Showing 171001 words to 174000 words out of 186291 words
shi ba, ya lura a yanzu bata da burin kayayyakin 'kawa, ba ta harkar kawaye, cikin dabi'unta masu Muni kaifin harshe ne ya rage mata, shima kuma dole ta rage indai tana gabansa.
Amma sakalci, sai ya ga tamkar tana girma, yana sake bin jikinta ne. Ya tabbatar har kukanta yana jerin abubawan da yake kewarsu.
Sai da ya kammala ya dubeta ya ce " ke kam kin ji kunya wallahi! Ai bai kamata ki tisa ni gaba kina mini kukan shagwaba ba, tunda dai jiya ba irin ro'kon da ban miki akan ki taimake ni ki mini abin da zan samu nutsuwa, amma ki kika shafawa idonki toka. Sai dai kuma na nuna miki ba zanci gaba da zuba miki ido kina mini iyashege ba. Da ace kin ji rarrashin da na miki, da kin ga yadda zan tarairaye ki, na lallashe ki, amma yanzu ko bubburwa zaki yi ba ruwana da ke, bare na san kina sakalcin banza".
Da rawar murya irin tana gaf da fashewa da kuka ta ce "kin yarda da na yi da kai ya isa ka gane sonka ne ba na yi, haka karfin da ka gwada mini, da har yanzu nake Jin ciwo a inda ka bubbbga mini guiwar hannunka ya almata mini kaima sha'awa ta kawai kake yi, amma ba so ba".
"Eh bana son ki".
Ya bata amsa a ta'kaice.
Ba'kin ciki ya turniketa ta ce "Allah ya kawo zazzabi anjima zaka gane lalle nima bana sonka".
Ya ma'ke kafada ya ce "Ameen! Ciwo na kan kowa, nawa ya yi kyau ai. Kema kuma na ki na tafe, domin ciwo ai ba a fatansa, idan yau kaine, gobe na ga waninka. Idan ubangiji ya juya abin ya dawo kanki, a lokacin zaki gane tsiyar ki ka'dan ce".
Ya mike ya na cewa "To ni kam dama kwanaki uku iyalina ta san zan yi. Yau kam ko hayar direban da zai tuka ni zuwa Kano, zan yi, bare kuma Ina fatan ubangiji ya bani ikon tukin da kaina.
Don bana cikin mutane masu yiwa masoyansu 'karya ko butulci, ko danne musu hakkin su".
Zuciyarta ta buga da tsananin gaske, ta san shagube ya yi mata, sannan kai tsaye yake nuna mata yau gurin Farida zai kwana, domin kwana ukun da ta bashi ya cika.
Haka suka dawo Kano, ba wani jituwa a tsakanin su.
Ya sauketa a kofar gidansu ya ja motarsa ya yi gaba.
Tunda ya ajiyeta yake jin tamkar ya rusa ihu, shi dai ko zasu kwana suna Yar tsama yafi son ya ganta a kusa da shi, ko da ba zata kula shi ba, haka nan shima ko ba zai mata maganar ba, amma dai ya ganta kusa da shi shine samun nutsuwarsa, ko shareta da yake yi, Karfin hali kawai yake yi da son kwatar kansa a hannunta, tunda ya san halin iyashegenta.
*Bayan sati biyu*
Tunda Suka dawo kullum Mk sai ya Kira Sa'a a waya, sau tari bata dauka, ranar da ta yi niyya ta dauka, to kuwa zai ta yi mata magana ne, sai ta yi kamar bata ji shi ba.
Bai yi fishi ba, a hakan dai yake 'kiranta, zuwa ne dai ba ya yi. Wani lokacin ma zai je shagon Baffah su sha hirarsu, amma ba ya neman Sa'a.
Suna cikin haka tafiya ta same shi zuwa jahar Akwa-ibom. Zasu yi wani bincike a Jami'ar jahar na tsawon wata 'daya.
Ya gama lissafinsa ba zai yiwu ta tafi da Farida ba, domin aikinta ba irin wadda za'a yi masa shan ruwan tsuntsaye bane.
A zuciyarsa yafi dokin tafiya da Sa'a tunda dai har yau bata bashi dama ba, ko waccan ma, da tsiya tsiya aka yi, shikuma so yake, ayi da yardarta da amincewarta, ta yadda zata shayar da shi kalololin soyayyarta masu gigita shi.
Saura kwanaki biyu ya yi tafiyar ya iske Sa'adah a gidan Sumayya.
Suna zaune a falon mai gidan.
Ya sassauta murya ya ce "Tafiya ce ta same ni, zuwa south, shine nake son ki yi mini rakiya, zan jima domin zan shafe akallah wata guda".
Ta girgiza kai ta re da cewa "ba inda zani".
"Umarni fa na baki".
"Gaskiya ba zanje ba, tunda dai ban tare ba, umarninka baya kaina, ka je ka tafi da wadda idan ka yi tafiya baka wuce adadin kwanakin daka fa'da mata zaka yi, saboda sonta da isar da ta yi.
Ya numfasa tare da mikewa yana cewa "na gode sosai da wannan shawarar, ya ajiye mata kudi masu auki, ga su nan ko wani uzzirin zai taso miki, sai na dawo".
Har ya kai bakin kofa, sai kuma ya juyo, ya kalleta ya ce "zuwa yaushe kika shirya tarewar?"
Kai tsaye ta ce "idan abin da nake so ya samu nan da wattanni hudu".
Ba'kin ciki ya kama shi, amma sai ya yi nufin su raba bacin ran tare ya ce "To kawai a barshi a rabin shekara mana, wattanni shida kenan"!
"To kawai mu bar shi a shekarar kawai".
Ta fa'da a kufule sosai.
Ya yi tafiyarsa ba tare da ya sake cewa uffan ba".
Sai itace tana ganin fitarsa ta fashe da kuka sosai, tana gasgata da gaske ne yafi son Farida akanta.
Mk yana tuki amma a fili yake cewa " Ubangi ka mallaka mini zuciyar Sa'adatu da tunaninta, Allah ba zan iya ba, kaine mai sarrafa zukatan bayinka, Allah ka hore mini wannan yarinyar da take neman manna mini hauka, bayan hawan jinin da nake fama da shi adalilinta!
Kai ka jarrabi zuciyata akanta, ubangiji kar ka jarrabe ni a cikin hankalina da tunanina akan sha'aninta".
Haka ya tafi Uyo shi ka'dai tamkar ba mai mata biyu ba, amma a kullum yana ro'kon ubangiji akan a mallaka masa tunaninta tamkar yadda aka mallaka masa zuciyarta, hakanan duk sallar duniya sai ya roki Ubangiji akan a sassautawa Sa'adah kishin dake neman jefasu yanayin da yake tunanin sun yi bankwana da shi.
Satinsa biyu da tafiya Wanda ya yi dai dai da watansu daya da dawowa daga Sokoto.
Sa'a ta kasa gane kanta, bata ciwon komai, amma yini take tana zubar da miyau, da ta gaji sai take fama da alawowi ko cingum, ko kuma kaninfari.
Matu'kar kuwa ba komai a bakinta to kuwa miyau zai cika mata shi.
Ga 'dan karen barci. Da kanta ta yiwa kanta alkalanci tabbas ciki ne da ita, domin tana iya hakaito haka cikin Jawad ya yi mata.
Duk da yadda ta gamsu tana da ciki sai da ta yiwa kanta gwaji da P.T strip, sakamakon kuwa ya kasance positive.
Wani irin tashin hankali ya dinga ziyaryarta, ita kuwa da wanne ido zata kalli Innah da kuma Anty Sumayya?.
Da wanne irin harshen zata musu bayanin da zasu gamsu, sau 'daya tak wani abu ya gitta a tsakanin ta da Mk, shima kuma ba da sonta da yardarta ba, fin karfi ya gwada mata.
Mk ya shammaceta kwarai da gaske, gashi yanzu ya dawo da asalin halayyarsa ta bagarar da ita da lamarinta.
Ta nisa tana tunanin hanyar da zata bi ta boyewa Innah halin da take ciki. Ta shafa cikin tana Jin wata irin zazzafar soyyaarsa na huda dukkan sassan jikinta.
Cikin Jawad ta same shi cikin kuruciya, da kuma sa Rai za'a samu tunda tana ganin da anyi aure ake samun ciki a haihu.
Cikin kanwarsa kuma bai zo mata a sadda take so ba, asalima unwanted pregnancy ne, sai dai bayan ta haifeta ta dora ido akanta aka dora mata sonta fiye da tsammani, a yanzu da hankali ya shigeta ta tabbata tana jin son cikin jikinta kwatankwacin yadda take jin son Jawad. Shine kuma cikin da ta yi 'mararin samuwarsa duk da bai zo a lokacin da ya kamata ba.
Washagari ta nufi asibiti, aka yi mata gwaji na sosai, sakamakon dai 'dayane da wadda ta yi da kanta. Ta dawo gida tana ayyana lissafin zuwanta Sokoto, lissafin cikinta wanda yana shirin shiga sati na biyar.
A yanzu ba abin da take so irin ta tare tun kafin a ankara da halin da take ciki.
Ta dinga tunanin yadda zata sanarwa Mk tana son tariya da wuri, ta tuna ranar da ya sameta gidan Sumayya kafin ya yi tafiyar, da muradinsa na son su tafi tare, Amma ta kekasa kasa ta 'ki. Ta nisa tana sake tuno sadda suke yiwa juna gatse, inda ita ta ce a bari sai nan da shekara guda.
Zuciyarta ta harba idan kuwa hakane har sai ta haihu, da kusan wata hudu.
"Tirkashi" ta furta a fili, tun yanzu kunyar Innah take ji, gashi dai a gabansu ta yi ciki, sa'ar da aka yi, ba cikin gaba da fatiha bane kamar yadda Inna ta gani a mafarkinta.
Kwanaki uku da zuwan Sa'a asibiti ta kasa daurewa saboda yadda kullum take Samun sababbin alamomin da Za'a fahimci halin da take ciki.
Da daddare tana kwance a dakinta, ta kalli agogo, ta ga lokaci ya fara ja, amma hakan ta kasa hakuri ta 'kira layin Mk.
Ringing biyu ya dauka, Yana ayyana zuciyarsa da ta Sa'aadah tare suke bugawa, domin kwnaciyar da ya yi ba abin da yake tunani sai ita, yana mamaki yadda bata neme shi ba, gashi har ya doshi kwanaki ashirin, amma ko ta 'Kira ta ji ko ya Isa lafiya.
Ya dauka! Amma ta yi shiru, ya nisa tare da cewa "Ina Jin ki, ta jima tana zumbure zumburen baki tamkar Yana gabanta.
Da kyar ta ce "Ina yini?"
Ya amsa da cewa "lafiya kuwa?"
Ta 'kulu amma ta daure ta ce "sai ba lafiya zan neme ka?"
"To na ga tunda na yi tafiyar nan ko Kirana ki ji yana isa baki yi ba. Ni kuma na kira ki ba adadi kin ki picking, saboda kawai ki nuna mini da gaske kike ba kya sona, ba kuma wani abu na alheri a tsakaninmu da cin arzikinsa"
Ya fa'da a dan tunzure ka'dan.
Ta yi shiru tsananin sonsa na ratsata mussaman cikin jikinta idan ta tuna bai yi gaggawar kaita auren wani ba, sai ta tsatson Mk ya fito sai ta ji kawai tana ambaton Alhamdulillah!
Babbar matsalarta kishin auren Farida , ta tabbatar da wata ya aura ma zata ji kishin amma ba kamar na Farida ba, domin shi ka'dai me dalilin da yake sawa ta ji tsanarsa da tsanar cigaba da kasancewar a doron 'kasa.
Hawaye ya cika idonta sosai, ta daure ta kuma cije bata bari kukan ya kwace ba, da rawar murya ta ce "yaushe zaka dawo?"
"Inace na fa'da miki sai na cinye kwanakin wata?"
Ta yi shiru!
Ya nisa ya ce "fa'da mini menene tunda na san haka kawai ba zaki nemi ni ba tunda kin ringa kin jefa ni sahun Marasa adalci da daraja a duniyar ki".
"Ni ni bani da lafiya ne".
Ta fa'da a rarrabe kuma a shagwabe.
"Me ya same ki?"
Ta yi shiru, ta kasa cewa komai.
"Na san dai ba kewata kike yi ba, tunda tuni kin cire ni a masoyinki".
"Dama zan fa'da maka ne, Anty Sumayya da Umman Fanshekara suna son zuwa su ga gidan da zan zauna".
Ya murmusa ya ce "Na san ki tamkar tafin hannuna, fa'da mini dai gaskiyar magana. Kawai ki ce kin fasa yin rabin shekarar kina son tarewa dan kar abin da kike boyewa ya bayyana a gaban su Baffah".
Zuciyarta ta tsinke, da sauri ta ce "me nake boyewa?"
Ya waske da cewa "Tarin Sona mana na zuciyar ki, bayan bakinki yana ta jifana da kiyayya".
Ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ni ai dama ban ta'ba cewa bana sonka ba, sai dai na ce da aure ne bana yi, saboda kaima ai ba ni kake so ba".
"Fahimtar ki ce hakan, kuma Wallahi ina taya ki jin kunyar ace kin rayu da ni shekaru bakwai, amma baki ki san wannene Mukhtar ba".
Ta katse shi ta hanyar cewa
"Ni yanzu me zance wa masu son zuwa ganin gidan?"
Kai-tsaye ya ce "ki ce ban kammala gyran gidan ba, sai nan da wattanni shida lokacin ya yi dai dai da kammaluwar na ki Shirin".
A mugun shagwabe ta ce "Bana son haka, bana so, ka daina daukar hakkina haka Nan".
Wani irin farin-ciki ya mamaye Mk ya ce "fa'da mini me na yi miki na daukar hakki?"
"Ni kawai ka fa'da mini gaskiyar abin da zan fa'da musu".
"Ki fa'da musu saboda kin ce sai kin gama shiryawa, ya sanya nima na shiririce. Da gaske ban tanadi inda zaki zauna ba".
Hakan da ya fa'da ya sa ta fashe masa da kuka sosai.
Ya matse dariyar da ta so subuce masa ya ce "Share hawayen ki kin ji my dear, ki bari idan na dawo sai mu yi maganar a nutse, ki fa'da musu bana gari, Amma da zarar na dawo, zamu tattauna".
Da yake son tariyar take yi a kwanakin nan yasa ta biye masa, suka rabu kalau.
Yana ajiye wayar ya dinga dariya yana fa'din Ubangiji ka kaddara addu'ar da nake yi ne ka karba, ubangiji ka kaddara hasashena ya zama gaskiya.
Ya yi shiru yana murmushi a zuciyarsa sai fa'dawa Ubangijinsa yake yi idan har ya tabbata ciki ne da ita azumi uku zai yi na godiya ga Allah, abin da ya da'de yana son ayi masa kenan haihuwa! yana son ya ga Jawad ya na da mahadi, yana son 'kananun yara.
Ya tuna lokacin da ya matsu Sa'a ta sake haihuwa amma kawayenta suka zugata wai zata tsufa da wuri.
Ya fesar da zazzafar iskar bacin rai, a fili Kuma sai ya ce "Na yafe komai, na manta komai".
Sati biyu Mk ya dawo, zuwa wannan lokacin cikin yana shiga sati na bakwai, ta fara wani irin fari, sai kuma ya canja salon ba komai zata ci ba, asalima bata isa ta sha tsurar ruwa ba.
Sai dai ta sirka ya dai canja launi.
Ga miyau bai tafi ba.
Kullum cikin Hijabi take da safa, saboda yadda kafafuwanta suka yi fari, suka yi fresh, da zarar Baffah ya tafi Gogel zata tafi gidan Sumayya, saboda kada Innnah ta ganota.
Washagarin dawowar Mk ya iso wajen Sa'a da tarin tsarabar manja da kuma kwakar manja.
Da rawar jiki ta kai ta zubo a bowl ta dawo ta hau ci tamkar nama.
Ya zuba mata ido yana ganin sauyuka a tare da ita karara.
Zuciyarsa ya gama gasgata zatonsa. Ya dinga Hamdala a ransa.
Lafiya Lau suka gaisa, ba bacin rai.
Ganin Bai sako maganar da ya ce sai ya zo ba, ya sa ta kawar da fuskarta gede ta ce " Ya maganar da na yi maka?"
"Wacce?".
Ta tura baki gaba ta ce "su Anty sun matsa mini akan zasu je su ga yanayin windows da kofofi saboda maganar labule".
Ya cije ya ce "idan dan wannan ne ba matsala na riga na tanade su".
"Kar ku damu".
Ta juyo ta ce "Na damu ni na gama shiryawa ranar juma'ah zan tare".
Dariya ta kwace masa sosai, yayin da itakuma ta hau kuka marar sauti.
Ya kalleta sosai sai fahimci kuka take tunda ga zuciyarta ba wai na shagwaba bane.
Ya hadiye dariyarsa ya ce "menene kuma amma dai kinsan ban son irin wannan kukan ko?"
Ta kasa magana. Sai da ya dinga rarrashinta ya samu ta daina kukan.
A hankali ta ce "Akan me zaka mini dariya bayan abin da ka janyo mini?"
Da sauri ya ce "me na yi miki?
"Abin da ka yi mini a Sokoto mana".
"Oh sorry Sa'adah! na dauka abin ya wuce ai".
"Ina ya wuce tunda kullum yini nake da yawu a bakina, ga idan Innah na girki sai dai na rufe daki, na yi ta amai ban son ta gane mai nake ciki."
"Ya waske, da cewa to ana boye ciwo ne? Tashi muje ki ga likita".
Ya kalleta gaba'daya ta yi laushi, ya san laushin da ta yi dan ta samu yadda take so ne.
"Ni ba inda zani".
Ya kuwa mike da sauri ya ce "shikenan na fita hakkin ki, mu yini lafiya".
Tana daga zaune tasa hannu ta ru'ko rigar farar shaddar jikinsa.
Ya juyo suka ha'da ido suka dinga kallon juna, suna jin wani irin tsumin soyayya yana tsuma su.
Sa'adah ce ta yi saurin dauke kai.
A hankali ta ce "da gaske na gama".
Ya juyo ga'ba daya ya ce " Sa'a ba zai yiwu na tare da ke a hakan ba, kina musguna mini, ban isa ki mini yadda nake so ba, ban isa na ce ga yaddda zaki yi, ki ce to ba, haka kawai fa kika ce ba zaki tare ba, sanin kanki maganar ba a hannuna take ba, tunda Baba Kika fadawa, shine kuma ya bani umarnin na lamince miki ki kammala shirin ki, yanzu kuma cewa zai yi na nuna bai isa da ni a karo na biyu ba".
Ta tura baki gaba ta ce "Amma ai da ka ro'ke ni akan ka kira shi , na fa'da masa zan tare da bakina".
"Eh na fa'da amma sai na ga bai kamata na matsa miki ba, shekaru bakwai na yi ina kuakan rashin ki, Kinga kuwa duk dadewar da zaki yi kina shirin ba zaki kai irin wannan lokacin ba. Ki Bari ko wata uku ne, nan gaba sai mu san yadda za'a tunkare shi.
Kuka ta fara tana cewa" ba wannan maganar, wallahi ba zan yarda Innah ta fahimci Ina da ciki ba, tunda ba za su gane da bada son raina hakan ya faru ba".
Ya zauana ya fuskanceta sosai, sai kuma ya tafi ya yi sujjud shukur, ya dago yana cewa "Alhamdulillah, ubangiji ya raba ku lafiya, na dade ban ji farin-ciki irin na yau ba".
"Tashi muje ki siyi abin da kike so a matsayin tukuici".
"Ni ba inda zani".
Ido kawai ya zuba mata, jikinta ya yi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa.
Ta mi'ke tsaye, tana tura baki gaba, irin wadda take yi masa a shekarun baya, mai ha'de da wani irin ta'bara da shi kawai take yiwa irinsa.
Nan da nan jikinsa ya hau tsuma da sauri, ya matsa kusa da ita, ya rungumeta sosai, dukkansu sun shiga wani irin yanayi mai tsuma jiki da gangar jiki gaba'daya.
A kidime Mk ya saketa ya shiga waiwayen inda zai ga hijabinta, can ya hango wani a ninke akan akwati.
Da kansa ya ware ya fara kicinyar saka Mata. Tmda taimkonta hijabin ya daidaita.
Ya kalleta sosai ya ce "Bari na fita, sai ki fito muje asibitin a duba ki, daga Nan sai ki raka ni unguwa".
Ta kasa yi masa musu, tana tsaye tana jin yana yiwa Inna sallama, ya fice ya barta tana faman tauna maganar da zata fa'dawa Innah.
Haka ta fito rataye da yar 'karamar Jakarta, ta kalli Inna da take kofar kicin a tsaye,