Showing 105001 words to 108000 words out of 162658 words
"Kwarankwatsi ban kuma rako ki waya. Ni ba da soyayya ni da dukan rana. To kusa ki nai mi mai rako ki tad'i walleh".
Dariya Binty ta yi ta re da dukan bayan ta ta ce,
"Allah ya ba ki sa'a Allah ta ji wannan rantsuwa a bakin ki, za ki fad'a masu". Fad'in Binty.
"Kin tuna dukan da Anna ta yi mana ni da ke a d'aki lokacin da mu ka yi wa Fasila rashin kunya?". Fad'in Fanan.
"Bar tuna min. Don yanzu haka jin zafin dukan na ke a jiki na. Ai Anna gwana ce wajan iya sarrafa bulala a jikin mutum". Fad'in Binty.
"Ai gidan sarauta ta tashi, ta na ganin yadda ake cafala mutane idan sun yi laifi da shirgegiyar bulaliyar da fadawa suke rik'ewa a hannunsu". Fad'in Fanan.
"Zan so watarana in je masarauta in ga yadda ake gudanar da mulki. Idan ina gani a cikin film abun burge ni ya ke yi walleh. Amma fa ban da zalincin wasun su". Binty ta fad'a.
"In da rai za mu je Binty in sha Allah. Za ki sha mamaki. Za ki ga yadda za'a rik'a mana wallahi ".
"Can't wait to see me their"..
*___________*
.........Bayan sun dawo gida, Goggo ta ba su abinci, shinkafa ce da wake da man k'uli da yaji. Sun ji dad'in abincin sosai don ba su tab'a ci ba sai yau.
Kandala ce ta shigo d'akin ta re da fad'in,
"Y'an matan Anna har kun dawo? Sannun ku da dawowa. Yauwa Binty zo kawun ki ya ce ki zo idan kun dawo".
Mik'ewa Binty ta yi ta re rik'o hannun Fanan, amma sai Fanan d'in ta nok'e ta re da fad'in,
"Dan Allah Binty ki je ki dawo, Allah na gaji so na ke na d'an kwanta ka min la'asar". Fad'in Fanan ba wai don abunda ta fad'a gaskiya ba ne, sai don bawa Binty damar kasancewar da kawun na ta ita kad'ai. May be akwai sirrin da su ke yin wanda ba su buk'atar ta a wajan.
Ba dan Binty ta so ba ta saki hannun na ta ta re da bin bayan Kandala har can k'uryan gidan d'akin matar Buba mai kwarankwatsi...
Su na shiga matar Buba Rahine ta fito ita da y'ay'anta kamar yadda mijinta idon cin naira ya fad'a mata.
Bayan sun fita, Kandala ta sakayo rub'arb'iyar k'ofar ta re da kunna torch light d'in sha kid'an ka bak'auyenta saboda d'akin ya yi duhu.
"Zauna magana za mu yi mai muhimmanci". Fad'in Kandala ta re da nu na mata tabarmar da ke shimfid'e a tsakar d'akin.
Ba ta re da musu ba ta zauna don ita kan ta ta na son tambayar ta manufarta a kanta.
Ita ma Kandalar samun waje ta yi ta zauna ta re da fad'in,
'Yauwa y'ar albarka. Kin san dai a fad'in duniyar nan ba ki da wata kamar ni ko?".
Wani irin d'ago idanuwa ta yi ta re da zubawa Kandala ka na ta yi murmushi ta re da fad'in,
"Ba ni da kamar Anna dai da zuri'ar ta. Na san dai ke ce silar had'uwata da su tabbas. Amma ban san menene manufarki a kai na da kuma wad'annan mutane ma su karamci ba. Ta sanadiyata kin samu kud'in da ko wani mai aikin gwannati bai samun haka. Ban to na miki asiri akan babu abunda mu ka had'a da ke ba, amma ban san menene dalilin ki na yin duk wannan abun da ki ke yi ba. Idan har da ba ni da wayau, yanzu ina da shi. Kar na ke kallon ki. Na san ba ni da wata alak'a da ke da kuma wannan k'auye da ki ka kawo ni. Amma zan iya aje hakan a mazaunin gudun ka da Anna ta zarge ki tsawon shekaru takwas ba ki ta b'a kai ni wajan sauran dangi ba. Amma abunda ya matuk'ar daure min kai shi ne, yadda y'an garin nan su ka aminta ni d'iyar wanda ki ka ba ni a matsayin mahaifi ne wato Hashimu. Mai ya sa ki ke duk wannan abun? Mai ya sa tun tuni ba ki tab'a kawo ni nan ba sai wannan karon? Tabbas akwai wani abunda ki ke shiryawa. Kuma ina san sanin menene shi". Fad'in Binty ta re da tsare Kandala da idanuwa.
Sosai mamaki da tsoro su ka bayyana a kan Binty. Don a wautar Kandala, Binty a wancan lokacin ta yi k'ank'antar ta fahimci ba ta da alak'a da ita. Duk a nata wautar saboda Binty ba ta tab'a yi mata maganar ta san ba su da alak'a ba, sai ta ke tunanin dagaske Binty ta yarda ita d'in yar mahaifin ta ce.
D'aure fuska Kandala ta yi ta re da fad'in,
"Sai me idan kin fahimci ba ni da alak'a ta jini da ke. Ko ki na tunanin za ki iya fad'awa Hajiya ne kuma ta yarda. Ton yarinya kin riga kin bar shiri tun rani. A yanzu haka zan iya miki ramin da zai afka da ke. Don haka gwara ma ki cigaba da amince akan ni d'in Baabar ki ce ko kuma ki bar daular da ki ke ciki kuma ki k'are a magark'ama. Ni a waje na ba abun damuwa ba ne idan na k'are a magark'ama don na gama cin nawa zamanin. Ke kuma yanzu ki ke gan ganiyar ki".
"Da ina da niyyar to na miki asiri, da tuni na tona. Saboda ki kwantar da hankalin ki, ni ba zan tona miki asiri ba sai dai idan Allah shi ya tona ki da kan shi. Amma ki sanj ramin k'arya, k'urarre ne. Ni yanzu abunda na ke so, ki fad'a min manufar zuwan mu k'auyan nan". Fad'in Binty.
Gyara zama Kandala ta yi ta re da fad'in,
"Yarinya kin kyautawa kan ki. Kuma ni manufata ta arziki ce, abun alheri na ke tafe miki da shi musamman yadda ba *BA KI DA GATAN* nan, za ki tara kud'i masu d'umbin yawa wanda idan Allah ya yi kin yi wani auran, hatta jikokin ki ba za su yi talauci ba".
Wani kallo Binty ta bi ta da shi ta re da fad'in,
"Ban ga ne idan na yi wani auran ba, da ma na tab'a aure ne da har zan sake wani auran?".
"Kash! Matsala ta da ke sauri. Ki ba ri ko mai zan warware ma ki. Yanzu kam ai budurwa ki ke ba ki tab'a aure ba. Amma fa wannan abu da zan miki hanyar shi, za ki ji dad'in shi. Amma hakan zai kasance sirri tsakanin ki da wacce za ku yi abun. Yanzu ba ni da hurumin fad'a miki komai sai kun had'u da matar tukun. Sanna akwai wani abun da ba ki sani ba, fallasa matar na nufin abubuwa uku ne, na farko rasa rayuwar wacce ki ke matuk'ar k'auna fiye da kan ki wato Annah, mai bi Mata, Fanan wacce ku ke ta re yanzu, sai na ukun su Fu'ad"..................
*PAID BOOK 08128755583*
*57-58*🌹
.............Dam! Dam! Dam! Haka zuciyar Binty ke bugawa kamar zai tsaga k'irjinta ya fito har Kandala da ke gabanta ta na jin bugun k'irjin na ta wanda hakan ya tabbatar mata da lallai Binty ta tsorata da abunda ta ce mata.
"Dan girman ubangijin halitta ka da ku tab'a mahaifiyata da y'an uwana, idan ku ka min haka ba ku min adalci ba. Baaba Kandala ka da ki alkhairi da sharri, ka da ki manta na san babu abunda na had'a da ke, amma dalili na ki ke amsar kud'in da ko wani ma'aikacin gwantanin bai samun haka amma na yi shuru na rufa miki asiri don ta sanadin ki na samu duk abunda na ke tak'ama da shi yanzu. *BA NI DA GATA*, ina rayuwa ne a kan bola cike da tarin jahilci da daud'a, amma yanzu na samu ilimi na addini da na boko duk ta sanadiyar Anna da ta mai da ni tamkar d'iyar cikinta ko in ce fiye da hakan, don say ta ri ta min abu ba ta re da ta yi wa Fanan ba. To ki na tunanin zan iya bari wani abu ya cutar da ita ko zuri'arta? Zan iya yin komai don Allah ta rayu in dai ba kauce hanya ba ne. Dan Allah ka da komai ya sa my Anna ta". Fad'in Binty ta re da k'arishe maganar da kuka mai sauti.
Tab'e baki Kandala ta yi ta re da harararta ka na ta ce,
"Ni ba kuka na kira ki ki min a nan ba, na dai fad'a miki sharud'd'an kin ji. Kuma wallahi ina mai k'ara tabbatar mi ki da cewar fitar da maganar ko rashin bin umarnita shi zai yanki tikitin salwantar rayuwar Anna da y'ay'anta. Kuma da ki ke maganar rama alkhairi da sharri, ni nan idan naga kud'i babu abunda ba zan iya yi ba, ku ma kud'in da aka ba ni, zan iya gyara k'auyan nan kaf in mai da shi ginin zamani, to ya kike tunanin zan iya ganin wad'annan kud'an nan in rintse idanuwana. Ai ba zai yuwu ba". Fad'in Kandala.
"Ki ji tsoron Allah, ki tuna ya na ganin duk abubuwan da ki ke aikatawa kuma da sannu za ki girbi abunda ki ke shukawa. Ki gaggawan fad'a min abunda zan maku don in bar garin nan gobe". Fad'in Binty.
"Hehehehhh! Kwantar da hankalin ki, da ma kwana ukun za ku yi ku koma, saboda biyo kin da wancan sha-sha-shar ta yi, da ace ba ta biyo ki ba, da ko garin nan ba za mu zo ba, za mu yi abun mu cikin kwanciyar hankali, amma tunda ta biyo ki, dole mu yi hak'uri har sai kin koma. Sannan abu na gaba, mutane biyu ne za ku yi wannan sirrin ta re, sai dai d'aya ba za ta tab'a sanin d'aya ta na sirrin da ke ba. Ke! Wallahi ya kamata ma ma ki dode min don ke kowa k'aunar ki ya ke yi za ki zama ta gaban goshi". Fad'in Kandala ta re da washe hak'ora.
Harara Binty ta watsa mata ta re da kau da kai ta na tunanin wannan wani irin sirri ne da za ta yi da wasu. Fatan ta dai Allah ya sa ba abunda zai cutar da Anna ba ne ko kuma ya cutar da wanda ba su ji ba ku ma ba su gani ba.
"Ki ta shi ki je ka da y'ar uwar ta ki ta ji shurun ya yi yawa. Dama ni abunda na kira in fad'a miki kenan". Fad'in Kandala.
Matar Buba da ke mak'ale a jikin taga ta yi saurin yin hanyar kewaye don gudun ka da Binty ko Kandala su fito su ganta a wajan su ga ne ta ji duka tattaunawar su.
Binty ce ta fito ta re da wuce wa sasan Goggo Shatu. Buta ta d'auka kamar za ta zaga ta shige ba yi ta re da had'e kai da bango ta na wani irin kukan da ke fitowa tun daga k'asan zuciyarta. Ba ta tabbatar da lallai cewar *BA TA DA GATA* ba sai yau.yau da ace da iyayanta kusa da ita wa ya isa ya mata wannan abu. Gashi yanzu ta dalilinta ta na naiman jefa wanda ba su ji ba, ba su gani ba a halaka.
Ta kusa minti talatin a bayin ka na ta fito. Allah ya so ma babu wanda ya yi k'ok'arin shiga bayin. Amma idanuwanta sun yi ja jawur alamar ta ci kuka ma'ishi.
Ko da ta shiga d'akin Goggo Shatu, hankali tashe Fanan ta k'ariso wajanta ta na fad'in,
"Sister mai ya faru? Wa ya saki kuka?". Ta fad'i hakane gaba d'aya hankalinta a matuk'ar tashe kamar za ta saki kukan itama.
Goggo da ke goga goro a magogi ita ma ta zubo masu idanuwa ta na tambayar abunda ya sa mu Binty.
Ita kuwa Binty ganin yadda Fanan d'in ta rud'e saboda ganin halin da ta me ciki, sai hakan ya k'ara zaburar da tashin hankalinta ta saki kukan mai sauti ta re da rungume Fanan d'in ta na fad'in,
"Ku ka d'ai gare ni, idan har babu ku ba zan iya rayuwa ba. Wallahi ina matuk'ar k'aunar Anna da zuri'arta. Ba zan ba ri wani abu ya same ku ba, zan iya ba da lafiya da rai na wa ku. Ina son ku Fanan". Binty ta fad'a cikin wani irin rikitacciyar muryan kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Wani irin kuka Fanan ita ma ta saki ta re da k'ara ruk'unk'ume Binty ta ma kasa magana.
Goggo Shatu kuwa wani irin jan d'uwawu ta yi ta re da rarrafe ta dafa bango ta mik'e ta rungumo Fanan da Binty ta re da fad'in,
"Ku bar kuka y'ay'an nan dan Allah. Ke kuma Binty dole ne ki yi kuka saboda rashin iyaye ai babban abu ne. Mu kan mu run da Hashimu ya mutu katanga ya zube. Ga shi kin zo kin ga irin rayuwar da mu ke yi a cikin k'auye ke kuma ki na can cikin daula wajan mutanan kirki. Ai Kandala ta hwad'i min komai. Kwarankwatsi ni kai na zan so ganin wannan uwa ta ki mai karamci baiwar Allah". Goggo ta k'arishe maganar ta re da mai da kallonta izuwa ga Fanan da ke gunjin kuka.
"Goggo ki ce ta dai na kuka dan Allah, wallahi ban son kukan ta. Na san Anna na can gabanta na fad'uwa". Fad'in Fanan.
"Kin ji ko? Dan Allah ki bar kuka idan ba so kike kan yarinyar mutane ya yi ciwo ba". Fad'in Goggo ta re da kama hanna yansu ta zaunar da su a bakin gado.
Da sauri ta saka bayan hannunta ta goge fuskan ta re da kallon Fanan ta ce,
"Sister na bar kukan, dan Allah ka da ki bari kan ki ya yi ciwo kin ji?". Fad'in Fanan ta na k'are share fuskanta.
"Na dai na, ke ma ki daina dan Allah". Fanan ta fad'a ta na had'iye kukan da ke tawo mata.
"Yauwa y'an albarka ku bar kuka kun ji. Ke kuma Binty addu'a da biyayya shine kawai za ki yi wa marik'anki ki biya su ba kuka ba, kin ji?". Fad'in Goggo.
Gyad'a kai Binty ta yi ta na mai had'iye sauran kukan da ke taho mata a duk sa'ar da ta tuna da maganar da Kandala ta yi mata ba cewar idan ba ta amince da sirrin nan ba to a bakin ran Anna da y'ay'anta.
*ABUJA*
............."Anna ni fa zan je Saminakar nan in d'auko su Binty. Gidan ba bu dad'i ko kad'an wallahi. Ke kan ki Anna na san dauriya kawai ki ke yi amma ki na missing d'in su over and over". Fad'in Barrister Fu'ad.
Wani wawan kallo Ya Bibi ya bi sa da shi ta re da fad'in,
"Yanzu ma za ka iya hawa hanya ka je ka d'auko su".
Sosa k'eya Barrister ya yi ta re da kallon Anna da ita kan ta gidan bai mata dad'i.
"To ya za mu yi Fu'ad? Dole mu yi hak'uri tunda wajan y'an uwanta ta je, su ma su na da