Showing 126001 words to 129000 words out of 162658 words
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Anna mai ya faru?". Fad'in Julaibib.
Fu'ad da ke tsaye, da bai yi niyyar k'arisawa ba ya yi sauri isa wajan, bai kai ga tambayar abunda ke faruwa ba ya yi arba da k'afar Anna.
"Je ka kawo mota gaban part d'in nan right now". Fad'in Julaibib.
Cikin saurin Barr Fu'ad ya mik'e ya fice.
Ita kuwa Anna da ba ta ma san k'afar na ta a kumbure ya ke ba, amma da ta ankara sai k'afar ta soma mata wani irin azaba kamar ana kwankwatsa k'ashin k'afar da diga. Tu ni ta soma karanto duk addu'oin da ya zo bakinta.
Kinkimarta Julaibib ya yi ta re da fitowa daga d'akin Binty bi ye a bayansa ta na kuka kamar ranta zai fita.
Da gudu Fanan da ke had'a masu breakfast a kitchen ta fito. Ta na arba da k'afar Anna ta saki wani irin ihu ta re da fashewa da kuka ta rungume Binty su ka had'a kai su na kuka.
Kwantar da ita flat a bayan motar Julaibib ya yi ta re da shiga gidan gaba, Barr Fu'ad ya ja motar da gudu.
Binty da Fanan kuwa da gudu su ka yi wajan driver ta re da ce masa ya bi bayan motar ya Fu'ad d'in da su yanzu.
A harabar wani babban asibiti su ka yi parking ta re da fiddo Anna, kasancewar Julaibib sananne ne kuma wanda su ka dad'e su na buk'atarshi a asibitinsu, cikin sauri su ka karb'i Anna su ka yi ICU da ita har da Julaibib kasancewar aikin k'ashi ya na d'aya daga cikin abunuwan da ya karanta.
Sai dai abunda ya baiwa likitocin da ke kan Anna mamaki da matuk'ar tsoro shi ne duk sa'anda su ka tab'a k'afar Anna ko su ka yi mata allura, k'afar sai ta k'afa fushi ta re da kumbura.
Hankalinsa ya kai k'ololuwa wajan tashi don ba su tab'a cin karo da makamancin haka ba a tsawon rayuwar aikin su. Sai uban zufa su ke yi.
Ya kai yanzu duk wanda ya kalli k'afar Anna zai iya zubawa da gudu don tsabar firgici.
Anna sai fizge-fizge ta ke yi ta na kuka. Duk dauriya irin na Julaibib sai da ya koka don ya San ba k'aramin ciwo ba ne ke saka zubar hawayan Anna.
Daga k'arshe dai sai da aka fitar da Julaibib don nai man sumar masu da ya ke son yi.
Kasancewar Fu'ad ya kira Alhaji Usman ya shaida masa komai, cikin k'ank'anin lokaci sai ga shi ya zo zufa babu in da bai keto masa don ya na matuk'ar k'aunar matar tasa.
Abu kamar wasa sai da doctors su ka shafa awanni har takwas a kan Anna ka na ta d'an dai na jin rad'ad'in kuma sun ka sa gano abunda ya haddasa kumburin k'afar.
Sun k'i barin kowa ya shiga ya gan ta ba yan Alhaji Usman.
Shi kan sa fitowa ya yi ya na sharar hawaye don ganin halin da matar ta shi ta ke ciki.
Ranar dai gaba d'aya wanna family su na cikin tashin hankali.
Binty da Fanan kuwa da ke gefe ko ruwa ba su iya sakawa a baki ba saboda tashin hankali ga shi an k'i ba ri su ga Anna d'in. Da kyar daddy ya lallab'a su driver ya mai da su gida.
Gaba d'ayansu yadda su ka ga rana haka su ka ga dare. Kuma ba bu wacce ta saka wani abu a bakin ta.
Da sassafe su ka da driver ya mai da su asibiti wanda zuwansu ya k'ara masa wani tashi hankalin domin d'ayar k'afar Anna ya harbu ya ma fi d'ayan kumbura da kyalli kamar an shafa mai a jiki. Sannan ta zama wata kamar mutum mutumi kwana d'aya kacal kawai.
Lokacin da aka bar su su ka tsaya ta wani wawakeken window mai d'auke da glass don ganin Anna kasancewar ba'a yadda wani ya shiga ba, sumewa Binty ta yi wanda sai da aka ba ta gado na tsawon sa'o'i uku ka na ta dawo hayyacinta ta na kuka kamar za ta mutu.
Julaibib da kan shi ya shiga in da ta ke ya yi lallashin duniya amma tak'i yin shuru.
Shi da kan shi duk da ya na cikin tashin hankali ya d'ibe su a mota ya mai da su gida ta re da buga masu concrete warning ka da ya k'ara ganin su a asibitin idan har ba da daddy su ka zo ba.
Abu kamar wasa ciwon Anna sai dad'a gaba ya ke yi, don yanzu ba ta iya gane kowa. K'ok'arin fita da ita k'asar ma ake yi zuwa India.
Zaune ta ke a d'akin su ta zuba uban tagumi, ta yi wani bala'in rama babu abunda ka ke hangowa a fuskanta sai karan hancinta. Idanuwanta duk sun zurma.
Wayarta ce ta soma k'ara, kallon wayar ta yi ta ga bak'uwar number ce ke kiranta.
Sai da ta kusa tsinkewa ka na ta d'aga ta re da karawa a kunne ta yi cikakkiyar sallama.
Daga d'ayan b'angaran ba ta re da an amsa mata sallamar ba ta soma fad'in,
"Ki na tunanin zan fad'i magana ce na kuma kasa cikawa? To kin yi kuskure y'an mata. Idanuwan ki dai sun gane miki yadda na yi da Annan ki, kuma ina mai tabbatar miki idan asibitin duniyar nan za'a zagaye baza'a tab'a samun maganin matsalarta ba. Ni da na saka mata cutar, ni kad'ai zan iya warware wa. Saboda haka zab'i na gare ki, Anna za ta iya warkewa amma da sharad'in amincewarki ki zamo matata mai d'auke min sha'awata, idan ba haka ba, nan da kwana biyu za'ayi kukan mutuwarta, daga nan kuma sai Fanan". K'it ta katse wayar.
Hankali a matukar ta she har ta na mik'ewa ta re da zaman y'an bori a k'asa ta re da rarrafe ta fita daga d'akin ka na ta mik'e. Da gudu-gudu ta sauko daga stairs d'in ta fita daga part d'in ta nufi part d'in Hajiya Mansura.
Caraf ta ji an cafki hannunta daga baya ta re da jan ta har garden d'in da ke gidan kasancewar bai fi taku goma ba daga in da su ke zuwa garden d'in.
"Natsu ki kwantar da hankalinki. Na san duk abunda ke faruwa, kuma ni nan da ki ke ga ni na zo ne domin ceton ki ta re da tseratar da ke daga muguwar matan nan Mansura". Fad'in Hajiya Zuwairah da ke kallo Binty cikin zuciya ta na had'iyar miyau.
"Na san duk wani sharrin da ta ke bin ki da shi, kuma na san abunda ta aikatawa Anna. Asiri ta mata mai matuk'ar k'arfi wanda zai iya salwantar da rayuwarta har abada. Idan ki na buk'ata zan iya taimakonki". Fad'in Hajiya Zuwairah.
"Dan girman Allah ki taimake ni wallahi zan mutu idan har Anna ta wani abu ya sa me ta". Fad'in Binty ta na kuma ta re da rik'e hannun Zuwairah k'am.
"Abu d'aya ne zai karya asirin da Mansura ta yi wa Anna, ba kuma wani abu ba ne fa ce barin ki cikin gidan nan". Fad'in Zuwairah ta na mai kallonta.
A zabure ta mik'e ta na kallon ta re da fad'in,
"Na shiga uku! Idan har na bar nan wallahi ban da wajan zuw...". Na ta k'arisa maganar ba saboda fad'owar da Yousouf ya yo mata a rai.
"Kar ki da mu, ni ina da in da zan kai ki, sai dai za ki d'an zauna ne na wani lokaci ka min ki samu wajan zama. Tausayinki da maraicin ki na duba shiyasa na ke son taimakar ki wanda hakan ni ma zai iya jawo min babbar masifa idan ta gano ni ta taimake ki. Yanzu ki yanke, shin za ki bar gidan nan ki ceci Anna ko kuwa za ki cigaba da zama ki mai da Fanan marainiya kamar ki, sannan ita kan ta ki salwantar da rayuwarta da yayunta?".
Ba ta re da wani dogon tunani ba Binty ta CE,
"Na zab'i barin gida domin ceton rayuwar mahaifiyata, zan bi ki in zauna a ta re da ke na kwanaki bakwai ka min na tafi in da zani. Nagode ta taimakon ki a gare ni". Fad'in Binty ta na sharar hawaye.
"Yauwa, wanna shine right time na guduwa saboda mazan gidan ba su nan, amma yanzu zan shiga wajan Mansura gudun zargi, ke kuma ki yi dabara ba ta re da wani ya gan ki ba ki shige motata ki kwanta a back seat, ba zan dad'e ba zan fito mu wuce". Fad'in Zuwairah.
Gyad'a mata kai Binty ta yi ta re da yin hanyar part d'in Anna ta na mai jin tsananin kewar Anna da Fanan tun ka min ta bar gidan.
Ta na tura k'ofar ta yi kicib'is da shi ya na tsaye a parlourn, cikin sauri ta nufe shi ta re da fad'in,
"Yayanmu ya jikin Annar mu?". Ta fad'i hakane hawaye na zuba.
"Ki kwantar da hankalinki kin ji? Anna za ta sa mu lafiya". Julaibib ya fad'a ta re da shafa kan ta ya na kallon fuskanta.
Langab'ar da kan ta ta yi, tsautsayi ya sa d'an kunnna kunnanta ya ka ma hulan sanyin da ke kanta.
Zame hukar ya yi ta re da cire d'an kunnan da ya mak'ale a hankali. Idanunsa ne ya sauka a k'eyarta, k'urawa wajan idanu ya yi har sai da ya kai hannu ya shafi wajan don tabbatarwa.
"Mai ya faru yaya?". Fad'in Binty ita ma ta na shafa wajan.
"Babu komai, ki je d'aki zan koma asibiti yanzu, anjima zan zo in kai ku. Ku kula da kan ku kun ji?".
Gyad'a masa kai ta yi hawaye na zuba. Hannu ya sa ka ya share mata hawayan ta re da nuna mata stairs.
Wajan ta nufa ta na tafiya ta na juyowa ta na kallon, duk san da ta juya tsaye ta ke ganinsa ya na kallonta har ta shige ka na ya fita.
Fanan ta sa mu ta na saka masu kayan guga a cikin wardrobe.
Ta baya ta rungume Fanan d'in ta re da fad'in,
"Ina k'aunar ku Fanan irin wanda ba zan iya misaltawa ba".
Juyowa Fanan d'in ta yi ta re da sakar mata murmushi ta re da fad'in,
"Mu ma muna k'aunarki sister".
Bayi Binty ta yi saurin shigewa ta turo k'ofar ta kunna panpo ta re da rushewa da kuka.
Ta jima ta na kuka a bayin ka min ta fito. Ko da ta fito ba ta samu Fanan a d'akin ba.
Saukowa k'asa ta yi, nan ma ba Fanan. Ta kitchen ta fita ta k'ofar baya cikin sauri-sauri ta re da nufar motar Hajiya Zuwairah ta yi saurin bud'ewa ta shiga gidan baya ta kwanta.
"Da har na cire rai ba za ki zo ba saboda ganin wannan babban wan na ku ya fito ya bar gidan". Fad'in Hajiya Zuwairah da ta dad'e a cikin motar ta na jiran zuwan Bintyn.
"Ki yi sauri mu bar gidan nan". Fad'in Binty.
Ta da mota Hajiya Zuwairah ta yi ta re da reverse su ka nufi gate.
Tafiya su ka yi ba tsawon mintuna sha biyar ka na Hajiya Zuwairan ta yi parking a bayan wata mota.
"Jira ni ina zuwa". Fad'in hajiya Zuwairah ta re da fita daga motar ta nufi motar gabanta.
Kwankwasa tinted glass d'in ta yi. Zuge glass d'in ta ciki ta yi.
"Kin bar ni ina ta jira Zuwairah". Fad'in matar cikin motar.
"Ke dai ba ri Junaina, da har na d'auka plan d'in mu ba zai yi aiki ba saboda dawowar babban d'an ta daga asibiti, cikin sa'a kuma bai dad'e ba ya fita. Yanzu haka ma muna ta re ita ta na mota". Fad'in Hajiya Zuwairah.
"To ki je ki zo da ita". Fad'in Hajiya Zuwairah.
Juyawa Hajiya Zuwairah ta yi ta re da komawa wajan motarta.
"Yauwa fito Binty". Fad'in Hajiya Zuwairah.
Fitowa Binty ta yi ta na kallon Hajiya Zuwairah ta na son k'arin bayani.
"Yauwa kin ga ba dama in aje ki a gida na saboda Hajiya Mansura ta na yawan zuwa waje na, kuma idan ta gan ki wani bala'in ne zai biyo baya, shiyasa na yanke shawarar ki bi k'awata ki zauna ka min komai ya daidaita, ko y'an aikace-aikace kya tayata".
Shuru Binty ta yi ra d'an wasu dak'ik'u ka min daga bi sa ni ta ce,
"To shikenan zan zauna a wajanta d'in in dai hakan shi zai fitar da Anna daga halin da ta ke ciki.
*A SHA WEEKEND LAFIYA🤪🤪🤪*
🌹 *69-70*🌹
..............."Gaskiya ki na son Anna sosai, kuma kin kyauta don wannan shi ake kira halacci. Mu je ki shiga mota ku wuce". Fad'in Hajiya Zuwairah.
Gaba Binty ta yi ta re da nufar motar Junaina hajiya Zuwairan na biye da ita a baya.
"To Junaina ga ta nan, sai kin ji ni". Fad'in Zuwairah ta re da komawa wajan motarta.
Ita kuma Binty zagayawa ta yi ta re da bud'e gidan gaba ta shiga ta re da gaida Junaina.
Aunty Junaina ka sa amsawa ta yi saboda ganin tsananin kyawun Binty a fili ya zarce na hoto. Murmushi kawai ta yi ta re da tada motar.
Sai da su ka isa bakin gate sannan Junaina ta kashe mota ta re da kallon Binty da ke hawayen kewan Fanan da Anna har da ya barrister tun San da su ka soma tafiya.
"Yarinya ki na jina? Na amincewa Zuwairah za ki zauna da ni a cikin gidan nan bisa ga sharad'i guda biyu ne kawai. Na farko, mai gida na ba zai amince ki zauna da ni ba har sai dai idan matsayin y'ar aiki za ki shiga. Kar ki damu, aikin ba wani mai wahala ba ne, kula za ki rik'a yi da y'ar mijina ta re da yi mata biyyata da kuma gudun b'acin ranta. Sharad'i na biyu kuwa, sai nan gama zan fad'a miki, ina fatan kin fahimta".
Shuru Binty ta yi ta na mai jin gudun hawaye a kan fuskanta. Jinjiga kai ta yi alamun ta aminci don