Showing 78001 words to 81000 words out of 186291 words

Chapter 27 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9729

zirga, ba tare da kalle shi ba, tace " wata'kila har wanka ya hau kanka".

Zuciyarsa daya ya ce "gaskiya kam idan na yi zanfi wartsake wa", ya kalli agogo ya ce bari na yi sauri na watsa ruwan kafin a kira sallah".

Ya mike ya yi dakinsa, ita kuma ta bishi da kallon tuhuma, da takaici mai yawa.

Da ya dawo bai nemi abinci ba, ta kara gasgata su Halima, ya taba jikin Jawad da yake kwance yana fama da zazzabin hakorin fi'ka, ya kalleta yace a kwance ya yini ne?"

Kai kawai ta daga masa, ya riga da ya saba da halinta na rashin bashi amsa da baki wani lokacin, dan haka bai damu ba.

Wani ikon Allah yau da wuri ya dawo, kamar yasan anshirya masa ya kwana a waje, haka suka kwana bai gane kan gimbiyar ba, ya daure, shima ya 'kyale ta.

Washagari suka tashi Jawad yana ta suma! ga wasu irin abu sun feso masa kamar borin jini, asibiti suka kai shi, aka bashi magaunguna bayan anmasa allurai, sunje siyan magani, suka tarar da Farida a pharmacy din, da azama ta zo gunsu ta karbi Jawad da yake hannun sa ta dudduba jikinsa tana fadin "Abban Jawad wannan ai 'kyanda ce(measles)".

Da kanta ta hado maganin da aka rubuta musu, har ta kara musu da wani sabulu da zai taimaka wurin baje fatar.

Lokacin da take yiwa Mk bayanin maganin da yadda za'ayi amfani da su, Allah kadai yasan yadda zuciyar Sa'adah ta ke tafasa, ko da Farida ta karaso fuskar Sa'adah a daure ta gaisa da ita, har Mk yaji kunyar yadda ta mata a gaban jama'a.

Ya mika kudin Farida ta ce "A a Uncle ka barshi, da dai na Gogel ne sai na barka ka biya! Amma ai Jawad 'dana ne nima", ta fa'da da sigar tsokana da wasa.

Ya yi godiya ta rakasu har mota, ya karbi Jawad a hannun ta, ya mika ma Sa'adah ta hakince a gaban mota, suka tafi.

Suna Isa gida bata jira ya gama daidaita parking ba, ta dauki ledar maganin da Jawad ta fice.

Tana kwantar da Jawad da yake ta barci tunda aka masa allura, ta samo biro, ta yiwa magaungunan nan shaida ta yadda ita kadai zata gane, ta daure ta ajiye su.

Ya shigo ya zauna, yana son yi mata magana amma ganin yadda ta 'daure fuska tamkar wadda ya zagi iyayenta, yasa ya mi'ke yana cewa " na tafi! Dan Allah kar kiyi wasa da bashi magani".

Ci kanka ba ta ce ba, ya gaji da tsayuwursa ya fita, yunwar da yake ji dole ya fita da abarsa, dan yasan tunda take wannan fishin ba yi zata yi ba, yasan ganin Farida ne ya sake tunzuro ta, tunda tun jiya take ta faman 'kunci, a ransa yana ayyana da jiya kuma ta ganshi yana taimaka wa kanwarta da ta samu admission zata karanta economics fa? Farida ba tasan komai a new side ba, tunda ita a old side take karatunta, shikuma sai ya rakasu a kokarinsa na kyautata mata kamar yadda take girmama shi a matsayin malamin ta.

Shi bai san har anzo anfesa mata ba.😄

Da yamma ya dawo, ya ya tarar da ita goye da Jawad, kayan da ya barta da su ya dawo ya same ta da su. kallo daya ya mata, ya gane bata ci komai ba, sannan bata yi wanka ba.

Ya rasa gane wannan masifar da ta 'dorawa ranta, da 'kyar ta bude baki ta ce "Sannu" ya amsa da yauwa ya isa bayanta yana duba Jawad da yake ta Nishi, shi dai ta masa wanka fes yake, sai dai jikinsa kamar wuta.

"Kin bashi maganin kuwa? na ga jikin, har yanzu bai sauka ba".

Ko kala ba ta ce ba, ya isa inda ledar maganin take ya bude ya ga ba wadda aka taba, bare a sha.
Ransa ya baci matu'ka da gaske, ya nunata da yatsa ya ce " Wai ke wacce irin yarinya ce marar mutunci?"

Ta yi 'kasa da kanta tamkar wadda ta saduda, yaci gaba da fadin "kin fara kaini bango Sa'adatu, kullum a cikin zullumi nake zaune da ke, masifar yau daban, ta gobe daban, haka ta jibi".

"Ai kaci moriyar ganga, sai ka kawo karshen zaman zullumi Mk" ta fada kanta tsaye.

A razane ya zuba mata ido, yana kallon ta, itama ta kafe shi da idon da suka cika da 'kwalla ba alamun tsoro ko shakka a cikinsu.

Ya kasa cewa komai, dan kuwa a yadda yake jin bacin rai zai iya na'da mata dukan tsiya, abin da baya fatan ya aikata kenan, dukan matar aurensa.

Ya mika hannun yana fadin "bani yaron, kai tsaye ta ce "idan kai ka haifar min, ba sai ka 'kwata ba".

Ya yi kanta yana fadin "Me kika sha ne? Bari na sauke miki iskancin da kike fama da shi".

Ga mamakinsa ko motsi ba ta yi ba, sa'banin da, idan ya mata irin haka take kwasa a guje ta 'buya.

Ya isa kusa da ita ya kama kafadunta ya girgiza da karfi har sai da Jawad ya motsa, ya ce " fada min me yake faruwa, me na miki har ya shafi wannan yaron da bai san komai ba?".

Tsaki ta ja, tare da fizgewa, ta koma gefe tana sake 'daure goyonta sosai.

" What! Ni Kika yiwa tsaki Sa'adatu? abin da kinfi kowa sanin na tsani a mini?"

Ai kuwa ta sake jan wani fiye da na farko, sannan tace " ka kashe ni! an maka tsaki Mukhtar".

Wani irin shock ya kama shi, a farko da tace Mk gatsal mamaki ta bashi, amma a yanzu da ta ambaci cikakken sunan sai ya gane ashe Mk din a mutunce ta fa'da.

" Allah ya tsare ni da kisan kai, duk bala'in da kike nufi na da shi, in sha Allah ba zai same ni ba".

"Tunda abin har ya kaimu ga haka, to shikenan! ki yi harkar ki na yi tawa, sauko shi na bashi maganin, sai ki mayar da shi".

"Baka ji mai nace tun farko ba? ka 'kwata' a shirye nake da mu karya yaron nan! idan har ni na tsugunna na haife shi wallahi ba zai sha wannan maganin ba".

"Ya zuba mata ido, yana jin haushin ta na samu gurin zama a zuciyarsa, ya ce "idan na siyo masa wasu zai Sha?"

"Idan na tabbatar da sahihancin su ba".

Ya dauki ledar maganin ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba".

Bai wani jima ba, ya dawo da su, a wata ledar mai tambarin lamco pharmacy.

Ya mika mata, tare da cewa "gashi" ya juya ya fice.

Ta dudduba ta tarar da su dinne, illah ledar da ya canja, ta yi 'kwafa ta dankwarar da su.

Ana idar da Isha ya dawo, ya tarar da maganinsa akan kujera ita kuma ta shige 'daki ta rufe kofar, Jawad sai kuka yake yi.

Ya duba maganin ya tabbatar ba'a bashi ba, ya hau dukan kofar, amma banda kukan yaron ba ya jin komai.

Ya kirata ya fi sau hamsin amma tamkar bata gidan.

Ya hassalo sosai ya ce "wallahi idan yaron nan ya mutu, ke kika kashe shi, da hannuna zan mika ki wurin hukuma".

Sai lokacin ta ce "yi sauri kar 'kuda ya riga ka, wato ka maida ni bagidajiya, ka fita da magani kamar gaske, ka sake dawo min dashi, idona tar yake, bazan bashi ba".

A fili ya dinga fadin "Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un".

Ya fice zuwa dakinsa, yana karfafawa kansa guiwar ya rabu da ita, ai ta fishi son yaron.

Karfe shadayan dare ya dinga jin kukan yaron, da farko ya yi biris, amma da ya dinga jin 'ka'karinsa baisan yadda akayi ba sai ganin kansa ya yi a jikin kofar dakin Sa'adah yana bugawa, yana cewa "ki dubi girman Allah ki bude min kofar nan, komai na yi miki, na yarda kimin komai, amma banda yaron nan, ki ji tausayinsa, ki ji tsoron hakkinsa".

Har ya gama bilayinsa bata tanka ba, tana jin ta shirya faruwar komai ciki har da rabuwarsu.

Cikin ikon Allah, sai Jawad ya sami barci adalilin ta bashi tea, ta bashi maganin zazzabin sa da yake da shi.

Da asuba kukan Jawad ya sake tayar da hankalin Mk, ya rasa inda zai tsoma ransa, a take ya kira Hajiyar Bichi a waya, bai fa'da mata komai ba, ya ce dai kwana suka yi Jawad bai yi barci ba.

Ba bata lokaci, ta taho,har da garin kunun ko zai dinga sha, tare suka shiga falon, ya dinga kiran Sa'adah amma ta 'ki budewa, sai da taji muryar Hajiya tana cewa"Sa'a, menene yake faruwa ne?"

Da sauri ta bude 'kofar, ta fito idonta, yayi luhu luhu, yayi ja tsabar kuka.

Ta mi'ka mata Jawad ta zauna a gefe tana kuka tamkar wadda aka yi wa mutuwa.

Hajiya ta kalleta, taga ta fita a hayyacinta, ta rame farat daya, ta maida kallonta ga Mk taga shima a firgice yake.

Tace ciwon Jawad ne ya susuta ku haka, ko kuwa wata matsalar ce?"

Ya dauko maganin ya mi'ka ma Hajiya ya ce "Dan Allah ki bashi maganin nan", ta karba, ai kuwa Sa'adah ta saka uban kuka tana cewa "Kar ki bashi Hajiya".

Hajiya ta rasa maganar wa zata dauka a tsakanin su, ta dubi Sa'adah tace "Yi shirunki bazan ba shi ba, fada min me ya faru?"

Ta kasa magana sai kukan da take yi mai dauke da shesshekar ajiyar zuciya.

Ganin hakan yasa Hajiya ta rufe Mk da fa'da, ta inda ta shiga, ba tanan take fita ba, tana jaddadawa laifinsa ne, tunda Sa'a ba me fitina bace.

Ya yi shiru ya dauki laifin da bai yi ba.
da lallashi, Hajiya ta samu Sa'adah ta fada mata dalilin da bata son maganin alhalin ba expired suka yi ba.

Da rawar murya ta ce " Budurwarsa ce ta siyi maganin, akan idona suka yi zance ta siya ta bayar".
Ta karasa cikin gunjin kuka.

Dariya abin ya bawa Hajiya, amma sai ta dake, ta dinga salati tana fadin "kice cin fuska ya miki? banga laifin ki ba, dole ki guji magani, ko nice haka zan yi".

Shi dai Mk ya zama tamkar gunki, yana kallon shari'ar son rai a wurin Hajiya.

Ba zato Hajiya ta ce yaje ya siyo wasu maganin.

Ya ce " Bafa su bane, tunda take wannan bala'in na zubar da su, na siyo masa wasu, amma ta "ki bashi"

Da rawar murya ta ce "Billahillazi, baka canjo wasu ba, duk abin da ya fito ta hannunta, na tsane shi, zan kuma gane".

Jin haka yasa Hajiya fadin "Bar Wannan gadddamar je ka siyo wasu a bashi ya dan sami sauki"

Bai q musa ba, ya mike, ya dauki ledar maganin, ya fita.

Sai da ya fita Hajiya ta dinga mata nasiha, tare da cewa "ki rage nuna masa kishinki a fili, sai ya samu dalilin da zai dinga musguna miki".

Ta kalleta tace "tunda da wuta jona ruwan zafi kuyi wanka".

Ta mike ta cika buta ta jona, mintina kalilan ta kashe kanta, ta juye, ta sake maida wani, kafin ta fito, Hajiya ta wanki Jawad a bandakin tsakar gida.

Ta dama musu kunu, ta juye a flask din shayi, ta zubawa Jawad a kofi, ta bashi, ya shanye tas har da kari, ta tabbatar shima har da yunwa ta sake gigita shi.

Sa'adah ta fito sanye da riga da zani na atamfa, dinkin ya zauna sosai, mussaman da bata cika daura zani ba.

Ta mikawa Hajiya kayansa, sai da ya koshi ta koge masa baki sannan ta saka masa kaya, dai dai lokacin kuma, Mk ya dawo dauke da magungunan, leda biyu, ya mikawa Hajiya, sai da Sa'adah taga na wurin Farida, ga kuma wadda ya sake siyowa, sannan ta saki ranta, a ransa fadi yake masifaffiya kawai.

Take Hajiya ta bude ta bashi, ta shafa masa na shafawa, barci ya dauke shi mai nauyi.

Sosai Hajiya ta musu fada, kuma duk na Mk yafi yawa, jan kunne 'daya, ta yiwa Sa'adah, kar ta sake saka Jawad a cikin fa'dansu, ta ki cin abinci, shi akan mai zata hana shi?

Ta cika kofi, da kunu ta mika wa Sa'adah tace "Shanye ki bani kofin".

Ta karba, ta fara sha, ya mata dadi sai kamshin kayan yaji yake yi.

Shi dai Mk yana kallon ikon Allah, anbawa Jawad, da Sa'a, shi ko oho.

Sai da Sa'adah ta shanye sannan Hajiya ta mike ta ce "zan tafi nasan ki da jin magana, na kashe wannan magana kar a kuma tada ta"

Da sauri ta amsa da "in sha Allah ta wuce".

"Na gode Miki Sa'a, Allah ya miki albarka".

Sa'adah ta amsa da "Ameen Allah ya kara girma" ta tashi tana mata rakiya hanyar waje.

Tare suka fita da Mk zai kaita, a hanya tana sake masa fa'dan, lallai ya kiyayi zungurar Sa'a, ta dora da cewa

"Kana ganin irin yadda take mutunta ni, tana haba haba da yan'uwanka, iyayenta mutanan kirki, lallai ba zamu shirya da kai ba, idan kace zaka wulakanta ta, mussaman ma akan wacce bata zo hannun ka ba".

Har ya kaita gida, kashedi take masa iri iri.

Da za ta sauka ya ce "kin basu kunu, amma Ni baki bani ba".

"Ina sane, kai Sa'a ce mai ba ka".

Murmushi ya yi, tare da cewa "Hajiya kar kisa na fara kishin yarinyar nan, naga tana neman zarta ni a gunki".

Ta yi murmushi tace " maza ka juya ka sake rarrashin ta, ka tsaya a hanya ka siya musu dan wani abin, kunu kadai bazai ri'ke ta ba, ta tara yunwa".

Haka kuwa, ya biyo ta titin Hausawa bawo road ya siyi wainar shinkafa da ake yi mai dadin gaske, a falo ya tarar da ita, tana zaune tana kallo.

Bata dago ta kalle shi ba, ta amsa sallamar sa, daga haka bata kara magana ba.

Ya tsaya ya ce "Ba ki mini sannu da zuwa ba fa".

Ba tare da ta kalleshi ba, ta ce "inace ka ce kowa ya yi harkarsa?"

"Na fa'da! amma dai Hajiya ta kashe maganar, ta ce kar a kuma tada ta".

"Ita maganar maganin Jawad ta kashe".

Ya zauna, yana cewa "ga waina na siyo miki, tashi ki zubo mana".

Kanta a kasa ta ce" ci abinka".

Ya kai kicin ya adana, ya zubo wadda zai iya cinyewa, tare da kunu a kofi, yaso ya shiga dakinsa, sai kuma yafi zumudin zama kusa da ita.

Ya zauna yana fadin "dan Allah sauko ki taya ni ci".

"Ba zan sake cin abinci da kai ba, tunda muka yi aure, baka taba kaini restaurant munci abinci ba, amma ka dauki wacce kake so kun je! ba ruwana da sabgarka".

Ta fa'da hawaye na balle mata, ya yi shiru, yana jin sabon tashin hankali, ya rasa da bakin da zai kare kansa.

Ya yi shiru, ya kasa cin abinci, ko kaffara ba zai yi ba, su Safina ne suka kawo mata wannan labarin.

"Ki yi hakuri kin ji Sa'adan Uncle".

Kamar ya watsa mata garwashi, ta zunkudo ta ce " ta Ina ka zama kawuna?"
Kai ba 'kanin Baffa bane, bare na Inna, daga jiya ba zaka sake jin bakina ya kiraka da Uncle ba, ita dai da kuka hada dangi, sai tayi ta fa'da na bar mata"

"Ashe lokacin da kace min dole kayi kishin mace, idan ka ganta a gaban motar wani da ba Muharraminta ba, 'karya ka fada tsagwaronta? To ita mai kuka hada daka dauketa a gaban motarka?"

Kansa ya kulle, ya kalleta ya ce "Na yarda ban kyauta ba, ki yi hakuri, ki bani wata damar, ko banci albarkacin komai a gunki ba, naci albarka cin mahaifiyata da tazo ta baki ha'kuri, ta kashe maganar".

Jikinta ya yi sanyi, ta ce shikenan na ha'kura".
Da'di ya kama shi, ya matsar da kwanon abincin kusa da ita, ya ce to sauko muci".

Ta girgiza kai, "Na hakura, amma ba zanci da kai ba".

Ya tura mata, "to ci wannan, bari na zubo wani," ya mike ya fita da sauri.

Cikin sa'a ranar bashi da lakca sai 'karfe daya, dan haka, bai fita ko ina ba, yan tare da ita, yana ta kokarin wanke mata zuciya, shi da kansa ya tabbatar a duniya ba abin da yake so sama da Sa'adah da 'danta, idan aka cire Hajiya.

Sai dai duk nacinsa bata yarda da shi ba, kan dole ya 'kyale ta.

Kwana biyu tana mai yawo da hankali, kafin ta ha'kura ta sallama masa kanta, cikin rawar jiki yake komai, yana ayyana distance fa yana da amfani, domin ji yayi ta dawo masa sabuwa.

Yana samun kudi kuwa, ya dauke su ita da Jawad suka je restaurant din Royal Tropicana suka ci abinci, suka yi hotuna, irin wadda ake wankewa a take, take & wash, suka zarce country mall, ta zabi abin da take so.
A hanya ya ce "shikenan yanzu na dawo Uncle?"

"Hmm! magana ta wuce ka daina dawo mini da ita".

Ya shagwabe fuska ya ce " idan har da gaske ta wuce, then called me Uncle".
Ta fara dariya, tana cewa "ashe son girma ne da kai ban fahimta ba?"

Shima ya taya ta dariyar sannan yace "tsakanin ki da Allah! Idan nace Miki Sa'adatu ba kya jin wani iri? ke da kike kanwata nasan kina jin ba dadi, bare ni ki gatsa sunana gatsal"

"Amma ai tun ranar ban sake fada ba".

"Eh baki sake ba, sai dai kimin ta kurame, kiyi maganar ki ba tare da kin kama sunana ba".

"Nifa Wallahi na tsani, waccan sunan da kake kulafacin sai na cigaba da kiranka da shi".

"To shikenan zabo min wani, mai sweet, kika rufe ido kika cemin wai baki hada dangi da Ni ba ko?"

Ta ce "eh mana ai ba karya na fada ba".

"Ni Malamin ki, Ni Mijin ki,Ni Baban danki, duk wannan ha'din kin raina shi?".

Ta tura baki gaba, ta ce "shikenan, ka zabi sunan da zan fada maka a cikin wadannan,Malam, Miji, ko Uban 'da"

Dariya ta kwace masa sosai, cikin dariyar ya ce, "ke yanzu sai ki dinga cemin Uban 'da?"







*Surayya Dahiru*
✍🏼✍🏼✍🏼
26/03.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺


*Lafazi writers*.


*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*


*Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*.


*GODIYA*
*Ina matu'kar godiya ga wadanda suka yi mini addu'o'in samun lafiya ga warwarewar lamura, tunda ga kan masu kira ta waya, da masu text, da masu yi mini ta dandalin WhatsApp, dukkanku na gode madallah, ubangiji ya fini yabawa*.




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login