Showing 72001 words to 75000 words out of 186291 words
kira ta a waya ya tabbatar ta karbe shi, sannan ya tari Adaidaita ya wuce shagon askinsa, yana tafe yana tunani biyu, na yadda zai bullo wa Sa'adah, da na sayan motar da yake shirin yi.
Tana zaune har taran dare ba MK ba Jawad, hankalinta ya tashi, ga wata muguwar yunwa na addabar ta, ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji dadi, kewar Jawad ta addabe ta.
Sai goma saura ya dawo, a dakinsa ya ci burki, ya kwantar da Jawad da yake ta barci, tunda Samira ta masa wanka ya yi barci. Sai da ya gama komai tunda ga wanka, har shafa'i da wutiri, ya nufi gurin Sa'adah, tana zaune a falo ta rasa me yake damunta.
Sallama ya yi bai jira amsawarta ba, ya shige daya dakin inda nan kayan Jawad suke, akwati babba ya dauko, ya hau zuba sabbin rigunansa da ba a kai ga bude su ba, sannan ya zuba na cikin drower kayansa, hatta bargonsa sai da ya saka cikin akwatin, da kyar ya zuge sannan, ya kashe fitilar, ya ja akwatin zuwa dakinsa, da ido ta bi shi, tana sake jin tashin hankali na kamata.
Dakin ta shiga, ta hau dubawa, ta tarar ba kayan Jawad sai tsirarru wadda suka fara yi masa kadan, sai dryar shanya.
Kuka ya kwace mata, tana raya duk bala'i, ba inda za'a kai mata yaronta.
Tana fitowa shi kuma ya shigo, ya zauna a kujera ya ce "Zo ki zauna, magana za mu yi."
Ba ta ki ba, ta zauna din, yana kallon yadda ta lalace tsabar fitinar da sanya a ranta.
"Gobe zan yi Asubanci zuwa Lagos, jirgin karfe shida zan shiga, kafin sallar Asuba Mahmoud zai zo ya kai ni Airport, zan kai Jawad wurin Anty Hafsa."
Kafin ya karasa ta fashe da kuka tamkar yarinya karama tana cewa " Billahillazi ban yarda ba, jaririn yaron za ka kai har Lagos?"
Dariya ta so subuce masa, ya cije yavce, "Ba yardaki na nema ba, fada miki na yi, saboda kina da hakkin ki sani".
"Idan na yarda Allah ya tsine mini, ai da ma na san yanzu ba ni da wani muhimmanci a gurinka".
Ficewa ya yi ya bar ta, ba tare da ya ba ta amsa ba, yana jin farinciki, da dukkan alamu shawarar Mahmoud za ta yi tasiri.
Kwanciya ya yi, bayan ya kashe fitila, addu'a ya fara yi, kawai ya ji ta shigo masa ba sallama.
Tasa hannu ta kunna fitilar dakin, suka kalli juna, na tsawon sakwanni, wani abu na taso musu a zuciya.
Shi ya fara dauke idanuwansa, murya ba amo ya ce, "Kin san dai ba na iya barci da haske a kaina ko? Yanzu kuma na gama fada miki Asubanci zan yi, don Allah ki bar ni na yi barci".
"Ka tashi mu yi magana".
"Ki adana maganar ki, idan Allah yasa na dawo lafiya, gobe irin wannan lokacin sai mu yi maganar".
"Wallahi yanzu za a yi ta". Ta fada cikin rawar murya hadi da kuka.
Ta zauna kusa da kafafuwansa, tana cewa " tsanar da ka mini har ta kai ka kaurace mini, sannan ka raba ni da yarona?".
"Ni ban kaurace miki ba, ba kuma zan raba ki da danki ba, kin taba jin inda aka raba uwa da danta? ko'ina na kai shi, ina tabbatar miki wataran da kansa zai neme ki. Ke kika ce idan ina son zaman lafiya sai dai a yaye shi, zaman lafiyar nake so".
"Wallahi ba zaman lafiya kake so ba Uncle, kawai so kake ka sake jefa ni cikin wani tashin hankalin, ai ba a nan kake kwana ba, sannan mene ne na kai wannan dan kilifin halittar har Lagos?"
"Kin ga Sa'adatu ni kwana a nan dakin ba ina nufin wani abin ba ne, kullum ni nake bin ki dakinki for more than a year, ke mai yasa yau ba za ki zo nan ba, ko kin zo na kore ki?"
Jikinta ya yi sanyi da jin kalmar Sa'adatu a bakinsa ta san fushi yake da ita.
A hankali ta furta, "So nake ka fasa tafiyarku Lagos".
"Ba zai yiwu ba, na riga da na fada mata gobe tasa a tare ni a Airport, kuma sai na koma nace na fasa zuwan?".
Ta fara kuka tana fadin, "Ba na son tashin hankali Uncle, na roke ka kar ka raba ni da yarona".
"Yau kusan sati ina fama da ke, ba irin ha'kuri da rarrashi da ban miki ba, amma kin runtse ido kina mini diban albarka, ko daukar yaron nan sai na miki wuta-wuta kike yi, dazu ga ki, ga shi, amma kika bar shi yana tsala kuka, zan zauna kullum a gida ne? Dole zan fita. Bayan haka kin daina yin komai a gidan nan tun daga kan shara, da girki, duk ban ce komai ba, ina yi, duk da haka ban tsira ba, duk maganar da ta zo bakin ki fada mini kike yi, har ki kalli idona ki sa mini sharadi idan ina son zaman lafiya sai na yi kaza".
Jikinta ya sake yin laushi, bai ba ta damar yin magana ba ya zarce da fadin, "Kin yi strike din wanka, da yi mini magana, akan cikin da ba ni kadai na samar da shi ba, ikon Allah ne. Kin san adadin matan da suke jika filon su duk dare a dalilin rashin haihuwa? Kin san adadin matan da suke fuskantar tashin hankali akan rashin haihuwa, ALLAH kadai Ya san adadin ba'kin cikin da irin wadaccan matan da suke cikin jarrabawar rashin haihuwa suke ciki, ke Allah ya ba ki, ba tare da kin sha wahala ba, ya sake kara miki, maimakon ki zama cikin bayi masu godiya, sai kika zama cikin masu butulci".
Zuciyarta ta yi sanyi, salama ta shige ta, ta fara fadin, "Astagafirillah!" A zuciya.
A fili kuma sai ta tsinci kanta da cewa "Ka yi hakuri".
Dadi ya lullube shi, amma bai nuna ba, ya ce "Ya wuce." A gajar ce.
Ya zuba mata ido yana ganin yadda idonta suka fada ciki, bayan rashin lafiya ya tabbatar har da yunwa ke sakadar ta.
Kafin ya yi magana ya ji tana cewa yunwa na ke ji.
Ya basar ya ce, "Babu kayan abinci ne a gidan?"
"Kwana biyun nan fa ba ni da lafiya, na san kuma idan ba na jin dadi kai ne kake dafa mana".
Ya harareta kadan sannan ya furta, "To na daina yi tunda ba kya gode mini, ba kya ganin kokarina".
Ta yi kasa da kai, sai kuma ta mike ta shiga toilet din dakin, ta yi wanka sosai, tana ayyana yau kwananta uku ko hudu ba wanka, ta fito ta tafi dakinta, ta shirya cikin Riga da wando iya guiwa na barci, ta feshe jikinta da turararukanta masu tsuma zuciya, sannan ta koma dakinsa.
Inda ta tashi nan ta sake zama, ya dago ya kalle ta, yana jin tamkar ya rungume ta, fiye da sati bai ganta a nutse haka ba, kamshinta, sai ratsa shi yake yi.
Ya dan kalle ta kadan sannan ya ce "Ba za ki kashe fitilar ba, na ce miki barci nake son yi kada na makara".
Kafin ta yi magana Jawad ya farka, ya fara kukan neman abinci.
Da sauri MK ya dauke shi, sannan ya fara hada masa Madararsa da take kan side drower, tun dare ya ajiye komai na bu'katar Jawad kusa da shi, jego ya same shi a kwatsam😃
A kunyace ta matsa kusa da shi sosai, ta mi'ka dukkan hannu ta ce "Kawo shi".
Bai musa ba don kuwa, so yake ta ba shi nono, amma ya riga da ya kudire ba zai kuma rokon ta ta shayar da shi ba.
Ya mika mata, yana ci gaba da kokarin hada masa madara, rabin hankalinsa kuma na kan Sa'adah da I'm ya ga ta kwantar da Jawad a jikinta ta na kiciniyar shayar da shi.
Da'di ya kama shi, amma sai ya waske da cewa "Gaskiya da ba ki ba shi ba, tunda dai ya saba yinin yau bai sha ba, da an bar shi, tunda gobe ai ba sha zai yi ba".
Tura baki ta yi, sannan ta ce "Zan ba shi mana".
"Lagos din za ki bi shi, ki ba shi?"
Cikin shagwabe fuska da kuma hawaye ta ce "Na ba ka hakuri fa, ka ce ka ha'kura, ba sai a fasa tafiyar ba".
Ta yi shiru yana kallon ta, yana kuma kallon yadda Jawad ke ta faman shan nono ba kakkautawa.
Tsintar kansa ya yi da tambayar ta mai za ki ci?"
Kanta a kasa ta ce "Komai na samu zan ci, amma mai zafi"
Ya kalli waya ya ga shadayan dare, ya mike ya shiga kicin ya dade a tsaye yana tunanin mai zai mata mai sauki? Ya bude fridge ya ga akwai ragowan ferfesun naman kaza duk da ba shi da wani yawa, ya fito da shi, a tunaninsa ta cinye tunda yasan ta da son kaza, sannan ta ki yin girki.
Ya dumama ya juye a bowl, ya hada tea sannan ya dauko bread, duk ya shirya a kan tray, ya dauka ya kai mata dakin.
Har a lokacin kuma Jawad sha yake yi.
Kusa da ita MK ya zauna, ya ce "Kawo shi ki ci abincin kar ya huce, a hankali ta dago yaron da yake shirin yin barci, ta mi'ka masa, Jawad jin an raba shi da abincin sa, yasa kuka, sai dai da yake ya koshi, dan jijjiga shi kadan Babansa ya yi ya koma barcinsa, yayin da Sa'adah take ta cin abinci tamkar tana ci da wani.
Sai da gama ta gane jirin da ta yini da shi na yunwa ne.
"Uncle ba ka ba ni ruwa ba, ya sake zuba mata wata irin hararar kauna ya ce, "Kar ki sha ruwan, ke wannan abincin ma dana hado miki biyan ki na yi, kin shayar min da yaro na, saboda adalcina, ni ma na miki ya kamata".
Dariya ta kama ta sai ta bige da cewa, "Ke nan dai Jawad ya fi ni a gunka?" Ta fada cike da shagwaba.
Shiru ya mata, ga mamakinsa, sai ji ya yi ta kafa masa kuka, ya tashi ya zauna, ya kalle ta sosai ya ce "Kin koshi ba! Shi yasa za ki dora daga inda kika tsaya? To Allah ya baki sa'a".
Ta kara karfin kukanta tana fadin, "Ruwa zan sha, wayyo cikina".
Kan dole ya tashi ya dauki tray din gabanta, ya fice, ya dawo da ruwan ya dangwarar, yana fadin "Ki ci gaba da yi mini iyashege".
Haka ta dauki ruwan ta sha, sannan ta ce, "Thank you dear!"
Bai kulata ba, ya ce "Idan kin gama sai ki kashe mana fitilar".
Da rarrafe ta isa gefen gadon da yake kwance, a durkushen ta kamo hannuwansa ta ri'ke, cikin rauni ta ce, "Am sorry dear, na gane ban kyauta ba, ka yi mini afuwa, ka manta duk wani inconveniences da ya faru pls".
Bai ja ba , ya ce "Shike nan na yafe miki, amma ki dinga sanin abin da za ki dinga fada mini".
Da azama ta ce "In sha Allah, sannan don Allah ka hakura da kai Jawad Lagos, idan Allah ya kai mu na haihu sai ka kai shi, sannan ya kara girma".
"Wannan ne kuma ba zai yiwu ba, ba kula shi, kike yi ba, idan na fita kullum hankalina, ba a kwance yake ba, Allah-Allah nake na dawo na kula da shi, kin ga aikina yana bu'katar nutsuwata, don haka ki yi hakuri, idan ya isa shiga makaranta zan dauko shi, idan kuma ta nuna sha'awar ci gaba da rike shi, to zan bar mata".
Ta sake ri'ke hannun sa sosai, tana fadin, "Wallahi zan kula da shi fiye da yana jariri".
"Na ji zan bar shi amma bisa sharadi".
Da sauri ta ce, "Ina jin ka ko mene ne zan yi"
Ya kalle ta ya ga ta matsu ta ji sharadin.
Ya nisa ya ce "Ba za a yaye shi ba har sai na ce".
Da sauri ta ce, "Na yarda, har sai na haihu ma".
"Ni ba ruwana da haihuwa, ko kin haihu idan da yiyuwar ya ci gaba da sha, za ki dinga shayar da shi, idan lokacin sa ya yi, sai a cire shi! Idan kin amince da haka shike nan, idan bai miki ba, tabbas gobe zai bar gidan nan".
Kai tsaye ta ce "shike nan na amince".
Ya janyo ta, ya kwantar da ita a saman kirjinsa, yana shafa bayanta, yana fadin, "Allah Ya miki albarka Ya sauke ki lafiya."
Yana ta ba ta misalai masu dadi, ba akanta aka fara irin wannan ba, sannan matan so ne su ke yin kwane.🤣
Rawahul Mk.
```Alkalamin
*Surayya Dahiru*
✍🏼
🌺 *HALIN YAU*! 🌺
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.
*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.
61-62.
Washegari da karsashi Sa'adah ta tashi, kafin karfe bakwai na safe, ta kammala soya dankalin turawa da sauce, gefe kuma ta dama kunun gyada da ake yi da danyar shinkafa.
Sai da ta share falon, sannan ta kai kayan abincin bayan ta shimfida ledar cin abinci.
Tana cikin share tsakar gidan ya fito yana sabe da Jawad, ya kalle ta, ya ce, "sannu da aiki." Ba tare da ta dago ba ta amsa da, "yauwa!"
Yana tsaye yana kallon ta har ta gama shararta ta kwashe, ta wanke hannuwanta, sannan suka rankaya zuwa falon, shi ya zuba musu, suka karya, Jawad na kwance yana ta shure-shure da furzar da yawu tabbacin yana cikin yanayin masu yin hakori.
Suna kammalawa, ya shiga wanka, ya fito a shirye cikin shudin (blue) jeans da fararar shirt, mai yarfin blue, sai tashin kamshinsa yake yi.
Har cikin dakinta ya bi ta ya tarar wanka ta yi wa Jawad, tun kafin a gama shirya shi ya yi barci.
Cike da farinciki ya mikar da ita tsaye, ya ja ta jikinsa, ya rungume, ya rasa kalmar da zai fada mata, kowacce kalma sai ya ga ta yi kadan ta wakilci yadda yake jin ta a rayuwarsa, a karshe dai cewa ya yi
"I really love you Sa'adah. Stay blessed!" Ya sake ta ya juya ya tafi ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ta dade a tsaye, cikin sanyi jiki, kalaman ba karamin tasiri suka yi a zuciyarta ba, da kyar ta tattara kayan Jawad ta mayar da komai inda yake, ita ma ta yo nata wankan ta shirya, ta kwanta kusa da Jawad, suka sha barci, don sai kusan sha biyun rana suka farka, ta fara kokarin hada abincin rana.
Haka rayuwarsu ta ci gaba da gudana, ranar da tashi da karfin jiki, za ta yi komai, ranar da kuma jikin ba dadi zai yi abin da zai iya, kullum cikin tattalin ta yake, ba ya kaunar abin da zai tunzura ta, mai ha'kuri ne, amma a wannan yanayin da gimbiyar take ciki, ya sake ninka hakurinsa akan lamarinta kwarai da gaske yake tausayin ta.
Har cikin ya shiga wata shida ba wanda ya sani, saboda kwatakwata ta ki fita, duk son ta da ta fita unguwa musamman gidansu, ko gidan su MK, amma yanzu juyin duniya ya yi da ita, fur ta ki zuwa, sai dai ta gaishe su ta waya.
Tun Inna ba ta damuwa da rashin zuwanta har ta fara damuwa, idan lissafin ta daidai ne tunda ta koma gidanta sau daya ta je musu, sannan aka yi wattanni shida da zuwan.
Ranar nan suna waya ta ce, "Iyah wato yanzu Jawad da mijinki sun debe miki kewata ko?"
Da sauri ta ce, "Haba dai Inna! Kullum fa idan ban ji muryarki ba, kin san ba na jin dadi, har yaushe na same su! da za su dauke mini hankali?"
"To ai gani na yi muna gari daya, amma ki iya shafe rabin shekara ba ki zo kin gan mu, mun gan ki ba. Mijin ki duk bayan sati biyu zai zo ya gaishe mu, abin mamaki har ki iya ba shi Jawad ya kawo mana, amma ke shiru! Anya za ki yi imani kuwa?"
Jin haka ya sa Sa'adah ta fashe da kuka, tana fadin, "Ban da lafiya fa Inna duk zuwan da Uncle din yake yi bai taba fada muku ba?"
A gaggauce ta ce "Me yake damun ki?"
Kuka kawai take yi, da kyar ta ce "Ni dai idan na mutu ki yafe mini, ba da gangan na ki zuwa ba".
Sai ta katse wayar tana goge hawayen, a fili ta ce, "Na san gobe zan gan ki kin zo, kin ga abin da nake boyewa."
Hakan kuwa! Inna kwana ta yi tana zullumin wane ciwo ne ya addabi Iyah haka?
Karfe goma na safe ta isa gidan don ma Baffa ne ya hana ta fitowar sassafe, da tuni ta dade da zuwa.
Mamakin cikin da ta gani jikin Iyah ya zarta wanda ta yi a lokacin cikin Jawad, ta rasa mai za ta ce musamman da ta ga ya yi kwari, har yana shirin fitowa duniya.
Ganin irin kallon mamakin da Innar ta bi ta da shi, yasa ta kifa kai a hannun kujera ta fara sana'ar kuka.
Da tausayawa Inna tace, "Ni kin san akan koke-koken nan naki, muke batawa, mene ne kuma na kukan? Mene ne yake damun ki?"
Sanin bata da matsalar komai sai na cikin nan da ya mata shigar sauri yasa ta kasa cewa uffan.
"Idan na fahimce ki, halin da kike ciki yasa kika mayar da kanki mujiya a cikin jama'a, ke baki san baiwa ce Uabngiji ya miki ba, ai ba kowacce mace ke samun damar samun irin wannan haihuwar ba".
Ta ja numfashi ta ci gaba da cewa "jiyan nan aka mana tarihin Nana Fadima a Islamiyyar da na shiga, ashe Sayyadi Hassan da Sayyadi Husain ba tagwaye ba ne?
Duk zatona 'yan biyu ne, ashe daban-daban aka haife su amma Malamai sun yi ittikafin wata goma sha daya ne tsakanin su, ashe matar da tayi irin wannan haihuwar abin alfahari ne a gurinta, abin a mata barka ne, don kuwa albarkar diyar Ma'aiki ta samu".
Haka ta dinga rarrashin ta har ta sami nutsuwa.
Ta kara da cewa "Har addu'a nake miki kar