Showing 117001 words to 120000 words out of 162658 words

Chapter 40 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42916

"Hakane yaya Bibi".
"Good girl, yanzu ki je d'aki ki kuma dai na tunanin komai. Da kin ji tunanin zai zo miki ki d'au Qur'ani ki karanta ko kuma ki yi alwala ki yi sallah kin ji". Fad'in Julaibib.
Gyad'a kai Binty ta yi ta re da fad'in,
"Nagode yaya Bibi". Ta fad'i hakane ta re da fita daga d'akin.
Ya kai minti biyar ya na kallon k'ofar d'akin ka min ya saki ajiyar zuciya ya shige bedroom.


"Ke ina ki ka je ina ta nai man ki? Anacin ki sai kira ya ke yi a waya kamar zai fasa wayan. Da ya katse wani kiran ya ke k'ara shigowa". Fad'in Fanan.
"Kin san yanzu jiki sai ka na yi ka na motsa shi saboda kar in yi kib'a kamar *MATAR SAYYADEE*". Fad'in Binty.
"To ai sai ki je ki kira d'an anacin na ki ya na can sai faman kira ya ke yi. Ni gajiya ma na yi ba bar d'akin".
"Kar dai ki za ge shi wallahi". Fad'in Binty ta re da hayewa sama.
Ko da ta shiga d'aki, kashe wayar ta yi gaba d'aya ta fad'a duniyar tunanin abubda ya faru. Can kuma ta d'auki shawarar da Ya Bibi ya ba ta shiga bayi ta re da d'auro alwala ta yi raka'a biyu ta re rok'on Allah ya tseratar da Anna da zuri'arta daga Hajiya Mansura.

Kullum Binty cikin zullumin abunda Hajiya Mansura za ta yi was su Anna ta ke yi, har hakan sai da ya haifar mata da y'ar rama. Gashi ta saka numbern Kandala a blacklist saboda yawan damunta da kira da ta ke yi ta na k'ara tsoratar da ita.
An kwashi sati d'aya, biyu har uku ba ta re da Binty ta ga wani yunk'uri daga hajiya Mansura ba. Sai hakan ya d'an kwantar da hankalinta har ta saki jiki ta cigaba da walwalarta saboda a tunaninta Hajiya Mansura ta tuba ta hak'ura.



*_______________*
Hankali ta she ta ke kallon screen d'in wayarsa har k'ara gwalo idanuwanta ta ke yi ta na kallon fuskan Binty da ta yi wani irin kyau.
Riga da wando ne da ya fito da shape d'inta, sai hulan sanyin da ke kan ta, ana kuma ganin gashin kanta da ta ra ba shi gida biyu, d'aya ya zubo har k'an k'irjinta, d'aya kuma zube a bayanta hannunta d'auke da irin k'aton lollipop d'in nan ta saka shi a bakinta ta na tsotsa, sannan ga emoji na heart k'ato a d'an sama daga gefe.
Gabanta haka ya ke bugawa fat-fat-fat saboda tsabar rikicewa da mugun kishi da kuma tashin hankali.
Kallon shi ta ke yi hannun shi rik'e da ice-cream ya na tawowa in da ta ke a zaune. Idanuwanta sun kad'a sun yi jazur.
"Yaya Bibi wacece wannan a wajan ka?". Fad'in Sabrin da ta ke ji kamar zuciyarta zai fasa k'irjinta ya fito don tsabar kishi.
Aje ice cream d'in ya yi a kan d'an teburin gabansa ta re da karb'an wayar. Sai da ya sake kallon hoton ya yi murmushi ta re da saka wayar a aljihun gaban rigar shi ka na ya zauna ta re da fad'in,
"Ga ice-cream nan sha mu tafi".
"Ba zan sha sai ka fad'a min wacece wannan". Fad'in Sabrin hawaye na zubo mata daga idanuwanta.
Wani irin kallo ya watsa mata ta re da fad'in,
"Ki na hauka ne za ki tasa ni ki na min kuka kamar na miki wani abu? Ma ye ruwan ki da ita, menene damuwan ki da sanin alak'ana da ita?".
"Saboda ina son ka ina k'aunar ka. Kuma ba na k'aunar ko wacce mace kusa da kai idan ba ni ba. Haba ya Bibi, za ka ce min ba ka fahinci irin son da na ke maka ba? Tun ina k'ank'anuwata lokaci da ma ceto rayuwata na ji duk duniya babu namijin da na ke son kasancewa ta re da shi idan ba kai ba. Kai ka d'ai na ke gani naji kwarin guiwar cigaba da rayuwa a doran k'asa. Dan Allah ka da ma bari wata ta kwace min kai. Wallahi na fita komai". Fad'in Sabrin cikin kuka ta re da ka mo hannun Julaibib.
"Ki na hauka ne? Ni na tab'a cewa ina son ki ne? Duk wasu abubuwan da na ke mini da kulawan da na ke ba ki, aiki na na ke yi da kuma tausaya mi ki saboda irin lalurar da ki ke d'auke da shi. Amma ba na tuna nin akwai wata macen da na tab'a bawa lokaci na har na ke jure surutunki kuma na ke zuwa irin wajajan nan da ita idan ba ke ba har k'anwata da mu ke ciki d'aya da ita wanda na sa nta dad's ta na fatan haka. OK hakane ya ba ki damar yi min rashin kunya har ki ce ki na sona ko? To data yau Kim dai na ganin hak'ora na a wake balls har ki samu in fita da ke. Kuma yarinyar da ki ka gani a wallpaper na, ita na ke da burin aura, ban ga wata macen da ta fita ba a waje na. Kin ji ko ba ki ji ba?". Fad'in Julaibib.
Wani irin gunjin kuka Sabrin ta saki ta re da d'aukar Jakarta da ke kan teburin ta yi hanyar da zai fitar da ita daga part d'in da gudu.
Tsaki Julaibib ya yi ta re da mik'ewa, juyawar da zai yi idanuwansa su ka sauka a kan ta ta na wani irin dariya cikin nishad'i ita da wani saurayi da kuma y'an mata guda biyu. Gaban shi ne ya buga da k'arfi ya na tunanin mai ya kawo ta wajan nan a wannan lokacin su da ba fita su ke yi ba.
A fusace ya mik'e dai-dai lokacin da su ma su ka mik'e su ka shiga wani waje.
Da sauri ya bi bayansu, amma bai ga ko kyallinsu ba. Cizon yatsar shi ya yi k'udurta irin Fad'an da zai yi mata.
Ya dad'e ya na dudduba si bai gan su ba, dag bisani ya fito ya yi wajan motarsa ta re da yi mata key.
Kai tsaye gida ya nufa. Parking ya yi, kai tsaye ya nufi part d'in Anna ya na huci. Murd'a handle d'in ya yi ta re da shiga, da ita ya soma cin karo kunnanta mak'ale da earpies ta na miming wak'ar namenj ba ta ma san ya shigo don ta k'ure wak'ar.
Fizge earpiece d'in ya yi ya tsittsinka. A furgice ta mik'e za ta gudi ya damk'o ta aiko ta ce,
"Annaaahhh ki cece ni ya Bibi zai karya ni".
Da gudu Anna ta fito saga kitchen Fanan a bayanta.
"Da uban wa na gan ki a park? Shine don munafurci har kin dawo kin canza kaya ko. Za ki yi magana ko sai na ta ka maki kai".
"Wallahi wallahi wani billahil azeem yau ko k'ofar nan ban je ba kuma ka tambayi Anna ka ji through out mu na ta re".











*WASAN YA SO MA*

_MATAR SAYYADEE_
🌹 *63-64*🌹


πŸ’ƒπŸ»πŸ”₯πŸ”₯ _Ku na inahh nee?πŸ—£οΈ to maza ku firfito ka da wannan garab'asar ta wuce ku. Shin ko kun san Mrs Abubakar ta k'ara zuwan maku da zuma gangariya mai jawo maki martaba da soyayya a wajan mijin ki?_

_Ta shi maza ki karb'o kud'in adashen ki da ki ke zubi wajan Ladidi domin ki siya ke ma ki zama sarauniya_πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»
_Gangararriyar gangariyar zuma mai k'ara kuzari da ni'ima ta re da k'ara miki sha'awa da kuma sa ka miki wani dad'i da d'and'ano na musamman ta re da saka mai gida sambatu da zubar miyau πŸ™ˆ da gigicewa. Wannan zuma guarantee ne sai kin gwada na tabbata sai kin godewa Hassana (Mrs Abubakar). Haka kazalika ina macen da ke k'orafi akan miji bai kai mata? To kwantar da hankalin ki Mrs Abubakar ta kawo miki waraka da izinin Allah domin idan ki ka yi amfani da wannan zuma mijin ki zai jima bai yi inzali ba kuma ya na k'ara ruwan maniyyi da lafiya a jikin mai gida_
_Maza garzaya ki nai mi Mrs Abubakar a lambar wayarta kamar haka_
_+234 814 193 4442_
_Sayan nagari, mai da kud'i gida_πŸ€ΈπŸ»β€β™€οΈπŸ€ΈπŸ»β€β™€οΈπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ”₯


..............Wani harara ya watsa mata ta re da mai da dubansa izuwa ga Anna ka na ya ce,
"Kin san a ina naga yarinyar kuwa Anna? A park fa, ita da wasu k'awayanta guda biyu da wani saurayi wanda sam ni ban yarda da shi ba. Da ma kenan haka ake barin su sakaka su na fita su na had'uwa da kowani kare da doki? Sam ba zai yu ba wallahi". Fad'in Julaibib har ya soma in'ina.
"To Mr Julaibib ka gama?". Fad'in Anna ta na kallon shi don tsaf tuni ta dad'e da harbo jirginsa akan Binty.
"Anna ban gama ba fa, wallahi yaran nan su ka k'ara fita daga gidan nan, sai na b'alla k'afarsu". Fad'in Julaibib.
"Amma wai ba ka ji abunda ta ce ba ne? Yaran nan ba bu in da su ka je yau wallahi. Kuma ko fita ne, idan har ba da driver ko Yayan su Fu'ad ba ban yar da su fita". Fad'in Anna.
"To daga yau na hana. Duk in da za su je su fad'amin ni da kai na zan kai su, ban son abunda za'a zo a ce ni babban banza ne. Dole in kula da su in kuma kare mutuncin k'annai na". Fad'in Julaibib.
Har Anna ta bud'e ba ki za ta ce da ya ke CANADA wa ke kula da su, sai kuma ta fasa ta re da fad'in,
"To naji uban y'an zuciya".
Sai da ya kalli Binty ta re da yin kwafa ka na ya fice daga d'akin.
Ita kuwa Binty doguwar ajiyar zuciya ta saki ta na kuma tunanin shin wa ya gani mai kama da ita haka.
Julaibib kuwa da ya isa d'akinsa mamaki ya ke tayaya haka har yarinya k'arama ta soma yi masa gizo.
"Kai tabbas ita ce". Julaibib ya fad'a kamar wani zautacce.
"Sai na binciki yarinyar nan. Ba zan iya jura ba wallahi". Ya sa ke maimaitawa ta re da d'aukar wayarshi ya shiga kallon hotonta da ke kan wallpapern shi.


*___________*
Tun da mahaifiyarta ta haifeta, ba ta tab'a tafiyan k'afa ba sai yau. Domin tun daga park d'in nan haka ta tako har Wuse II da k'afarta ta na tafiya ta na hawaye.
Kai tsaye part d'in aunty Junaina ta nufa har bedroom d'in ta. Hanan da Amrah ido su ka bi ta da shi ta re da tab'e baki su ka mai da duban su ga Tv.
Fad'awa jikin aunty Junaina ta yi ta re da fashewa da kuka har da shasshek'a.
Sai da aunty Junaina ta tab'e baki ka na ta d'ago kafad'unta ta re da fad'in,
"Sabrin lafiya? Wa ya tab'a min ke?". Fad'in aunty Junaina cike da damuwa.
"Aunty na shiga uku, ta ki bari na. Duk in da na bi sai ta bini. Ta kwace min komai a *LEAD BRITISH*, har makarantar na hak'ura na bar mata. Yanzu kuma ta kwace min shi". Ta gama fad'in hakane ta re da rushewa da kuka.
Shafa bayanta aunty Junaina ta yi ta re da fad'in,
"Ban fahimce ki ba, yi min bayani domin in ga ne".
"Aunty ya Bibi ya ce bai tab'a so na ba, wai tausayi na ya ke ji kuma wai ita zai aura ba ni ba". Sabrin ta fad'a kamar numfashinta zai fita.
"Ban ga ne ba, wace yarinya ce wannan?". Fad'in aunty Junaina.
Fiddo wayarta ta yi daga cikin Jakarta ta shiga gallery ta re da fiddo hoton Binty wanda ta tura a wayarta ta nu na wa aunty Junainan.
Wani irin waro idanuwa aunty Junaina ta yi ta re da fad'in,
"Wannan ai yarinyar da Zuwairah ta nu na min ce. Tabbas ita ce. Idan ko hakane zan jefi tsun-tsu biyu da dutsi d'aya yasin". Duk cikin zuciyarta ta yi maganar a fili kuma wani murmurshi ta yi ta re da fad'in,
"Maza share hawayanki Sabrin. Wallahi wannan yarinyar ta bar ta da miki da hankali. Kawo kunnen ki kiji".
Ba ta re da ta jira Sabrin d'in ta kawo kunne ba ita ta kai bakinta kunnan Sabrin d'in ta yi mata wasu maganganu.
Cikin sauri Binty ta kalli aunty Junaina ta re da fad'in,
"Really?".
"I'm very sure my lovely daughter". Ta fad'i hakane ta re da ba shi hannu su ka tafa.


..............Fitowarshi kenan daga cikin asibitin ya nufi wajan motarshi hannunsa rik'e da fara k'al d'in rigar likitoci idanuwansa su ka sauka a kanta ta na yi wa wata mata magana hannunta rik'e da wani kyakkyawan yaron da ba zai wuce 8 years ba.
Wannan saurayin da ya gan su ta re da shi a park shi ne ya bud'e ma su mota su ka shiga shi kuma ya zagaya ya shiga driver seat ya ta da mota.
Cikin azama Julaibib ya shiga motar ta re da yi mata key, sai dai abun takaici a kwai wata mota da ta yi blocking d'in sa. Tsaki ya yi mai tsawo ka na ya bud'e murfin motar ya fito ya nufi motar da ya ga ta shiga. Sai dai kash tuni har sun fice daga asibitin.
"Kaiiiiiiiiiii! Dam it". Shine abunda fad'a ta re da buga gaban wata motar da ke gefensa.
Can kuma ya juya ya nufi cikin asibitin ya na balbale fad'a akan wanda ya yi blocking d'in sa. Cikin sauri mai motar ya fito ya na ta na shi hak'uri ta re da matsar da motarsa.
Shiga motar ya yi ta re da nufar gida direct. Saboda gudun da ya ke yi, cikin mintuna k'alilan ya isa gida.
Sai dai abunda ya ba shi mamaki, ya na parking Alhaji Usman na parking kuma ta re su ke da Binty, Fanan har da Anna.
Sosai mamaki ya bayyana a kan fuskan shi ya na tunanin to wa ya gani a hospital.
Hakanan ya had'iye duk abunda ya taho da shi ta re da isa wajan su ya gaida daddy da Anna ka na ya wuce side d'in sa cike da sak'e-sak'e.

Binty kuwa tunda Anna ta hana su fita kamar yadda Julaibib d'in ya tsara sai ta shiga tashin hankalin rashin ganin masoyinta Yousouf.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login