Showing 150001 words to 153000 words out of 162658 words
Julaibib, Fu'ad da kuma Fanan.
Anna da Daddy kuwa wani murmushin da su kad'ai su ka san nufinsa su ka yi.
"Qalby mai ki ke fad'i haka? Kamar ya su bar miki ni har ki aurar da ni, mai hakan ya ke nufi? Dan Allah ka da Ku ce min ba Ku kuka haife ni ba". Fad'in Rauhiyy ta na kuka sosai da ya zawo hankalin Mas'ud da fitowarsa kenan daga part d'insa zai shiga main part.
Cikin sauri ya k'ariso parlourn don sanin abunda ke faruwa.
Cak ya tsaya har ya na wani lilo kamar zai kifa k'asa saboda gigicewa da kuma mamakin ganin Rauhiyyah ta zama biyu.
Hannu biyu ya kai ya yi weaving a dai-dai fuskan su duka don ganin idanuwansa ke masa gizo, ko kuwa dagaske ne.
"Momma dan Allah idona ne ke da matsala ko kuwa abunda na ke ga ni gaskiya ne?". Fad'in Mas'ud.
"Dan Allah duk ku nutsu ku zauna ayi komai dalla-dalla. Ku nutsu dan Allah". Fad'in Alhaji Usman.
Kowa samun waje ya yi ya zauna ya yin da Mas'ud d'osana d'uwawunsa ya yi a kan kujeran don ya na cikin mamaki kuma ya na buk'atar a warware masa komai.
"Dan Allah bawan Allah mu na san jin ta yadda wannan yarinya ta zo hannunku". Fad'in Alhaji Usman ya na kallon bawan Allahn nan.
Ajiyar zuciya ya saki ta re da fad'in,
"Mu y'an asalin Adamawa state ne, aiki ne ya dawo damu nan garin shekaru sha bakwai bakwai da su ka wuce. Tun bayan haihuwar Mas'ad Allah bai sa ke ba mu haihuwa ba wanda shi kan shi Mas'ud d'in sai da mu ka shekara Bihar ni da matat ka mun Allah ya ba mu cikinsa. Mas'ud sai da ya cika shekara bakwai sannan matata ta sa ke samun wani cikin. Lokacin da cikinta ya isa haihuwa, cikin dare wajajan sha biyun dare nak'uda ya ka ma ta. A rud'e na d'au mota mu ka nufi asibiti mafi kusa da mu. Muna zuwa cikin ikon Allah ta haihu lafiya sai dai d'iyar ba ta zo da rai ba, matata ta yi kuka sosai saboda ta kwallafa rai musamman ma da ta kasance mace kuma ta na son d'iya mace.. Kasancewar matata ta haihu lafiya sai ta ce a ba mu gawar kawai mu koma gida tun da dai lafiyar ta k'alau. Haka aka yi duk da sun so rik'e mu zuwa safe. To ahanyar mu ta dawowa mota ta tsaya mana dai-dai wajan wani bola, fitowa na yi don duba motar gashi dare ya yi don d'aya ta wuce da minti arba'in. Kukan jariri muka ji wanda ya firgita mu don duk a tunanin mu jaririyarmu ce. Sai dai jin kukan ba daga cikin mota ya ke fitowa ba sai hankalinmu ya k'ara tashi. Ita ta umurce ni da na duba kasancewar shekarar an yi yayin haihuwa a jefar da jariri. Cikin sauri na zagaya na aikuwa na yi arba da jaririya sanye cikin kayan sayin nannad'e da showel da kuma wani mafifici na d'awisu da kuma warwaro na zinari wanda aka rubuta sunan jaririyar a tsakiya. A nan ne muka san asalin sunanta kuma ba mu canza mata ba, yanzu haka ma su na d'aki na zan d'auko su. D'auko jaririyar na yi na kawo wa matata cikin mota. Cikin ikon Allah ina shiga na kunna motar ta ta shi mu ka nufi gida. Cikin daran nan muka yanke hukucin rike ta. Kuma a daran matata Rahima ta so ma shayar da Rauhiyyah wanda haka ya k'ara shak'uwa tsakaninsu. Kuma ba mu shaidawa kowa cewar ba y'ar mu ba ce. Washagari mu ka na sanar da dangi da abokai cewar ta haihu y'an biyu amm d'aya ba ta zo da rai ba. Sosai aka yi shagalin suna, cikin ikon Allah kuwa ba mu cika shekara ba aka canza min wajan aiki zuwa nan garin abuja".
..........Mik'ewa Rauhiyyah ta yi jikinta na rawa, can kuma ta tafi luuuuu ta suma.
Cikin sauri Julaibib ya shiga ba ta taimakon gaggawa. Ba ta jima ba ta farfad'o ta na sakin kuka ta re da k'ank'ame uwar rik'onta ta na wani irin narkakken kuka.
"Qalby ki ce mafarki na ke yi dan Allah. Ku ce ku ne ainahin mahaifa na dan girman Allah. Zan mutu idan Ku ka ce ba ki ne iyaye na ba".
Fanan da Binty, Anna da mahaifiyar rik'on Rauhiyyah kuwa kuka su ke yi su ma sabida Rauhiyyah ta ba su tausayi sosai.
Dakyar aka su daddy su ka lallashe su. Nan Anna ita ma ta kwashe duk labarin Binty ta shaida masu. Sosai su ka shiga tashin hankalin shin su waye aihanin iyayan Binty da Rauhiyyah.
"Ina son mu yi magana a keb'ance ni da Ku ban da yara" Fad'in Allah.
Mahaifin Rauhiyyah saurin ta shi ya yi ta re da fad'in,
"To ku fito muje wancan side d'in sai muyi magana".
Duk ta re su ka fice daga d'akin. Sun kai kusan awa d'aya ka na su ka fito daga cikin d'akin.
Sallama Anna su ka masu su ka fice don komawa gida. Kasancewar Anna za ta yi tafiya nan da sati bayan yanke hukunci a kotu.
*KOTU*
*PAID BOOK*
: 🌹 *83-84*🌹
*KOTU*
.............Cike yake mak'il da jama'a. Daga can gaba kuwa, lauyoyi ne daga ciki kuwa har da Barr Fu'ad da abokan aikinsa. Daga can gefe kuma wajan tsayiwar wad'and'a ake tuhuma, Suhail ne sanye da sark'a, su hajiya Mansura kuma gaba d'aunsu hannunsu sanye da ankwa ta re da dandazon members d'in su. Alk'aline ya shigo gaba d'aya kowa ya tashi. Bayan ya zauna sai ko wa ya zauna, ka na mai karanto k'ara ya karanto k'ara. Daga kan su Hajiya Mansura aka fara, alk'ali ya kalli Hajiya Mansura kasancewar ba su d'auki lauya ba ta re da fad'in,
"Shin kun amince da duk abubuwan da aka karanto ko kuwa Ku na da ja, kuma Ku na da lauya ne?".
"A'a ya mai girma mai shari'a ba mu da ja, duk abunda aka karanto mun aikata". Fad'in Hajiya Mansura ta na sharar hawaye.
D'an rubuce-rubuce mai shari'a ya yi ta re da kallon Suhail ya ce,
"Kai kuma fa, ka na da ja da abubuwan da aka kama ka da su a d'aki, kuma mai yasa ka ke aikata ta'addacin a k'asarka?".
Kuka Suhail ya soma yi ta re da fad'in,
"A gafarce ni ya mai girma mai shari'a, wallahi ban rasa komai ba daga wajan mahaifina ba, sharri shad'an ne da kuma sharrin abokai". Fad'in Suhail ta re da rushewa da kuka.
D'an rubuce-rubuce alk'ali ya sake yi ta re da fad'in,
"Ke kuma baiwar Allah menene ribar ki na d'aukar y'ay'an mutane Ku na tura su aikatau da kuma jefa su cikin wasu munanan harkan". Alk'ali ya fad'a ta re da kallon Kandala da sai zazzare idanuwa ta ke yi.
"Ya mai girma mai shari'a yasin-yasin sabida kud'i ne. Son kud'i ne ya yi min yawa ga shi zai jawo min k'arewa a gidan yari. Don Allah Ku yi min rai". Fad'in Kandala cikin Kuka.
Jinjina kai alk'ali ya sa ke yi ka na ya yi y'an rubuce-rubuce ka na ya d'ago ta re da fad'in,
"A bisa duba da kuma hujjojin da kotu ta gabatar da kuma amsa laifin da masu laifin su ka yi, kotu ta yankewa Suhail Usman mai rabo hukunci shekara goma sha biyar gidan yari ta re da horo mai tsanani, sannan kuma ta kotu ta sake yankewa Hajiya Mansura da tawagarta shekara goma sha takwas-takwas a gidan yari su ma da horo mai tsanani. Ita kuma Kandala kotu ta yanke mata shekara uku a gidan yari. Alhaji Mudi kuwa wanda Suhail ke kai masa makamai shi kuma ya baiwa y'an ta'adda da muke fama da su a k'asarmu, shi ma kotu ta yanke masa shekara ashirin a gidan yari da horo mai tsanani. Allah ya sa hakan ya zama izina ga wad'anda su ke son aikata irin wannan rayuwa da ma Wanda su ke ciki su tuba su sai da. Courttt". Ya na gama fad'in haka ya bubbuga sandar gabansa ta re da mik'ewa.
Gaba d'aya kotun ta hargitse da hayaniya wasu na tsine masu, wasu ba jin tausayi.
Yayin da Kandala ke ta sakin zawo a jiki, Suhail kuwa suma ya dunga yi, su Hajiya Mansura kuwa sai kuka su ke yi.
Ya yin da Amrah da Hanan ke kuwa kamar ran su zai fita saboda hukunci da aka yankewa mahaifiyarsu domin uwa uwa ce.
Alhaji Saifullahi ya rungumesu a jikinsa ya na lallashinsu ta re da alk'awarin kyautata masu da kuma sauke dak wani hak'k'i na su da ya rataya a wuyansa kamar yadda zan yi wa Sabrin. Ya kuma k'ara da alk'awarin yin adalci tsakaninsu da Sabrin.
Ita kan ta Sabrin d'in kuka ta ke yi sabida ganin halin da y'an uwanta su ke ciki. Kuma ba ta tab'a sanin haka ta ke jin su cikin zuciyarta ba sai yau da wannan al'amari ya kasance wanda ita Amrah ta na daga cikin sanadin tonuwar asirin mahaifiyarsu duk da ita ta ce ta yi don kub'utar mahaifiyarsu daga halaka ne ganin za ka saka rayuwarta da na su da kuma wacce ba ta ji ba, ba ta gani ba a bala'i.
Julaibib kuwa ya na daga can sama Binty (Rukhsana) na kusa da shi ya hana ta ko motsi, shi kuwa Fu'ad sai satan kallon Rauhiyyah ya ke yi, da sun had'a idanuwa sai ya yi saurin kau da kai. Kasancewar ta na da miskilanci sai ta yi kamar ba ta san ya na kallonta amma kuma ita ma ta na kallonsa da gefen idanuwanta duk motsinsa.
Shi dai Fu'ad zai ita cewa idan aka shak'e shi ba zai ce ga hukunci da aka Yankewa su Suhail ba. Duk da ya na gaba, amma idanuwansa na baya wajan Rauhiyyah inda ta ke zaune da Rahima mahaifiyar ruk'onta.
...........Bayan sun baro kotu, gaba d'aya gidan Alhaji Usman mai rabo su ka nufa har da su Rauhiyyah da kuma su Binty nan aka k'ara jajantawa juna.
Alhaji Usman ya kira kaf ma'aikatan shashin Hajiya Mansura ya sallame su, ka na ya kira Fasila da Wasila gaban kowa ya nuna masu duk abubuwan da su ke yi a cikin gidan ta re da sallamarsu bayan ya biyasu albashinsu har da k'ari ta re da yi masu dogon nasiha. Wasila da Fasila har da kuka da majina ta kuma kasa had'a idanuwa da Anna.
Har gaban Anna ta je ta duk'a ta na kuka majina na bin hancinta ta ce,
"Hajiya ki yi wa girman ubangiji ki yafe min duk abubuwan da ba aikata miki wanda ki ka sani da wanda ba ki sani ba dan soyayyar Allah da ke wa manzo SAW".
"Ba komai Fasila Allah ya yafe maka baki d'aya ke kuwa Allah ya sa sanadin shiryiwar kenan". Fad'in Anna.
Kayansu su ka tattaro daga maid parts su ka fice daga gidan cike da takaicin abunda su ka aikata ga shi ba su ci ribar komai ba sai tarin kunya da takaicin da da na sani.
Bayan sun ci sun sha, Fanan ta zo ta duk'a gaban Maman Rauhiyyah ta re da fad'in,
"Mommah dan girman Allah ki bar mana Rauhiyy ta kwana biyu a gidan nan mu sa ba da juna dan Allah". Fad'in Fanan a marairaice.
Murmushi ta yi ta re da shafa kan Fanan ta re da fad'in,
"Ba komai Fanan ga Rauhiyy nan ta zauna da ku tun da ma Anna tafiya za ta yi jibi sai ta taya Ku hira ta kuma saba da tagwainiyarta".
"Anna wai ni da ita wanene babba? Ni ce ko?" Fad'in Rauhiyyah ci ke da son girma".
"Ke dallah matsa can, ana ganin mu an san ni ce babba kwarankwatsi".
Gaba d'aya dariya su ka fashe dashi saboda tuno masu da Buba mai kwarankwatsi da ta yi kasancewar sun ba su labarin sa.
"Allahu masanin gaibu". Fad'in Anna ta na dariya don ta ga alamu daga Rauhiyy har Binty akwai son girma.
Sai dai Rauhiyyah ita ta na da kyaliya da kuma rashin son magana idan ba ta ga dama ba, amma Binty ita uwar aku ce sanna ba ta da kyaliya.
Ranar dai a nan gidan aka bar Rauhiyyah, Sabrin, da kuma twince wato Amrah da Hanan.
Wuni su ka yi a d'aki su na hiran school da kuma tuno halayan Sabrin d'in a da. Ita kan ta dariya ta ke yi sosai sai ta ji kamar ba ita ba ce ta yi hakan. Sai cin abinci da sallah ke tada su.
Barrister Fu'ad da Julaibib ranar wuni su ka yi a parlour su na lek'en upstairs ta inda Rauhiyyah da Binty za su fito su kuma su can sama su na jirarsu ta mata har da shewa don't su na jin muryansu daga nan parlour.
...........Ranar da Anna za su tafi kasancewar jirgi za su bi ita da alhaji Usman d'in, kiran Julaibib ta yi har d'aki.
Bayan ya shigo ya zauna ta kallesa ta re da fad'in,
"Alhamdulillah zan ta fi yau, kuma kai ne babba na san mahaifinka ya fad'a maka abunda zan je yi, sabida haka daga nan ka min na dawo, ka tabbatar ka fayyace sirrin zuciyarka idan ba haka ba ina dawowa zan ba ka mamaki". Fad'in Anna ba ta re da ta k'ara kallon inda ya ke ba ta sauka k'asa.
Gaba d'ayansu su ka raka Anna da daddy zuwa airport.
Rauhiyyah, Sabrin, Hanan da Amrah a motar Fu'ad yayin da Anna Binty da daddy a motar Julaibib.
Ba su baro Airport d'in nan ba sai da su ka ga tashin jirginsu Annan. Kuma ka min Anna ta wuce sai da ta k'ara jajjadawa Julaibib maganarsu na d'azu.
Wajan dawowa Binty ta nufi wajan motar Barr Fu'ad amma ka min ta isa wajan ta ji muryan Julaibib d'in na fad'in,
"Hayatiey zonan".
Sai da ta waiga dama da hagu ka na ta kalli gabanta ko a kwai wata amma ta ga wayam ka na ta kalli Julaibib ta re da nuna kan ta da d'an yatsa ka na ta ce,
"Ya Bibi ni ka ke kira". Ta fad'in hakane ta re da zaro idanuwa.
Shi ma waro mata idanuwan ya yi ta re da jinjina mata kai.
Kanta ne ya d'aure duk ta daburce. "Hayatiey" Ta maimaita sunan cikin zuciyarta.
"Ki zo a motata za mu koma? Ko da ma a wancan motar Ki ka zo airport d'in?". Fad'in Julaibib.
Girgiza Kai ta yi ta re da dawowa har in da motar ta ke kanta kuma a d'aure.
Bud'e motar ta yi za ta shiga ta ji muryan Fanan da k'arfi ta na fad'in,
"Babiiiii". Saurin juyawa Bintyn ta yi ta re da zabga mata harara.