Showing 156001 words to 159000 words out of 162658 words
y'an biyu.
Sabrin sai duk'ar da kai da sum-sum ta ke yi ita ala dole ta na gidan surukai. Ita kuwa mommah ba ta ma san ta na yi ba duk da Mas'ud d'in ya fad'a mata shi fa ya sa mu matar aure kuma Sabrin d'in ce.
Kullum Julaibib da ya dawo daga aiki ya ke tafiya gidan su Rauhiyy dan ganin sahibarshi.
Sosai Anna ta ji dad'in ganin sun had'e kawunansu don dama ita burinta kenan.
Kwanansu takwas a gidan Mommah su ka dawo gidan Anna, amma ban da Rauhiyy wanda hakan bai yi wa Fu'ad dad'i ba.
Yau bak'o su ke da shi, kuma bak'on ba wani ba ne fa ce Yousouf Muhammad Ahlam don godiya ga Julaibib da ya sa mo masa maganin cutarsa har ya warke garas.
Kyakkyawan tarba aka yi ma su shi da abokinsa. Tun da Yousouf ya kyallara idanuwa akan Amrah ya ka mu, kuma ita ma haka ya ke a wajanta. Musamman da ya kasance kyakkyawa kuma mai sanyi.
Bai yi k'asa a gwiwa ba ya k'arb'i numbernta ka min ya wuce.
Washa gari Hamdan ya taho da akwati nik'i-nik'i ya na ta zuba bala'i kowa ya manta da shi har da bestyn shi da ya yi ta dungurewa kai har sai da ta fad'a kan kujera. Nan su ka shiga mai da yadda aka yi lokacin da su ka tsince su a duniyar aljanu. Fanan da su y'an biyu sun yi dariya don Fanan har da hawa sama da gudu ta shiga toilet ta yi fitsari don tsabar dariyar fitsarin da ta yi ta saki don tsoro.
Sabrin ta shak'a ta watsa masa ruwa a fuska ta re da shiga ba su labari shi ma ai ya yi fitsarin har da zawo. Nan ma aka shiga yin dariya. Sai kuma aka koma kwantanta yadda Binty ta dunga suman tsoro da kuma kamannin Oumul Sahwat da ba Bak'ayatul mahruri.
*AFTER TEN DAYS*
.............Gaba d'ayan su su ka shiga kintsawa na tafiyar da za su yi zuwa bauchi, don dukkansu za su tafi, tun daga kan daddy, Anna, Julaibib, Fu'ad, Binty, Fanan, Rauhiyy, mommah, mijin mommah, mas'ud, Hamdan, Amrah da Hanan. Kowa sai kimtsa jakarsa ya ke yi don Anna ta ce masu tafiya ce ta kusan wata d'aya.
Duk da kasancewar Hamdan ya na final year d'in sa amma hakan bai hana ya k'i bin su ba.
Washa gari su ka bi jirgi sai Gombe (Ku yi hak'uri last page na saka Anna sun je bauchi, ba bauchi zan sa ba Gombe ne mistake ne).
Kai tsaye gidan sarkin Gombe su ka nufa wanda wa ne a wajan mahaifin Anna.
Gaba d'aya tsoro ne ya kama Binty ganin yadda ake karrama su da kuma gaida su duk in da su ka shiga.
Rauhiyyah ce dai ko a jikinta don sai d'aga kai ta ke yi ta re da basarwa kamar d'iyar sarauta.
Kai tsaye wajan kilishi su ka nufa wato uwar gidan mai martaba. Nan su ka ga mulki ganin yadda kuyangi su ke mata da su kan su. Cikin k'ank'anin lokaci har an cika gabansu da abinci.
Julaibib kuwa tuni har an yi masa iso wajan mai martaba.
Zaid ya hango cikin alkyabba mai shegen kyau, idan ka gan shi ka ga Julaibib don kamanninsu d'aya tsaf. Cikin sauri ya mik'e ya je ya rungume Julaibib d'in ta re da farin cikin ganin d'an uwan na shi cike da kewarsa.
Duk'awa ya yi ta re gaida mai martaba cike da girmamawa. Ka na ya shiga tambayarsa aiki da kuma Canada.
Binty kuwa sai fik'i-fik'i ta ke yi da idanuwa duk da ta na bala'in gidan sarauta sai ta ke jin ta wani iri.
Da daddare misalin isha'i su ka taru a parlour mai martaba gaba d'ayan su. Kallon Binty da rauhiyyah ya yi ta re da sakin murmushi ka na ya ce cike da k'asaita
"Masha Allah, har na tuna lokacin da mu ka je Sudan d'auro auran mahaifiyarku. Allah ya muku albarka".
Ci ke da mamaki kowa na wajan ya ce ameen.
"In sha Allah gobe za mu tafi yola da ku duka wajan mai martaba, mun yi waya da shi na ce masa gobe ina ta fe da manyan bak'i".
"Allah uban giji ya kai mu". Fad'in gaba d'aya d'akin.
Nan duk aka fita aka bar shi daga shi sai mijin mommah da momma da kuma Anna da daddy.
Washa gari su ka k'ara shiga jirgi dukkansu har da mai martaba sarkin Gombe sai yola. Nan ma uban motoci aka turo masu daga masarautar yola da kuma dogarai su ka zo su ka d'auke su.
Masarauta ce mai girma da tsari wanda tsaruwarta ya fi gaban kwantance.
Gaba d'aya masarautar an canza masa launi da kuma wasu abubuwan k'awa. Tun daga jama'ar gari da kuma na cikin masarautar a su na wajan masarauta domin tarbar mai martaba sarkin gombe da bak'in sa. Lokacin da su ka shiga cikin masarautar, mai girma sarki na fitowa gaba d'aya fadawa su ka rufesa da rigunarsu har ya isa part d'in sarkin yola shi d'aya, sauran kuma Jakadiya ta yi masu iso zuwa part d'in Fulani uwar gida wajan sarkin yola.
Kishingid'e ta ke ta na cin apple cike da is a da Yakama kuyangi na mammatsa mata k'afa. Farar bafulatana ce kyakkyawa sosai kuma mace mara jiki ko kad'an, za ta iya kai wa shekaru hamsin da biyar a duniya.
Ta na yin arba da su Binty da Rauhiyyah ta yi wani irin zabura da gigicewa, ita kan ta jakadiyar da ta yi masu iso sai d'igar zufa ta ke yi kamar wacce kunama ya cijeta.
"Ina ki ka samo wad'annan?". Fad'in sarauniya Fulani cikin harshan fillanci wanda gaba d'ayan su idan ka cire Amrah da Hanan sun ji abunda ta ce saboda su ma su na jin fillancin.
"Mai martaba ya ce in kawo wajanki, bak'i ne daga masarautar Gombe, kuma ta re su ke da mai girma sarkin Gombe d'in". Fad'in Jakadiya wacce ta ke ji ina ma a kwai hanyar ta gudu.
Zama Fulani ta yi ta re da korar kuyangin da ke wajan ta shige d'aki ba ta re da tankawa bak'in ko ba su wajan zama ba.
Daga can part d'in mai martabar sarkin yola kuwa, bayan gaisuwa ta girmama tsakanin sarakan biyu, sai su ka shi ga mai da magana. Sarkin Gombe ya yi gyaran murya ta re da fad'in,
"Ita Na'ima (Anna) ni na rik'e ta, mahaifinsu k'ani na ne uwa d'aya uba d'aya ai ka san shi. To lokacin da aka ta jimamin b'acewar y'an biyun amarya ta san labarin komai kasancewar ta zo mana ziyara daga can abuja gidan mijin ta. Cikin hukuncin ubangiji kuma sai d'aya daga cikin y'ay'an su ka kasance a hannunta. Yanzu dai duk mun tawo da marik'an y'ay'an za su yi maka bayani da kan su".
Cike da farin cikin da ya ka sa b'oyiwa a fuskan mai martaba ya ce,
"Alhamdulillah! Allah nagode ma ka. Huta idan ya so sai in sa a kawo su nan d'in". Fad'in Mai martana sarkin yola da ke kishingid'e.
*AFTER 3HOURS*
............Tun daga kan Sarauniya Fulani, Sarauniya Zameelah (matar sarki ta biyu), Sarauniya Maimoon wacce ita ce ta uku, sai babban d'an sarki wanda ya kusa sa'a da Julaibib, sai da ba shi da lafiya, irin yaran nan ne da aka haife su abnormal, duk da shi lafiya lau aka haifesa, sai dai ya na kai wa shekara bakwai ya ka mu da wannan lalura. Kyakkyawa ne sosai na gaban kwatance kuma d'a ga gimbiya Zameelah, wanda bayan shi ba ta k'ara haihuwa ba sai da ya shekara goma sha takwas ta haifi y'an biyu kuma washa garin sunan su aka nai me su aka rasa wanda haka ya tada hankali gaba d'aya masarauta. Ya na gefe wanda mai martaba ko kallansa bai son yi saboda wani tsanarsa da ya ke ji wanda hakan ya shafi mahaifiyarsu da ta zama saniyar ware a cikin masarautar wanda Fulani ke juya komai. Sai mahaifiyarsu mai martaba sarkin yola wanda shi kad'ai ne d'a namiji a wajanta. Da kuma waziri da ke ta zazzare idanuwa da kuma Jakadiyar sarki da ta ke ji kamar ta saki zawo don firgici.
Shuri d'akin ya yi, ya yin da ko makawo ya kalli Sarauniya Zaheeda ya kuma kalli su Binty ya San daga jikinta su ka fito, ka na ganin ta ka ga cikakkiyar Sudanese wacce kyawunta har yanzu ya na ta re da ita kuma daga wajan ta su ka yi gadon kyau da kuma irin launin fata duk da mai martaba shi ma ba baya ba ne.
Sabrin kuwa da su twins mamaki su ke yi wai yau ga su ka sarkin Gombe da na Yola wanda ko a mafarki ba su tab'a kawo hakan ba.
Hamdan kuwa cewa ya ke cikin zuciyarsa,
"Mummy, uncle Sauban ku zo ku ga asalin Binty ku girgiza ta re da fad'uwa a gabanta don ita d'in jinin sarautace wata muna-munan ce ta kawo ta kan bola.
*PAID BOOK*
🌹 *87-88*🌹
.............Anna ce ta mik'awa Sarauniya Zameelah wannan kwarya da Yousouf aljani ya bai wa Binty, idanuwanta na zubda hawaye ta karb'a ta re da fiddo kayan da ya ke ciki. Kuka ta saka sosai saboda wannan shi ya k'ara tabbatar da lallai su Binty y'ay'anta. Jakadiya ma kukan ta ke yi domin ita ce da hannunta ta saka masu wad'annan kayan da kuma awarwaron nan a cikin showel d'in su da kuma maficin d'awisu wanda wannan d'in tambarin sarautar Sudan ce, kuma d'in wanda ya had'a jini mai k'arfi da masarautan ana haifansa ne da zanen d'awisu a wuyansa. Ita ma Rauhiyyah duk abunda ke cikin kwaryan Binty haka ya ke cikin na ta.
Da kanta jakadiya ta isa zuwa wajen Binty ta duba k'eyarta, ka na ta koma ta duba k'eyar Rauhiyy. Kallon mai martaba ta yi hawaye na gudu a idanuwanta da kuma murmushi ka na ta fad'i a gabansa ta re da fad'in,
"Allah shi k'ara maka girma da yawan rai da lafiya, babu tantama wad'annan y'ay'anka ne, domin akwai zanen d'awisu da aka haifesu da shi wanda ke nuni da tambarin masarautar Sudan a wuyansu, sannan ga awarwaro na d'anyan zinari da mai girma Katanga (Mahaifiyarsa) ta ba su". Ta fad'i hakane ta re da mik'awa mai girma Kantanga awarwaron cike da girmamawa.
Duk da ta tsufa sosai bai hanata ga ne wad'annan awarwaro ba, domin kyautace da sarakuwarta kakar mai martaba ta ba ta a matsayin kyautar budurci don har da sunan kowannansu a ciki, ita da kan ta ta saka aka yi wannan ka na ta sakawa kowannen su a hannu.
Julaibib kuwa gaba d'aya hankalinsa ya na kan Mahensh da ke jirarar da miyau ya na nazartar ciwonsa.
Waziri kuwa fitsari ne ke nai man kufce masa domin bai tab'a tunanin wannan ranar za ta zo ba, Sarauniya Fulani kuwa ita har da zawo-zawo ta ke ji.
Cike da tak'ama da gadara mai martaba ya yi gyaran muryan ka na ya kalli jakadiya ta re da fad'in,
"Ina son sanin ta yadda y'ay'ana su ka b'ata a masarauta washa garin sunan su, idan ki ka yi karya ki sa ni a bakin ran ki ya ke".
Jakadiya fad'uwa ta yi a gaban sarki ta na burgima ta re da fad'in,
"Wane ni in yi was sarki na k'arya. Wallahi na amince ko kalma d'aya idan ban fad'i ba ayi gangani ka na a fille kai na".
Gaba d'aya d'akin zuba mata idanuwa aka yi, Fulani da waziri babu abunda zuciyarsu ke yi sai bugawa kuma k'ani ne ga mai martaba.
"Kowa a nan ya San cewa Gimbiya Fulani ita ce matar Sarki ta fari wacce kuma y'ar uwa ce a gare sa don k'anin mahaifin mai martaba ne wanda su ke uba d'aya ya haife ta, auran zumunci aka ma su, kuma lokaci d'aya ya aure su da Sarauniya Zameelah wacce su ka had'u a jami'atul Madina soyayyar da shak'uwa ta k'ullu tsakaninsu. Sosai mai martaba ya ke son gimbiya Zameelah kasancewarta kyakkyawar mace kuma mace wacce ta iya rik'e miji da tarairayarsa. Haka na matuk'ar k'ona zuciyar Sarauniya Fulani kuma ta na mugun kishi da Sarauniya Zameelah musamman yadda ta yi wani irin suna da farin jini a cikin gidan da kuma wajan Sarauniya Katanga. Cikin hukuncin Allah ba ta dad'e ba ta samu ciki wanda ya sa ka mai martaba cikin wani irin farin ciki, don ba zan manta irin kyautar da na samu mai tsoka ba saboda isar da wannan sak'on farin cikin. Sai dai cikin bai yi wata biyu cikakke ba ya zube wanda kowa yaji bak'in cikin haka musamman mai martaba da har ya fara hango an haifa masa magaji. Bayan wannan lokacin gimbiya Zameelah ba ta rufe wata uku ba ta kuma samun wani cikin wanda shi sai da ya kai wata biyar ka na jini ya b'alle mata babu wanda ya yi zaton za ta yi rai haka kuma ya k'ara ta da hankalin mai martaba, an sa mu nasarar ceto ranta sai dai cikin ne ya fita. Duk maganar nan da na ke ma ku gimbiya Fulani ba ta tab'a ko b'atan wata ba kuma haka na damunta sosai ganin ga wata ba re zata haifi magaji a masarautan ta. A tak'aice dai gimbiya Zameelah sai da ta yi b'arin ciki har takwas ka mun ta sa mu cikin Mahensh bawan Allah, lokacin da ta sa mu cikin ba ta fad'awa kowa ba idan ka cire mai martaba da Katanga, kuma sai ta dai na fita har sai da cikinta ya kai wata takwas ka na na san da cikin a wani zuwa shashinta da na yi domin kai sak'o. Sosai na yi mamaki da ganin cikin nan. Na ja baki na na yi shuru kamar yarda ta gargad'e ni. Lokacin da cikin ya isa haihuwa shi ne kowa ya san da zaman ciki wanda ya kusa saka gimbiya Fulani zarewa domin ta yi kondo-kondo na masifa akan b'oye mata cikin da na yi.
Cikin ikon Allah gimbiya Zameelah ta haifo d'anta k'atoto kuma kyakkyawan gaske fari tass mai kama da mahaifiyarsa ga gashi. Ranar duk wanda ya ke cikin masarautan ya shaida haihuwan nan domin kyauta mai martaba ya yi na ban mamaki don wani ma sanadin arzikinsa kenan. Ranar su na yaro ya ci suna Ibraheem sunan mahaifin mai martaba sai ake mishi kara da Mahensh. Sosai aka yi shagalin suna wanda aka kashe kud'i da kuma raba kyaututtuka na ban mamaki.
Mai martaba idan ya bar Fada bai rabu da Mahensh a wajansa, don ko barci a k'irjin mai martaba ya ke yin sa. Sun shak'u matuka irin shak'uwar da ko mahaifiyarsa ba ta yi da shi ba don tsakaninsu shi ne idan ya buk'aci abinci ta ba shi ya sa a kuma mai da shi wajan mahaifinsa.
Mahensh na girma kyawu da wayonsa na dad'a fitowa sosai da kuma basira da wayonsa. Ga wani tak'ama da isa ka na ganinsa ka ga jinin sarauta, sosai ya ke da shiga ran mutane. Sai dai ya na kai wa shekara bakwai a wata safiya ni da Kai na na isa d'akinsa domin shiryasa zuwa makaranta na yi katari da tashin hankali da masifa, domin dai ga shinan kwance cikin fitsari, kwayan idanuwansa ya juye bakinsa ya shagid'e sai zirarar da miyau ya ke yi kamar irin yaran nan da aka haifesu ba dai-dai ba ko kuma wanda su ka kamu da ciwon b'arin jiki sakamakon fad'uwar hawan jini. Da kyar na iya sanar da Sarauniya Zameelah halin da ake ciki wanda ya