Showing 69001 words to 72000 words out of 162658 words
ke yi wa junan su a jiki.
Sai bayan kowa ya watse ne, Sabrin da Hamdan su ka kwashi gift d'in shi su ka yi d'akin shi da shi.
Zama Sabrin d'in ta yi a kan resting chair da ke d'akin na shi ta re da fad'in,
"Washhh! I'm tired. Anya bazan kwana gidan nan ba kuwa, don wallahi ba zan iya driving ba, sai dai idan za ka kai ni gida".
"Ba ta re Ku ka zo da k'anwar ki ba, ai kamar idan ba idanuwa na ba ne, na gan ta lokacin da mu ke rawa". Fad'in Hamdan.
"Ita ce, ta wuce gida maman ta ta kira ta". Fad'in Sabrin ta re da kwanciya a kan resting chair d'in.
"To ba ri na yi wanka, sai na raka ki. Ni ma ina son zuwa Kaduna jibi in sha Allah". Hamdan ya fad'a.
Wani d'agowa Sabrin d'in ta yi ta watsa masa harara ta re da sakin dogon tsaki ka na ta ce,
"Wahalallan banza kawai, ba Kaduna ba ka zagaye duniyar. Wallahi na san ba uncle Sauban za ka je ga ni ba, wannan gantalalliyar yarinyar y'ar kan bolan da kullum ka ke ishen mutum da labarin ta za ka nai ma, kuma wallahi idan ba kai wasa ba, sai na Shiva wajan mummy na fad'a mata".
"Dan Allah ki fi jirgi gudu. Da ya ke ma iya mummyn da kan ta za ta aike ni Kadunan. Kuma idan dai Beauty ce, wallahi ba zan ga ji da nai man ta ba har sai Allah ya sake had'a fuskokin mu idan Allah ya k'adarta hakan a gaba. Wallahi ni fa duk wanda bai k'aunar Beauty, ni ma fa bai k'auna ta. A matsayin ki na Besty na, wallahi bai ka ma ta ki rik'a k'in Beauty ba. Na san ko ke kika gan ta, sai ta burge ki. Very beautiful girl. Ban tab'a ganin mace mai kyau irin ta ba". Fad'in Hamdan.
Haba tuni Sabrin ta kawo wuya. A zafafe ta mik'e ta re da fad'in,
"Mak'aryacin banza da wofi. D'azu a wajan birthday party d'in ka ka gama fad'awa mutane I'm the most beautiful girl you have ever seen, shi ne yanzu za ka ce wai wani ba ka tab'a ganin kyakkyawa kamar ta ba. Mayaudari kawai mai kan gwanda. I hate you. Kuma wallahi na fi ta kyau. Ita da *BA TA DA GATA*, y'ar *BOLA* da ita. Duk yarinyar da ka ga an yar da ita a bola, to *ZINA* a kan yi da uwarta aka haife ta. Shi ne har za ka tsaftatacciya kamar ni da datti irin ta. I hate.........".
Ka fin ta k'arisa maganar Hamdan ya katse ta da fad'in,
"Out..! Fitar min a d'aki right now. Sau nawa zan dunga fad'a mi ki akan ki bar kiran Beauty da y'ar *ZINA*? Idan ma haka aka yi aka haife ta, ai ba laifin ta ba ne. Ke ma ba dabarar ki ba ce da aka haife ki da aure. Out now before I loss my control". Hamdan ya k'arisa fad'in maganar da tsawa.
Mik'ewa Sabrin d'in ta yi ta re da fad'in,
"It Isn't your fault wallahi. Laifi na ne da Har na yi attending birthday party d'in ka shiyasa ka ke min wulak'anci. Kai da ba dan cousin d'ina ba ne, wallahi da yau ba za ka kwana a gidan uban ka ba, amma from now ka rubuta ka aje, ba ni ba ka, ni ba best friend d'in ka ba ce Ku ma. Kar ka sake kira na a waya. I'm deleting your number right now". Fad'in Sabrin ta re da fiddo wayarta ta yi deleting numbern Hamdan d'in ta re da fita daga d'angin ta bugo masa k'ofar.
Kicib'is su ka yi da mummy Saudat, rab'e ta ta yi ta re da wuce wa ko gaishe ta ba ta yi ba.
Mummy Saudat na kwad'a mata kira, amma ko juyowa ba ta yi ba ta wuce wajan motarta ta re da baron gidan.
D'akin Hamdan d'in ta nufa ta na dariya ci kin zuciyar ta, domin idan da saboda Sabrin da Hamdan sun saba irin wannan fad'in, kuma cikin kwana biyu su shirya kan su, shiyasa ba mai shiga tsakanin su, don idan za ta iya tunawa, to wannan fad'an na su shine na d'ari da Saba'in kuma su na shirya kan su ba ta re da Sanin kowa ba.
*_____________________*
............."Dan Allah Fanan ki yi sauri, wallahi na k'osa mu fita ka min Anna ta dawo ta ce ba za mu fita ba. Kin san fa ba nisa ta yi ba ". Fad'in Binty da ke tsaye a kan Fanan da ke kwalliya a jikin madubin d'akin na su. Sanye ta ke cikin atampa doguwar riga kamar maroon da toch of golden. Doguwar riga ce d'inkin zamani irin mai aljihun nan. Ba k'aramin kyau kayan su ka mata ba. D'aurin zamani, duk da nannad'e gashin ta da ta yi, sai da gashin ya fito ta k'asan d'aurin da ta yi. Sai dai ribom d'in da ta saka ta kama gashin, shi ya d'ago da d'an kwalin ta kamar ta yi irin ture ka ga tsiyan nan. Siririn gyale kalar maroon ne a k'afarta, sai flat shoe shi ma kalar maroon a k'afar na ta. Babu abunda ya fi d'aukar hanakali a jikinta kamar jan lallan da ke kan y'an yatsun ta da ya k'ara fito da kyawun hannun kasancewar ta farar mace.
"Dan Allah one minute. Yanzu zan gama". Fad'in Fanan da ke shafa jan baki a leb'anta.
Mik'ewa ta yi ta re da d'aukar gyalanta, ita ma irin shigar da ke jikin Binty shi ke jikinta.
"Muje ka da ki cinye ni d'anya". Fad'in Fanan.
Wayar ta da ke kan mirror ta d'auka ta re da fita Fanan na biye da ita a baya.
Su na fitowa Hajiya Mansura ita ma ta fito za ta fita, kallon Bintyn ta ke yi from head to toes ka na ta ce,
"Ina za ku je da ranar nan?".
Ka min su ba ta amsa sai da su ka gaishe ta, ka na Fanan ta ce,
"Za mu ce saloon ne, daga nan kuma za mu bi ya mu d'an yi shopping".
"To Ku kula da kan ku. Ke idan kun dawo ki zo part d'ina ki same ni". Hajiya Mansura ta k'arisa maganar ta na kallon Bintyn.
"To Hajiya". Fad'in Binty ta na kallon k'asa, don haka nan ta ji ta na mugun tsanar ta, shiyasa ko duk in da ta san za su had'u, ba ta bi ta wajan.
Ganin sun fito, tuni driver ya d'auko mota ya nufo har in da su ke, kasancewar umarni Anna ta ba shi akan duk in da za su, idan har ba Ya Fu'ad ba ne zai fita da su, to ba ta yadda su fita su d'aya ba, ya kai su.
Shiga motar su ka yi, saloon d'in su ka fara zuwa. Sun jima a wajan kasancewar gashin Binty na da yawa sosai.
Ko da su ka fito su ka zo wajan mota, Kamale driver har ya soma bacci sai da su ka ta da shi. Daga nan shop rite su ka nufa.
Wajan kayan shafa su ka soma zuwa kasancewar turare da kayan kwalliyan su sun k'are, kit kuma su ke so su sake had'awa.
Bayan sun gama da nan kuma su ka koma wajan da su ka fi auki wato wajan kwalama.
Juyowar da Binty za ta yi, idanuwan ta su ka sauka a kan shi. Gaban ta ne ya buga da k'arfi. Da sauri ta dafe saitin zuciyar ta da ke buga fat fat fat.
Dogone sosai, irin kyakkyawan nan ajin k'arshe. Fari ne sosai don duk hasken fatan ta ya fi ta fari, ya fi kama da irin farin Indiyawa. Ya na da manya idanuwa da dogon hanci, bak'in shi k'arami irin wanda akewa lak'abi da pink lips d'in nan. Ga sajan da ya k'ara k'awata fuskan shi ta re da d'an gemu irin na gayun nan da ya aje bak'ik'k'irin. Ya na da dimple a both chick d'in sa wanda motsa bakin ya yi sai ya lob'a. Siriri ne amma ba irin can d'in nan ba. K'irjin shi a bud'e ya ke amma ba can sosai ba.
Kasancewar ya na facing d'in ta ne shiyasa ta iya k'are masa kallo haka, amma Sam shi hankalin shi ma ba ya kan ta.
"Uncle Yusuf chocolate please". Fad'in wata kyakkyawar yarinyar da ba za ta wuce 8 years ba ta fad'a ta na jan hannun shi.
Kallan gefen da ta ke ya yi, Binty ba ta san lokacin da ta furta,
"Hasbunallahu wani'imal wakeel. Wayyo Allah!". Ta fad'i hakane sakamakon side view d'in sa da ta ga ni, sai ta ga ya fi kyau idan ya kalli gefe.
Chocolate ya d'auko ta re da mik'awa wannan kyakkyawar yarinyarta re da sakin mata murmushi.
Yuuu Binty ta tafi za ta fad'i, Fanan da tun san da Binty ta k'urawa wannan bawan Allah idanu wanda ita kan ta ya tafi da imaninta ta ke kallon ta ta yi d'aurin taro Bintyn ta re da fad'in,
"Haba sis kar ki ba da mu mana. Behave your self".........
*PAID BOOK 08128755583*
🌹 *39-40*🌹
............."Fanan ki na ganin abunda na ke ga ni kuwa? Wallahi guy d'in nan ya had'u sosai". Fad'in Binty.
"To ko za ki je ki masa magana ne? Tun da ba ki da aji. Idan rabon ki ne, ki na nan zai zo ya kula ki. Dan Allah ki nutsu". Fanan ta fad'a a d'an zafafe.
Sai a lokacin Binty ta dawo hayyacinta ta re da shan mur ta kuma dai-dai ta natsuwarta. Amma har a wannan lokacin ba ta dai na satar kallon shi ba.
Hannunta Fanan ta rik'e ta re da barin wajan su ka nufi wajan biyan kud'in abunda su ka saya.
Bayan sun biya an saka masu abubuwan a leda, Binty ta na d'auka ta na mai addu'ar Allah ya sa ta sa ke ganin wannan mutumin ko sau d'aya ne ka min ta bar shop rite d'in.
Juyawar da za ta yi su ka ban ga ji juna, sai da kayan da ke hannunta ya watse, shi kuma tsadaddiyar wayar da ke hannunsa ya sub'uce ya fad'i, a ta ke screen d'in wayar ta yi watsa-watsa.
"Yah subhanallah!". Guy d'in nan ya fad'i ta re da saurin duk'awa ya soma tattaro mata kayanta da su ka watse.
Fanan kuwa saurin zuwa ta yi ta d'aga ta ta re da fad'in,
"Kin ga irin abunda na ke guje miki ko. Ai Gashi nan garin kallon sa kin fad'i. Ai sai ki ta shi".
"Ni wallahi ba shi na ke kallo ba, karo mu ka yi ban san ya na baya na ba". Binty ta fad'a ya yin da ta ke mik'ewa kamar za ta yi kuka.
Wannan guy d'in k'arasowa ya yi hannun shi d'auke da ledar kayan Binty, wannan kyakkyawar yarinyar na biye da shi a baya ta na shan chocolate d'in da ke hannunta.
"I'm very sorry ma'am, hope you're okay". Fad'in guy cikin wata zazzak'ar muryan da ya sumar da Binty ta shiga bin bakin shi da kallo ba ta re da ta ce uffan ba.
Tsungilin ta Fanan ta yi a cinya wanda shi ya dawo da ita cikin hayyacinta ta re da saurin fad'in,
"I'm.... I'm okay. I'm very sorry too". Fad'in Binty cike da rawar murya ka na kuma ta mayar da duban ta izuwa ga wayarsa da ke ya she a k'asa a farfashe.
Cikin sauri ta k'arisa wajan wayar ta re da d'auko shi ta ce,
"Na shiga uku na fasa masa waya".
"Ohhh kar ki damu, tsautsayi ne ai ba laifin ki ba ne ba". Fad'in guy d'in nan ya na sakin murmushi da ke k'ara bayyanar da bayyanan nan kyawun sa.
Daga Binty har Fanan sakin baki su ka yi su na kallon shi, domin ba su tab'a tunanin za su ji Hausa a bakinsa ba. Duk a tunanin idan yaruka su ka wuce ukun nan, to ba su tsammanin ya na jin wasu yaran, wato English, Hindi ko Arabic.
"Ku na mamaki ne? Ina jin hausa sosai kamar jakin kano. By the way, I'm Yusuf Muhammad Ahlam. Can I know yours?".
Binty ta kasa magana, domin muryan shi ba k'aramin rikita ta ya ke yi ba. Guy d'in ya yi ne sosai.
Fanan ce ta iya k'arfin halin fad'in,
"I'm Fanan Usman mai goro, and my sister, Binty".
"Very nice name. You all have beautiful name". Fad'in guy d'in.
"No one Care's about mine? Hmm my name is Ayeesha Fairuz Ahlam, his youngest niece. I'm the last born". Kyakkyawar yarinyar nan ta fad'i ta na dariya. Kamannin su d'aya da wanda ya kira kan shi da Yusuf, ko ba ta fad'a duk wanda ya gan ta ya ga k'anwar sa ko y'ar sa.
"Ohhh you're soo beautiful dear". Fad'in Fanan ta re da rik'e kuncin yarinyar.
"I knew it". Fad'in yarinyar ta re da sa ka chocolate a bakin ta.
Gaba d'aya dariya su ka fashe da shi har da Binty da ta kasa magana.
"If you don't mind, can I drop you?". Fad'in Yusuf.
"Ohh no, don't worry, we are with our driver, he's waiting outside". Fad'in Fanan.
Murmushi ya yi wanda hakan ya kasance d'abi'ar sa ne ta re da kallon Binty ya ce,
"Hey miss Beauty, can't you talk?".
Kunya duk ta rufe Binty, duk sai ta daburce ta rasa mai za ta ce.
"She's so beautiful, please can we take a salfie?". Fad'in Ayeesha.
"Indeed she's beautiful. Please za ki ba ni ita in aure ta?". Fad'in Yusuf ta re da kallon Fanan.
Binty kuwa ba ta san lokacin da ta kwasa da sauri ba ta yi hanyar waje gabanta na fad'uwa at the same time kuwa ta na jin wani dad'i na mamaye zuciyarta.
Bud'e mota ta yi ta shiga, driver na mata magana ko sauraran shi ba ta yi ba.
"Indeed she's beautiful. Please za ki ba ni ita in aure ta". Maganar Yusuf ya k'ara yi ma ta gizo a kunnanta.
Dariya ta yi ta re da saka kan ta a tsakanin cinyoyinta.
Kusan mintuna goma Fanan ta taho da kayan da su ka siya. Both ta bud'e ta re da saka kayan, sannan ta zagayo ta bud'e gidan baya in da Bintyn ke zaune ta re da rufo motar.
Driver na ganin haka ya ja motar ta re da kallo baya ya ce,
"Gida mu ka nufa, ko kuwa akwai wani wajan da za ku sake zuwa?".
"Ah mun gama komai, gida mu ka yi". Fanan ta ba shi amsa.
Kallon ta Fanan ta yi ta re da fad'in,
"Juliet ta had'u da Romeo d'in ta".
"Ban ga ne ba, mai ki ke nufi da hakan?". Fad'in Binty ta na maka mata hararar wasa.