanen Yemen".
A sanyaye Mk ya ce"Amma ai na sha fa'da miki sunan kanwar Jawad Aisha