Showing 96001 words to 99000 words out of 162658 words

Chapter 33 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42915

ci abinci, ke kad'ai ake jira a k'asa". Fad'in Annah.
"To Anna ga ni nan". Binty ta fad'a ta re da saukowa daga kan gadon ta bi bayan Anna da ta fita.
Gaba d'ayan su ne zaune akan dinning d'in. Yanzu ma Binty a kan kujeran da ta zauna d'azu ta zauna, ta na fuskantar ya Bibi.
Ganin ba bu abokin ya Bibi da ya Fu'ad ya ce ta re za su zo, kallon ya Fu'ad d'in ta yi ta re da masa nu ni da hannu alamar ina abokin na shi. D'aga mata kafad'a ya yi alamar oho ta re da jan zip a bakinsa ya kuma nu na mata ya Bibin alamar ta yi shuru.
Sai da su ka kammala cin abincin ka na Ya Bibi ya kalli Anna ta re da fad'in,
"Anna ba ki ganin ya kamata Zaid ya dawo kusa damu? Kin san fa rik'on d'a sai iyayansa".
Saurin d'agowa Binty ta yi ta re da zuba masa idanuwa saboda kalmar rik'on d'a sai iyayansa da ya furta.
Harara Anna ta ma ka masa ta re da fad'in,
"Ya fad'a maka ana kankaran naman jikinsa ne a can? To ba zai dawo ba d'in. Idan kuma kai ne ubansa, sai ka je ka d'auko sa a wajan mai martaba. Don Zaid ya bar hannun Dattijo ya na wajan uwar gidan mai martaba". Fad'in Anna. Kasancewar Zaid mai bi ma Fu'ad tun wajan yaye mahaifiyar Anna ta amshe shi, ita kuma uwar gidan mai martaba ta yi mata fin k'arfi ita ma ta amshe shi. Da Julaibib d'in ma su ka so amshewa.
"Allah ya huci zuciyar ki Anna, dama kawai yadda na ga duk kan mu zuri'ar ki muna cin abinci a waje d'aya, shiyasa shi ma na yi masa kwad'ayin haka". Fad'in Julaibib ta re da mik'ewa.
"Kai ma ka kusa dai na cin abincin ta re da mu a nan kuma nan kusa don kwanaki zan yanke maka ka fiddo matar aure". Fad'in Anna ta re da harararsa.
"Anna a gaba yara. Dan Allah ki dai na min maganar aure a gaban su kar su raina ni".
"Au na manta fa, kai ka yankewa k'asa cibi. (Kwafa) kar ka fiddo macan aure sai na baka mamaki nan kusa". Anna ta sake fad'i.
"Ku bar nan ko in karya k'afafuwan ku". Julaibib ya fad'a ya na zazzarowa su Binty idanuwan sa.
Aikuwa da sauri su ka bar wajan, Binty kuwa saura kad'an ta zame, ya Fu'ad ya yi sauri kai hannu zai rik'o ta Allah ya ba ta sa'a ta dafa bango. Anna har ta mik'e. Julaibib d'in kuwa wani arnen harara ya jefi Fu'ad da shi ka na ya juya ta re da nufar k'ofa don zuwa wajan mahaifin sa.
Girgiza kai Anna ta yi ta re da kallon Fu'ad ta ce,
"Yauwa Fu'ad, gobe idan Allah ya kai mu, za ka d'auki Binty da Fanan ka kai su supermarket ka yi masu siyayya sosai, jibi za ta je k'auyansu ganin gida". Fad'in Anna.
Gaban ya Fu'ad d'in ne ya buga dam dam ta re da kallon Anna da sauri ya ce,
"Anna kuma kin yarda su tafi d'in?".
"Ka ji wani maganar banza da wofi. Na ce maka wajan danginta za ta je kuma sai ka ce na yarda ni da aka min kara da kawaici tsawon shekaru ba ta je ba run da ta zo nan. Amma ba ka da hankalin Fu'ad". Fad'in Anna.
"Anna wallahi ni kawai matar ce ba ta kwanta min a rai ba". Fad'in Fu'ad.
Harara Anna ta ma ka masa ta re da fad'in,
"Ka dai ji abunda na fad'a maka ko? Karfe sha d'aya na ke so ku tafi".
"To Anna Allah ya kai mu". Fad'in Fu'ad jiki a sanyaye.
Harara ta k'ara maka mashi ka min ta yi hanyar stairs.


Julaibib na fita hanyar part d'in Hajiya Huriya ya nufa domin ganawa da mahaifin sa.
Ya gitta side d'in Suhail kad'an ya yi saurin dawowa baya saboda warin wiwin da ya ji ta k'ofofin hancinsa da kuma hayak'in da ya ke gani ya na fita duk da d'akin a kulle ya ke.
Hanyar k'ofar ya yi ran shi a matuk'ar b'ace ta re da dukan k'ofar da k'arfi kamar zai karya.
"Wani d'an hegiyar ne ya ke dukan k'ofata haka iyeeee". Fad'in Suhail cike da maye.
K'ara dukan k'ofar Julaibib ya yi da mugun k'arfi.
A zafafe Suhail ya taso ya na rangaji daga shi sai boxer, tattoo d'in nan ya fito rad'o rad'o a jikinsa sai wani uban chain a wuyan shi har ciki, karuwarsa kuma ta na kwance a three sitter ta na zuk'an sigari da ga ita sai wani arnan rigar baccin da gaba d'aya jikinta ana ganinsa a waje.
Gadan gadan k'ofar ya nufo ta re da bud'e shi kamar zai kifa.
Wani irin kallo Julaibib d'in ya ke bin sa da shi har jikinsa ya so ma rawa don hatta naman kumatun shi rawa su ke yi. Tuni har idanuwansa sun kad'a.
Shi kuwa Suhail duk da ya na cikin maye hakan bai hana shi wani iri zabura ba ta re da komawa baya, don ko a mafarki bai tab'a tunanin Julaibib ba ne. Don shi bai da labarin ma ya dawo k'asar.
"Yyyyyyaya Bibi". Fad'in Suhail bakinsa na rawa kamar zai fad'o.
Wani wawan mari Ya Bibi ya d'auke sa da shi sai da ya kifa k'asa wanwar.
"Baby whats going on". Karuwar Suhail ta fad'a ta re da tasowa daga in da ta ke ta na rangaji.
Wani irin tuk'uk'in bak'in ciki ne ya k'ara mamaye zuciyar Julaibib har bai san san da ya saka k'afa ya take gaban Suhail d'in ba da k'arfi.
Wani irin ihu Suhail d'in ya saki ta re saka hannu biyu ya rik'e gabansa ya na tumbling.
Ita kuwa karuwar jikinta ne ya soma b'ari, saurin d'aukar hijjab d'inta har k'asa ta yi ta saka ta na k'ok'arin fita daga d'akin.
Wani irin fincikota ya yi ta re da yasar da ita a tsakar d'akin sai da ta kwallara k'ara saboda cikinta da ya bugu da k'asa.
K'arasawa wajan kayan kallo Julaibib ya yi ta re da fizgo wata waya ya shiga lafka masu ta ko ina a jikinsu dai dai lokacin Ya Fu'ad ya fad'o d'akin sakamakon ihun Suhail da kuma na mace da ya ji.
Fu'ad jikinsa b'ari ya soma yi saboda irin dukan da Julaibib d'in ya ke ma su. Ran shi ya yi b'acin da zai iya aikata komai. Da gudu Fu'ad d'in ya juya domin kiran Anna.
Ko kafin Anna ta shigo, Suhail da karuwansa sun yi suma uku su na farfad'owa.
"Julaibib ka bari na ce!". Amma ta fad'a a tsawace.
Amma inah Julaibib bai ma san ta na yi ba sai dad'a dagewa ya ke yi ya na bugun su.
"Julaibib ba da kai na ke magana ba". Anna ta sake fad'i amma duk da hakan bai bari ba.
"Salissssss!". Anna ta kira ainahin sunan sa a tsawace sai da d'akin ya d'auka.
Sai a lokacin ya yar da bulalan da har ya tsintsinke saboda irin dukan da Julaibib ya yi masu.
Suhail numfashi sama sama ya ke yi, ya yin da karuwar ta sa ko motsi ba ta yi.
Fu'ad bai ankara ba ya ji an d'auke sa da maruka har kala uku masu gigitarwa ka na ya nuna sa da yatsa,
"Kkkkkana kalll'o yii yah ron nan ya na is...kkan cin nan am..ma baza kullll...a da shi ba". Fad'in Julaibib cike da in'i na saboda b'acin ran da ya ke ciki.
Kauuuuuuuuuu! Anna ta d'auke shi da mari hagu da dama ta re da fad'in,
"Ban isa ba ko? Ni ban isa in fad'a maka ka bari ka yi ba ko? Yanzu idan ka yi kisan kai fa?".
Julaibib na son yin magana amma ya kasa saboda in inar da ta ci k'arfin sa. Hargitsa gashin kansa ya so ma yi ta re da soma buga k'afarshi a k'asa.
Hankalin Anna ne ya yi mugun tashi don ta san halin d'an na ta.
"Wuce side d'in nan right now". Anna ta fad'a wa Fu'ad.
Cikin sauri Fu'ad d'in ya fita saboda ya san wanene wan na shi.
Ita kuwa Anna hannun Julaibib d'in ta kama ta re da nufar side d'in sa. Sai da ta aje sa akan kujera ka na ta d'auko ruwa mai sanyi a fridge ta tsiyaya masa a cup ta re da mik'a masa.
Ba musu ya karb'a ya shanye. K'ara masa ta kuma yi, nan ma ya kuma shanye wa.
"Ta shi ka shiga ba yi ka je ka yi alwala ka yi sallah ka kwanta". Anna ta fad'a.
Ba musu ya yi wajan bayi, ita kuma ajiyar zuciya ta saki ta re da fita ta koma part d'in Suhail d'in.
Yadda ta bar su, haka ta sa me su. Ruwa ta d'auko a fridge ta re da bud'ewa ta d'iba ta shafa a fuskan yarinyar.
Wawiyar ajiyar zuciya ta sauke ta re da rushewa da kuka.
"Ta shi ki wuce gidan ku tun kafin ki rasa k'afar ki d'aya a cikin gidan nan". Fad'in Anna.
Cikin sauri yarinyar ta mik'e ta re da d'aukar takalminta mai tsini a hannu. Har ta kai k'ofa Anna ta ce,
"Ki ji tsoran Allah yarinya. Ka da ki manta ke macece, zaman gidan iyayanki ko gidan miji shi ya kamace ki ba bin gidajan samari ba su na yaudarar ki da kud'i da kayan shaye-shaye ba. Ki ko ma gaban iyayan ki kk ji tsoran Allah".
"Nagode". Shine abubda yarinyar ta fad'a ta re da saurin barin wajan gabanta ba fad'uwa don ba ta tab'a zaton za ta farka ba ta ji ta a kabari ba.
kallon Suhail da ke ta murd'e murd'e hannunsa rik'e da al'aurarsa ta yi ta re da fad'in,
"Ka d'an ka ga ni in dai ba za ka kiyayi duniya ka kuma natsu ba". Ta na gama fad'in haka ta yi waje.


*WASHA GARI*
🌙🌙🌙

Fuska kumbure Fu'ad ya tashi saboda marin da ya sha a wajan babban yaya.
Shikuwa Julaibib a masallaci wajan sallar asubha su ka had'u da daddy su ka gaisa, bai tambayesa dalilin rashin zuwansa ba, kasancewar ya na ganin duk abunda ya faru daga CCTV CAMERA da ke d'akinsa. Duk abunda Suhail d'in ya ke yi, Alhaji Usman na sane, wani abu ya ke jira akan sa saboda mummunar shiri da yake masa don har safarar cocaine d'in da ya ke yi ya na sane da shi.
Julaibib daga masallaci ya wuce asibiti ko saboda jiransa da ake yi kuma ya yi wa Sabrin alk'awarin zai za wajanta yau da daddare idan ya gama abunda ya ke yi da wuri.

"Fu'ad, mai ya samu fuskan ka?" Fad'in Anna wanda hakan ya sa daga Binty har Fanan da ke breakfast su ka juya su na kallon shi.
Binty har sai da ta b'arar da shayin da ke gabanta wajan mik'ewa. Sai da ta isa gaban Fu'ad ka na ta ce,
"Yaya na mai ya samu fuskan ka?". Ta fad'i hakane siraran hawaye na zubowa daga idanuwan ta.
"No kar ki kuka beauty, kwanciya na yi a kan tiles kuma jikina bai san sanyi shiyasa wajan ya kumbura, kuma zuwa anjima ma zai sace". Fad'in Fu'ad ya na sakin murmushi.
"Dan Allah Yaya kar ka k'ara kwanciya a k'asa". Fad'in Binty a marairaice.
"In sha Allah". Fad'in Fu'ad ta re da nufar dinning d'in. Sai da ya je dai-dai kunnan Anna ka na ya ce,
"Anna ke ki ka jawo min jin hannu maza a fuskata, aradu har na yi bacci ina jin zugi. Da kin bar ni na d'au mataki da ban samu kafta a fuska ba". Fad'in Fu'ad ta re da jan kujera ya zauna.










*Walleh ban yi niyyar yi ba yau, kawai tausay ma ku na yi. Amma ga shi nan ku d'and'ana*
🌹 *53-54*🌹
............Gimtse dariya Anna ta yi, don fisabilillah Fu'ad ya ba ta tausayi kuma ya ba ta dariya.
"Ka ba ri zan kai su supermarket d'in da kai na, kai na je ka huta kawai". Fad'in Anna.
"Anna a kan me? Zan iya kai su da kai na Allah, ba sai kin je ba". Fad'in Fu'ad da sauri.
"To ai shikenan, idan lokacin ya yi, sai ka zo ka karb'i ATM d'i na, don tafiyarta gobe ne". Anna ta fad'a ta re da cigaba da kurb'an tea.
"Ina da kud'i enough a account d'i na ba sai na karb'i ATM d'in ki ba". Fad'in ya Fu'ad.
Binty kuwa sai da ta had'a wani kasancewar ta zubar da na ta garin tashi ta je wajan ya Fu'ad don jin abunda ya same shi a fuskan shi.
"Anna amma ta re zamu tafi ko?". Fad'in Fanan ta na kallon Anna.
"Eh ta re za ku tafi mana". Anna ta fad'a duk a tunanin ta supermarket d'in ta ke nu fi.
Dad'i ne ya kama Fanan kamar ta tashi ta taka rawa.
Bayan sun gama breakfast d'in ne, su ka tattara kayan wajan su ka kai kitchen ta re da wanke su, don haka Anna ta ce masu in dai suna gida to su za su yi aikin gida ka da su je gidan miji ba su iya komai ba.


K'arfe goma da rabi Fanan da Binty su ka yi wanka ta re da kimtsawa cikin wani ora Orange less wanda aka masu d'inkin riga da skirt. D'inkin ya amshi jikin su. Farin gyale su ka yafa ta re da farin takalmi. Ko man su iri d'aya su ka saka har d'an kunne.
"Anna mun shirya". Fad'in Binty". Fad'in Binty.
"Ku sauka ku jira shi a k'asa, nasan shi ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login