Showing 123001 words to 126000 words out of 162658 words
Usman Ku ma ya zauna a gidan baya.
"Ka na hauka ne Julaibib? Ka dai na gudu da mu haka kamar za ka ta shi sama". Fad'in alhaji Usman.
Shi kuwa Fu'ad tu ni wani abu ya darsu a zuciyarsa ga me da wan na shi. Hankalin sa ne ya ta shi saboda sawa kan shi wannan tunanin.
Cikin mintuna k'alilan ya suka isa gida. Ko cikakakken parking bai yi ba ya fito da sauri ya nufi side d'in Anna.
Sama ya hau har d'akin su Binty wanda shi ne karon shi na farko.
Ta na nan kwance jikin Anna, Fanan kuwa sai kuka ta ke yi.
Ciccib'arta ya yi ta re da kwantar da ita a kan gadonsu ka na ya shiga k'ok'arin ceto rayuwarta dai-dai lokacin Alhaji Usman ta re Fu'ad su ka danno kai.
Ganin numfashinta ya k'i dawowa sai ya rik'e hancinta ta re da kai bakinsa kan nata ya shiga hura mata iskan bakin shi.
Fu'ad saurin saukar da idanuwansa k'asa ya yi hawaye na tsiyayo masa daga idanunsa.
Cikin second biyar ta ja wani irin dogon numfashi ta re da ware idanuwa.
"Alhamdulillah!". Gaba d'aya d'akin su ka fad'i.
"Wayyo Allah. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, wallahi aljani ne, ya na d'akin nan. Yousouf ba mutum ba ne". Fad'in Binty a gigice cikin fitar hayyaci.
Runguneta Julaibib ya yi tsam a jikinsa ya na mata addu'a cikin kunnanta.
Cikin k'ank'anin lokaci kuwa bacci ya yi awon gaba da ita.
Kwantar da ita ya yi a hankali ta re da ja mata bargo. Anna da Alhaji Usman na kallonsa, ya yin da Fu'ad ya bud'e k'ofa ya fice daga d'akin.
"Anna I'matsala wallahi". Fad'in Julaibibi cikin harshan fulatanci.
"Muje parlour ka da maganar mu ya ta she ta". Anna ta fad'a ita ma cikin harshan fillancin.
Ta re su ka fita zuwa parlour dukan su. A nan su ka taras da Fu'ad zaune a kan kujera ya rik'e kanshi da hannu biyu.
Bayan sun zauna ne Alhaji Usman ya kalli Anna ta re da fad'in,
"Ummu Julaibib yarinya nan ina ganin gamo ta yi. Don magana ta gaskiya yaron da ta ke fita ta samu da ta ce mana sunansa Yousouf Muhammad Ahlam, ba haka ba ne. Shi ainahin yaron shi muka je gaishewa ya na nan kwance kamar gawa a gidansu tsawon wata biyar. Ku ma kun dai ji sambatun da ta ke yi lokacin da ta farfad'o".
"Wannan shine ma babban damuwa ta". Fad'in Julaibib.
Anna kuwa ta kasa magana sai jikinta da ke rawa.
"Anna bazan jure ba sam wallahi". Julaibib ya sa ke fad'i.
Kallon shi gaba d'ayansu su ka yi. Anna ta ce,
"Kamar ya ke nan?".
Sai a lokacin Julaibib ya dawo cikin natsuwarsa jin katob'arar da ya yi.
"Ba bu komai". Ya fad'a ya na wani sunnar da kai k'asa kamar wanda ke gaban surukansa.
Anna da alhaji Usman ba su san lokacin da dariya ta kubce ma su ba.
Saurin mik'ewa Julaibib ya yi ta re da barin d'akin ya na sosa k'eya.
*Washa gari*
Anna ba ta samu cikakkan barci ba, bini-bini ta ke zuwa d'akin su Binty domin duba jikinta. Duk lokacin da ta je sai ta samu ta na sharar baccinta.
Hakan ya sawa Anna baccin bayan sallar asubha.
Gefen Julaibib kuwa kasa rintsawa ya yi, tunanuka ne ke masa yawo sosai a kwakwalwarsa ga me da Binty.
Ita kuwa Binty, ko da ta farka wasai ta tashi, sai dai jikinta da ke d'an mata tsami-tsami.
Hannu ta kai domin mai da gashin da ya zubo mata ya rufe fuskanta. Karaf idanwanta ya sauka a kan zoben da Yousouf ya saka mata wanda su ka yi wa juna alk'awari.
Tsurawa zoben idanuwa ta yi ba ta re da kyafatawa ba, sai ta ga kamar fuskan Yousouf ta ke gani a jiki. Tuni komai na jiya ya dawo mata cikin kwakwalwarta.
"Dagaske kai aljani ne masoyi?". Fad'in Binty ta na kallon zoben.
Saurin b'oye hannun ta yi a bayanta gabanta na fad'uwa ganin zahiri fuskan Yousouf d'in ya fito a jikin zoben ya na d'aga mata kai.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!". Shi ne abunda ta fad'a ta re da dafe k'irjinta. Ta dad'e a haka ka min ta mik'e ta shiga bayi.
Wanke fuska ta soma yi ka na ta kalli fuskanta a jikin madubin da ke jikin bayin.
Waro idanuwa ta yi ta na son yin ihu amma ta kasa ganin Yousouf b'aro-b'aro a jikin mirror ya na kallonta.
"Mai sona, ba haka mu ka tsara rayuwar mu ba. Kin manta alk'awarin da mu ka yi wa junan mu? Kin yi alk'awari za ki rayu da ni cikin ko wani irin hali, shin kin shirya karya alk'awarin ne?". Ya fad'a ya na mai fitowa daga cikin mirror d'in.
Matsawa baya ta yi ta re da jingina da bango. Sai da ya zo daf da ita har su na jin numfashin juna ka na ya ce,
"Mai Sona mun kasance ta re ni da ke tun ina k'arami ke kuma ki na jaririya. Da wannan hannun nawa na ke shayar da ke madaran shanu har ki ka rayu. Zafi, sanyi, ruwa ina ta re da ke ban tab'a ba ri wani abu ya cutar da ke ba. A duk lokacin da ki ka kwanta rashin lafiya ta re muke jin ya. Du bi baya na....". Ya fad'i hakane ta re da kware rigar da ke jikinsa ya juya bayan na shi domin ta ga ni.
Wani irin zaro idanuwa ta yi sakamakon manya-manyan yanka na wuka har cikin jikinsa ta ko'ina a bayansa.
Mai da rigarsa ya yi ta re da fuskantar ta ya ce,
"Kullum wanna yanka da ki ke gani a jikina shine karin safe ne. Zuri'a sun kasance su na yak'i da bil'adama ne a sanadiyar wani tsautsayi da ku bil'adama Ku ka yi ya jawo rasa rayuwar kaka na na bakwai tun ya na jariri. Ni kuma ina karb'an wannan hukuncin ne saboda ke kasancewar na tsaya tsayin daka sai na taimake ni. Yanzu haka kaka na kurkukun Daulatun Bahashan ya na karb'an azaba daga sarkin hukuncin Daulatul Sira wato masarautar mu. Kaka shi babban amintaccan bawan sarkin da ya mulki Daulatul Sira tun daga zamanin sarauniya Oumul Quwaisi wacce ta yi mulki shekara dubu arba'in da hud'u da suka wuce. Yanzu haka sarauniyar da ke mulkar k'asar mu ta ba da umarni a kamo ni ko da rai ko ba rai duk a sanadiyar tsaya miki da na yi. Dan Allah Binty kar ko guje ni". Yousouf ya k'arisa maganar hawayan jini na zubo masa daga idanuwansa.
*Wallahi tausayinku na Ji na d'an yi maku*
🌹 *67-68*🌹
.............Tausayin sa ne ya ka ma ta. Jikinta na rawa ta ce,
"Mai ya sa kai min k'arya tun farko? Ku ma ta yaya ni da na ke bil'adama zan yi rayuwa da jinni? Ka duba ka gani kai ma". Fad'in Binty.
Zuba mata idanuwa ya yi sai da ta tsorata saboda yadda idanuwan na sa su ka koma kamar jini tsabar ja. Ajiyar zuciya ya sauke ta re da fad'in,
"Mai sona, abunda ya sa na b'oye miki ni wanene saboda gudun ka da ki guje ni ne. Ku ma zancan ke bil'adama ce ni kuma jinni ki aje a gefe. A wajan ubangiji duk d'aya muke. Kamar yadda aka halicce ku domin bautawa ubangiji, mu ma haka ne. Ba mu da banbanci a wajansa. Zan iya rayuwa da ke kamar yadda jinsin ki zai yi rayuwa da ke, fiye da su ma saboda bil'adama bai da amana, ya na wulak'anta mace da cin mutuncinta. Kar ki manta Binty, ba ki da kowa a cikin duniyar nan sai ni. Ko wad'annan mutanan da ki ke zama da su, ba su san komai a kan ki ba, kuma ka da ki cire tsammanin ranar da za su juya maki baya. Kowa na shi ya ke so a wannan zamanin da mu ke ciki. Binty ki min halacci, da yanzu ba ki cikin wannan duniyar amma na jure azaba da tashin hankali a kan ki. Na k'auracewa mahaifiyata da dangina da masarautar mu wanda a tarihi bai kamata tsatson amintaccan bawan sarki ya yi wa masarauta butulci ba. Ni nan saboda ke Binty na jawo wa masarautar mu wani gagarumin yak'in da ke tunkaraso su. A kwai wani dad'ad'd'iyar yarjejeniya tsakanin Masarautar Daulatul Bahashan da da Masarautarmu wato Daulatul Sira wanda Oumul Sahwat ke mulka. Masarautun nan biyu sun dad'e su na fad'a da juna tun shekaru dubu tamanin da shidda da su ka wuce. Yak'in ya soma ne sakamon jinnun Daulatul Sira da su ke shiga cikin bil'adama su na aiki da su, wanda hakan ya ja Masyush d'a ga Dahdaz wato sarkin Daulatul Bahashan kuma magaji tilon namiji kasancewar y'an uwansa matane ya nai mi d'an wajan Sarki Hawan kakan Oumul Sahwat da ke mulki a Daulatul Sira a yanzu da ya fitar da shi zuwa duniyar mutane kasancewar su an haramta masu shiga cikinsu. Cikin tsautsayi dawowar da ba su yi ba kenan saboda juye trailern siminti da wani attajiri ya sa aka yi a companyn shi, su kuma su na wajan kasancewar yara ne su a wannan lokacin don ba za su wuce shekaru saba'in ba. A kan su a ka juye wannan siminti wanda ya yi ajalinsu har lahira. Wannan abune ya jawo mummunan yak'i tsakanin Daulatul Sira da Daulatul Bahashan. Sai bayan hawan kakan Oumul Sahwat ne ya kira sulhu a bisa yarjejeniya akan Daulatul Sira ba za su k'ara shiga Bil'adama ba, kuma ko cikin mafarki ba za su shiga duniyarsu ba. Daulatul Sira ta amince da sharad'insu har ta sarkin wannan zamanin ya saka hannu da jinin jikinsa. Hakane ya samar da sulhu tsakanin masarautun biyu. Sai dai zuwanki cikin rayuwa ya k'ara d'ad'd'ago wani bargon bala'in fitinan da na ke gani babu makawa Daulatul Sira za ta shafe a tarihi saboda wacce ta ke mulkar Daulatul Bahashan Bak'ayatul maharuri ba k'aramin azzaluma ba ce, don bayan hawanta mulk'i sai da ta bibiyi tsatson wanda ya yi sanadiyar mutuwan kakanta na uku ta shiga jifansu da bala'i wanda yanzu haka d'an jikan tattab'a kunnan bawan Allah nan ya na halin matsanaicin ciwo yanzu haka, kuma shine wanda na yi k'arya da sunan shi, wato Yousouf Muhammad Ahlam. Saboda san kasancewa da ke shiyasa na ke ta yawo k'asa-k'asa ina gujewa hukuncin sarauniyar Daulatul Sira, duk da haka kullum sai na karb'i hukunci duka da takobi mai k'aifi a baya. Ke ce kwarin guiwata shiyasa na kasa nesa da duniyar nan. Dan Allah ki bi ni mu gudu zuwa wata duniyar da babu wanda zai takura mana. Ki Cuba halaccin kaka na a wajanki wanda ta re da shi muke ta jigila da ke".
Sosai Binty ke kuka har da shasshek'ar tausayin Yousouf.
"Yanzu duk a kai na ka yi wannan Yousouf? A kai na ka ke jure azaba haka? Mai zan yi in saka maka Yousouf? Ina ma zan iya abunda ka ke so na aikata". Fad'in Binty ta na kuka sosai.
"Ki rayu da ni Binty, za ki iya, dan Allah".
Sosai ta k'ura masa idanuwa ta re da fad'in,
"Su waye iyaye na?".
Girigiza kai ya yi ta re da fad'in,
"Ni ma ban sa ni ba Binty".
"A ina ku ka tsince ni? Ko ni ma aljanar ce kamar kai?". Fad'in Binty.
"Binty ke mutun ce, labarin tsintar ki kuma, kaka ne kawai zai iya ba da shi, ni ban san komai ga me da haka ba". Fad'in Yousouf.
"Ya za'a yi na ga kaka?". Binty ta fad'a.
"Idan ki ka amince ki ka bi ni domin mu rayu mu zama d'aya, dole kaka da kan shi zai nai me mu, a lokacin za ki san labarin ki da na mahaifan ki".
"Zan bi ka, amma ka ba ni lokaci tukun don shawara". Fad'in Binty.
"Nagode mai sona. Na ba ki lokaci har sai kin nai me ni. Da gin buk'aci gani na ki murza zoben hanunki zan bayyana". Fad'in Yousouf ta re da juyawa ya koma cikin mirror, sai da ya mata bye-bye ka na ya b'ace.
Dogon ajiyar zuciya ta sauke ta re da cire kaya ta sakarwa kanta ruwa ta yi wanka ka na ta fito daga bayin.
Sai da ta shafa mai ta saka kaya ka na ta nufi d'akin Anna domin gaishe ta. Kwance ta sa me ta a kan darduma ta na bacci. Duk'awa ta yi ta re da sumbatar kumatun Anna ka na ta ce,
"Anna ina son ki, ke uwa ce a gare ni wacce ban da kamarta. Nagode miki Anna, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi".
"Ameen d'iya ta, ni ma ina sonki". Fad'in Anna da ta tashi zaune ta na kallon fuskan Binty.
"Ya jikin na ki?". Anna ta sa ke fad'i.
"Naji sauk'i Anna". Fad'in Binty ta re da mai da dubanta izuwa ga k'afar Anna da ya yi wani irin fushi har kyalli ya ke yi kamar wacce maciji ya sara a k'afar.
Zaro idanuwa binty ta yi ta re da fad'in,
"Wayyo Allah Anna mai ya samu k'afarki?". Fad'in Binty ta na kai hannu zuwa k'afar Anna.
Ita sam Anna ma ba ta lura da k'afar na ta ba ma sai Binty ta yi magana. Ita ma zaro idanuwa ta yi ta na kallon k'afar da ya yi wani irin kumbura don sai ka had'a k'afar Binty sau goma zai ba ka k'afar Anna d'aya. Kuma k'afa d'aya ce ta yi wannan kumburin.
Sosai hankalin Anna ya ta shi, amma sai ta danne domin ta kwantarwa da Binty hankali ta re da fad'in,
"Ke kar ki damu, ina ga kwanciyar k'asan da na yi ne ya jawo min kumburin amma zai sace in sha Allah. Yanzu sauka k'asa ki je ki karya maza".
Rushewa da kuka Binty ta yi ta re da fad'in,
"Anna wallahi ba ko da lafiya, kalli fa yadda k'afar ki ta yi". Ta fad'i hakane daidai lokacin da Barr da Julaibib su ka shigo d'akin.
Turus dukansu su ka tsaya su na kallon Binty da ke duk'e ta na kuka.
Saurin k'arasawa Julaibib ya yi ta re da fad'in,
"Ke me......." Bai k'arasa ba sakamakon idanunsa da ya fad'a a kan k'afar Anna da ya yi suntum.