Showing 66001 words to 69000 words out of 186291 words

Chapter 23 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9716

zuwa gida, ke ba sai ki dinga zuwa ba".

"Ba ku da hankali"

Har gida Zainab ta raka Inna sannan ta tafi gidansu.

Allah- Allah Inna take yi Baffa ya dawo ta ba shi labarin Iyarsa ta kusa zama uwa.


Tunda su Inna suka tafi, ta debo kayansu da ya wanke jiya, ta zauna ta fara guga.

Ta kammala nasa tsab ta-ci karfin nata, ya dawo.

Ta fara kokarin tashi ta karbe shi, ya tsaya daga inda yake ya bude murya ya ce "Yi zamanki ki ji da kanki".

Ta koma ta zauna tare da cewa "Sannu da dawowa"

Bai amsa ba ya shiga kicin ya ajie ledar hannunsa, ya zubo abinci a plate, tare da cokula biyu.

Gefe kuma ya wanko guiba ya zubo a bowl.

Yana zama tun kafin ya yi magana ta sa hannu ta dauki gwaibar ta fara ci.

Ya kalleta ya ce
"Sau nawa zan ce miki ki daina gugar nan idan na sami dama zan yi?"

"To ina zaune haka ai bai fi motsa jiki ba, ni fa har wankin ma zan iya mana, kawai dai na bari ne saboda ka ce ba ka so.

Ya zuba musu abincin, yana fadin mun yi Ba'ki ne yau, ko kuma wani abin za mu yi da daddare?"

Tana murmushi ta ce "Yau babbar bakuwa muka yi baka nan"

Ya zuba mata ido cike da neman karin bayani.

"Inna yau dai Allah ya nufa ta zo"

Da sauri ya ce shine baki fada mini za ta zo ba?"

"Ni ma fa ban sani ba kawai ganin su na yi ita da Zainab".

"Ba ni labarin yadda ta kaya, kin saka hijabi kin boye cikin?"

Tana dariya ta ce "Ban saka ba, amma dai na ji kunya ba kadan ba, ita fa ba ta san ya girma haka ba".

Shi ma cikin dariyar ya ce "To me kika ba su da za su tafi?"

"Ban basu komai ba".

Ya rage fara'a ya ce "Kai Iyah don rowa?"

"To ai na ga farkon zuwa na na kai mata atamfa da sabulai, zuwan da na yi na karshe ma ka ba da kayayyaki na kai mata, yanzu ni kuma ba kudi ne da ni ba".

"Kudin da yake cikin durowa a dakina fa?" Ya tambayeta yana kallon ta.

"Uncle ai ban fada maka zan taba ba, sannan kuma cewa ka yi na sayayyar kayan Baby ne".

"Daga yau ban miki iyaka da komai nawa ba, akan su Hajiya da Inna, komai kika ba su ba zance don me ba?".

"Tom shike nan na gode zan gyara".

"Ina ta cin abinci baki sa hannu ba?".

"Ci abinka ni kunu zan sha, dazu Zainab ta taya ni muka yi".

"Kwana biyun nan ban san me yasa ba na son shinkafa ba".

Sai da ya kammala cin abincin ya tashi ya zubo mata kunun a katon mug, sannan ya jona gugar ya ci gaba da yi.

Suna zaune aka fara kiran Magariba, daidai lokacin kuma ya kammala musu gugar gabadaya.

Ya yi alwallah ya nufi Masallaci, ita ma ta tashi da kyar ta yi alwalar.

Kafin ya dawo ta shirya kayan su cikin durowa, ta tattare falon, ta kunna turaren tsinke na Touch Me.

Haka kwanaki suke ta shudewa har watan haihuwa ya kama, komai na Sa'adah ya sake canjawa, fuskarta, ta yi wani iri, hanci ya bude sosai, baki ya zama kato tamkar ba Sa'adah yar kwalisa ba.🤣

Ita da kanta ba ta son ganin fuskarta a madubi, MK idan ya kalle ta dariya take bashi, amma ba ya iya dariyar a gabanta, tun kwanaki da ya kalle ta ya fashe da dariya, ita kuma ta saka masa kuka mai tayar da hankali, da kyar ya shawo kanta, shike nan bai kara ba, sai idan ya fita ko ya shiga dakinsa ya yi mai isarsa.

Ranar Alhamis da yamma ya isa gidansu, bayan sun gaisa da Hajiya Babba, ya tambaye ta yadda za a yi akan sayayyar kayan haihuwa.

Ta kalle shi da kulawa ta ce "Haihuwar ta matso ne?"

Ya ki tankawa.

Ta yi murmushi ta ce yanzu fa an daina wannan ala'adar, a yi sayayya amma wai sai ranar suna da a ba da kaya, kawai ku je ku sayo kayanku, ku ajiye Allah ya raba su lafiya".

A zuciyarsa kawai ya amsa, ya mata sallama ya yi dakin uwarsa!ya mata bayanin yadda suka yi da Hajiya Babba.

Ta ce "Shike nan a yi yadda ta ce din, ko ka hada su da Samira ta raka ta, tunda ku ba ku san mai aka fi bukata ba".

A gidan ya ci abinci kasancewar daga makaranta ya zarto, sannan ya musu sallama ya tafi.

Haka kuwa aka yi tare da Samira suka je kasuwar kayan jarirai ta asibitin Nassarawa suka zabo kayayyaki daidai misali, wadda za a fi bu'katar su.

Ganin kayayyakin nan ya karawa Sa'adah kaguwar ta haihu, da MK ya dawo ya ga yawan kayan da kyaunsu, shi ma ya ji dadi tare da yabawa Samira.

Dadi ya kama shi ganin da ya yi Sa'adah tana ta murnar kayan. Ya ce mai ya rage ba a saya ba?"

"Uncle komai an siya kawai rigunan ne unisex, sai anyi haihuwar za a sayi na mace ko na namiji, sai durowar Baby kawai".

"Tom shike nan su ma zan saya muku, ke ina naki kayan?"

Ta fara daddaga kayan gun tana neman ledar da kayan suke ciki, shi ne ya hangota ta fada tsakanin kujeru, da kyar ya janyo ta.

Ya bude yana ganin inner wears ne, sai pads, saboda ya tura Lagos Anty Hafsatu ta siyo mata lace da shadda.

Ya daga bireziyar da ta masa kyau sosai, har zai mayar, sai ya yi niyyar tsokanar ta, ya ce
"Anya wannan za ta miki kuwa?"

"Za ta mini mana ba ka ga an kara size din akan wadda na saba sawa ba?"

"To abin ne na ga kamar ba za ta rufe su ba".

"Kuma haka zan ta zama, ai Inna ta ce zan huce".

Ya guntse dariyarsa ya fita yana fadin, yanzu zafi ne da ke?"

Sai da ya dawo ya zauna ya ce, "Ki fito da kayan da zan kai miki dinkin".

Shiru ta yi masa tana ala'adarta ta zumbura baki.

Ya maze ya ce, "Da ke fa nake magana kin san na sha fada miki ba na son na miki magana ki yi kamar ba ki ji ba.

Ga mamakinsa sai ya ga hawaye na zuba a idonta, kafin ya tambayi ba'asi ya ji tana cewa, "Da alama idan na yi kiba daina sona za ka yi, kullum sai ka mini dariya, ina kallon ka kawai sharewa nake yi, don ma kai ka mayar da ni hakan din".

Ta kare tana kifa kai a hannun kujerar da ta ke zaune, tana masa kukan iyashege.

Maimakon ya ji ya damu sai kawai dariyar ta zo masa sosai, ya dinga kyakyatawa.

Lamarin da ya harzuka ta, ta tashi ta koma daki tana kuka sosai.

Sai ya yi shiru da ya hasaso yadda hanci da bakinta suka zama sai ya sake fashewa da dariyar, ya jima kafin ya samu dariyar ta tsaya masa.
Ya shiga mayar da kayan cikin ledoji ya kai su dayan dakin da ba kasafai suke amfani da shi ba, ya bude wardrobe ya zuba su ya rufe.

Dakin ya bi ta, ya samu tana ta goge fuskarta da tissue, kusa da ita ya zauna ya rungumo ta ta gefe, so take ta fizge amma ta kasa, ya fara magana a hankali.

"Me ya sa kike da saurin kuka ne Iyah? So kike Babyn mu ya zama mai kukan banza? Me yasa ba ki san wasa ba, ko buhu kika zama wallahi ba abin da zai ragu a son da nake miki, ba sha'awar ki nake yi ba, ba jikin ki nake so ba, ke nake so. Tsufa ko tawayar halittar ki ba za su canja soyayyar da nake miki ba, ki ri'ke wannan".

Sai ta lafe sosai a jikinsa tana sha'kar kamshinsa, ta sa hannu ta balle links din dake gaban rigar ta zura hannu tana shafo kirjinsa.

Cikin lokaci kalilan suka birkice, Sa'adah, ba karamin kidima MK take ba, nauyin cikinta baya tasiri a wannan fagen. Sosai kalamansa suka sata farinciki, shi yasa ita ma take mayar masa da tarin soyayyar da take masa a aikace ba ka jin komai sai numfarfashin MK.
Soasai suka sha shagalinsu, katon cikin su ba ya hana su komai, sai dai Mk ya san yadda yake yi ba tare da ya takura ta ba.

Yana tsaye gaban madubi, yana daura Agogon hannunsa, ita ma ta fito daga wanka daure da tawul, a bakin gado ta zauna tana ta numfarfashi, shi ya taimaka mata da shafa mai, pant da siket kawai tasa ta zura doguwar riga marar nauyi.

Ya dauke tawul din ya shanya a kofar bandakin. Ya dauke bireziyar da ba ta saka ba ya mayar inda take ajiye su.

Dake ya saba da tsokanarta ya kalle ta yace, "Iyah na lura idan kina koke-kokenki inviting dina kike yi ashe, daga yau na fahimta. I will be noted".

Hararar sa ta yi tare da cewa "Ka daina ce min Iyah, ba na so".

"Ni kuma ina so".

Duk wani abin da za a bukata lokacin haihuwa MK ya tanadar mata, hatta dinkunan da za ta saka ya karbo, ba abin da suke jira illa zuwam ranar haihuwa.

Ranar Talata da ta yi daidai da hudu ga watan Mayu 4/5, tun Asuba take faman murkususu, tun tana daurewa har ta gaza, a sukwane ya samo Adaidaita Sahu suka nufi asibitin Murtala, waya ya yi wa Hajiya Babba, ita ma a gaggauce ta bi su, sai da ta isa, sannan ya koma gida don dauko akwatin da suka shirya kayan zuwa asibiti, da kuma tabarma.

Karfe 1:45pm na rana Sa'adah ta haifo sankacecen yaro namiji mai cike da koshin lafiya, kukan da yake canyarawa ne ya tabbatar ma Hajiya Babba, Sa'adah ta sauka.

Ana zuwa albishir da karban kayan jariri, MK na isowa, ya tarar da labari mai dadi.

A Daren ranar aka sallame su, bayan an tabbatar da lafiyar uwa da jaririnta.



```Alkalamin Surayya Dee```
✍🏼


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.






57-58


Kafin wayewar garin labarin haihuwa ya isa kunnen Yan uwa da abokan arziki.

Umman fanshekara da ta kasance kanwa ga Baffa, Ya'yan Baffani su ke(cousins)! za ta zauna da Sa'adah kasanitacecewar mijin ta ya kwana biyu da rasuwa, kuma ba ita kadai bace tana da abokiyar zama.

Sosai Mk yake hidima da mai jego, komai akace ana bu'kata da rawar jiki zai kawo, har wadda ma ba a nema ba.

Umma sai yaba kirkin Mk da iyayensa ta ke yi, kullum suka zauna da Sa'adah sai tace "kin yi Sa'a Iyah, kin hadu da miji da ya gaji arziki d mutunci a wurin iyayensa, shi kam bai shure kyawawan dabi'un gidansu ba".

Murmushi kawai Sa'adah ta ke yi tana gasgata maganar Umma.

Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifin Mukhtar, wato Muhd Kabir tun a ranar kuma Samira ta lankaya masa Jawad.

A zuciyar Sa'adah ba Jawad ta so ba, amma saboda kara ga kanwar Mk sai bata canja ba.

Sosai aka yi shagalin sunan Jawad abinci mai kyau aka yi a gidan su Mk, aka ciko manyan kuloli aka zo da su, jollof din shinkafa, bandashen Gurasa, da Alale. ga kuma dangin kayan sha irin su zobo, ginger, da kunun Aya masu dadi da sanyi. mai daukan hoto da video duk motsin Sa'adah sai dai ta ga hasken camera, tun safe kafin a cika suka sha hotuna da Mk cikin kwalliya ta burgewa.

Da azahar sai ga Halima da Safina sun zo kwatsam,sama sama suka gaisa da Zainab Ma'aji ta gabatar musu da abinci da kuma abin sha, yayin da Sa'adah keta rawar jiki akan su, suna ta yatsina, hatta abincin ma ko hannu ba su saka ba bare su ci.

Cike da murmushi Sa'adah tace "idon ku kenan, sai yau kuka tuna da Ni, ashe ma kunsan inda na ke! nema na ne baku yi ba?".

Halima da tafi Safina ginshira ta ce " Akan mai zamu neme ki, inace kin dauke mu kin watsar a shara, shiyasa muma muka manta da ke, kin ri'ke miji kin manta da kowa! zuwan ma yanzu da muka yi ba naki bane, na 'Dan mu ne ko kin fada mana kin haihu?"

Dariya sosai Sa'adah ta yi, tana fadin "shikenan yana godiya"
tare da cire nono a bakin sa, a kafada ta saba shi, sai da ya yi gyatsa sannan ta nade shi a shawul da ke canja masa riga aka yi, ta mi'ka ma Safina da tafi makwaftaka da ita.

Ido ta zuba tana yaba kyaun jaririn, ta ke ta ji sha'awar ta samu nata, ta jima tana ri'ke da shi, har sai da Halima tace " Ba za ki bani na ganshi bane?"

Sannan ta mi'ka mata tana fadin "Babyn ne so mashallah". Halima na zuba ido akansa taga kamannin Uncle Mukhtar sak a fuskar yaron.

A fili ta furta "Allah dai yasa kar ka kwaso mana halinsa".

Da sauri Sa'adah tace "Uncle din kike cewa kar ayi halinsa? ai kuwa zan fada masa".
Ta no'ke kafada, alamun ko ya ji Ina ruwanta.

Har kusan maghrib sannan suka tafi, suka ajiye mata leda mai dauke da rigunan yaro masu tsada guda uku da Pampers mai 48, ta musu godiya. Zainab tana daga falo tace ku gaida gida! da kyar ta basu ledar da ta ke rabawa mai dauke da sunan jaririn!cikin kuma memo ne mai hoton Jawad.

Kwana uku da suna dan kishiyar Umma ya rasu, daga ciwon ciki kawai sai mutuwa, dole ta tafi, ta taya yar uwarta zama da juyayi! mutuwar matashi akwai gigitarwa.

Kwanaki biyu a jere Inna ke zuwa da safe ta mata wanka da sauran hidima, sai ta mata wankan yamma sannan ta tafi.

Ganin zirga zirgar zata mata yawa kullum, yasa ta roki Baffa ya bari Sa'adah ta zo gida ko sati biyu ne, ta kula ta ita, ita kadai tasan me ta gani, da dukkan alama daki daya suke kwana da mijin ta, tunda Umma ta bar gidan.

Bai tsananta ba, ya amince amma da sharadin idan mijinta bai amince ba, baza'a matsa masa ba.

Tace "Ni ai da iyayensa zan yi magana, idan ka bani dama a daren nan zanje gunsu".

Bai hana ba, itakuma bata yi sanya ba, tana idar da magariba ta tafi gidansu Mk, a falo duk ta same su har Hajiyan Bichi, bata bata lokaci gurin fayyace bu'katar ta ba.

Dukkansu sun yi shiru!sai Hajiya Babba ce ta yi kundunbalar cewa "tunda har kika zo ba za'a hanaki ba, sai dai ki yi hakuri da kaina zan kawo miki ita, idan aka shirya".

Godiya sosai Inna ta yi ,har kofar gida suka rakota suna ta yiwa juna godiya.

Har ta isa gida tana mamaki! ko kishiyoyi nawa ne suka dace da kyakkawan zama irin na iyayen Mk? ko
Ana samun adalar uwargida irin Hajiya Babba, mai hade kan ahalin gida babu banbanci, ko kai sukar wani ga wani, da sauran gutsiritsoma irin na tsofaffin mata masu kitsa munafunci da sunan kishi? Ko
Ana samun amare masu kawaici da biyayya da sanin mutunci da alherin uwayen gida irin Hajiyan Bichi? sha'awar zamansu ya kamata tana jin inama, itama tana da abokiyar zama, ba yabon kai ba, da zata yi koyi da Hajiya Babba.


Da murna ta bawa Baffa labarin yadda suka yi, shi da kansa sai ya zaku Iyah ta dawo kusa da shi duk da dai bai furta ba.

Suna komawa gida, Hajiya Babba ta Kira Mk a waya, ta sanar da shi bu'katar mahaifiyar Sa'adah! ya yi shiru ya rasa mai zaice, jin shirunsa ya tabbatar mata da bai ji dadin maganarta ba, bashi kuma da niyyan amincewa.

Dan haka sai ta kwantar da murya cikin hikima tace " Da na yi karambanin amincewa, har naci alwashin da kaina zan kai musu ita, amma ba zai zama komai ba, idan banyi daidai ba, sai na koma na lashe amai na".

Cikin takaici iri iri yace "Ni bance ba, tunda kin amsa shikenan! amma dai sati daya za ta yi".

"Akan mai zaka 'kayyadewa iyayen ta kwanakin da zata yi a gaban su, ba ka ga mutunci irin nasu ba? neman alfarma suka zo yi gaban iyayenka, saboda girmama hakkin aure. ba dan basa sonta, ko dan sun gaji da ita suka dauketa suka baka ba, yau kusan shekara guda. me zai sa ka shata musu layi dan su nemi su kula da lafiyar yarsu?"

Ya yi shiru yana jin maganar na shigarsa sosai, ya nisa yace "Shikenan Hajiya duk yadda kika yi dai-dai ne"

Dadi ya kamata! ta shiga jero masa addu'ar albarkar ubangiji a dukkan kasafin sa.

"Tunda ka yarda da hukuncin da nayi, duk da ba ka so! Ni kuma zan fada musu sati uku za ta yi maimakon wata guda".

Takaici ya sha'ke masa wuya, wai har sati uku, shi ya dauka anyi wuta ta yi sati biyu, to da fiye da wata ake nufi zata yi ko me?

Sa'adah na zaune a daki tana shayar da Jawad, shi yana falo yana musu guga, ya tattara kayan ya kulle ya kashe iron din saboda yadda jikinsa ya mutu da 'bacin rai.
'
Jiki a mace ya shiga 'dakin bai kalleta ba, ya wuce ya hau gado yana jin zazzabi na namen kama shi.

A gigice ta dinga tambayar sa lafiya kuwa, me ya same shi?

Jinsa shiru yasa ta shimfi'de Jawad! ta isa kusa da shi tana ta'ba jikinsa ta ji ko zazzabi ne yake san'darsa.

Ras ta ji jikinsa, sai rashin kuzari, ta shiga tambayar sa, ya kasa bu'de baki ya mata bayani, amma ganin zata masa kuka, ya fisgota jikinsa ya kankameta, yana sakin ajiyar zuciya.

Tsawon lokaci suna haka, cikin rashin kuzari yace "Tun yanzu na fara kewar ku"

Gabanta ya fadi ta kalleshi ido a bude "Tafiya zaka yi ka barmu?"

Sai kawai ta fara hawaye, ya kalleta yana jin sonta na sake daskarewa a zuciyarsa, shagwabarta, rauninta, soyayyarta na sake gigita shi.

Ya sake kankameta sosai yace " Kune dai za ku tafi ku barni, yanzun nan wayar da kika ji inayi!Hajiya Babba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login