Showing 120001 words to 123000 words out of 162658 words

Chapter 41 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42911

Daga baya ta tsiri fita ta na had'uwa da shi a can gaban layin su kad'an ba ta re da sanin ko Fanan ba.
Oga Soloman dai kullum ya na ganin ta na fita, amma ba shi da damar magana tun da ba huruminsa ba ne.


Yauwa kamar kullum Yousouf ya kira ta, ta fita. Bayan sun gama zancan su ta shafo hanya za ta dawo gida, daidai lokacin Julaibib ya danno hancin motarsa layin.
Gaban shi ne ya buga saboda ganinta da ya yi ta na ta sauri domin zuwa gida.
Parking ya yi ta re da fitowa, cikin sauri ya k'arasa wajanta ta re da fincikota ya wanka mata mari ka na ya nufi wajan mota da ita ya bud'e ta re da tura ta ciki shi ma ya zagaya ya Shiga.
Babu abunda k'irjinta ya ke yi fa ce bugawa dam dam dam har su ka isa cikin gida.
Ko parking mai kyai bai yi ba ya kamo hannunta ta re da yin part d'in Anna da ita.
"Alhamdulillah Anna ga ta nan". Fad'in Barr Fu'ad da su ka ci nai man Binty ba su ganta ba, hankalin Anna ya yi mugun tashi.
"Ina ki ka je Binty?". Fad'in Anna ta re da k'arisa wajanta.
"Ba na fad'a mini yarinyar nan fita ta ke yi waje ba ta re da izini ba baki yarda ba. To can na ganta ta na ta zuba sauri za ta dawo gida".
Gaban Anna da na Fu'ad a ta re su ka buga dam dam dam. Dai-dai lokacin Alhaji Usman ke saukowa daga stairs.
"Binty ki ji tsoran Allah ki fad'a min gaskiya in da ki ke zuwa".
Hawaye tuni sun soma wanke fuskan Binty jikinta sai rawa ya ke yi har da Fanan da ke gefe wacce tasan idan magana ta fito ta shiga uku don ta sha taimaka mata ta na fita su had'u da Yousouf su fa ke da zuwa saloon ko shopping.
"Ba da ke ake magana". Julaibib ya fad'a da tsawa.
"Kai ban san hauka. Ku yi mata a hankali. Zo nan y'ata ki fad'a min in da ki ke zuwa". Fad'in Alhaji Usman.
Mik'ewa Binty ta yi kamar an tsoma jab'a a koko ta isa wajan Alhaji Usman ta re da tsugunawa.
Zama ya yi a kan kujera ta re da fad'in,
"Da wa ki ke had'uwa idan kin fita?".
Bakinta na rawa ta ce,
"Ka yi hak'uri daddy ba zan k'ara ba".
"Waye shi?". Daddy ya sa ke fad'i.
"Sunan sa Yousouf Muhammad Ahlam". Ta fad'a bakinta na rawa.
"Yousouf Muhammad Ahlam". Julaibib ya maimata sunan.
Yayin da Barr Fu'ad ya ji wani jiri na nai man kaisa k'asa ya yi saurin dafe bango.
"Abun mai sauk'i ne ai. Ai mahaifinsa aminina ne ta re mu ka yi makaranta. Da shi d'in doctorn sarkin Adamawa ne wanda ya rasu. Ai gidan mutanan kirki ne. Da ma d'azu ai na ke maka magana a kan ku shirya kai da Fu'ad za mu je gaida wani d'an sa da ya dad'e bai da lafiya". Fad'in daddy ya na mai kallon Julaibib da idanuwansa su ka yi jazur.
"Ke Binty ka da ki sake yin irin wannan kuskuran kin ji abunda na fad'a miki ko?".
Gyad'a Kai ta yi ta re da fad'in,
"Nagode daddy".
Anna ko haushi ne ya kamata domin ko cikin mafarkinta ba ta tab'a kawo Binty za ta iya fita su had'u da wani a waje ba don ba tarbiyan da ta d'aura su akai ba kenan.
Ba ta re da Julaibib ya ce komai ba ya fice daga d'akin haka ma Fu'ad.
Binty kuwa da Fanan saurin hayewa sama su ka yi.
Su na shiga d'aki Fanan ta turo k'ofa har da murza key ka na ta kalli Binty ta re da fad'in,
"Ke ki na hauka ne Binty? Da ma fita ki ke yi ku na had'uwa da Yousouf duk da an hana mu fita? Mai yasa bakya jin magane Binty?". Fad'in Fanan.
"Ki yi hak'uri Fanan, wallahi idan ya kira ni ne ban iya hak'uri har sai mun had'u tukun na ke samun salama. Wallahi ina matuk'ar k'aunar Yousouf". Fad'in Binty.
"Na san ki na son shi sis, but d'an Allah ki rik'a controlling feelings d'in ki". Fad'in Fanan.
"Ni wallahi tsoro na Anna, na san sai ta yi fushi da ni sosai".
"Gaskiya kam wallahi. Don ba ki ga yadda ta yi da fuska ba". Fanan ta fad'a.
Zama Binty ta yi ta re da zuba tagumi hannu bibbiyu.



*AFTER ISHA*
Gaba d'ayansu cikin shiga iri d'aya. Shadda ce gezna mai matuk'ar kyau da maik'o kalar sararin samaniya a jikinsu. Fu'ad ne ke tuk'i yayin da Julaibib ke gidan gaba Alhaji Usman kuma a gidan baya su ka nufi gidan Alhaji Muhammad Ahlam da ke Maitama.
A gaban babban gate d'in gidan Barr da ke ji kamar zuciyarsa za ta buga ya danna horn.
Cikin 'y'an seconni mai gadi ya wangale gate d'in gidan.
Alhaji Muhammad Ahlam da kan shi ya zo ya ta re su cike da fara'a ta re da kai su parlourn bak'i.
Nan da nan aka cika masu gabansu da abinci da kuma drinks.
"Alhaji mu k'ara gaisawa, ina wuni ya harkoki da kuma iyalai?". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam.
"Alhamdulillah, ya na k'ara harkokin da kuma mai jiki?". Fad'in Alhaji Usman.
"To, sai dai mu ce alhamdulillah". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam a sanyaye.
Ajiyar zuciya ya saki ta re da fad'in,
"Allah ubangiji ya ba shi lafiya". Fad'in Alhaji Usman.
Gaba d'aya daga Barrister har Julaibib su ka gaishe sa ta re da tambayansa ya mai jiki.
Amsa masu ya yi da alhamdulillah ta re da fad'in,
"Wannan shine babban d'an ka Julaibib ko? Shugaban gwagwaran Africa ko?". Alhaji Muhammad ya fad'i hakane ya na dariya.
Shima Julaibib d'in murmushin yak'e ya yi don shi ka d'ai yasan mai ya ke ji a zuciyarsa.
"Shi ne nan". Fad'in Alhaji Usman.
Kallon shi Alhaji Muhammad Ahlam ya yi ta re da fad'in,
"Kai Julaibib, ga mata nan da yawa a gari. Ka fiddo mata ko mu yi maka irin na da". Fad'in Alhaji Muhammad ya na dariya.
Murmushin dai ya sake yi wanda bai kai ciki ba.
"Mu je ciki ku ga jikin na shi ko". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam.
"OK muje". Fad'in Alhaji Usman ta re da mik'ewa dukan su suka fito daga part d'in su ka yi cikin gida.
Kusan gaba d'aya gidan ne a kan mara lafiyan wasu na kuka wasu na addu'a.
Su kan su Julaibib, Fu'ad da Alhaji Usman sai da jikinsu ya yi matuk'ar sanyi.
Ga mutun nan dai a kwance amma kamar gawa, abinci ta drip ake ba shi.
Sosai su ka masa addu'a ka na su ka fito jiki a mace.
D'akin bak'i su ka koma su na k'ara jajantawa Alhaji Muhammad Ahlam d'in.
Alhaji Usman ne ya gyara zama ta re da fuskantar Alhaji Muhammad Ahlam ta re da fad'in,
"Ni ko a cikin y'ay'an ka wanene yusouf?".
Kallon shi Alhaji Muhammad Ahlam ya yi ci ke da mamaki ta re da fad'in,
"Yawan y'ay'an har ya sa ba ka iya banbance su kenan? Ai Yousouf shi ne mara lafiyan da ke kwance. Yanzu haka watan shi biyar a kwance wanda a da k'ark'ari wata uku ya ke yi ya mik'e, amma wanna karan ya kai har wata biyar, ko lokacin ne ya yi". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam.
Daga Alhaji Usman, Fu'ad da barrister gaba d'aya zaro idanuwa su ka yi su na kallon Alhaji Muhammad cike da mamaki.
"To idan har Yousouf na kwance wata biyar bai motsi, wanene wanda Binty ke fita su na had'uwa?". Fad'in Julaibib a zuciya wanda Fu'ad shi ma tunanin da ya ke yi kenan.





*_______________*
"Hello ki na jina kuwa?". Da fad'in Yousouf.
"Ina jin ka masoyi, na k'osa ka fad'amin wallahi".
"Kin tuna min yi wa junan mu alk'awatrin zamu rayu da junan mu a kowani irin hali, kuma d'aya ba zai guji d'aya ba?". Fad'in Yousouf.
"Kwari kuwa, kuma ba zan tab'a canzawa a kan haka ba". Fad'in Binty da ke juyi a kan gado ta na kallon zoben da ke hannunta da Yousouf ya sa ka mata.
"Binty akwai abunda na dad's ina b'oye miki saboda gudun ka da ki gujemin".
"Haba reality, mai ba ka guje min ba bayan ka san ni ba kowa ba ce, sai ni CE zan guje maka. Sam ba zan tab'a guje maka ba ko kai wanene". Fad'in Binty.
"Kin tabbata mai sona?". Fad'in Yousouf.
"Na tabbata masoyi". Fad'in Binty.
"Mai sons ni da ke jinsun mu ba d'aya ba ne. Ma'ana ni aljani ne".
Dariya Binty ta bushe da shi ta re da fad'in,
"Yau kuma zolaya ka ke jin yi?". Fad'in Binty ta na dariya.
"Ba ki yarda ba kenan? To ban minti d'aya". Ya na fad'in haka ya kashe wayar.
Kallon screen d'in ta yi still ta na dariya.
Wani irin zabura ta yi ta re da mik'ewa ta zaro damuwa sakamakon ganin Yousouf da ta yi a jikin bango zaune a kan kujera.
"Binty kar ki tsorata, bayyana miki wanene ni ya zama dole saboda tone-tone da babanki na nan gidan da y'ay'ansa su ka yi. Binty na dad'e ina d'awainiya da ke tun ki na jaririya. Ke ce macen da na fara so....".
Wani irin ihuu Binty ta yi ta re da zubewa a k'asa sumammiya. Dai dai lokacin Fanan ta turo k'ofar ta shigo........









*DAN DAN DAN! MUJE ZUWA*



*PAID BOOK 08128755583*
🌹 *65-66*🌹
.............."Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Binty, Binty, mai ya sa me ki?". Fad'in Fanan ta re da k'arasawa wajanta ta na jijjigata amma ko motsi ba ta yi.
Da gudu Fanan d'in ta sauko k'asa ta na ihun kiran Anna da ke zuba Andrew liver salt a cikin cup saboda cikinta da ya lumbura sakamakon cin alale mai zafin da ta yi.
A zubure Anna ke kallonta ta re da fad'in
"Mai ya faru ke?".
"Anna Binty ce.... Ta.. Ta mutu. Ta na kwance ko motsi ba ta yi". Fad'in Fanan jikinta na rawa.
Da gudu-guda Anna ta yi sama ta re da tura d'akin su Binty da k'arfi saboda yadda ta rud'e ta yi wajan Bintyn da ke ya she a k'asa ba numfashi.
Jijjigata ta soma yi ta na salati da kiran sunanta amma shuru.
"Ban ruwa Fanan". Fad'in Anna ta na k'ara jijjiga Binty.
Cikin sauri Fanan ta yi cikin toilet saboda rud'ewa ta d'ebo ruwan ta kawo mata.
Hannu hannunta har rawa ya ke yi wajan karb'a ta d'iba ta shafa mata har sau uku a fuskanta, amma shuru ba ta farfad'o ba.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Fanan d'auko min wayata a parlour". Fad'in Anna.
Da gudu Fanan da ke kuka ta fito ta d'auko wayar Anna ta re da dawowa d'akin ta mik'awa Anna wayar.
"Kira min Julaibib ki saka a hands free".


*************
"Ku ma ba ka da wani d'an mai suna Yousouf bayan mara lafiyan?". Fad'in Alhaji Usman.
"Gaskiya ba bu, wanda ka ga ni dai a kwance shi ka d'ai ne d'ana mai suna Yousouf. Wani abun ne ya faru?". Fad'in Alhaji Muhammad Ahlam.
"Lallai kam da kwai matsala, don wani me ke zuwa wajan y'ar waje na, kuma sunan da ya fad'a shine Yousouf Muhammad Ahlam". Fad'in Alhaji Usman.
"To gaskiya k'arya ya ke yi ina ganin irin y'an yaudaran nan ne kawai. Ni d'ana ma a tarihin rayuwarsa sam bai tab'a budurwa kuma haka na da nasaba da lalurar shi don ya ce ba zai auri yarinyar da zai zama mata liability ba". fad'in Alhaji Muhammad Ahlam.
Jikin Julaibin har ya soma tsuma ta re da rayawa a zuciyarsa irin mugun rashin mutuncin da zai yi wa wannan d'an iskan saurayin da ya ke k'arya da sunan wani ya na yaudarar Binty.
Fu'ad kuwa ya yi wa kan sa alk'awarin ba zai cuci kan sa ba, su na komawa zai fallasa sirrin zuciyarsa a wajan Binty idan ya so a yi masu aure kawai kowa ya huta.
Wayar Julaibib ce ta shiga ringing. Kasancewar ringing tone d'in da ya sawa Anna da ban ne shiyasa ya gane ita ke kiran wayar.
Fiddota ya yi daga cikin aljihu ta re da picking ya daura a kunnansa.
"Julaibib duk in da Ku ke ku dawo yanzu Binty ba ta numfashi".
Mik'ewa ya yi da sauri ta re da fad'in,
"Ga ni nan zuwa yanzu nan".
"Mai ke faruwa?". Fad'in Alhaji Usman.
"Anna ce ta kira Binty ba lafiya".
Cikin sauri Fu'ad ya mik'e, Alhaji Muhammad kuwa cewa ya yi,
"Subhanallah! Ku hanzarta ku je Ku ga halin da ta ke ciki".
Tuni har Julaibib ya fice Fu'ad bi ye da shi. Shi ya zauna a driver seat ya yin da Fu'ad ke gefensa. Alhaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login