Showing 72001 words to 75000 words out of 162658 words

Chapter 25 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42986

"Love at first sight ko? Na ga wannan. Wannan irin kasa control d'in kai haka, lallai Yusuf ya daki zuciyar ki lokaci guda. To ki kwantar da hankalin ki, domin shi ma ya fowler, ba kuma ba shi numbern ki, sai ku yi ta k'onewa, amma kuma kar ki sake Anna ko ya Barrister su sani, na san ba ki manta dukan da ya barrister ya wa wannan anacin da ya din ga biyo ki tun daga wajan saloon ba har cikin gidan nan. Kar ki manta ya Barrister ya ce ba yanzu za mu fara kula samari ba, kuma Anna ta goyi da bayan shi. Saboda secret love za ku yi kamin a ba mu dama".
Ya mutsa fuska Binty ta yi ta re da fad'in,
"I don't understand, ki na nufin kin ba shi number ta, to wa ya saki? Ni fa kawai burge ni ya yi ba wai son shi na ke ba. Kin b'ata min rai. Ai wannan jawo min zubewar aji za ki yi". Fad'in Binty har da wani shan mur.
"Iyyyeeee, to ki sa ni bariki dai babu riba. Ki fad'a uban da bai san halin ki ba. Ke ni fa ko da d'uwawu ki ka yi magana sai na fahimci abunda ki ka ce bare na ga abu b'aro-b'aro. Maza ki kula da titi".
Dariya Binty ta yi sosai ta re da fad'in,
"Ban ga ne in kula da titi ba".
"Eh saboda motoci mana". Fad'in Fanan ta na hararar Binty.
Dariya Binty ta yi ta re da fad'in,
"Wai dan Allah dagaske ya karb'i number ta?".
"Ni ma ban sa ni ba". Fad'in Fanan ta re da kallon window.
"Haba sister, dan Allah ki fad'a min mana. Na bar miki autan, yanzu ke ce autares d'in Annan mu".
Harara Fanan d'in ta k'ara sakar mata ta re fad'in,
"Bariki".
"Ke dai kalmar bariki ta ka ma bakin ki. Dan Allah Sister ya ki ka ga guy d'in, ya had'u sosai ko?". Fad'in Binty.
"Kamar saman alalen gwangwani kuwa". Fad'in Fanan ta na dariya.
"Wallahi k'arya ki ke yi, sai dai idan ba za ki fad'i gaskiya ba. Amma Yusuf had'ad'd'an guy ne wallahi. Komai na shi mai kyau ne. Fuskan shi, tsayin shi, maganar shi, murmushin shi, kai infact everything".
Ba ki sa ke Fanan ke kallonta ta re da fad'in,
"Har yaushe ki ka san shi haka da za ki ce everything about him? Yaushe ki ka san everything d'in?".
"Man ta kawai, amma sincerely speaking guy d'in ya yi over". Fad'in Binty.
"Kar dai ki haukace". Fanan ta fad'a ta re da daukar wayar Bintyn da ke kan ciyarta ta yi kwafe numbern Yusuf a wayarta ta re da sakawa a wayar Bintyn ta yi mata saving da Mr Right ta re da mik'a mata wayar.
"Ga shi nan na miki saving numbern shi, kin ga da ya kira kin san ko waye, saura ki yi shirme". Fad'in Fanan.
Karb'ar wayar ta yi ta re da tsurawa numbers d'in idanuwa. Cikin minti d'aya ta haddace numbers d'in kasancewar special number ce.
Labarin Yusuf su ka din ga yi har su ka kai gida. Cikin ikon Allah kuwa, har wannan lokacin Annah ba ta dawo ba.

...........Ko da su ka shiga d'akin su, sallar la'asar su ka yi kasancewar a hanya ta riske su. Bayan sun idar kuma su ka d'aura hirar Yusuf.
Sai k'arfe biyar su ka sauko don d'aura girki saboda tun sa su ka kammala makaranta su ke girkin dare. Idan wannan ta yi yau, gobe wannan za ta yi, ko kuma su had'u su duka su yi ta re, haka Anna ta tsara masu.
Su na kitchen Fanan na gyara kayan miya, Binty kuma na blending, Fasila ta shigo. Sai da ta fakaici idanu ta watsawa Binty harara wacce ba ta ma San ta na yi ba, ka na ta yi gyaran murya duk su ka juyo su ka kalle ta ta re da fad'in,
"Aunty Fasila ke ce?". Hakan su ke kiran ta, kasancewar ta girme su kusan da shekaru biyar. Don ita za ta kai ishirin da uku, su kuma sha takwas gare su.
"Autan Anna sannun ku da aiki". Fad'in Fasila ta na murmushi.
"Yauwa aunty Fasila". Ga ba d'ayan su suka amsa.
Fasila mai da duban ta ta yi izuwa ga Binty ta re da fad'in,
"Binty Hajiya Mansura na kiran ki, ta ce ki zo yanzu".
Zaro idanuwa Binty ta yi ta re da fad'in,
"Na shiga uku! Wallahi na man ce ta ce idan mun dawo in zo in sa me ta".
"To ai sai ki hanzarta yanzu ki je ki ji kiran da ta ke miki. Ba ri ni na taya Fanan mu yi aiki".
Binty ta ce,
"To aunty nagode". Ta fad'i hakane ta re da tara hannun ta a panpo ta wanke ka na ta goge hannun ta towel ta re da cire apron d'in da ke ji jikinta ta aje a wajan da ake rataye shi a nan kitchen d'in ka na ta fito daga kitchen d'in ta d'auki hijjab d'in ta da ke parlour ta saka ta fito ta yi hanyar part d'in Hajiya Mansura.
Za ta iya rantsewa da Allah yau ne karo na hud'u shigowarta part d'in Hajiya Mansuran. Gwara ma part d'in Hajiya Huriya, kasancewar ta na da d'iya mai suna Sunaina, to su kan d'an shiga wajan don ita kan ta Sunaina irin d'abi'ar mahaifiyar ta gare ta na nai man kud'i. Ka na duba status d'in ba bu abunda za ka ga ni sai uban kayan kitchen da lesis da atampopi har da kayan yara da ta ke ordering d'in su idan mutane sun mata magana su na so sai a kawo mata ta ruwa, sea shipping.
Ba bu kowa a parlour, sai y'ar aikin ta Wasila da ke goge dinning.
Kallon ta Wasilan ta yi ta re da hararar ta k'asa-k'asa ka na ta ce,
"Ki hau sama, ta na can ta ke idan kin shigo ki je ki same ta". Fad'in Wasila kamar ta na da cuta a mak'ogwaro.
Ba ta re da Binty ta ce komai ba ta haura sama. Sai da ta yi knocking aka ba ta izinin shiga kamin ta saka kai cikin d'akin.
Kwance ta taras da Hajiya Mansuran daga ita sai brezia da underwear, ga ta ba ka d'an, don Mansura irin shiirgegiyar matan nan ne kamar giwa.
Kawar da kai Binty ta yi don ta ji kunya da ta ga Hajiya Mansuran a haka.
"Ina wuni Hajiya?". Binty ta fad'a ba ta re da ta kalle ta ba.
"Lafiya lau. Ya a ka yi na ce idan kun dawo ki zo ki same ni, amma ba ki zo ba. Ko Na'ima ta hana ki zuwa waje na ne?". Fad'in Hajiya Mansuran.
Girgiza kai Binty ta yi ta re da fad'in,
"A'a wallahi. Anna ma ba ta nan. Mancewa na yi da muka dawo shiyasa ban zo ba".
Kallon Binty ta ke yi ta na jin kamar ta tashi ta rungumeta ta re da sauke sha'awarta. Ji ta ke wani irin wutar sha'awar Bintyn na taso mata tun daga kwakwalwarta.
"Zo ki zauna a nan, wani d'an abu za ki min". Fad'in Mansura ta re da nuna mata gefen ta.
K'arasowa Bintyn ta yi ta re da zama a wajan da Hajiya Mansuran ta nu na mata.
Shafa bayan Binty ta yi ta re da fad'in,
"Yarinya ta tubarkalla ki na da kyau mai d'aukar hankali, ina ma ki zamo suruka ta".
Banbara kwai haka Binty ta ji maganar, wai suruka. Tur Allah ya kiyaye mai za'a yi da Suhail a matsayin miji.
Duk cikin zuciyar ta ta yi wannan maganar.
"Jiki na duk ya min tsami wallahi. Kin san jikin tsufa. Dan Allah massage na ke so ki min in ji dad'in jikin nawa". Hajiya Mansura ta fad'a ta na k'ara shafa bayan Bintyn.
Binty ba ta kawo komai a ranta ba, don Annah ma ta na sa su ita da Fanan su danna mata jikin ta har k'afafu.
Ruf da ciki Hajiya Mansura ta yi, ita kuma ta shiga danna mata jikin tun daga k'eyarta har k'afafunta.
Tuni Hajiya Mansura ta soma lumshe idanuwa, kasancewar ta saka wani abu daban a cikin zuciyar ta, sai ta ke ji kamar Bintyn romancing d'in ta ta ke yi.
Binty ta fi k'arfi minti talatin ta na yi was Hajiya Mansura massage. Sai da Hajiya Mansura ta gamsu don bala'i, ka na ta ce wa Binty ya isa ta re da kwararo mata godiya har da mata kiss a kumatu.
Ita kuwa baiwar Allah ba ta kawo komai a ranta ba, ta fice daga d'akin.
A k'ofar fita daga part d'in su ka yi kicib'is da Suhail shi kuma zai shiga wajan mahaifiyar sa.
"Keee!". Suhail ya fad'i ya na k'are mata kallo har da had'iyar yawu.
Gitta shi ta zo yi za ta wuce, aikuwa ya damk'i hannunta da k'arfi ta re yin side d'in shi da ita.
Binty turjewa ta ke yi, amma Sam ya k'i sakin ta gashi ba bu kowa balle wani ya cece ta.
Sai da ya kai ta har kan gadon shi, ka na ya yasar da ita ta re da yi mata rumfa..........








*PLEASE MANAGE, WALLAHI INA WANI AIKI NE MAI MAHIMMANCI*


*MATAR SAYYADEE*
🌹 *41-42*🌹
.............Wani ihu mai k'arfi ta saki sakamakon jikinsu da ya had'u waje d'aya da ya haifar mata da wani azaba a saman fatanta kamar ana d'iga mata ruwan dalma.
Hannun shi ya saka ta re da toshe mata baki, d'ayan hannun Ku ma ya soma yawo da shi a jikinta.
Binty ba ta san sanda ta saka duka k'arfinta ta cire hannun shi a kan bakinta ba ta re da k'ara sakin wani k'aran. Saboda the more hannun shi na tab'a jikinta, the more azabar da ta ke ji a jikinta na k'aruwa.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel, inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Dan girman Allah ka dai na tab'a ni. Fatan jikina na k'onewa. Na shiga uku Anna ki cece ni". Binty ta fad'i da k'arfi, amma babu mai jin ta saboda d'akin a rufe ya ke, ku ma ko za ta kwana ta na ihu babu mai jin ta.
Mari ya d'auke ta da shi ta re da fad'in,
"Uban baban ki, wallahi ko wa ya tsaya miki yau sai na d'and'ana roman ki, ba zai yu ki zauna a gidan nan mahaifi na na kula da ke ba, ba dangin iya ban mori wannan kyakkyawan jikin na ki ba. So gwara ma ki tsaya mu yi cikin jin dad'i, in ji dad'i ke ma ki ji". Fad'in Suhail ya na k'ok'arin farke rigar jikin na ta.
Wani irin nin kin azaba ta ke jin a jikinta duk sa'adda ko farcensa ne ya tab'a jikinta.
Bakin shi ya kai zai had'e da nata ta yi wani irin nishin azabar da ta ke ji ta re da wani irin huci wanda Suhail bai san sanda ya yi k'undun bala ya fad'o daga kan gadon ba, sakamakon hucin da ya fito daga bakin ta ya tab'a leb'an shi, sai ya ji kamar kyasta masa wuta aka yi a kan leb'an nasa, don har wajan ya tashi ya yi wani irin bororo kamar ya k'one.
Ita kuwa Binty da ta ga ya d'aga ta ya koma gefe, wani irin tsalle ta yi ta sauko daga kan gadon ko hijjab d'in ta da d'an kwalinta da ke yashe a k'asan d'akin ba ta yi ba ta fita ta bud'e d'akin, da gudu ta yi side d'in su ta na kuka ta na soshe-soshe ta re da kwala kiran sunan Anna.
Da gudu Anna da tun d'azu ta dawo ta zauna a parlour ta na jiran dawowar Binty ita da Barr Fu'ad da ke gefen Anna ya na cin apple su ka fito. Fanan da ke kitchen har ta riga su isa wajan da Bintyn ta ke ta re da ruk'o su.
"Anna na shiga uku, Anna na shiga uku. Bayana, jiki na, Anna k'onewa na ke yi ki taimake ni". Fad'in Binty ta re da kwace jikinta a jikin Fanan d'in ta na wani irin kuka ta re da birgima a k'asa.
"Na shiga uku, Fu'ad taimake ni ka d'auko min ita ka kawo ta d'aki". Fad'in Anna hankali ta she.
Da sauri Barr Fu'ad ya je in da Binty ta ke ta re da ciccib'arta.
Aikuwa ta Ku ma tsandara wani uban k'ara sakamakon jikin Barr Fu'ad da ya had'u da nata jikin sai azabar ya k'aru.
"Wayyooooo Annah mutuwa zan yi wallahi. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, na shiga uku". Binty ta sa ke fad'i.
"Anna muje asibiti kawai". Fad'in Barr Fu'ad ta re da nufar parking space hannunsa rungume da Bintyn da sai zamewa ta ke yi ya na sa ke rik'eta ta na fizge-fizge kamar mai shigar aljanu.
"Muje kawai, ke Fanan ki koma ki kula da girki". Fad'in Anna ta re da nufar parking space.
Da gudu-gudu Fanan d'in ta bi bayan Anna ta na kuka ta re da fad'in,
"Anna dan girman Allah ki ba ri na ni Ku, wallahi ba zan iya natsuwa ba idan har ban san halin da Binty ta ke ciki ba".
Ba ta re da Anna ta sa ke cewa komai ba ta bud'e gidan baya ta shiga, Fanan ma ta yi saurin shiga motar. Da gudu Barr Fu'ad ya motar su ka bar gidan.
Wani irin gudu ya ke yi wanda ya wuce misali, amma saboda tashin hankalin da Anna ta ke ciki, ba ta iya kwab'a masa ba har su ka isa asibiti.
Parking ma ba mai kyau ya yi ba, hakanan duk su ka fito gaba d'ayan su. Barr Fu'ad ya fiddo Binty da ke ta kuka a gaban mota. Jikin su na kuma had'uwa ta tsandara wani irin ihun da sai da ya zawo hankulan jama'ar da ke farfajiyar asibitin.
Gudu-gudu Barr ya nufi cikin asibitin, aikuwa cikin sauri nurses su ka kawo wanna gadon gungura marasa lafiya Fu'ad ya d'aura ta akai. Da shi aka gungura ta zuwa d'akin taimakon gaggawa, sai da su na zuwa bakin k'ofar aka hana Barr Fu'ad shiga.
Anna da Fanan su ka k'araso in da ya ke hankalin su gaba d'aya a ta she. Babu wanda ya iya cewa kowa k'ala a cikin su. Idanuwa Barr Fu'ad ya kad'a ya yi jazur, ya yin da Annah sai share hawaye te yi. Fanan kuwa riris ta ke yin kuka.
Sai da su ka kwashi awanni biyu a kan ta, ka na su ka fito da ita su ka kai ta d'akin hutu amma sun hana kowa ya shiga. Doctor ne da ya fito ya ce su bi shi office.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login