Showing 99001 words to 102000 words out of 186291 words

Chapter 34 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9757

suka iso ko uffan ba suce ba, wannan sabuwar rayuwar ta yiwa Sa'adah tsauri matu'ka da gaske mussaman da bata saba ba, ya riga ya sabar mata da wasa da raha, uwa uba kullum shine cikin rarrashinta da son ganin murmushi a fuskarta, shiyasa yanzu sauyin ya zo mata da tashin hankali.

Hatta Inna sai da ta yi 'kwalla da taga irin ramar da ta yi, sai dai fa'da sosai ta mata tana fadin tasan itace duk ta jànyowa kanta komai take ciki.
Cikin kuka ta ce "Ni damuwata 'daya yadda Anty zata ga rashin kirkin banje na gaishe ta ba".

Da sauri Inna ta ce "ba zata ga laifinki ba ai tasan aure ki ke yi, ba zaman kanki ba, kar ki damu ta warware sosai, Ba ki ga Anis ba ya yi 'bul'bul da shi, ki bi mijinki a hankali kin ji".

Haka suke rayuwar yau fari gobe tsumma, shi kansa Mk so yake ya manta komai amma maganganunta sun dasa masa wani irin ciwo a zuciyarsa, sun yi karfin da suka sababa masa hawan jinin da yake shan magani kullu yaumin, idan ya tuna sadda ta ke fada masa matan bariki na da daraja fiye da matan aure sai ya ji tamkar ya sume.

Ranan asabar da safe suna karyawa da wainar shinkafa da miyar ganye da ta ji tantakwashi, sammako ta yi ta shirya masa tare da kunun farar shinkafa da danyar gyada, tasan yana son wadannan abincin, sai da ta yi wanka ta ci kwalliya sosai sannan ta gabatar musu.

Suka kammala ta kwashe komai, ta zauna kusa da shi sosai, a ladabce ta ce "Malam ina son na je asibiti".

Ya kalleta ya ce,"me za ki yi?
Ta sunkuyar da kanta 'kasa ta ce " abin nan zan cire ".

Ya zuba mata ido yana jin tausayinta na neman kama shi, yasan so take ta yi abin da zai sa shi farin ciki, dan haka sai ya sassauta ya ce "Inace tun a Abuja na ce ki bari mu gani tukun, ko abin da nake fata zai kasance, idan ki ka haihu kun zama ku uku lissafi zai canja".

Ta dago idonta cike taf da hawaye ta kalle shi " Na dauka ka fasa tafiyar da ni, tunda yanzu ka canja mini akan komai".

Ta fa'da hawaye yana zubo mata. take ya ji sonta ya dawo daga suman da ya yi, Ashe son ba raguwa ya yi ba, comma ya shiga.
Ya bude mata dukkan hannuwansa biyu, a yau bata tsaya jan aji ba, da sauri ta fada masa, yasa dukkan hannuwansa ya rungumeta tsantsan ita kuma tana kuka kasa kasa.

Baice komai ba, illah shafar bayanta yana jin sau'kin 'daurin da kirjinsa ya yi akanta.

Tun daga ranar ya canja, ya daina 'daure fuska, sannan ya bu'de mata kofar nisha'di a tsakanin su, sab'anin satikan da suka shude da ya rufe ta rif.

Saukowar Mk ya sa ta fara murmurewa, tashin hankalin da ta shiga yasa ta manta da wayar ta Bb, sai yanzu da ta sami nutsuwa take fitowa da ita, idan ya fita.



* Tsautsayi*


Ranar da ta zama 'bakar Rana ga rayuwar ma'auratan guda biyu, wadda tarihin rayuwar su ba zai cika ba, sai an sako ranar.

Asabar ce cikin watan Augusta da safe bayan sun kammala karyawa cikin walwala, ya shirya ya mata sallama, zai je ta'aziya Baban Abokinsu ya rasu daga nan zai zarce gidan su ba zai dawo ba sai yamma, ta masa addu'ar dawowa lafiya,ya tafi tare da Jawad. Kafin ya fita ta nemi iznin za ta je kitso, bai hana ba, ya amince mata.
Sai da ta gama komai na gyaran gida, ta yi wanka, ta tsaya jikin wardrobe tana nazarin rigar da zata sanya.

Wata daguwar riga ta janyo data jima bata sa ta ba, garin janyowar ta hado da ledar kayan da su Halima suka kawo mata na tsarabar khalil, wadda ta manta da su, ta leka ta ga rigunan Jawad ne da agogon ta, sai kwalin wayar Blackberry, ta jefa kan gado akan sai ta dawo zata san yadda zata yi ta nunawa Mk rigunan, dan ta fara sakawa Jawad tunda tsadaddu ne.

Ta dauko wayar daga inda take boyewa, ta jona a caji, ta shirya ta rufe gidan ta fita, zuwa bayan layinsu inda take kitson.

Mk da ya fito daga gidan rasuwar gidan Mahmoud suka zarce adalilin motar Mahmoud din ta lalace, dan haka ya kai shi, ai kuwa Jawad ya ce anan zai zauna wurin Dady.

Anan ya 'bata lokaci, ganin hadari ya hadu sai ya yanke hukuncin komawa gida ya huta bayan la'asar sai ya je wurin Hajiya.

Ya isa gidan, da mukallin hannun sa ya bude gidan, ya shiga, dakinsa ya kwanta sai ya tuna yana son dauko Agogon sa dake dakin Sa'adah da bai dauko ba, kullum sai ya fita yake tunawa.

Ya mike ya doshi dakinta, ya duba ya dauko Agogon, har ya kai bakin kofa sai ledar kan gadon ta ja hankalinsa, mussaman da ta kasance ta waje ce, dan haka sai ya koma ya dauko ya bude, ganin kaya ne, ya zazzage su akan gadon, kayan Jawad basu dauki hankalinsa kamar tsadadden agogo da kuma kwalin wayar ba.

Zuciyarsa ta dinga bugawa, wani irin tsoro, da razani suka shige shi, shaidan ya kawowa zuciyar sa caffa! kawai sai ya dinga tuno sadda take cewa matan bariki na mallakar duk abin da suke so cikin gaggawa.


Innalillahi wa ilaihir raji'un kawai ya ke ambata, ya kalli socket ya hango wayar da bai san da ita ba, ya karasa gurin ya dauko, yana dubawa, ganin Blackberry ce kuma babbar sai hankalinsa ya sake tashi, ya kasa budewa saboda ta sa mata password.

Da yake data a kunnen ta ke
Ya dinga ganin sakonni na shigowa ba jinkiri.

Ya dinga jin jiri na katantanwa da shi, bai taba jin tashin hankali irin na yau ba,me Sa'adah take yi haka? A ranar ya gane duk yadda yake daukarta ta wuce nan.

Kusan mintina talatin yana zaune a dakin nata, cikin tashin hankali iri iri.

Daidai lokacin ta shigo gidan a sukwane, tunda ta ga motarsa a waje ta shigo a hanzarce, zuciya na 'bari, ba ta yi zaton zai dawo ba, wacce irin 'kaddara tasa ta bar kayan nan da waya a fili?

Kai tsaye 'dakinsa ta shiga dan ganin wanne kallo zai mata?

Har 'bandaki baya nan, bugun zuciyar ta ya karu, cikin shahada ta nufi ta nufi falon , bata ganshi ba, fargabar ta ta 'karu ta tabbatar ya ga wayar nan.

'Karfin hali ta lalubo ta dora a fuskarta duk kuwa da zuciya da gangar jikinta sun 'ki karban wannan 'karfin halin.

Da sallama a bakinta ta shiga dakin, yanayin da ta iske shi, sai da ya ka'da mata 'ya'yan hanji.
Bai 'dago ya kalleta ba, amma ya amsa sallamarta da murya marar amo.

Ta aro jarumtar 'boye kaduwar da take ciki, ta matsa kusa da shi tana cewa "Ba ka jin dadi ne, da kace sai yamma za ka dawo, a Ina ka baro Jawad?"

Ya dago yana kallon ta, yana jin wata irin tsanar ta na neman Samun muhalli a zuciyar sa.

Bai amsa mata ba, ya zuba mata ido yana jin tamkar ya tashi ya yi ta dukanta. marar gaskiya akace ko a ruwa gumi ya ke yi, ta dinga jin 'barin jiki irin na fargaba, ta yi sukuri tamkar ace 'kyat ta fece da gudu.


Ya mi'ke ya isa inda take tsaye yace " A Ina kika samo wadannan kayayyaki masu daraja?"

Cikin rawar murya tace "Anty Sumayya ta aiko mana, dama na fito da su idan ka dawo, ka gani"

Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ke shirya zancen da babu azanci a cikinsa, ledar kayan ta nuna daga Egypt kayan suke, sannan a cikin kwalin wayar akwai risit din siyan wayar a ciki mai dauke da sunanta a takaice( S.B). Kwanan watan ya nuna ta kai wattanni biyu a hannun ta.

Ya ce "Sumayya yaushe ta je Egypt ban sani ba? Ta hannun wa sa'kon ya same ki?"

Ta muzanta kwarai da gaske, ta kasa bude baki ta yi magana.

Ya dauko wayar yana cewa "Wannan wayar da ta lashe manyan ku'da'de Sumayya ta aiko miki? Ko kuma saurayin ki, ki ka fa'dawa mijinki ya gaza?"

Ya mi'ka mata ya ce "Bu'de mini! tashin hankalin ta ya ninku, Baki na rawa ta ce "kar ka yi aiki da zato, wayar Halima ce ba tawa ba".

Idonsa ya canja zuwa jah, jijiyoyin kansa suka bayyana ru'du ru'du, makoshinsa ya bushe, zuciyarsa ta cushe da tsananin bacin rai, hankalin sa ya kai 'kololuwa wurin tashi.

"A zafafe sosai ya ce " wacce maganar zan kama, wayar Halimace ko Sumayya ce ta kawo miki?
ki bude min wayar nan tun kafin na tozarta ki, domin sai na dauke ki munje gaban Halima, Ina rantse miki da ubangiji agaban Baffa za'a yi komai".

Ta fara kuka tana cewa "Ajiya ta kawo mini itama ba tata bace, dan Allah ka yi hakuri, gaskiya na fada maka".

Karon farko da hakurinsa ya kwace ya dauke ta wani irin mari mai katse ji da gani na wucin gadi! ya ce "Da aurena Sa'adatu, da aurena akan ki? Idan wayar Halima ce to wannan Agogon da kayan na uwar waye?"

Tsananin zafin marin yasa habo ya goce mata, duk da hakan bata damu ba, asalima kukan tsayawa ya yi cak duk da hakan furucinsa ya fi firgita ta sama da marin

A gigice ta ce " gaskiya na fada maka, ka yarda da Ni"

Ta riga ta kudiri aniyar komai zai mata ba zata bude ba, domin a jiya ma sun yi chart da Khalil, duk da ba wani dirty abubuwa suka tattauna ba, amma akwai maganganun da ba zata so Mk ya gani ba, mussaman hotunan sa da ya turo mata, ita kuma ta tura masa na Jawad.

Hankalin Mk ya kai ma'kura wurin tashi ya matsa kusa da ita sosai yace "ki bude min wayar nan idan ba so kike ki wulakanta kanki ba".
ta karba, amma ilahirin jikinta rawa yake yi na tsananin tsoro da firgici.

Fiye da mintina goma tana ri'ke da waya amma ta 'ki budeta, lamarin da ya sanya Mk ya ce ta fita suje gidan su Halima, ya tasa ta a gaba har tsakar gida, anan ta coge akan ita ba zata je gidansu wata Halima ba.

Ya nuna ta da yatsa ya ce "Billahillazi sai kin je, daukota zamu yi, muje gaban Baffa shine al'kalin wannan jahilcin na ki".

Ta rasa inda zata tsoma ranta, ta tabbatar Halima kai tsaye za ta ce ba wayarta bace tunda ba ta 'ki ta kashe auren Mk ba dama.

Ya koma 'daki dauko mukallin mota, tashin hankali yasa ya kasa ganin inda ya ajiye, yana cikin dube dube kawai sai jin 'karar fashewar abu ya ji da karfin gaske.

Ya fito da sauri, ya ga wayar ta rotsa, ta fashe sosai, ta wargaje yadda ba zata tashi ko ta moru ba.

Bai san sadda ya isa gareta ba, ya sha'keta sosai, sai da ya lura tana dab da sumewa ya wancakalar da ita, ya hau dukanta da hannuwansa.

Ganin yana dukan amma ba abin da yake ji na sauki sai ma 'karin tafasar zuciya, ya kyaleta ya zauna a kasa dabas ya dinga ambaton innalillahi wa ilaihir raji'un, hawaye bakin ciki na tsere akan fuskar sa.

Ta dago da 'kyar ta ga yadda ya ke zubar d hawayea! a fili bai damu da aga yana kukan ba, duk wata dauriyarsa sa ta kwace a YAU.

Hankalin ta ya sake ri'banya tashi, ta dinga kuka tana fadin " Ka yafe mini, wallahi ba wayata bace".

A tunzure ya antayo ashar irin wadda bata taba jinta ba, ya maka mata, tare da cewa "Idan ki ka kuma bude baki da nufin yi min, magana ko bani ha'kuri Billahillazi sai na miki abin da baza ki manta ba".

Wayarsa ya ciro aljihu, da kyar ya iya lalubo sunan Fahad Auwal!
Dalibinsa ne tun a FGC yana cikin samarin Sa'a duk da dai bata ta'ba kulashi ba, sannan yanzu ma dalibinsa ne a B.U.K.

Da girmamawa ya gaida Mk.

Cikin rashin sukuni Mk yace "Fahad cikin class mate din ku na FGC akwai mai karatu a Egypt kuwa?"

Dan Jim Fahad ya yi sannan yace"Khalil Ibrahim ne kawai a Egypt".

Ko godiya Mk bai tsaya yi ba, ya katse wayar.

A fili ya ce "ban da tabbas, amma idan har yanzu kuna tare na tabbatar kun tabbata wakilan manyan shedanu a doron 'kasa".

Ta 'kara karfin kukanta ta ce "Mala.. ya katseta ta hanyar jifanta da takalminsa da hagu. Tare da cewa "ki mini shiru, dama ai na fada miki ba zan sake yi miki uzziri akan shedanun yaron nan da baisan kimar da darajar aure ba".

Ya jima yana ambaton addu'ar we yayewar ba'kin ciki, *"YA HAYYU, YA QAYYUM BI RAHMATIKA ASTAGIS*.

Ya 'dan sami nutsuwa ka'dan ya kalleta ya ce " kin yi wankan ko ba ki yi ba?"

Da'di ya kamata mussaman da ta tuna da asuba ya gama mitar hakurinsa ya 'kare, wannan karon period dinta takes too long. ta yi dariya ta ce bai 'karu ba kawai matsuwar da ka yi ne, amma dai nasan ba tantama I will be ready today.

Tunaninta nemanta zai yi tunda dabi'arsa ce ya kusanceta a lokacin da ya ga shaidan zai dagula zaman lafiyar su.

Da hanzari ta ce "Na yi".

Ya zuba mata ido sosai yana so ya ji ko akwai sauran gurbi a zuciyarsa da zai sake yi mata uzziri, sai ya ji babu saura, yana jin idan bai rabu da ita ba, tabbas ba'kin cikinta ne zai zama ajalinsa.

Dan haka muryar sa cike da rauni, hawaye na zirarowa ya ce "*Na sake ki, saki daya Sa'adatu*! Na ba ki dama ki zama yantacciyar da ki ke fata".

Ta 'kwala uban ihu mai gigitarwa.




30/04.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/



*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai satar Dukiya._*

_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_

*Godiya ga makaranta*
*Ina matu'kar Jin dadin yabawar ku kan rubutuna, Hakika da kune Halin Yau ya je inda ban yi zaton zai je ba. na gode muku dukkan makaranta littafin HALIN YAU da fatan ana lura da sakon da nake nufin isarwa, ana watsi da shiriritar da yake ciiki, Ubangiji ya bamu damina Mai albarka*.

*Bari na sada zumunta da ku masoyan Sa'adah*
*Hajiya Rabi Sani*
*Aisha(cisse)*
*Tababa ta Malam*
*Asma'u Umar Ingawa*
*Samira Annuri*.
*Khadija Sadiq*
*Safara'u Niger*.
*Zainab Abdallahi*
*Aishatu maina*
*Khadija Bishir(Dijengala enterprises)*.
*Masoyan da yawa mu tara a shafin gaba*.

* SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.



78.




Kuka ta ke yi tamkar ranta zai fita, ta rarrafa ta ri'ke kafarsa ta dama.
Cewa ta ke yi " Kar ka mini haka Malam, laifina bai kai ka 'dau wannan hukuncin ba, dan Allah ina sonka, ina son zama da kai".

A hanzarce ya fincike kafarsa, ya nunata da yatsa amma ya kasa bude baki ya mata magana saboda yadda yake jin wani irin sanyi na ratsa shi duk kuwa da yanayin garin a daure yake da zafi, saboda hadarin da ya hadu amma ruwa bai sauko ba.

Da 'kyar ya mike, ya shiga dakinta, ya dauko mukallin motar wadda yana tsakar dakin a yashe, rashin nutsuwa ya hana shi ya gani.

Ya fito, ya tsaya yana kallon yadda take kuka mai tsananin ciwo, irin kukan nan da ba ya sa a ji sau'kin tashin hankalin da aka tsinci kai a ciki.

A hankali ya ce "Tashi muje na kai ki gida".

"Dan Allah Malam ka yi hakuri Ni bazan tafi ba".

Fuskar nan a daure tamkar hadari ya ce " Ba za'bi na baki ba, ki tashi na kai ki cikin mutunci, tun ba ki tafi dutse a hannun riga ba".

Hawaye face face a fuskarta, Ta ce "iddah zan yi a dakina kamar yadda shari'a ta tanadar, ka girmama shari'a.

A kufule ya ce "wallahi ba anan gidan ba, ki je, ki yi a gidanku duk wata zan aiko miki abin da zai ishe ki! Na 'ki na girmama shari'ar, ke iyakokin ubangiji nawa ki ka take saboda son zuciyar ki, yanzu ne ki kasan ka'idojin shari'ar?"

Ta yi 'kasa da kanta dan kaucewa kallon tsanar da yake mata.

"Tashi muje" ya fada a kausashe.

Ta 'ki koda motsin kirki, sai shesshekar kukanta kawai, wadda ta ke yinsa har cikin 'bargonta.

A hasale sosai ya ce " Sa'adatu taurin kai a yau ba zai amfane ki da komai ba, bazan dauke ki da karfi ba, amma ki sani idan har ba ki tashi na mayar da ke cikin mutunci kamar yadda aka bani ke cikin mutunci ba, komai zai iya faruwa a tsakanin mu, na tsani na bude ido na ganki".

Nan ma ko uffan ba ta ce ba, sannan kuma ta 'ki tashin.

Ai kuwa ya ce "shikenan! Komai ya faru ki kuka da kanki, ya shiga 'dakinsa, mintina biyu ya sake fitowa ya dubeta tana kuka tamkar Baffah da Innah sun mutu rana 'daya, amma ko tausayi ba ta bashi ba.

A kausashe ya ce "Zan fita yanzu! kuma wurin Baffan zani na fada masa yau na mayar da ke 'yantacciya, amma ki sani Billahillazi idan har na fita ni ka'dai na haramtawa kaina ke, idan haka ta faru, shari'ar ta ce ba dalilin ki zauna kimin idda a gida ko?".

Tamkar tab'ab'biya ya ga ta mike ta fita waje a guje, ya bi bayanta dan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login