Showing 93001 words to 96000 words out of 162658 words

Chapter 32 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42924

"Zan koma ka da Fanan ta yi ta jira na".
"To yanzu kuma sai yaushe? Tun dai gidan ku ba barin fita ake yi ba". Fad'in Yousouf.
"Laa! Na manta ban fad'a maka ba, jibi zan yi tafiya zan je garin mu, amma ba zan dad'e ba. Idan na dawo za mu had'u". Fad'in Binty.






















*PAID BOOK 08128755583*
🌹 *49-50*🌹
............."Gaskiya zan bi ki, mu tafi ta re kawai don ba zan juri rashin ki har na tsawon sati guda ba, zan samu matsala". Fad'in Yousouf.
Dariya Binty ta yi sai da kumatun ya lob'a ta re da rera masa baiti cikin zazzak'ar muryanta,
" *Sai wata rana masoyi zan bar ka, sai wata rana rabuwa ba mutuwa ba. D'an uwa rabin raina ban so mu yo rabuwa*"
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Mai sona sassauta muryan ki dan Allah ka da wani ya ji. Don na tabbata wannan zazzak'ar muryan ta ki zai iya haifar wa da mazaje da dama matsalar da zai jawo abunda ki ke gudu kuma ki ka hana ni furtawa". Fad'in Yousouf.
Hannu ta sa ka ta rufe bakinta ta re da fad'in,
"Afwan Reality, hakan ba za ta sake faruwa ba. Ka san ban k'aunar b'acin ran ka".
"A'a, hakan fa za ta sake faruwa, amma sai muna a kad'aice in da babu wani namijin da zai ji muryan ki sai ni d'aya". Fad'in Yousouf ta re da lumshe idanuwansa.
"An gama my reality, daga yau rowan muryata zan rik'awa mutane".
"Da kin kuwa kyauta wa Yousouf".
Dariya su ka yi gaba d'ayan su. Hanya ya nuna mata ta re da fad'in,
"Mu je ko in kai ki ka da sister Fanan ta ji shuru". Yousouf ya fad'a.
Jerawa su ka yi su na tafiya ta re da hira cikin nisha'di irin na saurayi da budurwa.

Sanye ta ke cikin riga da wando pallazo red colour, as usual ta yi parking d'in gashin ta a tsakiyar kan ta. Sai d'an siririn farin gyale da ta yafa a wuyanta zuwa kafad'unta da kuma farin takalmi mai tsini. Ba k'aramin kyau ta yi ba, sai dai gaba d'aya suran jikinta a waje ya ke. Duk inda su ka wuce maza da mata kallonta ake yi.
"Besty ba ka ganin yadda ake bi na da idanuwa kamar za'a cinye ni. Ni kai na na san ni mai kyau ne. Ni madubin dubawa ce ga jama'a wallahi".
"Hmm". Shi ne abubda Hamdan ya fad'a ta re da kallonta ta gefen idanu.
Duka ta d'aka masa a tsakiyar baya ta re da fad'in,
"Uban hmm, na tsane ka! Na gama koro magana sai ka wani ce min hmm kamar bai ciwon hak'ori". Fad'in Sabrin.
"Ai ni matsala ta da ke kenan gajen hak'uri gare ki. So fa na ke na ce miki ai ke d'in ce kyan ki ya yi yawa. Ba ki ga wani har kusan fad'awa kan wata budurwa ya yi ba garin kallon ki". Hamdan ya fad'a.
"Shege ina kallon shi ai, kuma ni kwalelen sa ce. Back to maganar mu, mai ka ke tunanin zan yi in burgesa? Shi mutum ne mara son magana da hayaniya. Wallahi besty ina matuk'ar son shi sosai. Ban tab'a son wani namiji a duniya ba kamar sa. Ya ce min in sha Allah zai samu lokaci ya zo next tomorrow. Dan Allah wani tarba zan masa ya burge sa?". Fad'in Sabrin dai-dai lokacin lokacin da za su shigo ta wani k'ofa, su Binty kuma za su fita.
Ba ta re da gaba d'ayansu sun kula da juna ba, Sabrin ta bangaje ta.
K'urawa juna idanu su ka yi. Shi kuma Hamdan wani d'an allura ya soki takalminsa ya duk'a ya na k'ok'arin zarewa.
"Binty lafiya?". Fad'in Yousouf.
"Lafiya k'alau Binty ta yi saurin fad'a ta re da yin gaba.
"Binty Hisham mai goro?". Sabrin ta fad'a gabanta na tsananta fad'uwa.
Cak Binty ta tsaya, dama zargi ta ke yi amma kiran cikakkiyar sunanta da Sabrin d'in ta yi ne ya sa ta tabbar ita d'in ce. Juyowa ta yi ta re da d'an sakin murmushi ta re da fad'in,
"Kamar Sabrin ko?". Ta fad'i hakane ta re da d'an matsowa.
Sai da Sabrin ta isa daf da ita, ka na ta ce,
"Wanna fuska ta ki ba zai yi sauri mantuwa a waje na ba, billahi na yi alk'awarin in dai ni jinin Alhaji Saifullahi ce, sai na lallata wannan d'an k'aramin kyawun da ki ke tak'ama da shi". Ta na gama fad'in haka shi kuma Hamdan ya d'ago ta re da kallon in da Sabrin d'in ta ke. Hakanan ya ji gabansa ya buga da k'arfi ya na k'ara k'arewa Binty kallo zuciyar sa na wani irin zillo da buguwa.
Juyo wa Sabrin d'in ta yi ta re da dawowa wajan Hamdan ta ce,
"Mu je". Ta fad'i hakane ta re da yin kicin-kicin da fuska.
Shikuwa Hamdan sai kallon Binty ya ke yi da ta tsaya kamar statue ta na kallon Sabrin d'in.
Yousouf da ke gefe ya k'araso kusa da Binty ta re da fad'in,
"Mai sona lafiya? Ya naga duk jikin ki ya yi sanyi. Kin san ta ne?".
K'ak'alo murmushi ta yi ta re da fad'in,
"Eh na santa, ta re mu ka yi primary school a *Lead British*".
"OK. Mu je to". Fad'in Yousouf ta re da sa ta a gaba ya na biye da ita a baya.
"Ko za ka bi ta ne?". Fad'in Sabrin a k'ufule.
"Wallahi haka na ke ji a jikina kamar na Santa". Fad'in Hamdan.
Banzan kallo ta watsa masa ta re sa yin tsaki ta yi gaba.
Shikuwa Hamdan sai da ya k'ara bin su Binty da kallo ka min ya bi bayan Sabrin da ta ke ji kamar ta buga saboda ganin halittar da ta tsana a duniya.


Bud'e mata gidan gaba ya yi, sai da ta shiga ya rufe ka na ya zagaya ya shiga driver seat ta re da rufe motar.
Ita kuwa Binty gaba d'aya jikinta ne ya yi sanyi k'alau da maganar da Sabrin d'in ta fad'a mata. Ta d'auka Sabrin d'in za ta canza a gaba, amma sai ta ga kamar abun na ta k'aruwa ya yi.
"Ba zan yi wa motar nan key ba idan har ba ki fad'a min abunda ke damun ki ba, wallahi ko da hakan na nufin za mu kai sha biyun dare a nan wajan". Fad'in Yousouf da ya zuba mata fararan idanuwansa.
Saurin kallon sa ta yi ta re da k'ak'alo murmushi ta ce,
"Ba fa abunda ke damu na, kawai schoolmate d'ina ce da na ga ni ta ba ni mamaki". Fad'in Binty.
"Wani irin mamaki kenan ta ba ki?". Ya sake je ho mata tambaya ta re da tsare ta da idanu.
"Ta na da isa da tak'ama ne tun muna yara, sai na ga abun bai ragu ba ko da mu ka girma, shi ne abun ke ba ni mamaki".
Murmushi Yousouf ya yi ta re da fad'in,
"To hakan ya dai na damun ki, ko wani mutun da ki ka gani a duniya da irin yanayin sa da kuma d'abi'ar sa. Ki saki jikin ki, ko mu kwana a nan".
Zaro idanuwa ta yi ta re da fad'in,
"Wallahi na saki, mu tafi". Ta fad'i hakane ta re sa sakin fuskanta.
Dariya ya yi ta re sa yi wa motar key ya yi reverse ta re da fita daga wajan. Ita ta yi masa kwantance har su ka iso wajan.
Sai da ya k'ara rik'e ta kusan mintuna biyar ya na k'ara zayyane mata yadda ya ke jin ta a zuciyar sa da kuma jaddada mata alk'awarin su Ka na ya bar ta ta wuce.
Ta baya ta biyo kamar yadda ta fita ta baya. Ko da ta shiga shagon, tuni har an kammalawa Fanan lalle har ta wanke. Kan ta ake busar mata.
Fanan d'in na ganinta ta saki ajiyar zuciya ta re da fad'in,
"Ina nan ina zullumi wallahi. Gaskiya kin kyauta da ba ki makara ba". Ta fad'i hakane ta re da karb'an ribom a hannun mai saloon d'in ta kama gashin da kan ta, ka na ta mik'e ta kakkab'e jikinta ta re da ba mai saloon d'in kud'inta har da na lalle ka na su ka fito.
Driver na zaune a mota ya na sauraran labarai a wayar shi, ya na ganin su ya gyara zama ta re da yi wa mota key. Su na shiga ya d'aga su ka nausa titi.
K'arfe shidda saura minti goma su ka shigo gida. Da ya Fu'ad su ka ci karo a parlour ya na cin pop corn ya na kuma kallon wani Indian series mai suna *JODHA AKBAR* a tashar Bollywood, sam shi ba ma fahimta ya ke yi ba, kawai ya canza tasha ne ya ga su na yi kawai ya bar shi.
"Kai, ina ku ka je ku ka yi yamma haka?". Fad'in ya Fu'ad ya na kallon su.
K'arasawa wajan sa su ka yi ta re da zama a gyefansa. Binty na gefen dama, Fanan kuma na hagu ta re sa saka hannu su ka soma cin pop corn d'in.
"Ba ma sai kun ban amsa ba, hannun ku kawai ya shaida min inda ku ka je. Masha Allah lalle ya yi kyau". Fad'in Ya Fu'ad ya na kallon zanen lallan hannun Binty da ya yi bala'in yi mata kyau kamar dan ita aka k'irk'ire shi.
"Anna ta ce in ce maku idan kun dawo ku d'aura girki. Kuma ku nutsu don yaya Bibi zai ci abincin kuma ta re za su zo da abokinsa. Don haka kallo ba na ku ba ne, aje a sauya kaya a shiga kitchen". Fad'in ya Fu'ad.
Ai har rige-rigen wuntsulowa su ka yi ta re da nufar sama don canza kaya su shiga kitchen d'in. Barr Fu'ad ba masu dariya.





*WAYE YOUSOUF MUHAMMAD AHLAM*
..........Cikakken bakatsine ne haifaffan garin Abuja. Mahaifin ya tara dukiya sosai do min shi ya ke da *SUNCITY ESTATE*. Mahaifin sa mace d'aya gare shi mai suna Saratu. Y'ay'an su takwas, hud'u maza hud'u mata. Sai dai estate d'in damk'am ya ke da zuri'arsa. Muhammad Ahlam mutum ne mai k'aunar zumuni, wannan dalilin ne ya sa gaba estate d'in shi, zuri'ar sa ne. Ana kiran sunan estates d'in da gidan kyawawa kasancewar mazan su da matan su kyawawa ne.
Yousouf shi ne d'a na biyu a cikin y'ay'an Dr Muhammad wanda ya kasance a da shi d'in likitan Tsohon sarkin Adamawa ne wanda ya mutu d'an sa ya hau, kasancewar sa mai amana ya sa ya zama kamar family a masarautar Adamawa kuma har gobe bai dai na ziyarta su ba duk da ya yi retired.
Yousouf ya yi karatunsa a k'asar *US*, engineer na'ura ne. Kamar yadda cikakkiya mace ta kware a sarrafa tukunya, haka Yousouf ya kware wajan sarrafa computer ko da kuwa idanuwansa a rufe ya ke. Kullum cikin busy ya ke, wannan dalilin ne ya sa ko kusa mata ba sa gabansa. Computers d'in sa su ne matansa. Mace ba ta gaban sa sam, kuma hakan ba Wai ya na nufin bai da lafiya ba ne. K'alau ya ke. Abokansa sun yi tsiyar har sun gaji sun kyalesa.
Yousouf na da matuk'ar kishin abunda ya ke so, hakan na d'aya daga cikin dalilan da ya sa ye gujewa mata saboda ya na da matuk'ar saka abu a zuciyarsa. Idan har ya na son abu to fa ya na san shi har abada kuma bai son a kusanci abun nan.
Yousouf na da wani ciwo tun ya na yaro, babu k'asar da ba'a je ba domin nai ma masa magani ba, amma har yanzu cutar ba ta warke ba, sai da kuma ya na dad'ewa bai ta shi ba.
Wata cuta ce da idan ta taso masa, zai iya wata biyu zuwa uku a kwance, ba ci ba sha, kuma sai dai a ba shi abinci a drip. Sannan kuma bai motsi sai dai ya yi ta bin mutane da idanuwa. Hankalin ahalin Dr Muhammad ba k'aramin tashi ya ke yi ba duk san da ciwon Yousouf ya ta shi.
Kwatsam kuma sai ga shi ya had'u da sahibul ruhinsa da ya ji ya na matuk'ar k'aunarta kuma zai iya ko mai saboda ita. Har cikin ran shi ya ke jin ta.
_wannan kenan._




*_____________________*
Cikin abunda bai fi awa guda ba, har sun kammala girki. Lafiyayyan tuwon shinkafa su ka girka da miyan wake da yaji bushasshen kifi da nama, sannan kuma su ka sake yin miyan ayoyo da kuma stew a gefe.
Sai da su ka jera komai a dinning ka na su ka haura sama don yin wanka.
7miss calls Binty ta ga ni a wayanta duk na Yousouf. Ba ta bi bayan call d'in ba sai da ta yi wanka ta re da d'aura alwala don an kusa kira isha'i. Su na girki aka yi magriba su ka sake su ka je su ka yi.
Mai kawai Binty ta murzawa jikinta ta zura doguwar riga mai hula ta re da saka dogon hijjab don har an riga da an yi kiran sallar isha'i.
Bayan ta idar da sallar ne ta bi kiran Yousouf. Katse kiran ya yi ta re da bin bayan kiran na ta.
Ringing biyu ta d'aga ta re da karawa a kunnanta,
"Amincin Allah ya tabbata a gare ki mai sona". Fad'in Yousouf.
"Ameen ta re da kai *Reality*". Binty ta fad'i ta re da kwanciya flat a kan gado.
"Ya ki ka ko ma gida?".
"Alhamdulillah! Kai fa?". Fad'in Binty.
"Cike da tunanin ni".
Anna ce ta turo k'ofar ta shigo ta re da fad'in,
"Da wa ki ke waya Binty?".......









*KU YI HAK'URI DA WANNAN MU HAD'E GOBE*
🌹 *51-52*🌹
............Cikin saurin ta yanke wayar ta re da mik'ewa zaune ta ce,
"Annah da school mate d'ina ce, mu na magana ne akan admission da zai fito".
"To maza ki sauko ki zo ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login