Showing 90001 words to 93000 words out of 186291 words
daf da tata, numfashin su ya dinga haduwa, tsinin hancinsa akan nata, jikinsu ya dauki wani irin tsimi.
Ya raba hancinsu, amma fuskokinsu a hade. Cikin wata murya da Sa'adah bata sanshi da shi ba yace "Ina sonki, ina son na rayu da ke! Dan Allah stay with me".
Jikin Sa'adah ya yi la'asar, da murya marar amo tace "kana ganin zan iya barinka ne Malam?"
"Matu'kar kina tare da su Halima, kina basu damar da suke cusa miki ra'ayinsu Ina tabbatar miki zasu raba ni da ke" ya fada cikin rawar murya.
Kafin ta yi magana ya zarce da fadin "Ina miki son da zan sadaukar miki da komai, idan nace komai, ina nufin har rayuwa ta amma ke baki fahimci hakan ba"
Ya sake ri'keta sosai, cikin wata murya irin ta karaya da lamari yace "Bana son kaifin harshe Sa'a, bana miki akan me zaki dinga mini? zan ro'ke ki! dan Allah fada mini inda na kuskure miki da ban cancanci ki zauna da ni lafiya da kyautatawa ba?"
Ta yi shiru tana jin hawaye na cika mata idanuwa, haka kawai take jin tamkar wani abu na tashin hankali zai biyo baya.
Jin shirunta sai ya zarce da fadin "ki bude baki, ki mini magana, ki fada min inda na gaza sai na gyara tunda ubangiji ya dora mini sonki da son zama da ke".
Ta girgiza kai muryar ta na rawa tace "Ba ka gaza ba Malam".
Ya nisa yace "Am not good in bed?".
Kunya ta kamata, ta cusa fuskar ta a kirjinsa, yace "magana muke yi ta gaskiya".
Ta dinga dan dukan kirjinsa tana cewa "Ai kasan dai kure ni ka ke yi anan ma."
"Idan kuwa hakane, to mai ya kawo Kika canja, mai yasa kike bijire mini?"
"Ka yi hakuri zan canja".
Yaushe zaki canja din?".
Ta tura mai Baki gaba cikin shagwaba tace "Na canja fah".
Da'di ya kamashi ya dinga kai mata kisses ta ko ina tamkar mayunwacin zaki.hannuwansa suna ta kai komo a jikinta.
Da kyar ya sarara mata, dukkansu sai numfashi suke mayarwa, daga inda yake ya mika hannu ya janyo ledar yogurt ya bude ya fara bata a baki, Yana cewa "ke Amaryace yau! irin Amaryar da ta kerewa mata hudu"
Da'di ya kamata, ta sha iyakar shanta, ya shanye ragowan da ta bari daga nan ya sa harshe yana lashe mata baki, ya janyo harshenta Yana sucking irin deep din nan, daga haka suka fada zazzafar soyayya mai dimautarwa.
Haduwar ta zama so ma sha Allah, saboda hadin kai da Sa'adah ta bayar, sabanin kwanakin baya da take zame mishi very doll.
*Surayya Dahiru*
✍️✍️
07/04.
🌺 *HALIN YAU*!🌺
NA
*SURAYYA DAHIRU*.
lafazee writers.
*A guji taba Wañnan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.
*Doka mi lamba ta 68 ta yi nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*.
*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*
*Tukuici ga*
*HAJIYA RABI SANI*
*Bisa yaddda kike son rubutun Halin Yau, Na gode, Allah ya shirya zuri'a*
*SA'ADAH NA GAISUWA*.
71-74.
Wannan dare ya shiga cikin dararen da ba zai shafe a zukatan su ba, saboda sun jiyar da junansu farin ciki na ban mamaki. Sosai Mk ya bawa Sa'adah soyayya da kulawa mai yawa, kullum suna tare ba inda yake zuwa idan ba masallaci ba, itama kuma bata komai sai gyaran daki, wannan hutun ya sabunta soyayyar su, ya kara musu shakuwa, ya kuma goge dukkan tsattsar dake zukatan su, aminci da Nishadi ya cika 'kalbinsu.
Kwanaki biyar suka yi amma fahimtar da suka samu a cikinsu ya zarta na wattanni biyar.
Ana gobe za su dawo da daddare, suna kwance ya rungumeta sosai tamkar zai maida su halitta 'daya, hatta bugun zuciyar su suna ji, sai dai bugun da zuciyar Mk yake yi ta zarce ka'ida.
A hankali Sa'adah ta ce "Malam baka da lafiya ne?"
Murya a dakushe ya ce "me kika gani?"
"Bugawar da zuciyarka take yi yanzu ya sha ban ban".
Cike da rauni ya ce "fargaba nake yi Sa'adah! bana son mu koma Kano ki canja mini, na fi son wannan rayuwar da muke yi, mai cike da nutsuwa da girmamawa".
"Nace komai ya wuce fa, sannan ai na baka ha'kuri, mai yasa ba ka gamsu ba?"
Kai tsaye ya ce "ki mini al'kawarin yanke kawancenku da su Halima, Ina rokon ki, ki rabu dasu, sannan ki mini al'kawarin baza ki dinga 'daga mini hankali ba, komai kike so a hankali zan miki kin ji? Ni dai fatana mu zauna lafiya".
Haka kawai ta ji hawaye na zubar mata karon farko da ta ji tausayinsa ya cika mata zuciya, sai take jin tamkar mutuwa ce zata sure wani a cikinsu.
Jin 'dumin hawayenta na zuba akan kirjinsa, yasa nasa hawayen da tun dazu yake kokawa da su, suka kwace masa! kwatsam Sa'adah sai jin saukar hawayensa ta yi akan goshinta, karon farko da ta ga ko jin hawayensa a cikin shekaru biyar da ta yi tare da shi, hatta mutuwar Hajiya Babba da ta masa mugun bugu, ita dai bata ga hawayensa ba.
Kuka sosai Sa'adah ta saka tana cewa "Malam me kake yi haka, me na yi haka? me yasa kake zullumi har haka akaina? Kai baka ganin laifin kanka sai nawa ka'dai?"
Da rawar murya ya ce " Nan duniya ba wadda zai cusa mini ra'ayi akan ki na yarda, saboda na fishi sanin ki, hakanan son da nake miki ba za bani kuzarin da zan cutar da ke ba".
"Nima ba a cusa mini ra'ayi akan ka ba".
Murmushi mai sauti ya yi wadda baya dau'ke da nishadi ko ka'dan.
Ya ce "shikenan fatana dai ki kulle kofofin da kika bude wasu suke shigowa cikin matsalar mu, wadda Ni da ke kawai ta shafa".
"To Malam ya maganar makaranta ta?"
"Da gaske za ki yi, amma sai kin dawo mini Sa'adah ta, kinsan tun farko bana shiri da Gogel badan komai ba, sai dan rudeness dinta, shine yanzu zaki dawo mini a Gogel din?"
Ta 'dan dara kadan! kafin ta yi magana, ya rigata da cewa "Ban so na fada miki yanzu ba, amma bari ki ji, kinsan naje Abuja na yi jarrabawar scholarship, idan na Sami nasara, zan yi PhD dina tsawon shekaru hudu a kasar England, so nake idan na tafi, naga da yiwuwar ku bini ke da Jawad sai ku bini, sai kiyi karatun ki acan, amma ba al'kawarin hakan na yi ba, Ina fatan dai hakan ya kasance, muna komawa zaku yi passport, na riga na yi nawa, idan hakan bai samu ba sai kiyi anan, kafin na dawo kinci karfin karatun ki".
"Allah ya zaba mafi alheri"
Inji Sa'adah.
"Ameen ameen" MK ya amsa mata.
Da haka ya shiga lasarta cikin wani salo mai gigitarwa, tsawon lokaci yana sarrafata kafin su fada duniyar masoya mai nauyin bayyyanawa.
Karo na biyu da Sa'adah ta gasgata ana kwana ido biyu, a ranar basu runtsa ba, dan kuwa a kunnen su aka fara kiran sallar asuba, wanka Mk ya fito ya ganta kwance tamkar matacciya barci na kai mata caffa
"Daurewa za ki yi, ki yi wanka ki yi sallah, sai ki yi barcinki".
Da kyar ta tashi tana Jin dukkan gabb'anta sun mata nauyi wadda ba komai bane ya sababa hakan ba illah sububurdar da ta sha a hannun Mk hatta farcenta nauyinsu take ji, ya fice masallaci yana jaddada "kar fa ki koma".
Ta yunkura ta nufi toilet din tamkar mai koyon tafiya, da ruwan mai zafi ta yi wankan, ta jima zaune cikin ruwan saboda yadda take jinta a bude, tana ayyana me yasa shi baya kaita toilet ya gasa mata jiki, ai yasan yau bai mata da sauki ba.
A daddafe ta yi sallah, akan sallayar ta kudundune tana ta fama da kanta tare da fatan ta sami barci ko ta dawo daidai.
Koda ya dawo ya iske ta a kasa, murmushi ya yi sannan yace "ga ta da kwadayi ga kuma lalaci".
Ya dauke ta cak ya dora a gado, ya cire jallabiyarsa, sannan ya kwanta ya lullube su da bargo, a tsarinsa so ya yi su tafi daidai wannan lokacin, rashin barcin da bai yi ba, yasa ba zai iya tuki cikin nutsuwa ba, dan haka ya kwanta yana raya ko da la'asar zasu iya tafiya kaduna, su kwana acan, jibi da safe sai su wuce Kano, a lokacin hanyar Abuja zuwa kaduna cike take da aminci da tsaro, Allah mun tuba, Allah ka dawo mana da aminci da tsaro a yankin arewa da Nigeria gaba'daya.
Lafiya Lau suka dawo kano, a gidan su Mk suka fara tsayawa suka ci abinci, Hajiya sai Ina ka saka ta ke yi da su, mussaman ta dinga murnar yadda ta ga Sa'adah ta yi kiba ta yi kyau alamun ba ta da matsala.
A lokacin Sa'adah ta ga freezer Hajiya irin ta su ce, da alamun tare ya siyo musu, sai cinikin kankara da pure water take yi kuwa.
Ta gabatar musu da abinci wadda shinkafa da wake ne, da miya sai salad, yayin da Sa'a tace da mai da yaji take sha'awar ci, da hanzari Hajiya tace duk Ina da su, ta fice cikin sauri tana ayyana Allah ya sa ciki ne da ita.
Ta dawo ta ajiye mata tana cewa " jiya Mahmoud ya kawo mini Jawad, ku shiryawa darunsa dan yace ba ruwansa sa da ku, tunda kuka gudu kuka barshi shi ka'dai.
Suka zube mata doya da dankalin turawa da tuffa, sannan suka tafi, ga mamakin Sa'adah sai ta ga ya sauka kan titi ya fada layin unguwar su, farin cikinta ya kasa boyuwa ta ce "Na gode Malam ".
Tare suka shiga gidan suka gaisa da su Baffa da yake yana gida yana fama da mura, sun dan jima tare da Baffa sannan ya fice dan dubo shagonsa.
Hira sosai Sa'adah suka sha a lokacin kuma ta ga gyaran da aka yiwa gidan nasu.
Baffa ya kalleta yace "Iyah Dan Allah ki dinga yiwa mijinki biyayya, ki kyautata masa, ki zauna da kowa nasa bisa karamci, ki ga yadda Gidan nan ya dawo duk aikinsa ne, Ni kam ba abin da zaki mini ki sanya ni farin ciki irin ki zauna da mijinki lafiya da kyautatawa, mazajenku suna wanke mini takaicin rashin haihuwar Namiji, ba abin da zance musu sai dai Àllah ya yiwa nemansu albarka ya shirya musu zuri'a".
Inna ta amsa masa da "Ameen ameen".
Suna cikin haka almajirai suka shigo da doya da dankali.
Mk da Sa'adah sun sha albarka da nema musu tsarin shaidan da makiya.
Da zata tafi Baffa ya ce "kice da mijinki ranar juma'ah ya taho mini da Jawad na kwana biyu ban ganshi ba, kewarsa da ta surutunsa ne suka sukurkutani ba mura ba".
Dariyar jin dadi ta yi tare da cewa "Zan fada masa kuwa Baffa".
Ranar wata alhamis ta ce ya kaita asibiti ta cire abin tsarin iyalin da ke jikinta, da kansa ya ce ta bari suga ko tafiyar za ta yiwu, sai ta cire a can.
Sosai suke zaman lafiya, saboda Sa'adah ta daina zungurar rigima, shi kuma yana kaf kaf da farin cikin ta. A haka har suka kwashi wattanni biyar.
Rannann ya dauketa suka je filinsa da ake ta aiki, ya dinga nuna mata yadda fasalin ginin zai kasance, amma bata fahimci komai ba.
Sai da suka dawo ya dako littafin zanen gidan ya nuna mata, ta yi muranr ganin katafaren gidan da zai zama mallakinsu, sai dai ta kalubalanci ta yaya kafar bene zata zama biyu?.
"Ke kika ce kafar bene a falo kike so?
wannan kuma ta baya ne sai kin shiga corridor sai ki ga kafar benen, idan Ina sama, kina da bakin ki, zan fita ta bayan, ko kuma idan Ina tare da bakina baki da matsalar komai, bari a gama, na tabbatar zai burge ki.
Ta tura baki gaba ta ce"Na ga sama ma katon falo ne ga dakunan barci tamkar na 'kasa sannan har da kicin, ko dai na Amarya ne?"
Ta fada tana matso 'kwalla, ya wurgar da littafin, ya ru'ko ta jikinsa ya ce, "Ke ce uwargida kuma amarya ta, da gaske nake kin cike mini gurbin mata hudu, ki daina wasiwasi akan maganata, ko an kaddara mini zan 'kara aure ina tabbatar miki, ba zan hada ki da kowa a gidan ba, daga ke sai yaranki ki yi yadda kike so".
"Ban cike gurbin mata hudun ba kenan?"
"Oh Sa'adah! kin zarta mata hudu ma, kawai ban son na miki al'kawarin da za'a jarrabe ni da rashin cikawa ne, kinsan bamu muke tsarawa kanmu rayuwa ba, idan haka ne kuwa bai kamata mu yi katsalandan akan goben mu ba, Ina tabbatar miki a burina ke kadai kin isheni rayuwa, sannan har yau ban taba jin son wata a zuciyata da ya kai matsayin da zan aurota ba".
Ta lafe a kirjinsa tana jin dadin yadda ya ke rawar jiki idan za ta botsare masa.
Kudin da Mk ya samu sun yi albarka kwarai da gaske, ya fadada shagon askin sa, ya sake budewa Ahamad wani shagon, hatta gidan da suke ciki ya sha gyara na mussaman, ya sakewa falonsu kujeru da sauran abubuwan more rayuwa da ya dace da ra'ayin gimbiya Sa'adah.ya kuma biya kudin aikin Hajj.
Sa'a kam ba a maganar yadda take lasar kudi har gold ya sai mata, waya ce dai bai siyi wacce take so ba, amma ya bata waccan da ta raina da kuma ainihin tata da ya karbe.
Baba Isa da su Baba umaru duk Sun Sami tagomashin inconclusive, duk da dai dama akai akai yana waiwaryasu da abin da zai iya na Alheri da neman albarkar su.
Shigowar what'sapp ya taimaka wurin tabarbarewar tarbiya, a farkon shigowar sa ya rudi mutane da yawa mussaman Mata dan hatta abinci sai andauka an dora a WhatsApp, gida mai kyau kuwa kullum cikin tallansa ake yi. Ya zama ba sirri, mussaman idan mace tana cikin wadata ta hanyar status take bayyana matsayin ta, hakan ya sake jefa Sa'adah cikin buri sosai kullum cikin kara son kayan garari ta ke .
Sannu a hankali aka fara bude groups daban daban ciki har da na tsofaffin dalibai, babbar mastalar group din su Sa'adah hade yake da mazan set dinsu tunda makaranta tasu hadaka ce da maza.
A haka Khalil ya samu numban ta, suke gaisawa lokaci zuwa lokaci, duk da baya nan yana Egpt yana karantar sociology.
Ta hanyar what's app ya mallaki hotunanta dana Jawad, idan ta yi status zai yi saving, ba a karan kanta ta ke tura masa ba.
Haka Kuma taron tsofaffin dalibai (reunion) sai ya zama ruwan dare, ko Ina taron tsofaffin dalibai ba 'kak'kautawa.
A wannan lokacin FGC Kano ta shirya nata tunda ga kan daliban farko har zuwa daliban da suka kammala a shekarar taron.
Taron ya kai taro, mafiya yawa daliban ma'aikatane ko manyan Yan kasuwa' har tsoffin Malaman duk sun halarta, dan haka Mk ma ya je, manyan mata masu aji, wadda suka yi wanka da ilimi da gogewar rayuwa duk sun kewaye harabar makaranta.
Sai farin ciki ake yi, mafiya yawa kuma cikin shiga ta alfarma suke, Sa'adah na cikin jerin da basu da makusa tun daga kan suturarta har zuwa fatar jikinta, kawai na'kasun ta 'daya ba a motar kanta ta je gurin ba, bata ji muzanci ba, sai da Mk yace mata zai tafi idan sun kammala ta wuce gidan Inna zai 'dauketa acan.
Kusan 'Yan set dinsu kowa da mota ta je har 'yanmatan cikinsu, Halima a motar Safina suka je, motar da Sa'adah taga Farida a ciki ta matu'kar tsaya mata a rai.
Hira ake ta yi, ana zuga wadda rayuwar su ta yi nasara ta hanyar kambaba lamarinsu, wasu kuma ana yi musu gadar zare, daga gefen su Sa'adatu, wasu matan ke hirar da ta ja hankalinsu, duk da seniors din sune sosai, 'daya cikin matan ta ce
"Ni da aure kuma mun yi hannun Riga, ba komai a cikinsa sai jidali, da hawan jini, baka da ikon yin komai na ra'din kanka, sai ka jira namiji, sannan baka da 'yanci ko kadan a aure".
'Dayar wadda da alamun ra'ayin su daya da wadda ta kammala bayani itama ta cafe da cewa "ai kuwa dai lubna da gaskiyar ki, dare, asuba, tsakar rana kowanne lokaci miji saka'dar ka yake yi tamkar jaka, amma da za ka bijiro da bu'katar ka, ba za'a maka ba, ko za'a maka din kuwa sai ka gama wulakanta".
Lubna tace da Asiya "Ashe kin gane karatun! dan haka tsakanin mu da namiji a hadu ayi ar'kallah kowa ya kama gabansa, yanzu kiga da ka ke cin gashin kanka cikin kankanin lokaci ka mallaki abubuwa masu daraja, wadda macen aure sai ta shekara fiye da ashirin ba ta mallake su ba".
Wata cikin su, tana bude Baki ta ce "Amma kuma matan aure sun muku zarra da mutunci da kuma 'kima, macen aure tana tsufa tana sake daraja, adalilin gatan da musulunci ya mata".
Dukkan su suka sa mata dariya, suna ganin wautarta, Lubna ta ce "kai ku rabu da Hajara kunsan tunda ta gama wannan makarantar ba ta sake shiga aji da nufin zurfafa ilimin ta ba, kenan kanta a duhu yake bata san komai ba, tana cikin jerin matan da maza suka rufe a gidaje suke gallaza musu, suka kuma hana su fahimtar cigaban da duniya ta samu"
Su Halima da suke jin tattaunawar suka kwashe da dariya suna fadin "ai yanzu duk wadda ta zauna namiji na mata mulkin kama karya mata ta rako duniya, a wannan karnin da ilimi shine komai yaushe zaka yarda a barka da jahilci, barin ma idan mijin naka mai ilimi ne? Da zarar muguntar namiji ta motsa sai dai ki ji ya amarce da mai ilimi, ko kiga yana jin kunyar ya saka ka a al'amuransa".
Jikin Sa'adah ya yi sanyi ganin itama cikin rukuninsu ita kadai ce mai sakandiren, haka akayi ta kutsiri tsoma, ba a gama da wannan maganar ba, a saketa a kamo wata, da za su tafi, a motar Safina suka dunguma har kofar gidansu suka kaita, a hanya suka yi hirar Humaira Suraj da a yanzu take aure a sokoto, dama can