Showing 126001 words to 129000 words out of 186291 words
yi akan cikinsa fatar jikinsu na manne, yana jin nisha'di sosai ya dinga mata addu'a, yana gode ma ubangiji na yadda duk shine ya fara bude matan da ya aura, ya tsare kansa bai taba Zina ba, ubangijinsa kuma sai ya mutuntata shi ta hanyar bashi katangaggun mata.
Zuciyarsa ta buga da ya tuno Sa'a yasan sharrin zuciya ne da yake jin tamkar tana ha'intarsa ne, amma shi da kansa yasan zai yi wahalar gaske ta aikata wannan al'amarin.
Jikinsa ya dinga bari har Farida ta dinga jin barin, saboda yadda ya ke jin wani iri abu da baisan dalilinsa ba, yau gashi da Farida a cikin yanayin da Sa'adah kawai ya ta'ba tsintar kansa a ciki, ko ya take ji a dalilin aurensa yasan idan itace ta yi aure tabbas sai ya kwanta a gadon likita.
A sanyaye Farida ta ce "baka da lafiya ne? jikinka na rawa fa".
Murya a dashe ya ce" farin cikin yadda na same ki ne, duk son ki ne yake kidima Ni"
A ransa kuma fa'di yaushe zan iya fa'da miki abin da ya kidima ni ai ya zama tamkar cin fusaka ne, gangar jikinmu a hade amma tunanina da zuciyata na wani waje daban.
Ita kuma zuciyarta ta yi fari kal har tana ganin sannu a hankali zata iya mantar da shi Gogel kamar yadda Gogel din tasa ya manta da lamarinta a baya.
Yini zur Mk ya yi da Farida bai yarda ya mayar da ita ba sai bayan Isha, wadda sai da ta yi kuka, domin kuwa da murje idonsa zai yi ya kwana da amaryarsa, kafin su tafi ta fahimci mabukaci ne na gaske, domin sai da ya sake yin second round ,sannan yana daukar lokaci yana abu 'daya tabbacin yana da lafiya yana kuma kula da lafiyarsa.
A iya wannan awannin da suka yi sai da Farida ta dinga yiwa Iyah jajen rashin mijin da iya sarrafa mace, lalle Gogel jaruma ce da ta iya shafe wannan lokaci babu zumar da ya 'dade yana lasa mata, ita yau kadai da suka kasance da shi addu'a take yi, da neman tsarin abin da zai rabata da Mk.
Fata take ta kasance da shi muddin rai, zata yi dukkan ladabi da biyayyar da zata dauwamar da ita a zuciyarsa, zata yi ha'kuri da duk wani abin da baya so koda ita tana so, matu'kar zasu samu zaman lafiya , ta kuma rayu da shi, idan har zai iya rabuwa da Gogel tsawon lokaci bai waiwaye ta ba, to ta tabbatar ita idan ta yi kuskuren da suka rabu shafeta zai yi gaba'daya.
Suna tafe yana tuki yana ta mata hira da suke nuni da kololuwar jin dadin yadda ya sameta, ita kuma tana ta murmusawa alamun tana Jin dadin yabawar ta shi, a ranta tana fa'din karatu a Jami'a baya sa mace ta lalace sai idan dama lalatacciya ce.
***
Har Mk ya tafi ba su hadu da Sa'adah ba, domin ko da yaje gidan ana gobe zai tafi, ya fadawa Baffah zai tafi amma nan da sati biyu su Jawad za su bishi, cikin karfin hali Baffa ya yi masa addu'a tare da fatan alheri.
Inna kuwa ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar sa, tare da yi masa fatan alheri a aurensa.
Ya jima a zaune bai ji Inna ta hau Kiran Iyah ba, dama ita ce take yin hakan a kokarinta na su dinga gaisawa har a samu ayi sulhu, amma wannan karon bai ji hakan ba, illah shigewa daki da Inna ta yi ta bar shi da Baffah akan tabarma.
Yayin da ita kuma Sa'a tana kwance akan gado tana fama da zugin zuciya duk da dai Alhamdulillah ansamu cigaba kwarai da gaske akan kwanakin ukun da suka shude.
Tana jinsa Amma sai ta ji a duniya ba halittar da bata son gani kamar Mk, tabbas ya wulakanta ta, ya tozarta mafi munin tozarci, hawaye ya dinga silalowa ta gefen kunnenta, ta dinga hasashen me ya Mata na alheri ne, me ya mata na kyautatawa wadda bai cancanci ta ji wannan tsanar da take ji akansa ba, ta gama duk lissafinta ta yi alkalanci, ta yarda a zamansu bai zalunce ta ba, ta kuma gamsu ya kyautata mata, ta kuma gasgata itace ta janyo komai.
Amma kuma hukuncin da ya dauka akanta ya yi tsauri matu'ka da gaske, zargin da ya jefeta da shi ya ketare iyaka, haka nan kin mayar da ita, kafin ya sake aure tozarci ne Babba ya mata, kishi ya daure mata kirji, duk irin alheri da dawainiyar da ya mata har bayan ya rabu da ita a yanzu duk sai ya tashi a banza a idonta, tana jin ba wani alherinsa data sani da zai lullube cin mutuncin da ya mata, a kuma wannan lokacin ta yanke duk wata mu'amala da shi, tana jin idan har ta sake yiwa Mk kallon masoyi, ko kallon Rahma tabbas ta zama asararriya.
Kunya sosai ta hana Mk tambayar Baffah Sa'a! Sai ya buge da sake bawa Baffah hakuri, tare da neman afuwa.
Duk da a ran Baffa ba ya jin da'din yadda yake ganin Iyah adalilin Mukhtar, sai ya ce " Ba komai Mutari, har yau kuma ban kullace ka ba, kawai dai ina son ka ka daina mini kallon wannan matsalar zata lalata amincin da ke tsakanina da Kai, kallon uba kake mini, Nima kallon 'da nake yi maka, har abada mun hadu ga Jawad nan a tsakanin mu".
Jikin Mk ya sake yin sanyi tunda a da cewa yake yi, idan da saura zama a tsakanin ka da Iyah da kanku zaku shirya kanku, bana ji a jikina an rabu kenaan ba, sai kuma yau ya ce ga Jawad a tsakani, kenan Baffah ya karaya ya daina jin zasu sake zama ma'aurata a tsakaninsa da Iyah.
Ya dade zaune Baffa na ta yi masa nasihar ya kula da amanar yarinyar da aka bashi tunda zai dauketa ne ya kaita wata duniyar da ba ta san kowa ba sai shi, sannan ya sa ido sosai akan Jawad kar ya bari ya koyo dabi'un yahudu wal Nasar😀
Da kyar ya mike ya na kallon dakin Sa'adah da fitila a kunne tabbacin idonta biyu, ya tuna idan ya zo gidan ta dinga sintiri tsakanin dakinta da tsakar gida, ta dinga bare bare kenan, ba ita ba hatta mahaifiyarta rawar jiki take yi, ta dinga fa'din Iyah kaza, zo ki kawo masa kaza mana, amma yau duk sun yi likimo tabbacin sun watsa shi a kwandon shara.p
A sanyaye sosai ya bar gidan.
Washagari kuwa ya bi jirgin Mangal air zuwa Lagos daga can ya shiga jirgin arik air zuwa kasar Birtaniya.
Haka Sa'adah ta cigaba da jinyar zuciyarta, tana samun karfin guiwa wurin mahaifanta da Sumayya, domin Baffah da ya ga sun hade masa kai a gidan dole ya ajiye powaer sa ta maigida ya lallashe su da kalmomi masu laushi, da kuma sanin muhimmancin hakuri.
Ya sake fa'da musu ba su fi shi takaicin auren Mukhtar ba, amma tunda shari'a bata hana shi ba, akan me shi zai kullace shi?
Ya rufe da cewa "kuna ganin laifina dan ban roki Mutari ya zauna da ke akan dole ba, alakawari na yi ba zan bada auren 'yata ba sai a inda nasan za ta yi daraja, a farko da yake so ai na bashi, idan kum zaki fadi gaskiya ai ya ri'ke ki da daraja! a yanzu kuma, da baya so, bashi da abin da zan kalla da zan nemi ya zauna da ke akan tilas, hakuri wuya ne da shi, idan aka daure sannu a hankali za'a cimma buri".
Ya nisa ya sake 'daure su da cewa "A zatona Salamatu, da ke da yaran da kika haifa mini da kuma duk abin da kuka mallaka zan yi iko da ku kai tsaye, ba tare da jin shakku ko fargaba ba, amma tunda laifine dan na yi ikon da abin da yake mallakin Iyah ne to ku mini afuwa, Iyah ta bini bashi in sha Allah zan biya a hankali"
Kunyar kalamansa suka kama su mussaman Innah da ta bari hankalinta ya kwace akan wannan lamarin. A ranta ta dinga fa'din babbar jarrabawar da aka yiwa mata kishi ne, domin da yawa Mata sun halaka adalilin kishi, da yawa sun rasa Imani, ubangiji ka tsare mu ka sau'ka'ka mana.
Hakuri suka bashi, Innah ta ce "Ba siyar da filin bane ya ta'ba ni ba, yadda ka shiga cikin lamarin auren ka yi kane kane ne ya kidima ni, amma ka mini afuwa wallahi ban taba jin bin da ya dama mini lissafi irin halin da na ga Iyah a ciki ba, amma Alhamdulillah komai ai ya wuce ina rokon kar Allah ya sake maimata mana wannan wakiar".
Sa'adah ta nisa ta ce " Dayan filin ma na barka maka Baffa tsakani da Allah bana so, tunda na mallakesu ne adalilin Mukhtar. Kawai so nake ka daina nunawa ya fini a gurin ka, sannan ka mini afuwa akan komai ka daina fushi da ni, domin a yanzu Ni Mukhtar ya zalunta".
Ya yi murmushi ya ce " ko Sumayya ba ta fiki ba Iyata, amma ina son ki gane gaskiya ko kuna tare da Mutari ba zan 'ki shiga hidimar auren sa ba, domin ya mini alkairori daban daban da bazan mance su ba, duk girman kuskure kuwa bai kamata Dan adam ya shafawa idonsa toka ya mance alheri ba, nasani hukuncin da ya dauka akan ki ya yi tsauri da yawa, adalcin da nake yi masa shine ban san mai kika yi masa ba, sannan auren da yayi ba zaluntarki ya yi ba, domin kuwa ko kuna tare zai yi aure shari'a ta bashi dama, idan yana so kuma zai iya adalci. Fatana ki kwantar da hankalin, ki yi hakuri in sha Allah komai zai daidaita miki, Na da'de da ya yafe miki Iyah, fatana ki bu'de zuciyarki ki fuskanci goben ki, sai kinyi nazari hadi da tsinkaye masu zurfi sannan gobenki zata inganta, na yarda da nutsuwar ki a yanzu, na kuma gamsu a kame kike dan haka bana fargabar zamanki!
Amma ba ina nufin kita zama a hakan bane, ki bawa masu sonki kofar da za su tunkare ki, domin a hakan kika samu Mutari, yanzu kuma da kika barwa Allah ya miki zabi, ina da yakinin ba zai barki haka ba".
Jikinsu ya sake yin sanyi, suna gasgata maganganunsa, mussaman Sa'adah da take jin karfin zuciya na dirar mata, tana hango ya kamata ta budewa kanta kofofin farin-ciki, zata dawo da kwalliyar da ta da'de da daina yi, sannan zata sake dagewa a makaranta domin a yanzu da Mukhtar ya auri Farida sai take ganin tamkar ya raina arzikinsu ne.
*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.
16/06.
🌺 *HALIN YAU*! 🌺
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*A guji ta'ba wannan LABARIN ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.
*Gaisuwa da fatan alheri ga*
*HADIZA TINAU*.
*Ki yi yadda kike so da wannan shafin, farar mai farar zuciya, ubangiji ya yi mana abin da bamu yi zati ba na alheri*
*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.
89- 90.
Maganganun Baffah sun sake 'karawa Sa'a kwarin guiwar gina sabuwar rayuwar da babu Mk a cikinta.
Tana kwance har tsakiyar dare tana nazarin yadda zata koma sabuwar Sa'adah da bata san Mk ba, ta nisa tana hakaito abubawan da zata nema, bata da bu'katar sutura domin tana da su ba adadi tsadaddun gaske, da yawansu ma bata sake waiwaryasu ba.
Kayan kwalliya da waya tafi bukata a yanzu, sai hanyar da zata dinga samun ku'di tunda yanzu bata bu'katar na Mukhtar, tasan shima ba zai yi gigin bata ba.
Ta sani iyayenta da Sumayya suna iyakar kokarinta amma dai ba zai yiwu ace dukkan lalurarta sai an yi mata ba.
Saura kwana uku tafiyar su Jawad, Ahamad ya kawo shi gurin Sa'adah inji Hajiya ya kwana mata biyu, tare da sallama, tunda Mk ya yi aure Hajiya ta shiga cikin wani hali na kunyar Sa'a da iyayen ta, mussaman da Mk ya fada mata Baffan Sa'a ne ya biya masa sadaki, sai ta ji inama ace Hajiya Babbace a raye ita kuma a mace, tasan Hajiyar ta fita juriya da shanye 'bacin rai.
Sosai Sa'adah ta samu sau'kin zuciya cikin sati biyu nan, domin ko da ta ji tafiyar da Farida da Jawad za su yi bata wani damu ba, illah ta ji ba da'di, Jawad ne ma ya nemi karya mata zuciya da yawan tambayoyinsa akan me yasa ba zata bisu ba?
Da daddare suna kwance kansa na kirjinta yana bata labarin abubuwan da zai siyo mata idan zai dawo.
Can ya ce "to kawai Mami mu tafi tare mana, kema ai baki taba hawa jirgi ba".
A hankali ta ce "Malam bai ce na je ba, Aunty Amarya ya ce ta je".
"Mami idan kin je ai ba zai yi fa'da ba".
Cike da soyayyar 'danta ta ce "Ai bai biya mini kudin jirgi ba".
Ya yi shiru sai ya ce "Na ji kafin ya tafi ya fa'dawa Hajiya, Baban Antin ya ce shi zai biya kudin tafiyar mu".
Zuciyarta'daya ta ce " To ka ga ba ni a tafiya kenan tunda Ni Baffahna bashi da ku'di".
Ya yi shiru, can kuma ya kalleta tamkar wadda aka kitsa masa ya nisa! ya ce "Ni zan tara ku'di da yawa na kai ki, har jirgin ma zan siya miki".
Hawaye ya cika mata idanuwa, ta yi kokarin gogewa ba tare da ya gani ba.
Sai da ta shanye kukan da ya zo mata ta shafa kansa ta ce "Allah ya nufa Jawad, ubangiji ya maka albarka, idan ka je ka dinga sallah da wuri, komai Anti ta ce ka yi, kada ka yi mata musu kawai ka yi, ka dage da karatu sosai banda wasa, domin wadda zai siyi jirgi sai ya zama mai jin maganar iyayensa ya kuma yi karatu tukuru.
U.K.
A airport suka tarar da Mk yana fama jiran isowar su, da Jawad ya hango shi, da gudu ya nufe shi, da azama Mk ya daga shi sama domin abin da Jawad ya ke so kenan ya ga Babansa ya daga shi sama ya'ki yarda ya girma.
Taxi suka hau, zuwa gidan da zasu zauna, a hawa na takwas gidan yake dan haka Suka shiga lifta abin da ya burge Jawad, domin dai shine bai santa ba, tunda Farida ta saba fita kasashen waje.
Gajiyar hanyar da suka kwaso bai hana Mk sake dorawa Farida wata gajiyar ba, domin a matu'kar takure yake sai da ya samu ya zubar da abin da ya takura shi sannan ya ji shi daidai.
Rayuwa suke cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, Mk ya shayar da Farida mamaki da ya samar mata gurbin karatu a Jami'ar da yake inda zata yi masters dinta duk dai akan sanin magungunan (Pharmacy).
Ya ce " wurin aikin ki sun baki damar tafiya ne dan ki zurfafa ilimin ki, gara mu ki kiyaye ka'ida, sannan kema baza ki yi zaman kadaici idan bana nan, kuma Jawad yana school"
Cikin gaskiya da amana take ri'ke da Jawad komai yake so yi masa take yi, duk sadda ta je makaranta bata mantawa sai ta siyo masa abinda zai ji da'di, sun shaku sosai, da ke mai son jiki ne indai suna zaune to kuwa rabin jikinsa yana jikinta, sau tari Mk ke cewa "kina fama da kanki, amma sai ki kama katon yaro ki jingina wa kanki".
Murmushi take yi ta ce "Duka duka nawa ne adadin nauyinsa?"
Sosai ta samu saukin Ciwonta duk tashin da zai yi baya kayar da ita, kamar sadda take Nigeria, domin kwararren likitan ('kashi) take gani a asibitin jamiar, sannan zurfafa ilimin da take a fannin magunguna ya na taimakawa wurin sake sanin maganin da ya kamace ta.
Jawad yana ta karatunsa domin haziki ne sosai kamar Babansa bai yiwo shiriritar uwarsa ba, ko acan da suke da tsarin ilimi mai nagarta sosai yake ja, domin parfomance dinsa is very high hakan na farantawa iyayen nasa rai shiyasa komai ya ce yana so suke rige rigen yi masa.
Ba abin da yake damunsa sai rashin Jin muryar uwarsa a waya, tunda Mk yana ha'dasu da Hajiyar Bichi, da kuma Baffah, amma ya kasa samun layin Inna da Sa'adah ta ke amfani da shi, ita kuma tunda take ganin missed call din lambar waje ta kuma gane lambar Ingila ce sai ta yi blocking din layin shiyasa basa samun layin. kunyar Baffah take hana Mk tambayarta. Rannan Jawad sun gaisa da Baffa ya ce "Baffah ka bawa Mami wayar zan yi magana da ita".
Baffah da bai san Iyah ta rufe musu hanyar samunta ba ya ce "yanzu tana makaranta, Ni kuma bana gida ku nemeta a layinta ko na Innar ta.
Domin kuwa basu jima da barin kasar ba ta ce da Sumayya tana son waya, a satin ta turo mata da kudin waya mai tsadar gaske, tunda murna suke yi ta yarda zata ri'ke waya, alamun ta cire komai a ranta akan Mk, zata fuskaanci rayuwarta ta gaba.
Tsawon wattanni takwas kenan Jawad bai ji muryar uwarsa ba, a hankali sai abin yake 'dan ta'ba shi har abin ya fara bayyana a komai nasa, ya rage yawan surutu, ya daina walwala a tsakanin su, ya zama shiru shiru, sannan yafi son zaman daki fiye da falo.
Abin ya fara damun su mussaman Farida, ta yi tambayar duniya ya ce ba komai,