Showing 114001 words to 117000 words out of 162658 words
na so neee da k'auna, aiki na kiran ki ne. Dana fad'a kiji, ki ba ni agaji, in dai na rangajiii ki d'an yi tsokaci. Ki ba ni ma'ajih, ba zancan nagaji, ki kauda k'uduji, a so b yaaji. Labarin zuciyaaah, ni za ki tambaya, abinda nakkajiiii ya zarce duniyaaah. Idan na waiwaya, ko ko na sunkuya, amsar guda na ke ji kin zaman habibiya. Da sonki na banu, a kan ki na sanu, abunda baki so nai nai tai in bar shi na hanu, ke da sirri zai ganu, ki damk'am a hannu, shi zai fi min yau sauk'i in bar maganganu. Ki zo ki daf dani, so zai min lahani, ki tausayawa ruhina ki ce ki nai da niiii. Ba na ji ban gani, to wa zai kula da ni, I Dan ya zamma sab'aninki to a bar ni ni. Ina k'ulafuci, sai kin ci za ni ci, har wanda za na cin ki ci tun da ba bu rikkici. Ya za ai in burge wacce na ke so da k'auna, ya zaaa'ayi? Kalamai na sun kad'anta fahimce ni sannan ba hanyaaa. Kalamainaah sun kad'anta fahimce ni sannan baaa hanyaah. Ina so ta soni ni ba guru ba bu laya, babu d'age babu k'arya, ni bani san riyah. Ba dan kwalliya ba kuma ba dan dukiya ba, ba dan zantuka ba kullum tai min maraba. Ina son ki , ina son ki , ina sonki. Ina son ki so na gaske ba yaudara ba. Ina son ki, ina son ki, ina son kiiii. Ina son ki so na gaske ba yaudara baaaaah*_π»
Ya k'arisa ina son ki so na gaske ba yaudara ba ta re da kashe wayan ya na kallon idanuwanta.
"Ina son ka ni ma yousouf ba da yaudara ba". Fad'in Binty.
"Naji dad'i sosai da na saki cikin nishad'i. Wannan videon shi ne zai zama abun kallo na through out yau idan na koma gida".
"To ni ma ka tura min". Fad'in Binty.
"Ina son ka, zamu kasance ta re har abada". Fad'in Binty.
"Wannan maganar mai dad'i da ki ka min ma kawai ya ishe ni. Shiva xender in tura miki, ko kuma zan tura mi ki ta WhatsApp". Fad'in Yousouf.
"OK to shikenan, raka ni gate, ka min sister ta fara jera min kiran da zai kashe min waya yanzu". Fad'in Binty.
"You wish is my command my lady". Fad'in Yousouf ta re da yin gaba ta na biye da shi a baya.
*________________*
............Abu kamar wasa, sai da su Suhail su ka washi wata tara a India ka min Suhail ya samu sauk'i cikin hukuncin ubangiji, kuma ya yi wa kan sa alk'awarin da Binty zai fara gwada lafiyar mazantakarsa.
Ya yin da a gefe guda Hajiya Mansura ta yi bala'in rama saboda sawa zuciyarta soyayya da sha'awarta cikin zuciyarta ta re da k'osawa su dawo Nigeria domin nufar da k'udirinta.
Yau dai su ka duro k'asar, Julaibib bai yi jinkiri ba, har d'akin uwarsa ya tadda sa ta re da shimfid'a masa concrete warning akan y'an aikin gida da kuma Binty wacce ya yi masa alk'awarin ko yatsarsa ya yi k'ok'arin kai wa jikinta, wannan karan mazantakar na shi gaba d'aya zai cire masa. Kuma a gaban Hajiya Mansura ya fad'i haka wanda ya kusa saka ta fitsari a tsayan da ta ke yi saboda hango wani b'oyayyan sirri a idanuwan Julaibib a game da Binty wacce ta d'auki d'amarar mai da ita abokiyar shaid'ancin ta.
"Lallai akwai babban bala'in da ke tunkaro gidan nan soon akan duk wanda ke k'ok'arin shiga tsakani na da buri na". Fad'in Hajiya Mansura cikin zuciyarta.
*BAYAN SATI GUDA*
............Wayar Binty ce ta yi k'ara alamar shigowar kira. Kallon screen d'in wayar ta yi. Gabanta ne ya buga da mugun k'arfi har sai da ta dafe k'irjin na ta ganin sunan Kandala b'aro-b'aro a jikin screen d'in.
Hannunta na rawa ta d'aga wayar ta re da karawakarawa a kunnanta ba ta re da ta yi ko tari ba.
"Yanzu nan ki je d'akin Hajiya Mansura, kuma ka da ki saki wani ya gan ki. Ina fatan kuma ba ki manta da sharud'd'an da na karanto miki ba idan ki ka sab'a?". Fad'in Kandala.
"Ban man ta ba". Fad'in Binty ba ki na rawa.
"Madallah. Sai ki hanzarta". Fad'in Kandala ta re da yanke wayar.
*PAID BOOK 08128755583*
*YAN ZU BA ZA KU RIK'A GANIN UPDATE DA SASSAFE BA SABODA AN KO MA SCHOOL KUMA NI D'IN TEACHER CE. DOLE SAI NA DAWO DAGA SCHOOL SANNA ZAN MA KU TYPING NAGODE*
: πΉ *61-62*πΉ
ππ»π₯π₯ _Ku na inahh nee?π£οΈ to maza ku firfito ka da wannan garab'asar ta wuce ku. Shin ko kun san Mrs Abubakar ta k'ara zuwan maku da zuma gangariya mai jawo maki martaba da soyayya a wajan mijin ki?_
_Ta shi maza ki karb'o kud'in adashen ki da ki ke zubi wajan Ladidi domin ki siya ke ma ki zama sarauniya_ππ»ππ»ππ»
_Gangarar gangariyar zuma mai k'ara kuzari da ni'ima ta re da k'ara miki sha'awa. Ta na sa ka wani dad'i da d'and'ano na musamman ta re da saka mai gida sambatu da zumar miyau π da gigicewa. Wannan zuma guarantee ne sai kin gwada na tabbata sai kin godewa Hassana (Mrs Abubakar). Haka kazalika ina macen da ke k'orafi akan miji bai kai mata? To kwantar da hankalin ki Mrs Abubakar ta kawo miki waraka da izinin Allah domin idan ki ka yi amfani da wannan zuma mijin ki zai jima bai yi inzali ba kuma ya na k'ara ruwan maniyyi da lafiya a jikin mai gida_
_Maza garzaya ki nai mi Mrs Abubakar a lambar wayarta kamar haka_
_+234 814 193 4442_
_Sayan nagari, mai da kud'i gida_π€Έπ»ββοΈπ€Έπ»ββοΈππ»ππ»π₯
...............Gaba d'aya hankalin Binty ya gama tashi musamman da ta ji part d'in Hajiya Mansura za ta. Tunanin ta dunga yi wani sirri ne za su yi da Hajiyan da har za ta kafa mata wad'annan sharud'd'a haka.
Da kyar ta iya jan k'afafuwanta ta sauko daga sama. Babu kowa a parlourn, hakan ya mata dad'i. Cikin sauri ta fita daga part d'in ta yi part d'in Hajiya Mansura ta na waige-waige.
Murd'a handle d'in k'ofar ta yi gabanta na dukan tara-tara don ba ta san abunda za ta taras ba.
Ba bu kowa a parlour, kai tsaye stairs d'in ta hau ta isa k'ofar d'akin Hajiya Mansura zuciyara na tsananta bugawa.
Kwankwasawa ta yi, da ga ciki Hajiya Mansura ta ce ta shigo.
Tura k'ofar ta yi ta re da shiga zuciyarta na bugawa.
Tsaye ta sa mu Hajiya Mansura hannunta biyu goye a bayanta ta kuma zuba mata idanuwa.
"Ina wuni Hajiya". Fad'in Binty bakinta na wani irin rawa.
Wani malalacin murmushi Hajiya Mansura ta yi ta re da matsawa kusa da Binty ta kamo kafad'unta ta re da zaunar da ita a bakin gado ka na ta duk'a a gabanta ta na kallon tun daga kanta har k'afafunta ka na ta ce,
"Binty ki kwantar da hankalin ki, ni ba cutar da ke ba zan yi ba. Na san Kandala ta riga da ta miki duk wani bayani so akan rashin bin umarni na, kuma wallahi har cikin zuciya idan har ki ka sab'a umarni na, zan kashe su kuma dole ki yi abunda na ke so don na san ke wacece. Ke ba komai ba ce face *MARA GATA* wacce uwarta ta yi cikinta ta yasar da ita a kan bola. Kin ga kenan b'atar da ke ba zai min wahala ba don na buga da wad'and'a su ke da *GA TA* ma kuma ni na ci riba. Don haka kawai ko ba da kai ki ceci rayuwar masoyanki na asali idan har za ki masu halacci". Ta k'arisa maganar ta na wani shu'umin murmushi.
Jikin Binty har tsuma ya ke tsabar tsoratar da ta yi, hawaye har ya wanke idanunta, cikin kuka ta ce,
"Dan Allah ki fad'amin abunda ki ke so min in miki. Dan Allah kar ki cutar da Anna ta".
Mik'ewa Hajiya Mansura ta yi ta re da k'arisawa wajan k'ofa ta murza key ka na ta dawo inda Binty ta ke zaune ta cire hulan da ke kanta kasancewar doguwar riga ce mai hula a jikinta. Dogon gashin kanta ya zubo har bayanta.
Hannu ta kai ta shafo wuyanta zuwa bakinta, ka na ta mata kiss a goshi.
Mamaki ya kashe Binty da ke zaune zuciyarta na k'aryata abunda kwakwalwarta na hasaso mata.
Doguwar rigar atampar da ke jikinta ta zame kasancewar ta zuge zip rigar sai ya fad'o k'asa ta kasance haihuwar uwarta don ko brezia da pant ba bu.
A gigice Binty ta mik'e ta re da runtse idanunwanta ta na maimaita,
"Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un, Astagfurullah, Allahumma arji'ini fi musibati". Jikinta rawa ya ke yi sosai ta na mai dana sanin zuwan da ta.
Dariya Hajiya Mansura ta fashe da ita ta re da kwanciya a kan gado ta yi pillow da hannayanta ta na kallon Binty da ke tsaye idanuwanta rufe kuma jikinta na wani irin rawa.
"Hmmm! Yarinya ka da ki wasa da wuta za ta k'ona ki. Wannan shi ne abunda na ke so mu ruk'a yi ni da ke. Zan aure ki in kula da ke, zan mai da ke sarauniya. Ki amince da wannan harka za ki k'aru kuma za ki samu dukiya mai tarin yawa. Ba zan tab'a bari ko yatsa mace ko namiji su d'aga mi ki ba. Kar ki da mu, ko na aure ki, zan bar ki ki auri namiji don gudun zargin mutane, ni kai na abunda ya sa na yi auran kenan ba wai don namiji na gaba na ba, don namiji babu abunda zai iya min. Amma for now ba zan takuraki ki aminta dole ba, sai dai za'a fara zaman makoki a gidan nan, don tabbas sai na kashe su, kuma Na'ima ita ce first target d'ina, daga ita sai Fanan sai Fu'ad, wani ma na nan shigowa wanda mutuwarki shi ne ta ki". Hajiya Mansura ta k'arisa maganar ta re da wani shu'umin dariya da ihu-ihu.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Hajiya ki ji tsoran Allah. Wannan abu da ki ke so mu aikata ba k'aramin bala'i da masifa ba ne. Don darajar Allah ki yi hak'uri ki janye wannan maganar na miki alk'awarin rufa miki asiri babu wanda zai ji har gaban abada. Kuma ke ma ki tuba don ki na cikin bala'i da tsinuwar ubangiji kuma wallahi ki ka mutu a haka wuta za ki ba makawa". Fad'in Binty still idanuwanta a rufe don ba ta k'aunar sa ke arba da tsiraicin wacce ta isa ta haifi irinta guda biyar.
"Ke! Ba wa'azi na kira ki min ba, idan wa'azi ne, wajan ki ka zo don ni mahaifina ma malami ne. Saboda haka wa'azin ki ba zai yi tasiri a nan ba. Kuma dole ki yarda ki aure ni mu rik'a biyawa junan mu buk'ata". Fad'in Hajiya Mansura a tsawace.
"Wallahi ba zan yi wannan masifa da bala'i ba. Ba zan aikata wannan sab'on ba, kuma wallahi babu abunda ki ka isa ki yi wa Anna don mu na tare da ubangiji kuma zan kai k'aran ki wajan sa. Kuma na tabbata idan na amince da buk'atarki don in tseratar da Allah daga abunda ki ka shirya masu, wallahi Anna ba za ta tab'a yafe min ba don wannan ba tarbiyanta ba ne, no wonder d'an ki ya kasance kamar bunsuru, a she a nono ya tsotsa. Ina sha Allah ke da d'an ki ba za ku tab'a samun abunda ku ke so a waje na ba". Fad'in Binty ta re da nufar k'ofa.
"Yarinya kenan, da k'afafuwarki za ki zo ki na rok'ona lokacin da lokaci ya riga ya k'ure miki don tabbas Anna sai ta bak'unci lahira".
Cikin sauri Binty ta murd'a key d'in ta fice saboda lokacin da Hajiya Mansura ta kulle ba ta zare key d'in ba.
Sai da ta goge hawayanta sosai ka na ta fito daga part d'in, amma duk da haka duk wanda ya ganta zai ga ne ta na cikin firgici.
Ta shawo kwana su ka yi kicib'is da Julaibib shi kuma zai wuce part d'in sa don yin wanka zai fita an kira shi.
Kallonta ya yi from head to toes, ita kuwa zuciyarta ce ta tsananta bugu har wanda ke kusa da ita ya na iya jiyo bugun zuciyarta.
Hannunta ya damk'a ta re da nufar part d'in sa da ita ran shi a b'ace.
Sai da ya bud'e k'ofar da d'aya hannunsa ka na ya tura ta ciki ya shigo ciki ka na ya mai da k'ofar ya rufe ta re da k'ura mata idanuwa ko kyaftawa ba ya yi.
Ita kuwa kallo d'aya ta yi masa ta sunkuyar da kanta ta saboda yadda zuciyarta ke bugawa kuma ba za ta iya jurar kallon cikin idanuwansa ba.
"Binty asara ki ke so ki min?". Fad'in Julaibib in a very cool voice ya na kuma kallonta.
Saurin d'agowa Binty ta yi ta kalle sa ta na mamakin asarar mai kuma za ta masa.
"Daga ina kike? D'akin Suhail ko?". Ya sa ke fad'i.
Girgiza kai ta soma yi tuni har hawaye sun wanke mata idanuwa ta re da fad'in,
"Wallahi yaya Bibi ban je d'akin shi ba. Ni tun da su ka dawo ma ban gan shi ba. Yaya mai zai kai ni d'akinsa kuma? Wallahi ba daga can na ke ba". Fad'in Binty ta na hawaye.
"To daga ina kike? Kuma mai ya ke damun ki? Dole akwai abunda ya b'ata ran ki don naga mode d'in ki alamu ya nuna ki na cikin firgici. Kin san I study psychology, zan iya karantar ki tsaf". Fad'in Julaibib.
Tsoro ne ya cika Binty, kuwa ba ta tunanin za ta iya fad'a masa abunda ke faruwa sam. Kallon sa ta yi for one second ka na ta ce,
"Ina jin ba dad'i ne na rashin fara school d'in mu bayan Fanan ta samu admission amma ta k'i fara makaranta saboda ni ban samu ba. Kuma na yi da ita ta fara idan ya so next year ni kuma sai in fara in sha Allah amma ta k'i. Kuma gashi gaba d'aya y'an set d'in mu duk su na school".
Kallonta ya ke yi har na kusan minti biyu ka na ya k'ara rage muryansa ta re da fad'in,
"OK to ki kwantar da hankalin ki kin ji? Ban son ku na damuwa kin san ni doctor ne kuma damuwa na saka ciwo a zuciya, idan har na bar ki kina yawan tunanin Anna ba za ta ji dad'i ba za ta ce ni yayan banza ne, kuma kin ga dole in tashi tsaye in kula da ku ka da wani abu ya samu lafiyar ku, ko ba haka ba?".
Sosai mamaki ya ka ma Binty, don ba ta tab'a tunanin yaya Bibi ya iya rarrashi haka ba, saboda ta san shi mutum mara son magana da hayaniya ga zuciya, kuma bai cika sake mata fuska ba.
"Ko ba haka ba?". Julaibib ya sa ke fad'a.
Murmushi ta yi ko in ce yak'e ta re da fad'in,