Showing 102001 words to 105000 words out of 162658 words

Chapter 35 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42913

ita Binty za ta iya cewa wannan shine karonta na biyu, lokacin da zo garin Abuja da kuma yau, Fanan d'in ma dai haka ne, sau d'aya ta tab'a zuwa Gombe sai kuma yau, gomben ma ba za ta iya cewa ga yanayin nisan ba don tun ta na yarinya ne.
Sai gab da magriba su ka shigo k'auyan Saminaka. Yara sai bin motar su ke yi da gudu. Hatta manyan ma bin motar su ke yi da idanuwa.
Kandala ce ta soma fitowa, aikuwa wad'and'a su ka san ta su ka yi mata caaaa su na mata oyoyo. Matan gida kuwa duk an firfito waje, wasu ma daga su sai d'aurin kirji. Wasu kuma yara ne d'auke a hannunsu su na shan nono amma haka su ka fito waje su na lek'e.












*KO YA ZA'A KWASHE A K'AUYAN SAMINAKA?*


*PAID BOOK 08128755586*
🌹 *55-56*🌹
.............Binty da Fanan su ma su ka fito sai bin mutanan su ke yi da idanuwa kamar yarda su ma mutanan su ke bin su da kallo.
Kandala ce ta dubi driver ba yan ya gama firfito masu da duka kayan su ta ce,
"Bawan Allah amma kwana nan za ka yi ko? Na ga dare ya yi kuma tafiyan dare akwai damuwa musamman yadda k'asar ba tsaro yanzu ga kuma mutanan nan da su ke garkuwa da mutane". Kandala ta fad'a kamar mutuniyar arziki.
"In sha Allah, Allah zai tsare ni kamar yadda mu ka zo lafiya, zan koma gida lafiya. Yanzun nan zan juya". Fad'in driver ya na rufe both d'in mota.
Karyar da wuya Kandala ta yi ta re da fad'in,
"To shikenan, Allah ya tsare ya kai ka lafiya. Amma wallahi ni ban son tafiyar daran nan. Ko fa abinci ba ka ci ba".
"Kar ki damu Hajiya" Fad'in driver ta re da zagayawa ya shiga mazaunin sa ya yi reverse ya bar k'auyan.
Kandala ajiyar zuciya ta sauke ta re da umartan yaran nan da su ka zagaye su akan su d'auki jakan kunan su Binty su shiga da shi cikin gida.
Wani irin babban gida ne mai shashe-shashe. Ka na ganin yanayin gidan ka san gida ne na mutune irin gidan gandun nan.
Haka gaba d'aya yaron su ka bi yo su Binty wanda su ka masu lak'abi da bak'in Larabawa har cikin gida.
Wata tsohuwa ce da ke zaune bi sa kujera y'ar tsuguno ta d'ago da kan ta kasancewar bakace ta ke yi don tuni ta d'aura sauwa.
"Kai kai! Gidan uban wa za ku haka da ku ka shigo min gida riii kamar kun rako amarya? Maza ku fice ku ban......." Ta kasa k'arisa maganar saboda ido hud'u da ta yi da Kandala.
"Jakar uban can! B'atan kai ki ka yi ne, ko kuwa gizo ki ke min ni shatu d'iyar Duna?".
"Goggo Shatu ni ce, ba gizo ki ke gani ba. D'iyar y'ar uwar ki ce ta dawo gare ki". Fad'in Kandala.
"Ke dalla tafi can ki baiwa mutane waje gantalalla kawai. Uban wa za ki yi wa bariki? To kar na ke kallon ki gulmamma, wai wani d'iyar y'ar uwar ki ce ta dawo gare ki. To maza tun muna mu biyu ki fice daga gidan nan tun kamin in miki yekuwa jama'a billahi". Fad'in Goggo Shatu.
Hayaniyar Goggo Shatu ce ta fito da kafatanin mutanan gida yaransu da manyan su don baiwa ido abinci.
Bagazan-bagazan ya shigo cikin gida. Alwala ya ke yi wa ni yaro ya tafi da gudu ya shaida masa Baaba Kandala ta zo daga birni.
Su na had'a idanu da Kandala ya fashe da kuka har da face majina ya na fad'in,
"Kandala ke ce? Ke ni ke gani yau da idanuwa na? Don Allah ki kai ni wajan d'iyar Hashimu in gan ta ko zan samu sauk'i a zuciyata. Allah sarki Hashimu Allah ya ji'kan ka". Fad'in Buba ya na k'ara face majina.
"Ga d'iyar Hashimu nan a gaban ka yau na kawo maku ita". Fad'in Kandala ta na nuna Binty da gaba d'aya mamaki da takaici sun cika ta. Kawai ikon Allah ta ke kallo.
Fanan kuwa tausayi ne ya cika zuciyar ta da ta ga irin kukan da Buba ya ke yi ta re da rok'arwa Mahaifin Bintyn gafara.
Wajanta ya k'ara sa ta re da fad'in,
"Wayyiiyoo Allah! Yarinya ina kallon fuskan ki na ga Hashimu. Kamar ku d'aya kamar ya yi kaki kwarankwatsi. Allah dai ya ji'kan ka Hashimu. Ga y'arka nan kyakkyawa kamar uwarta Karime. Karime ba dai kyau ba duk k'auyan su ba kamar ta kwaran kwashi".
"Wai mi ka ke hwad'i ne haka Buba? D'iyar wacece na ji ka ke hid'i. Kamar sunan Hashimu na naji ka na hid'i ko ban jiya da kyau ba ne?".
"Kwaran kwashi hakannan na hid'i Goggo. Yau ga jikan yar ki a kusa da ke billahi". Fad'in Buba.
Mik'ewa Goggo Shatu ta yi ta na d'ingisawa har ta k'araso wajan da Binty ta ke tsaye ta na k'are mata kallo tun daga ka. Wani irin kuka ta fashe da shi ta re da fad'in,
"Allah na gode maka da ka hadd'a huskata da na d'iyat Hashimu. Kande ya akai ki ka kwatota wajan dangin mahaifiyar na ta?". Fad'in Goggo Shatu ta na kallon Kandala ta re da share kwallar fuskan ta da bakin zanen ta.
"Goggo wannan dogon bayani ne, ki ba ri mu nutsa tukun sai in miki bayani. Yanzu mun kwaso hanya ga yunwa da k'ishirwa. Ai duk wannan dad'ewar da na yi ban zo ba duk a kan ta ne billahi".
"Muje ciki kande. Allah dai ya miki albarka". Fad'in Goggo ta re da ka mo hannun Binty. Ita kuma Binty ta kamo na Fanan su ka nufi D'akin Goggon.
Cikin k'ank'anin lokaci har kwanuka sun cika a sasan Goggo kasancewar matan y'ay'an ta maza kaf a cikin gidan su ke zaune da iyalansu.
Goggo ta mak'ale Binty ku sa da ita wacce ita Sam ta kasa sakin jiki da ita don ta san sam babu wani alak'a ta jini da su ka had'a. Sai dai kwakwalwarta cike su ke da tambayoyin da ta kasa bawa kanta amsa game da Kandala da kuma Hashimu da ake alak'antawa da mahaifinta.
Sam Binty ta kasa sakin jiki ta ci abinci, Fanan kuwa ta ci dambu wanda ya mata dad'i sosai ga shi ya sha zogale da gyad'a ga yaji mai dad'i har da man k'uli Goggo Shatu ta tsiyaya mata cikin na sana'arta saboda dambun ya mata dad'in ci sosai.
Goggo Shatu ba ta samu damar keb'ewa da kandala ba domin ta mata bayanin yadda aka yi ta iya zuwa gari i gari har Bauchi ta taho da d'iyar Hashimu kuma dangin mahaifiyar ta su ka yadda su ka ba ta.
Sasa-sasa haka aka dunga bi da Binty da Fanan su na gaida mutane. Duk in da aka je za a ce mata wannan shine wane, ko kuma wannan ita ce goggo wance. Sai da aka karad'e kaf gidan da ita ka na su ka dawo d'akin Goggo a gajiye don har mak'ota sun fara shiga sai Binty ta ce masu su na son yin sallah kuma ana bin su azahar da la'asar kasancewar a hanya ta riske su.
Bayan sun idar da sallah ne su ka nai mi ruwan wanka domin sun saba wanka duk dare kamin su kwanta. Aikuwa nan da nan Goggo Shatu ta sa matar Buhari d'an ta na uku ta hura wuta ta saka masu ruwan wankan.
Sabrin d'in ce ta fara zuwa domin ta yi wanka. Da kyar ta iya yin wanka saboda yadda bayin ya ke. Ba wai kazanta ne a bayin ba, k'asa ne a k'asab ba flour, idan ta zuba ruwa sai kasan ya rik'a tab'a ta wanda hakan ke sa ta ke jin kyankyamin jikinta.
Binty ma dai haka ta k'ok'arta ta yi wankan ta dawo d'aki.
Kayan bacci ta saka ka na ta jawo wayarta domin yi wa Yousouf message kasancewar rabon da su yi magana tun su na gab da shigowa k'auyan Saminaka. Kuma a yanzu haka k'auyan da su ke ba network sai mutum ya fita ta wajan wani k'aton dutsi network d'in me dawowa.
Tsaki ta yi k'asa-k'asa saboda takaicin rashin network d'in da za ta hau WhatsApp ta yi charting da ruhinta ta samu natsuwa.
"Yaushe za mu koma gida ne?". Binty ta fad'a a kunnan Fanan.
"Ke yau fa mu ka zo har kin fara tambayar yaushe za mu koma gida". Fanan ta fad'a.
"Ni ban iya rayuwa ba network. Ba waya da Anna, ya barrister da kuma ruhi na Yousouf. Yanzu haka wallahi ji na na ke kamar a kan k'aya".
"Haka nan za ki yi hak'uri. Ai na ji Baaba Kandala ta na fad'in sai an hau wani dutse ake samun network. Gobe ba sai muje wajan ba. Na san Anna ita ma na can cikin damuwan ko mun sauka lafiya".
"Ke dai bari. Allah dai ya kai mu goben, da sassafe zan je wajan dutsin nan". Fad'in Binty.






*Washa gari*
****************
Kasancewar su Binty sun saba tashi da asuba, da asubar fari su ka ta shi da ciwon baya kasancewar a gadon kara su ka kwana. Abunda ya ba su mamaki gaba d'aya gidan sun ta shi sai kai wa da komowa su ke yi kasancewar kusan duka gidan kowa da sana'ar sa. Wasu kunu da k'osai, wasu masa, wasu d'an wake, wasu kuma alale. Shiyasa su ke tashi da safar assalatu su soma hada-hadan sana'ar su.
Ko kafin bakwai har kowacce ta fita da kayan sana'ar ta, kuma kamar jiya lokacin da su ka iso, haka ma yau aka cika su da abinci kala-kala. Duk mai sana'ar nan sai da ta aje kwana silver na abincin sana'arta.
Binty dai alale ta ci, Fanan kuma kasancewar ta na son d'an wake kuma ba ko da haushe Anna ke yi ba, shi ta ci, shi ma da ta ci, sai ta ji na Anna ya fi dad'i.
Wajajan k'arfe goma, Kandala ta saka su Binty a gaba ta na ta zaga dangi da ita. Duk in da su ka je, wasu har hawaye su ke yi, wasu kuma mamaki ne k'umshe a fuskokin su na canzawar d'iyar Hashimu zuwa baturiya duk da mahaifiyarta d'in fara ce amma a kashi d'ari na farin d'iyar tata kashi biyu ta ke da.
Sai bayan azahar su ka gama bulayin bin dangi. Daga nan kuma wani yaro ya raka su can kan dutse domin su kira gida.
Anna su ka fara kira a waya, sun kusa awa su na waya da ita. Fanan sai fad'a mata yanayin k'auyan ta ke yi cike da nisha'di.
Bayan sun gama waya da Anna ne su ka kira Barrister Fu'ad. Shi ma haka suka kwashi tsayin lokaci su na waya da shi ta re da fad'a masa yadda su ka yi missing d'in sa.
Binty na yanke wayar kasancewar da wayarta gaba d'aya aka yi kiran. Sak'onni ne su ka shigo wayar tata har guda sha d'aya kuma duk daga Yousouf ne ya na fad'a mata yadda hankalin shi ya ke a tashe saboda rashin samun ta a waya.
Ta na k'ok'arin kiran shi, kiran na shi ya shigo wayar. Murmushi ta yi ta re da picking call d'in.
Wa ni ajiyar zuciya ya sauke ta re da fad'in,
"Haba mai sona kin san yadda na damu kuwa da rashin jin ki a waya? Ina ki ka shige ne ba'a samun ki a waya?". Fad'in Yousouf.
"I'm sorry love, wallahi garin ne ba network sai an zo wajan wani dutsi ake samun network d'in kuma ban samu damar zuwa wajan ba sai yanzu saboda kai ni wajan dangi da aka yi ta yi tun safe".
Ajiyar zuciya ya sa ke saukewa ta re da fad'in,
"Mai sona ni dai zan biyo ki kawai".
Dariya ta yi mai d'an sauti ta re da fad'in,
"Haba Love ka kwantar da hankalin ka, ai saura kwana shidda mu dawo. Ke nan haka na nufin bayan mun yi aure ba za ka iya ba ri na na yi tafiyan wata d'aya ba kenan?".
Tari ne ya sark'e shi. Sai da ya gama sanna ya ce,
"Haba mai sona, kashe love d'in na ki za ki yi? Kin san Allah, tafiya idan ta wuce ta kwana biyu ba ki zuwanta".
Zaro idanuwa ta yi kamar ya na ganinta ta re da fad'in,
"Haba mana love. Kar ka yi min haka. Ni da na ke so duk bayan kwana biyu in rik'a zuwa gidan Anna in yi sati guda ka min in dawo gida".
Dariya ta ba shi, sai da ya dara ka na ya ce,
"Ai Anna ma ba za ta yadda ba. Ke idan ma ta yadda tu bak'i biyu za ta rik'a gani duk bayan kwana biyun nan".
"Suwa da wa kenan?". Fad'in Binty.
"Ni da ke mana".
Dariya sosai Binty ta yi ta re da fad'in,
"To ina za ka ri'ka kwana kenan? Gwara dai ni ina da d'aki na".
"To ni ma ai a d'akin na ki zan kwana". Fad'in Yousouf.
"Kai". Ta fad'a da sauri.
"Ke". Shi ma ya fad'a.
Dariya su ka kwashe da shi. Nan su ka cigaba da musayan kalaman soyayya.
Fanan da duk ta k'osa saboda ranar da ta kwallo ta na gasa ta, ita kuwa Binty da ta fad'a kogin soyayyan ko zafin ranar ba ta ji.
"Ke wallahi ki kashe wayar nan ko in wuce in bar ki kwarankwatsi".
Bushewa da dariya Binty ta yi saboda yadda Fanan ta furta kwarankwatsi kamar yadda ta ji Kawu Buba ya fad'a jiya wanda hakan ya kasance d'abi'ar y'an k'auyan.
"Dariyan mai ki ke yi haka mai sona?". Fad'in Yousouf.
"Zan ba ka labari idan mun dawo. Sai mun yi waya gobe. I love you". Ta na gama fad'in haka ta katse wayar baki d'aya saboda ta san idan shi ne bai k'i su kwana su na waya ba. Don wani lokaci a gida haka su ke yi sai su raba dare su na waya har kunnanta zafi ya ke mata. Sometimes a hands free ta ke saka wayar ta aje a gefe.

Saukowa su ka yi daga can saman dutsin rik'e da hannun juna.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login