Showing 87001 words to 90000 words out of 186291 words

Chapter 30 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9756

hakuri dan Allah".

Idonsa a rufe, bai bude su ba yace "Ni dama barcin da kike hanani yi da daddare ne, bana so, hakuri na zai iya :kwacewa, idan zaki yi kukan ki ban hana ki ba, amma pls stay away from me, na riga na gane ban da mutunci ko ka'dan a gurinki, zaki iya zagina kan ki tsaye, zaki iya fada min duk maganar da ta zo bakin ki, na zuba miki ido ki yi duk abin da kika ga dama, amma ki jira sakamakon zagin da kika min, na rantse miki! ba zai tafi a banza ba".
Ya karasa da rawar murya saboda 'bacin rai.

Hankali Sa'adah ya yi mugun tashi, mussaman yadda ya yi maganar da dukkan zuciyarsa, ta zuba masa ido tana ganin yadda yake numfarfashi tamkar wadda ya yi gudun fanfalaki, dan tsananin bacin rai.

Ta zame ta durkusa a jikin gadon ta ru'ko hannunsa "ka yi hakuri, ba zan sake ba".

Ya bude ido da suka yi jah yace "wallahi za ki sake, ba dai kin bada kofar da wasu suka shigo cikin rayuwar aurenmu ba? ba kin fi gaskata maganganunsu, sama da nawa ba, nace ban son su zo min gida, kin nuna ban isa ba, saboda kina jin isar gidan na ki ne, na sha jan kunnen ki akan kaifin harshen ki, amma kullum sake koyon dabarun ba'kaken magana kike yi, ki rubuta ki ajiye wañnan *HALIN YAU* din da suke cusa miki, kina dauka babu nazari bare tsinkaye, ba inda zai kai ki sai nadama, na fara gajiya da halin ki, hakuri na ya fara kaiwa geji gaskiya, Menene bana miki da kike wulakanta ni haka?"

Jikin Sa'adah ya yi wani irin nauyi, zufa sai karyo mata take yi ta ko Ina, ta kasa bude baki ta yi magana, dan hatta harshen ya mata nauyi ainun, hawaye kuma tamkar an bude famfo, Jawad da yake tsaye yana kallon su, ya karaso ya fara goge mata hawayen, Yana cewa "biskit za ki ci? ko Malam ne ya doke ki?"

Ta kasa magana kamar yadda hawayen ya ki yankewa,ya zuba musu ido yana ganin yadda Jawad ke goge mata hawayen,yana kuma fa'din ta yi shiru, zai goyeta a kekensa, wani irin abu mai kama da tausayi ya tsirga masa yana ayyana karfin soyayyar da ke tsakanin uwa da 'da.

Murya a dashe Mk yace "ki ci gaba da kukan, so kike ya 'kullace ni, ya zaci kamar Ina gallaza miki ne, idan girma ya cimmmani ya'ki jin 'kaina"

Da sauri ta dago manyan idanuwanta ta zuba masa, a fili akan idonsa tace " Malam plz ba kai bane, ka dawo wancan Malamin nawa! mai yawan yi min afuwa, mai tausasa mini".

Ya mayar da idonsa ya rufe yace "shikenan ya wuce, dauki "danki ku tafi gurinki barci zan yi".

"Ka yafe mini?"

"Nace ya wuce" ya fada a gajarce.
Taja hannun Jawad! amma yaron ya coge alamun ba zai bita ba, ta tsaya tana kallon sa ya hau gadon ya kwanta jikin Babansa, Mk ya rungume shi yana ji a ransa shima fa Jawad na sonsa sosai😀Mk manya.

Kwana biyu, Sa'adah ta sauko, tana komai yadda ya kamata, ta bangaren Mk shima yana iyakar kokarinsa na bai sake yin wata maganar ba, zai ci abincinta, idan ta masa magana, yana amsawa kadaran kadahan, kawai a shimfida ne ba ya kulata, ta gama shure shurenta, ya yi biris, duk da shima fama yake da shan lemon tsami.

Tana zaune tana tunanin mai zata masa ya ta'ba ta, hawaye na siraro mata, saboda yadda abin ya dagula mata lissafi, mussaman yadda ta san shi da rashin ha'kuri a wannan harkar, idan ta hasaso ko a waje yake samu sai ta ji tamkar ta sume, ta sake ramewa ta yi zuruzuru, kamar ance kunna radio, aikuwa nan ta ji sanarwa a gobe litinin hukumar zartarwa ta kwalejin tarayya ta kano (F.C.E.) zata rufe yin registration.dan haka duk dalibin da bai yi ba ya hanzarta kafin a rufe.

Ta yi shiru, ta tabbatar Malam yasan ranar da aka bude dan farawa, dan kuwa yana da aboki da yake aiki a gurin, duk da ba lakcara bane.(Non academic staff)ne.wani sashi na zuciyar ta yace kika sani ko ya biya miki ne? Da haka ta samu sukuni kadan.

A ranar bai dawo da wuri ba, dan haka ta danne komai ta barshi ya gama komai cikin nutsuwa, sai da suka kwanta ta bijiro da maganar da ta ji a radio.

Tsawon lokaci ya mata shiru, zuciyarta ta sosu da wulakancin nan da ya tsira, ashe haka yake jin rashin dadi idan ya mata magana ta share? ta daure tace "kana tare da ni kuwa?".

"Ina jin ki, na sani, har na biya miki, yasa hannun ya ja drowar gefen gadon ya fiddo da teller ya nuna mata, farin ciki ya mamayeta, kafin ta yi magana sai taji yana maganar da ta kasa gane manufarsa.

"Na gama miki komai illah wurin da yake bu'katar signed dinki!amma a yanzu na fasa, matu'kar da aurena akan ki! wallahi ba za kije makarantar nan ba".

Cikin rudu tace "Ban gane ba fa?"
Ya tashi ya kunna fitila, sannan ya zauna! ya zuba mata ido yace
"Ina nufin idan har sai da yardata zaki yi karatu, to baza kiyi ba, idan kuma ya zama dole sai kin yi, sai dai kije a matsayin single amma ba matata ba".

Hawaye ya balle mata, ta ru'ko hannuwansa cikin rawar murya tace
"Na roke ka kar min haka! dan Allah kar bari na gasgata masu fadin ba zaka taba barina na yi ilimi ba".

Ido cikin ido yace "gara ki gasgata su Sa'adatu, ada kam na kudiri aniyar ilimi sai kince ya isheki! amma Billahillazi yanzu na fasa, ba ki fara karatun ba, kina iya zagina, bare kuma na baki damar da kullum sai kin fita, kin yi cudanya da mutane daban daban, tunda na gane kawaye zasu iya rinjayar ki, zasu iya canja miki dabi'a, zasu iya ruguza mana kyakkawan zaman mu, daga lokacin na gane barinki karatu mai zurfi ha'dari ne, ilimin sakandiren da kika samu, yasa kina jin kina da yanci, Ina kuma ga kin shiga babbar makaranta, ki zauna ki yi rainon Jawad kawai, tunda nace ki cire loop din nan, amma sun zuga ki, kar ki bari ki tara yara mu tsufar da ke, to ki zauna ki tabbata da kuruciya".

Kuka take yi, tana bashi ha'kuri, yace "na gama maganata, zabi na gareki, dan kuwa wallahi ba za kije ki koyo mini karatun raini da rashin da'a ba, a haka kina iya zagina,nan gaba kuma sai dai na ji mari."

Kuka take yi tun daga kasan zuciyar ta, a duk tsayin rayuwarta a duniya a ranar ta fara sanin Ashe kuka ma kala kala ne, duk wadda tayi a baya na nisha'di da shagwaba ne, na yau ne take yin na zunzuruntun bacin rai.

Ya kalleta yace "Ba abin damuwa bane Wannan fa, domin na riga da na baki damar ki, dan hakama nake ta dan jah baya, dan mu dan saba da rashin tarayyarmu, Ina tabbatar miki idan kin zabi makaranta akan aure! Wallahi zan dauki nauyin karatunki, kuma zan wanke ki a gun su Baffa, zan dauki laifin rabuwarmu Ni ka'dai."

Murya na rawa tsabar kuka tace, "Dan girman Allah yaushe na zage ka?"

"Kina nufin na miki sharri ba ki zage ni ba?"

Ta sake ru'ko hannuwansa da kyau tana harhado kalmomi tace " Ni bance haka ba Malam! amma dan Allah ka yi hakuri, na canja Wallahi, ba zan sake ba"

"A ranar da kika zage ni dama na tabbatar miki u will pay for it! zaki yi karatu da yardata ka'dai, idan na gamsu kin canja din da gaske, idan na tabbatar ba mahalukin da zai canja ni a zuciyar ki".

Ya zare hannuwansa daga nata ya mike, itama ta mike ta tsugunna ta ru'ko kafafuwansa, tana fadin "Malam bazan iya barinka ba, dan Allah, ba dan halina ba, ka janye wannan kudirin ina son karatun amma da yardar ka nake so".

Yace "idan kuwa kina son karatu da izinina, wallahi ba bana ba, to be frank Sa'adatu! ban san time din ba, har sai na gamsu ba third party a tsakanin mu, sai na gamsu na wuce zagi da diban albarka ta kowacce fuska daga gareki".

Ta sake shi! sanin halinsa idan ya rantse shikenan ya gama magana, ta ha'kura tana jin bakin ciki tamkar ta mutu! ta huta. Kuka ba irin wadda ba tayi ba, Mk da kansa mamakin kansa ya ringa ji, bai taba zaton zai iya mata haka ba, sai dai wata'kila yadda take gasa masa duk maganar da ta zo bakinta yasa ya iya jarumta haka.

Sa'adah tana ji, tana gani, ya hanata makaranta, duk ta zama wani iri, zaman nasu dai gashi nan, ta koma shiru, ba walwala sosai, kullum cikin kunci take amma bakinta dif, sai kuma yanayin data koma ya dame shi, fata yake su koma kamar da, rayuwar farin ciki, amma abin na neman cin tura, a zahiri dai suna zaune lafiya amma kuma babu nisha'di a cikin zaman.

Saboda su Halima da suke fadin "dama ai sun san pooling dinta yake yi, ba wata makarantar da zai barta, duk dan'iskan namiji zai yi iya yinsa ya kulle matarsa a gida saboda sun San Annabi baya tuntuben harshe, duk abin da ka yi da matar wani, sai anyi da taka.


Wattanni kusan biyu zamansu ba armashi, bata masa komai na laifi, amma kuma ta dadare ranta, suna cikin haka, aka fara babban zabe na kasa, kowa yasan Malaman jami'oi ne baturen zabe, Dan haka wata guda aka dauka ana yiwa su Mk horo na mussaman kan yadda zasu kare muradan yan kasa, kar su yarda ayi amfani da su, ayi wa dimokaradiya kafar ungulu, Malaman addini suka dinga musu wa'azi na suji tsoron Allah su yi gaskiya a cikin aikin da za su yi, karshe suka rufe bayanin da cewa duk wadda aka bashi kudi dan ya yi magudi, to ya karbe kudin ya adana, sannan ya yi adalci, ma'ana ya fadi sakamako na gaskiya.

A yanzu da suke shiga shekaru biyar da aure shi da kansa ya tabbatar tsoron ta yake yi, idan akwai abin da ya tsana to ta share shi, ko ta tsiri fushi, ko ya fita sai ya dawo, yasan yadda ya yi ya shawo kanta, yayin da ita kuma take jin kanta a sama komai take so sai ta same shi, SUMAYYA kanta mamakin yadda Sa'adah ta dawo take yi, kullum cikin tsadaddun sutura take , hatta salooon din da Sa'adah take zuwa one in town ne, kullum suka yi waya sai ta mata nasiha ta saukaka buri, ta rage dorawa mijinta hidimar da bai kai ya yi ba.
Itakuwa sai tace da ba zai iya ba, ai da bai yi ba, ya hanani karatu ai kuwa dole yamin yadda nake so, tunda idan ban ci ba ma, na waje ne zasu ci, har Sumayya ta gaji ta zuba mata ido tana mata addu'a.

Rannan da yamma Zainab Ma'aji ta ziyarce ta, kasancewar ana daukan lokaci kafin su hadu a dalilin Zainab din tana karatu ne a Jami'ar jahar kaduna(K.a s.u). ba kowanne hutun ma take zuwa Kano ba, sai take barin hoste ta tafi gidan kanwar mahaifiyarta ta yi hutunta indai ba mai tsayi bane.

Mamamki ta tsaya yi ganin yadda Sa'adah ta koma, ta goge sosai, fatarta ta yi fresh tabbacin tana samun tsadadden mai, tasan Sa'adah Yar gaye ce, amma ko kusa ba kamar yanzu ba, da ta ke samun dukkan wants dinta.

Sauyi sosai ta gani tunda ga jikinta, da abubawan more rayuwa na gidan, da cima ta mussaman, ga wata irin ginshira da ta gani a tare da ita.

A sanyaye Zainab tace "Kin zama wata Hajiya ko big madam zance? lallai Uncle a gaishe shi, ina Jawad? hatta maganar Sa'adah ta canja sai anfitar mata da wani salo na daban. lamarin da Zainab ta dinga dariya tana fadin ko za ki yiwa kowa wannan iyashegen ban da ni.

Suka yi dariya gaba daya sannan suka shiga hira, a gidan Mk ya tarar da ita, ta gaishe shi da girmamawa, shikuma ya dinga mata barka da zuwa cikin karamci, a dan dawowarsa da ya yi , Zainab ta fahimci abubuwa biyu, Uncle Mk ya gama lalacewa akan soyayyar kawarta, yayin da ita kuma Sa'adah take amfani da hakan take yin duk abin da take so.

Zainab ta tsinci kanta da adduar ALLAH yasa su Halima ba su jefa ta cikin HALIN YAU na bin malaman tsubbbu, domin ta tabbatar tun shekarun baya da Halima bata gama sanin kanta ba, take zuwa gidan malamai, ko aiken uwarta ko na kanta.

Har ta bar gidan tana jinjina wa Mk tana fatan Allah ya bata miji mai kwatankwacin halayyar sa.

Manyan kudade Mk ya samu a zaben da aka gudanar, saboda karamar hukumar da aka kai shi, itace mafi yawan jama'a, ganin gwamnati mai ci zata sha kaye, sai ta hargitsa zaben wannan yankin, tare da kiran Mk har gidan gwamnati a sirrince, aka tura makudan kudade a asusunsa akan ya canja alkulluman zaben, ya karbe kudin kamar yadda aka sanar da su.
bai canja alkulluman ba, amma sai sakamakon ya zama inconclusive, ma'ana bai kammala ba.

Kwana biyu yana jin farin ciki, yana ayyana indai kayan 'kawa sune muradin Sa'adah zai mata su, zai kashe mata ko nawa ne dan zamansu ya dawo tamkar shekaru biyun farko na aurensu.


Ba zato, ta ganshi da deep freezer, hankalinsa ya kwanta da ya ga Sa'adah ta yi murna, rabon da ya ga murmushinta sosai irin haka tun kafin su fara yar tsama.

Tare suka fita, suka yi siyayya mai uban yawa da tsada, hatta Sa'adah da kanta sai da ta girgiza da irin manyan laces da atamfofi super, da kuma shadda getzner da Mk ya dinga dibar mata. matu'kar tace abu ya mata kyau zaice ta dauka.
Barin takalma kirar itali da dogayen riguna rantsatsu, hatta turaren Escada da yasan tana so amma baya iya siyansa saboda tsadarsa, a wannan lokaci guda biyu ya siya mata, bayan kayan kwalliya na garari, suka zarce bakin asibitin Nasarawa, suka yiwa Jawad siyayyar hadaddun kaya masu yawa, hatta dan gidan Mahmoud da ya kasance jariri(Dady) sai da suka masa siyayya sosai.

A hanyar su ta komawa ya bata labarin inda ya samo kudi, ya kara da cewa
"Ina son na kewaye mana filinmu, a kuma fara ginin zuwa inda zai samu, a hankali kuma sai na dinga yi, har na kallama".

Ya kalleta ya ga farin cikin ta ya kasa boyewa yace "ki nutsu ki fada mini irin tsarin da kike so a miki a ginin, nasan dai kina son garden?"

Da azama tace "Da swimming pool, sannan upstairs nake so, irin wadda kafar benen zata kasance a tafken falo, a mini dining area, sannan kicin ya zama a cikin falon yake a fili, Ina fatan ka gane irin wadda nake nufi?"

Cike da shauki yace "Na gane duk da bai gama zuwa mana ba, nasan kema a finan finan ketare kike ganin kicin din, ba damuwa za'a miki irinsa Ummu Jawad my dear".

Ta rufe ido tana jin duk wani kunci na zuciyarta ya wanke mata tas. Shikuma yana ta barin jiki wirin sake sata walwala.

Tafiya ya shirya musu zuwa Abuja, duk a kokarinsa na son dawo da amincin dake tsakanin su.

Gidan Mahmoud da yake Goron Dutse, aka kai Jawad saboda makaranta, kuma yafi kusa.

Ranar Alhamis suka tafi, sun Isa lafiya, karfe uku suna madaidaicin Hotel din da ya kama musu daki.

Sallah suka yi, sai cin abinci ya biyo baya, wadda a hanya suka tsaya ya siyo, sai da suka koshi, suka yi wanka dan warware gajiya, sannan suka dora da sallar la'asar.

Barcine ya gwada musu fin karfi, Mk ne yafara yi, Sa'adah ta zuba masa ido tana kallon kyakkawar fuskarsa, da yadda yake sauke numfashi a hankali cikin nutsuwa, wani irin shauki na mamayarta, tana jin sonsa na bin duk wata kafa ta jikinta. A haka itama barci ya wuce da ita ba zato.

Sai daf da maghrib suka farka, suna mamakin lokacin da suka shafe suna barci.

A gurguje, Mk ya dora alwallah ya fita neman massalaci, ai kuwa cikin sa'a bai yi tafiya mai yawa ba, ya samu.

Kafin ya dawo Sa'adah ta ninke shimfidar gadon, ta dauko bedsheet din da ta zo da shi ta shimfida, ta sake dauko burner ta jona ta zuba turaren wuta, nan da nan daki ya dauki daddadan kamshi.

Ganin lokaci ya tafi bai dawo ba ta gane sai ya sallaci isha lafin ya shigo.

Ya dawo ya sameta cikin kwalliya sosai, ga sanyi ac da kamshin turarenta da kuma na turaren wuta ya cakude, dakin ya zama na mussaman.

Da sauri ya yi wurgi da ledojin hannunsa wadda gasasshiyar kazace, sai kuma ruwa da yogurt masu sanyi. ya isa kusa da ita yasa hannun ya rungumeta tsantsan yana ta shin shinarta, ita kuma ta lafe a jikinsa tana jinta in a new world.

Sun jima a hakan, kafin ya saketa, ya zauna a kasan kafet, idonsa ya kada, leda ta bude ta dauko plate da ta juye musu kazar, suna ci ta gabatar masa da shayi a dan karamin flask ga kuma cup da spoon a ciki, ya kalleta da murmushi yace "shiri kika yi haka?" Murmushi ta yi kawai.

Suna kammalawa Sa'adah ta yo brush, ta hadawa Mk ruwan wanka. Kafin ya fito ta shirya cikin sabbin nighties masu daukan hankali. Ya fito daure da faffadan tawul, ya tarar da jallabiya da gajeran wando akan gado, ga kuma body spray dinsa na Malizia.

Turaren kawai ya fesa ya dauke kayan ya dorasu kan side drower.

Ya zauna sanyi dakin na ratsa shi, yana ayyana suna komawa zai sanya musu Ac.

Tana tsaye tace "ba zaka sanya kayan ba?" Ido ya kanne tare da fadin "Ban bukatar su a yanzu".

Kunya ta kamata, ta waske da fadin "Mai ba zaka shafa ba shima?"

Maimakon ya amsa mata sai ware ya dukkan hannuwansa biyu alamun ta zo gare shi, ta tsaya tana kallon sa, ta kasa motsawa, yace "plz Dear come to me".

Cikin kunya ta isa gare shi, ya zaunar da ita kan cinyoyinsa ya rungume ta tamkar zai hade su.
Ta lafe a kirjinsa tamkar wadda zai shayar da ita, ya sunkuyar da fuskarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login