Showing 63001 words to 66000 words out of 186291 words

Chapter 22 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9702

har da doriya, ban yi wani abin da kika gamsu son ki nake yi da iyakacin gaskiyata ba? Ko a lokacin da kike ganin ba na tarairayarki, ai kona mini rai kike yi, na ce ba na son ganin ki da dan iskan yaron nan, amma ba ki ji ba, haka na yi ta ha'kuri ba don ina son ki ba za mu yi auren ne?"

Ya sake tausasa murya ya ci gaba da fadin, "Saboda Allah indai dama ba wani abu ne a ranki ba, mene ne na dawo da abin da ya wuce, ba haka kawai na fada miki maganar da kika kullace ni a ranki ba, ke kika janyo, ko ba ni da alaka da ke zan yi kishi yanayin da na gan ki, a matsayinki na mace mai daraja".

Ya yi shiru yana jin shesshekar kukanta, tana ta ajiyar zuciya tamkar wadda ya yini yana dukanta.

"Na roke ki, ki daina kukan nan haka, na yarda ban kyauta ba ki yi hakuri".

Ta yi shiru, kamar yadda ya roka din har da gyara kwanciya, da lulluba alamun barci za ta yi, tana sakin ajiyar zuciya, a ranta kuma tana fadin sai kuma rikicin gobe.

Ya so su kasance tare, amma saboda tsoron kar ta ci gaba da masa kuka yasa ya kyale ta, ba a jima ba ya ji saukar numfashinta alamun barci ya yi awon gaba da ita.

Ya saki gauron numfashi, ya haska fuskarta, da hasken wayarsa ya ga hawaye duk ya bushe a fuskar, kuma wani abin dariya ita da kanta ta boye fuskarta a jikinsa. Tsintar kansa ya yi da gyara mata kwanciyar yadda za ta ji dadin barcin.

Ya dawo Masallaci, ya tarar ta dira sabon kuka ga akwati a kan gado sai zuba kaya take yi tamkar mai shirin yin balaguron wata guda.

Zama ya yi gefen gadon yana kallon ikon Allah, da Asubar fari za ta fara masifa tamkar jiya ba ta yi ba, duk irin ha'kurin da ya ba ta ashe bakam ta masa. Yana kallon yadda ta gama shirya akwatin ya kasa cewa komai saboda gaba'daya He is speechless.

Wanka ya ga ta shiga yana zaune ta fito, ta shirya cikin riga da skirt na English wears, skirt (purple) iya guiwarta rigar kuma body hug (pink) an rubuta *BABY GIRL* ta kama ta ainun musamman daga kirji, ta gyara zaman ribon dinta a kitsonta na shuku, ta masa kyau ba kadan ba, har ya dinga raya don ta tayar masa da hankali ne yasa ta yin wannan shigar da Asubar nan tunda ta san yau ya kwana bai taba ta ba. Ta shafe jikinta da turararuka kala-kala tun daga na jiki har na kaya, sannan ta dora bakar doguwar riga akan kayan ta yane fuskarta da dan mayafin rigar.

Ta dauko takalmi da jaka ta saka sannan ta ja akwatin ta nufi kofar barin dakin.

Wata irin fizga ya mata ta dawo da baya kamar za ta fadi sai kuma ta dire kan kafafunta. Kafin ta yi magana ya riga ta da cewa "Me kike shirin yi ne haka, ina ce tun jiya magana ta wuce?"

Hawaye yana zubar mata ta ce "Wallahi ba ta wuce ba don kuwa ni ba zan sake zama da kai ba".

Dariya ce ta subuce masa wadda babu nisha'di ya ce "Ok tunda haka ki ka zaba shike nan, sai na ga wadda zai raba ki da ni".

Ta juya za ta sake fita, wannan karon da karfin gaske ya janyo ta ya jefa ta gado tare da fadin "Wannan shi ne gangan, ba za ki fita ko ina ba, bai wani bata lokaci ba ya bita ya turmushe ya sakar mata dukkan nauyinsa.

Ta kasa koda kwakkwaran motsi, sai da ya tabbatar ta yi laushi sannan ya daga ta, sai kuka take masa mai sauti bai kula ba, sarrafa ta yake yi kawai, tun tana tirjewa har abin ya shiga jikinta ta yi lakwas ta sallama.

Tsawon lokaci kafin ya samu nutsuwa.

Sai da ya huta sannan ya tashi ya fita bayan ya zura jallabiyarsa, a shirye ya fito hannunsa ri'ke da mukallin mashin, tana kwance inda ya barta tana kallon sa, ta tura baki gaba ta dauke kai.

Murmushi ya yi ya ce "Kin ga kwana uku ke nan ina fita da yunwa amma yau a koshe zan fita, kullum haka zan dinga miki".

Harara ta watsa masa tare da cewa "Idan na zauna ba".

Murmushi ya yi tare da fadin "Ba inda za ki iya tafiya ki bar ni, wa zai iya da wannan fitinar ta ki ai sai ni din".

Ganin magana yake nema yasa ta daina tankawa.

"Zan tafi, ki tashi ki yi wanka ki karya, idan na dawo ban tarar da abinci ba, ki tabbatar ke ce abincin."

Ya fita yana fadin "Sai na dawo." A fili sharewa ta yi amma a zuciyarta addu'a take masa.

Yana barin tsakar gida ya janyo kofar ya rufe ta da kwado ya saka mukallin a dan jikin flowers, ya fitar da mashin dinsa, ya bar kofar gate din ba tare da ya rufe da jamlock ba.

Wanka ta sake yi, tana yi tana tsaki, haka kawai an mayar da mutum kamar agwagwa wanka dai wanka dai ba kakkautawa.

Ta mayar da kayan da ya cire mata bayan ta shafa mai, doguwar rigar ta ninke ta mayar durowa, sai da ta gyara gidan fes ta share ta goge ko ina. Ta kunna risho ta dora tukunya don dafa indomie, dogon Hijabi ta dauko ta saka, ta dauki kaskon turaren wuta, lekawa za ta yi ta samu yaron da zai samo mata garwashi a gidan Maman Nana, jan duniya kofa ta'ki budewa ga shi kuma ba da mukulli aka rufe ba, kan dole ta ha'kura bayan ta hango kwado ta yar karamar kofa, murmushi ta yi tana fadin
"Ya dauka da gaske tafiyar zan yi".

Tana karyawa ta yi wanke-wanke, ta dora abincin rana, farar macaroni ta dafa ta fito da miyar kifi daga fridge ta dumama ta bar ta akan rishon, ta juye macaronin a foodflask ta ajiye, ta tsinci kanta da son hada masa zobo, nan da nan ta dafa ta hada ta saka a fridge.

Sai da ta gyara kicin din sannan ta tafi ta kwanta, ba ta jima da kwanciyar ba, barci ya yi awon gaba da ita.

Bude ido ta yi ta gan shi tsaye a kanta alamun shi ya tashe ta, mi'ka ta yi ta sake juyawa don ta ci gaba da yin barcin.

"Ki tashi ki yi sallah biyu fa ta wuce".

Kan dole ta tashi don kuwa ba karamin jin dadin barcin ta yi ba, har ta idar yana kishingide a gefen gadon, ya kalle ta ya ce

"Kin yi abincin, ko kuwa ke ce abincin?"

"Don Allah ka barni na ji da abin da ya dame ni, ina dai rufe ni ka yi, ba ka tunanin faruwar gobara ko wani abu na ibtila'i, ina kulle ba?".

Cike da rashin damuwa ya ce "Na fi ki tattalin lafiyar ki, na riga da na yi riga-kafin komai. Ba ki amsa mini tambayar da na yi ba?"

Shiru ta yi ta kyale shi, ganin haka ya mike ya na cire rigar shaddar jikinsa, ya cire wandon, ya yi saura daga shi sai Boxer da singileti.

Inda take zaune ya nufa ya mikar da ita yana fadin "Taso".

Kwacewa ta yi ta fita falo a guje, tana fadin, "Wallahi ba za ka tsofar da ni ba, ga abincin can a kicin".

Yana dariya ya biyo ta ya zauna a kujera ya ce "Zubo mana"

"Ni na koshi".

"To ni zubo mini".

Ta fita tana kunkuni ai tun farko shi ne ya'ke zubo musu abinci, sai yau zai ce ita za ta zubo.

Haka ta shiryo masa abincin har da zobo, dadi ya kama shi sosai, ya dinga cin abincin hannu baka hannu kwarya, tabbacin tunda ya fita bai sa komai a cikinsa ba.

Yana kallon yadda ta zauna a falo ya san ta ki shiga daki ne don kar ya mata wani abu, abin da ba ta sani ba a falon ma ba abin da zai fasa.

"Sa'adah! Don Allah mu shirya haka nan, wallahi na gaji da fushinki, ki yi hakuri kin ji na janye wallahi ke kamila ce, mai kirki ce".

Ko kallon sa ba ta yi ba, bare ta amsa masa.

"Kin ga siyar mini da fushin to".

Ta zumbura baki sosai, ta sake yin shiru.

"Ki shirya gobe na kai ki, ki yini a wurin Inna, idan za mu dawo sai mu tsaya a Sahad store mu sayo iron din da ki ka ce na sayo miki"

Nan ma shiru ta yi.

"Kin ji"

"Ni wallahi albarka".


"Tom shike nan satin sama makaranta za ta tura mu Jami'ar Jos Seminar, ki shirya mu je, ki gaida Anti Sumayya".

Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta.

Shi ma murmushin ya yi tare da tambayar "Kin sayar?"

Kai ta daga tare da cewa "E amma fa har da fitar goben".

"Na sani ai, tunda mun shirya, mu je ki taya ni barci, kin san jiya ban yi wani cikakken barci ba, kuma na yi fitar sassafe."

Sai da ya fita ya kewayo sannan ya kwanta, ta bi shi tana masa tausa har ya yi barcin.

Shike nan rikici ya kare.

Ranar da suka tafi Jos ba su isa ba sai yamma likis, don haka a Hotel suka sauka, duk da Sa'adah so ta yi ta sauka a gidan Sumayya.

Washegari da safe da zai fita wurin aikin da ya kawo shi ya ce ta shirya ya raka ta, da yamma zai zo su dawo, nan da nan Sa'adah ta canja fuska, tana fadin "Ni dai ka bar ni na dinga kwana a can tunda dai kwana uku kawai za mu kara yi".

Kai tsaye ya ce "Ba zan miki karya ba, ba zan iya ba, zan dinga kai ki da safe, idan yamma ta yi, zuwa Maghrib zan dinga zuwa muna dawowa".

"Ni gaskiya kwana nake so na yi"

Ido ya zuba mata sosai, ba tare da ya ce mata uffan ba, ta sunkuyar da kai kasa, saboda yadda ta ke jin kallon na ratsata.

"Yini za ki yi"
Ya sake maimatawa a gajarce.

Bata rai ta yi sosai amma ba ta ajiye kayanta da ta dauka ba.

Ya kalle ta ya ga ta yi kicin-kicin da fuska, ga kuma kaya a hannun ta, shi ma ya daure tasa fiye da yadda ta yi.

"Ni ko kwana daya ka barni na yi".

Ransa a bace ya ce "Ke ki yi duka kwanakin ma, mu hadu a tasha ranar tafiya, idan kuma kwanakin ma sun miki kadan, ki yi ta zama har sai kin gaji".

Ajiye kayan ta yi, sannan ta bi shi suka tafi. Kowa sai kunci yake yi da dan uwansa.

Shatar taxi ya dauka suka nufi unguwar su Sumayya, ba mai cewa kowa uffan.

Da murna Sumayya ta karbe su, cikin kankanin lokaci aka cika gabansu da abin karyawa, a gurguje ya ci abincin ya tafi, ciki-ciki Sa'adah ta ce "Sai ka dawo" Ba tare da ta raka shi hanya ba.


"A hakan kike so ki mallaki mijin?" Sumayya ta tambayi Sa'adah.

"Tunda kuka zo fuskarki a daure, sai da ya tashi, kika ware, tun yanzu za ki koya masa bagarar da lamarinki? Tun yana tsoron ganin fushinki, har ya daina?"

"Da bakinsa ya ce mini zai zo Jos, na shirya zai kawo ni na gaishe ki, kuma yanzu ya ce ba a nan zan sauka ba, sai dai na dinga zuwa yini, akan mai zai hana ni kwana?"

"Akan ya damu da lamarinki mana, ke yanzu ba ki ga alherin da ya miki ba, idan kuwa haka za ki dinga masa zai daina kokarin kyautata miki. Me ya kai ki yin musu, har da fushi akan abin da ya zartar?"

Haka ta dinga mata nasiha cikin rarrashi, har Sa'adah ta ji ba ta kyauta ba.

A ranar Sumayya ta fahimci Iyah na da ciki, amma ganin ba ta san tana da shi ba, yasa ita ma ba ta mata maganar ba, kuma lafiyar ta kalau, ba wani tsirin abinci ko laulayi, kawai dai yawan kwanciya take yi.

Da kanta ta masa waya, da ta ga an yi Magariba bai zo ba, tana tambayar yaushe zai zo.

"Kin fasa kwanan ne?"

"Yinin da na yi, ba tare da kai ba, a daddafe na yi, sai yanzu na gane, ko kace na kwanan ma ashe ba zan iya ba."

Da'di ya kama shi ya ce "Har na dawo masaukinmu amma bari na zo".

Sosai suka huta, zuwan su Jos sai ya zama tamkar Honey Moon a gurinsu. Son juna ya karu a zukatansu.

Wani irin so da zazzafan kishin MK, ya cika zuciyar Sa'adah, zuwa yanzu ta tabbatar ya iya soyayya, irin wadda ma ba ta yi zaton akwai irin ta ba.



Alkalamin *SURAYYA DAHIRU*
✍🏼✍🏼.
[6/7, 11:54] Aminan Ibrahim: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*





55-56




Kwanan su uku da dawowa, jikin Sa'adah ya rikice da wani irin zazzabi da amai.

Ganin kullum ciwon gaba ya ke yi ba baya ba, yasa ya kaita asibiti, test aka ba su, tunda kan Taifod, malaria, da ciki (P.T).

Sakamakon na fitowa komai Negative, illa na cikin da ya kasance positive.

Maganin tsayar da amai da karin jini aka ba ta. Sai Panadol, tare da fadin sai a hankali za ta sami lafiya tunda jikinta na samun sauyin yanayi.

Sosai MK ya ji dadi, sai fadin Alhamdulillah yake yi har suka dawo gida.

Sannu kuwa har gajiya da amsawa take yi, motsi kadan zaicce sannu, tamkar mai nakuda.

Kwana biyu ta warware ta shiga harkokinta ba wata matsalar komai, lafiyayyen ciki ta samu komai ci take yi, ko sau nawa MK zai neme ta ba ta gajiya, wani lokacin ma ita take yin dalilin da za su hadun.

Mamakin yadda ta zama expert a wannan harkar take yi ba gajiya, har Allah-Allah take yi idan ya fita ya dawo, ko kuma dare ya yi.
Ta san mabukaciyace ita, amma ko kusa ba kamar yanzu ba. Tunda ta sami ciki, ba ta sake hadiyar Viagra, bare ta ce ko shi ne yake sababa mata yawan son sex.

Daga dukkan alama cikin ne ya zo mata da wannan salon, wadda take fatan kar ya zame mata dabi'a ta dindin, MK da'din hakan yake ji ba kadan ba, kullum a cikin fadin "Madalla da Babyn nan yake."

Cike da zumudi suke goyon cikin, wani irin kyau Sa'adah ta yi, fatarta ta sake yin laushi, ta goge ta yi tas, MK baya gajiya da kallon ta musamman yadda kirjinta ya cika dam, kugunta ya bude sosai.

Shi kansa MK ya murje farinsa ya karu sosai, kallon su kawai za a yi a san suna cikin kwanciyar hankali, da mutunta juna.

*BAYAN WATA SHIDA*

Zaune take a tsakar gida tana waya da Inna, "Inna har yau ba za ki zo kiga inda nake ba?".

Daga can bangaren ta amsa da cewa " To Baffanku ne ya hana ni, wai mai zan zo na yi miki".

"Cikin shagwaba ta ce "Na san da kin karfafa Inna da tuni kin zo, haka na sha jinya har na warke ba ki zo ba, da Anty Sumayya ce a garin nan take rashin lafiya da kin je kin ganta, amma ai ni ma Baffa ya zo ya ganni." Ta fada a sanyaye.

Dariya ta yi tana cewa "Iyah ashe dai har yanzu da saura, na dauka kin yi hankali sosai, musamman da na ga kina zaune lafiya da mijinki kuma kin tsare kanki ba kya yawo".

"To Inna yanzu na kai wata biyar ban zo gidan nan ba, tunda na ji fa'danku, ba na yawo na tsare kafata, ba sai ki dinga zagayowa kina gani na ba".

"E gaskiyar ki, to ki kwantar da hankalinki, ina tafe tunda ga Baffanku ma yana jin ki da kunnensa".

Da haka suka yi sallama ta kashe wayar, da kyar ta samu ta tashi saboda yadda cikin ya mata nauyi sosai tamkar ba cikin fari ba. Watansa bakwai, amma sai a yi zaton a watan nan za ta haihu, duk da cewar watansu takwas da aure.

A fili ta ce "Gara ki zo ki gan ni, ki ga yadda na zama".

Washegari kuwa bayan azahar sai ga Inna da yar rakiyarta Zainab Ma'aji.

Mamaki ya yi matu'kar kama Inna ko kadan ba ta san cikin har ya tsufa haka ba, ta san dai tana zargin ko da cikin tunda rabon da ta sa Iyah a idonta an kai wata biyar koma ya zarce hakan.

Ta zauna tana mamakin yadda ta aune ta zama babbar mace komai nata ya bude, da kyar take zama da tashi.

Kallon Zainab Inna ta yi ta ce 'Ashe kin kusa zama uwa amma ba labari?"

Dariya sosai Zainab ta yi tare da fadin "Inna Ina zan iya hirar haihuwarmu ta fari".

Yayin da Sa'adah ta sunkuyar da kai kasa alamun kunya.

Zainab ce ta shiga kicin ta hado ruwa da lemo ta kawowa Inna, ta sake komawa ta dauko tiren da ta gani an shirya kayan abinci a kai.

Hira suka yi, cikin walwala har Inna ta fahimci sauyin da Iyah ta yi, ta fara yin hankali.

Sai da suka zo tafiya, ta fashe da kuka, kamar wata sokuwa.

Cike da tarin kauna Inna ta sata a jikinta, tana fadin "Kukan na menene kuma Iyah? so kike ki tayar mini da hankali bayan cike nake da murnar ganin ki cikin nutsuwa da walwala, ko wani abin na damun ki ne?"

Cikin kukan ta ce "Ni so nake ki dinga zuwa".

Cikin rarrashi ta ce "Wani satin zan dawo, ai yanzu kam dole Baffanku ya bari na dinga zuwa akai akai".

Da haka ta lallaba ta suka rabu lafiya, ta raka su har gate bayan Inna ta shiga dakunan ta gani tare da sanya albarka.

Suna tafe Inna ta ce da Zainab "Ina murna Iyah ta yi hankali ashe dai da saura, indai ba so take na zama uwar zamani ba, ina ni ina zarya a gidanta?"

Dariya sosai Zainab ta dinga yi tana fadin "Mene ne a ciki Inna? Kin san Baffa ne ya hana mijinta barin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login