Showing 51001 words to 54000 words out of 162658 words
min abunda na miki sai in ba ki hak'uri kin ji".
Wani haske Binty ta ga ni ya gilma ta fuskanta sai da ta yi saurin dafe kuncin ta saboda azababbar zugin da ta ji a wajan.
Fanan da ke lab'e sai da ta zaro idanuwa jikin ta ya soma rawa domin ta san Binty ba ta san miye fad'a ba, domin ba za ta tab'a iya rama abunda Sabrin d'in ta mata ba. K'ok'arin fitowa ta soma yi daga mab'uyar ta domin ta isa wajan da su ke. K'amewa ta yi k'am, mamaki ya cika ta ta re da zaro idanuwan ta sakamakon wani irin mik'ewa da Binty ta yi ta d'auke fuskan Sabrin da mari ta re da fad'in,
"Bazan d'auka ba. Anna ta fad'i min ka da na saki na zalinci wani, kuma ka da ba bari a zalince ni. Na tambaye ta menene zalinci, kuma ta min bayani. A bayanin da tai min, irin wannan abun da ki ka min yanzu, zalinci ne. Duk da Anna ta ce min in kasance mai hak'uri da juriya, amma ba zan iya hak'uri da wannan abun da ki ka min ba shiyasa na rama. Da kin fad'a min abundan na miki, da ni kuma zan ba ki hak'uri kamar yadda ki ka buk'ata. Ko yanzu ma ki ka fad'a min abunda na miki, zan ba ki hak'uri". Fad'in Binty ta na kallon cikin idanun Sabrin da ta mutu da mamaki. Domin idan aka cire mahaifiyar ta, babu wani mahaluk'in da ya tab'a saka hannu ya mari fuskan ta sai wannan yarinyar da ke gabanta da ta ke jin tsantsar tsanar ta har cikin b'argon ta.
"Binty, mai ki ka tsaya yi a nan wajan? Kun manta abunda na fad'a muku ko? To zo mu wuce. Ina Fanan d'in?". Ya Fu'ad ya fad'a.
Saurin juyowa Binty ta yi ta re da nufo in da ya ke ta ce,
"Yaya anan na bar ta, ban san in da ta yi ba". Fad'in Binty ta na waige-waige.
Fanan na jin su, sai da su ka yi d'an nisa ka na ta kalli Sabrin da har a wannan lokacin ta na rik'e da kuncinta idanuwan nan na ta ya kad'a ya yi jazurr.
Cikin sand'a Fanan ta bi bayan su Binty ba ta re da Sabrin d'in ta gan ta ba ta na jin wani irin farin ciki ya mamaye zuciyar ta saboda yadda Binty ta wanke fuskan Sabrin da mari.
Sabrin da ke tsaye kamar statue kuwa, ji ta ke kamar ta k'ona kan ta a wajan da ta ke. Abubuwa sun had'u mata goma da ashirin. Ga wanke fuskan ta da mari da Binty ta yi, ga kuma tsananin tashin hankalin da ta ke ciki na ganin wacce ta ninninkata a kyawu.
Wani irin k'ara ta saki mai k'arfi wanda ya saka hankalin mutane dawowa gare ta, wasu kuma da gudu suka nufo inda ta ke...........
*DAN ALLAH KU YI HAK'URI DA RASHIN JI NA JIYA. GAJIYA CE WALLAHI. GA SUNAN DA MU KA SHA NA YA TA, GYEFE GUDA KUMA JIYAN OGA NA YA DAWO DAGA TAFIYA. SHIYA BAN MUKU TYPING BA. AMMA GA WANNAN DAI KU YI HAK'URI DA SHI*
*PAID BOOK 08128755583*
🌹 *29-30*🌹
.........."Lafiya Sabrin, what happen?". Amrah y'ar wajan aunty Junaina ta tambayeta. Yayin da Hanan tagwainiyar Amrah ta tab'e baki ta re da kallon gyefe. Bodyguard d'in da aka had'o su da ita kuwa, tuni har sun zagaye ta su na tabayarta abunda ke faruwa.
"Take me homeeee". Sabrin ta fad'i a tsawace kamar tana magana da sa'o inta.
Dogon tsaki Hanan ta ja ta re da yin gaba. Amrah ta bi bayan ta, ya yin da bodyguard su ka yi gaba, wasu kuma su ka tsaya a bayanta ita kuma ta kasance a tsakiya har wajan katuwar ranger over bulletproof.
Bud'e mata su ka yi ta shiga gaban baya. Dama y'an biyu ba mota d'aya su ke shiga da Sabrin ba, komai na ta daban ne. Ba ta yarda ai mata abu iri d'aya da su ba.
Ta na shiga cikin motar ta b'arke da kuka ta re da had'e kai da gwiwa. D'agowa ta yi ta re da shafa kumatunta ta furta,
"She slapped me". Ta fad'i hakane ta re da k'ara rushewa da kuka.
"Wallahi sai na nai mo yarinyar nan na ga uban da ta ke tak'ama da shi, sai na lalata fuskan da ta ke tak'ama da shi in kuma yanke hannun da ta yi amfani da shi ta tab'a fuska ta".
..........."Ai kun yi na farko kun yi na k'arshe. Ban k'ara fita da ku. Kun san dai Anna ta ce ka da mu dad'e, shi ke Fanan har da shigewa wani wajan muna ta nai ki". Fad'in Yaya Fu'ad ya na gallawa Fanan harara.
"Sorry bro, wani tedy na je nai ma". Fad'in Fanan.
"Tedo ba tedy ba. Ai gobe ma rana ce yara".
"Yi hak'uri yayan muuuuuuu". Fad'in Binty a cikin kunnen sa da k'arfi sai da ya saka kafad'arshi ya toshe kunne d'aya.
"Binty za ki cire min kunne ne? To na ji na hak'ura tun kan ku sa ni hatsari. Koma ki zauna". Fad'in Yaya Fu'ad.
Ko ma wa Binty ta yi ta zauna ta re da d'aukar chocolate ta b'are ta saka a baki. Can kuma ta gutsiro chocolate d'in ta sai saitin bakin Fu'ad ta re da fad'in
"Eat bro". Ta fad'i hakane ta re da tura masa chocolate d'in a baki.
"Iyyeeeeeh, k'anwata ta iya turanci. Ahh lallai. Idan har ki na k'ok'ari haka, to na miki alk'awari duk weekend sai na kai ki shopping. Ki yi k'ok'ari ki iya turanci". Fad'in Yaya Fu'ad.
"Yaya ni kuma na maka alk'awari zan ko yi turanci har in fi Fanan iyawa ma. Ai Fanan za ki koya min ko?". Ta k'arisa maganar ta re da kallon Fanan d'in.
"Zan ko ya miki amma sai ni ma Yaya ya min alk'awari ta re zai rik'a kai mu shopping d'in". Fad'in Fanan ta na gutsirar chocolate.
"To shikenan. Idan har ki ka yi k'ok'ari ki ka koya mata ta iya da kyau, to ta re zamu rik'a zuwa shopping d'in". Fad'in Yaya Fu'ad.
"I promise daga yau zan fara koya mata. Magana ma mun dai na yi da hausa, daga turanci sai fulatanci". Fad'in Fanan.
"Yauwa y'ar k'anwata. Ke kuma Binty sai ki dage kin ji".
"To Yaya zan dage". Fad'in Binty.
Haka su ka yi ta hira har su ka iso gida. Kamar yadda Anna ta ce, haka ya yi, sai da ya kai su har sama cikin d'akin ta, ka na ta fito ya koma na shi side d'in domin yai wanka ya d'an huta.
Da daddare bayan Anna ta shigo as usual ta duba su ta fita ta re da rufo masu k'ofar. Fanan ta ta shi zaune ta re da kira sunan Binty.
Ita ma Bintyn ta shi zaunen ta yi ta re da fad'in,
"Fanan mai ya faru?". Binty ta fad'i ta na tab'a jikin Fanan d'in.
"I saw what you did a cikin shopping mall d'in nan. Kin mari yarinyar nan. Na ga ni ai". Fad'in Fanan ta na kallon Binty duk da ba haske a d'akin don Anna sai da ta kashe wutan d'akin ka na ta fice.
"Ai ita ta fara mari na ban san mai na mata ba. Kuma Anna ce ta ce min ka da na yarda a cuce ni".
"Ai ni ma ban ce kin yi laifi ba, da ma na tsani yarinyar wallahi. Sam ba ta da kirki bare mutunci". Fad'in Fanan.
"Kin san ta ne Fanan?". Binty ta tambaye ta.
"School d'in mu d'aya da ita. In fact ajin mu d'aya da ita. Ni ina gaba, ita kuma ta na baya. Ina fad'a miki yarinyar sam ba ta da kirki. Ga nu na isa da mulki kamar d'iyar sarauta. Ko Anna da ke jinin saurata ba ta irin abunda ta ke yi. Ko fa siblings d'in ta hake ta ke masu. Hmm Sabrin, she's very wicked. Ai na k'osa ki shiga makaranta. Na san za ki samu fans da yawa fiye da ita".
"Miye fans?". Binty ta tambaya.
"Masoya mana". Fad'in Fanan.
"Ni ma na k'osa in shiga makaranta in dai na zama a gida. Ina so in yi karatu sosai in zama kamar Yaya Fu'ad". Fad'in Binty.
"Lawyer ki ke so ki zama kenan? Ai ya Fu'ad barrister ne. Shi ma law ya karanta ai. Big bro kuma ya karanta Medicine. Kuma har yanzu karatu ya ke yi".
"Waye bigi bro kuma?". Fad'in Fanan.
"Za ki fara shirman ko. Ba bigi na ce ba, big, big, big bro. Maimaita inji". Fad'in Fanan.
"Big bro. Ai na iya tsokalar ki na ke yi. Ai tun tuni ki ka koya min". Binty ta fad'a ta na dariya.
"Mu kwanta ka da Anna ta ji motsi. Kin ga kuma gobe Monday akwai school".
"Okay bye, sai da safe". Fad'in Binty ta re da kwanciya.
*___________________*
Alhaji Usman Mai Rabo, d'an asalin jihar Gombe ne. Wato fulanin gombawa. Su takwas ne a wajan mahaifan sa. Idris shi ne babba, sai Mika'ilu, sai Lukman sai shi Usman sai Abubakar, sai Lurwanu, sai Shafi'i sai autar su da ta kasance mace Rumana. Su na da rufin asirin su dai-dai gwargwad'o. Mahaifiyar su mai su na Khadija, mace ce y'ar boko, haka ma mahaifin su mai su na Adamu. Shiyasa su ma su ka ta so gaba da son boko.
Tun daga kan Mika'ilu har zuwa Rumana, sai da su ka had'a degree su ka yi aure. Kuma gaba d'ayan su aikin gwamnati su ke yi idan ka d'auke Alhaji Usman Mai rabo. Shi a Abuja ya yi karatunsa wajan wan mahaifin su Baba Salisu. Shi ya rik'e sa saboda shi Allah bai tab'a ba shi haihuwa ba, shiyasa k'anin na sa Alhaji Adamu ya ba shi Usman halak malak.
Tun daga primary sa har zuwa jami'a ana abuja ya yi sa. Alhaji Usman ya na da kaifin fahimta sosai. Ya samu sunan mai rabo ne a wajan wan mahaifin na sa saboda a cewar shi shi mai rabo ne a rayuwa kuma ina sha Allah duk abunda ya tab'a sai ya yi albarka.
A jami'a su ka had'u da Na'ima d'iyar k'anin sarkin gombe. Sosai kowa ya yi mamakin kasancewar ta re kasancewar kusan kowa ya san wacece ita.
Babu abunda ya burge Alhaji Usman a wajan Na'ima sai rashin jijji da kai da kuma d'agawa irin na y'ay'an masarauta wanda ya kasance a jinin su ya ke.
Farkon tarayyar su ba da soyayya ya soma ba, abunda ba ta gane ba ya ke koya mata. A hankali a hankali abun ya juye zuwa soyayya mai zafi wanda ko k'adan ba su son abun da zai gifta ya rabasu. Musamman ma alhaji Usman don gani ya ke shirman banza ya ke yi, shi da ba shi da komai, ta yaya zai samu d'iyar k'anin sarkin gombe a matsayin mata gare shi.
Kasancewar shi ya na level 4 ita kuma ta na level 2, ya riga ta kammala makaranta har ya ta fi service. Cikin hukuncin ubangiji, ya na fitowa ya samu aiki da EFCC.
A lokacin ne kuma Na'ima ta koma gida gombe Hutu. Da ma mahaifiyar ta ta san labarin Usman kaf don duk ta je hutu sai ta mata maganar shi. Usman kaza, Usman kaza.
Da ya ke matar mutum k'abarin sa, Usman ya shaidawa mahaifin sa shi fa ga wacce ya ke so. Sam wan mahaifin na sa bai ji d'ar ba, ya kwashi jiki shi da abokan arziki da y'an uwa su ka nufi Gombe. Cikin mutunci kuwa aka karb'e su. Bayan sun karanto abunda su ke tafe da shi. Iyayan Na'ima su ka ce su je za su yi bincike akan yaro, za su nai me su daga baya.
Haka kuwa aka yi, cikin k'ank'anin lokaci aka kira su ta re da shaida ma su an basu.
Tu ni har an gama komai kamar ba jinin sarauta ba. An kai sadaki dubu d'ari da duk wani abunda ya ka mata. Bayan an d'aure aure aka had'o ta da kuyangi ta ce ita ba ta so bautar aure ta zo yi ba a yi mata bauta ba.
Dama wan mahaifin na sa ya ba shi gida self-contained a nan cikin abuja mai kyau. A nan su ka cigaba da rayuwar su mai dad'i da kyautatawa juna. Har ta haifi d'an ta na fari aka saka masa suna Salis, takwara ya yi wa marik'in na sa, sai ake kiran sa da Julaibib.
Julaibib na da shekara uku, aka kori Alhaji Usman a wajan aiki sakamakon sharri da aka k'ulla masa akan an binciki wani da satan Mayan gwamnati, shi kuma ya bai wa Alhaji Usman d'in cin hanci UA rufe case d'in.
Sosai su ka shiga wani yanayi na rayuwa. Ga shi an buga can, an buga nan ba'a samu aikin ba. Haka nan ya fad'a sana'ar hannu domin ya rik'a iyalan sa. Babu sana'ar da bai yi ba har da ga ruwa da sai da pure water a tasha. Daga k'arshe ya wani bawan Allah ya ba shi taxi ya soma ja a cikin garin Abuja. Wata rana ya d'auki wani bawan Allah a cikin taxi d'in, sai bawan Allah ya mantuwar jakar sa. Kuma dama ya na sauke bawan Allahn nan gida ya ni niyyar komawa. Kwatsam sai ga jaka. Ya na bud'e wannan jakar yar arba da mak'udan kud'ed'en da ya firgita shi. Sai cikin hukunci ubangiji sai ya ga katin shaida na wannan mutumin. Cikin daran nan sai da ya bi diddigi har ya ga no gidan mutumin nan ya kai masa jakar nan.
Mutumin kuwa shi har ya cire rai da ganin kud'in saboda yadda duniyar ta lalace na Allah sun yi k'aranci sai ga Alhaji Usman da jakan kud'i ya kawo masa kuma sile bai yi ciwon kai a ciki ba.
Sosai bawan Allah ya din ga gode masa ta re da saka masa albarka. Daga k'arshe saboda dad'in da ya ji dama shi d'in d'an kasuwa ne, sai ya tsunduma shi cikin business d'in sa shi ma ya rik'a samu. Dama kaya ne kala-kala ya ke order daga k'asar waje ana kawo masa ta cikin ruwa. Ba k'aramin mai kud'i ba ne. Domin sai ka ga k'aton jirgin ruwa ya yi lodin kaya kuma na sa ne shi kad'ai.
A hankali a hankali aka soma damawa da Alhaji Usman, cikin k'ank'anin lokaci kasancewar ya na da basira da kuma amana ga shi ya iya mu'amala da customer, shi ma ya soma yin order kamar yadda uban gidan na shi ya shawarce shi da kuma ba shi jali mai tsoka.
Tuni ya soma shigowa da su keke napep, motoci, kayan Kitchen, shaddo ji da lesuka, da duk wani kayan electronics. Tuni shima ya soma suna saboda ka yan shi ma su ingan ci ne da kuma rahu sa.
Ya bud'e tank'ameman mall. Lokacin y'ay'an sa uku. Bayan Julaibib, an sa ka haifan Fu'ad, sai k'anin sa Zaid. A wannan lokacin ne kuma Alhaji Usman ya k'ara aure ya auro Mansura yar gidan wani babban malamin zaure, zuwan ta ba dad'ewa ta haifi y'a mace mai suna Shema'u, bayan shema'u ta haifi Suhail wanda tun daga nan ba ta k'ara haihuwa ba. Bayan Mansura alhaji Usman ya sa ke auro wata mai suna Huriya, tantagaryar y'ar kasuwa kenan, don a wajan kasuwancin sa ma su ka had'u. Ita ma dai ta haifi d'iya d'aya da shi mai suna Sunainah.
Sam Hajiya Huriya ba ta damu da harkan matan mijin ta ba, ita kawai ta yi Sana'a ta rik'e kud'i. Ya yin da Hajiya Mansura kuwa, aurar ma gaba d'aya ta yi sa ne don ka da jama'a su saka mata idanu. Sam ita namiji ba ya gaban