Showing 129001 words to 132000 words out of 162658 words
duk a tunaninta yarinyar da za Junaina ta ce za ta kula da ita ba ta wuce three years ba.
Ba ta re da ta k'ara magana ba ta tada mota ta re da yi wasa gate man horn.
Cikin sauri ya wangale gate ita kuma ta tura hancin motar ciki ta re da nai man waje ta yi parking.
Junaina ce ta fara fitowa ka na Binty ta fito. Kai tsaye part d'in Junaina su ka nufa ta na gaba Binty na biye da ita a baya wanda haka nan ta ji gabanta na fad'uwa.
Murd'a handle d'in ta yi ta re da kutsa kai ciki sa'annan Binty ma ta biyo baya.
Zaune ta ke a kan two sitter cikin riga da wato da tasha tocking gashin nan ya sha gyara ta kuma yi parking d'in sa a gefe, fuskanta ya sha glasses da ya kusa cinye rabin fuskanta ta re d'aura k'afa d'aya a kan d'aya ta na taunar cingam k'as-k'as-k'as.
"Yauwa k'araso ciki, kin ga wacce za ki yi wa hidima nan, ki kuma tabbatar kin yi mata duk wani abunda ta ke buk'ata ban san jin k'orafinta". Fad'in aunty Junaina ta na mai nunawa Binty Sabrin d'in.
Cire glasses d'in fuskanta ta yi ta re da huro cingam d'in bakinta ya yi kwai ka na ta fasa ta re da mik'ewa ta na kallon Binty da mamaki ya gama kasheta baki sake sakamakon ganin fuskan Sabrin.
Sabrin d'in kuwa zagayeta ta soma yi ta re da k'are mata kallo ta na wani shu'umin murmushi ta re da hura mata cingam a fuska.
Aunty Junaina dariya ta yi ta re da wucewa side d'inta da ke upstairs.
"Wa ma ki ke da suna? Binty ki ke ko wa?". Fad'in Sabrin ta na dariya.
Wani murmushi Binty ta yi mai k'ona zuciyar wanda aka yi wa gashi ya k'ara fito da tsantsan kyawunta ka na ta ce,
"Lallai! Ashe na tsaya a ran ki haka? Gaskiya a gaishe ni domin tsayin shekaru kin ka sa manta ni, hakan na nufin ina d'aya daga cikin mutanan da ki ke tsoro su ke kuma sa ki fargaba".
"Ki iya bakinki yarinya! Domin ki na cikin gidana ne, gidan ubana". Fad'in Sabrin a tsawace.
"Haba? Sannu dodon kod'i wanda ko wani lokaci shi da gidansa ya ke yawo". Fad'in Binty.
"Lallai ni na ke fad'e ki na fad'e a cikin gidan ubana? Sai na koya miki hankali, sai na b'ata wannan banzan fuskan da ki ke tak'ama da shi ta yadda ba za ki k'ara burge wani d'a namiji a raguwarki ba. Ba ki isa ki kwace duk wani abu da ya ke mallaki na ba. Julaibib nawa ne ni d'aya, babu wata mace da ta isa in yi takara da ita, kin tafka babban kuskure a rayuwarki na son duk wani abunda ya ke mallakin Sabrin". Fad'in Sabrin ta na nuna Binty da yatsa.
"Ke ba ki kai matsayin da zan yi takara da abu d'aya da ke ba, hasali ke ce ki ke bakin ciki kasancewar na fiki komai. Ba ri ki ji in fad'a miki wani abu, tun lokacin da ki ka bar *LEAD BRITISH*, na manta da wata yarinya mai suna Sabrin, ni ba kya rai na saboda ban d'auke ki komai ba, ke ce na tsayawa anan". Fad'in Binty ta re da nuna mak'ogoranta.
"Waye ubanki? Kin san ko ni wacece kuwa?". Fad'in Sabrin a fusace.
"Ke wacece ki ke tambayata? To saurara ki ji, ke ba komai ba ce face d'igon maniyi, wacce a hankali ki ka koma gudan jini ki ka ko ma tsoka akai ma ki halitta sannan aka busa ma ki rai, kuma a karshe za ki mutu a binne ki a k'asa a barki daga ke sai halinki, aikin da ki ka shuka a duniya walau na khairi ko akasin haka, shi za girbe".
Hannu Sabrin ta d'aga za ta wanke fuskanta da mari, caraf Binty ta rik'e hannun. Sabrin ta yi- ta yi ta kwace amma ta kasa sai da Binty ita da kanta saki hannun da izza ta ra da fad'in,
"Kada ki k'ara tunanin kwatanta haka, za ki yi nadama don na san ba ki manta had'uwan mu na farko ba a mall d'in babanki".
"Za ki yi nadamar abunda ki ka aikata, sai kin duk'a bisa k'afafuna ki na nai man gafarata, ni kuma wallahi ba zan yafe miki ba, sai na koya miki hankali, banza wacce ba'asan asalinta ba". Fad'in Sabrin ta re da hayewa sama ta na huci.
Zama Binty ta yi a kan kujera ta re da rik'e kanta ta na jin sam ba za ta iya zaman gidan ba.
Murd'a handle d'in k'ofar ta yi ta re da shiga ta yi banging k'ofar.
Aunty Junaina da ke cire d'an kunne a gaban mirror ta yi saurin juyawa ta kalleta.
"Kin saka na tura miki 10million a account d'in ba ta re da daddy ya sani ba, ki ka kuma k'ara buk'atar wa ni 5million na kuma d'aukar wayar daddy na miki transfer shi ma ba ta re da ya sani ba duk a dalilin alk'awarin da ki ka min na cewar za ki kawo min Binty har cikin gidan nan kuma sai ta duk'a min. Tabbas kin kawo ta ga ta can a k'asa, amma ba ta duk'a min ba sai maganganu da ta yi min masu zafi da k'ona zuciya, dama kin shirya hakane don zuciyata ta buga in mutu?". Fad'in Sabrin ta na nuna saitin zuciyarta.
Kamo ta aunty Junaina ta yi ta re da zaunar da ita a bakin gado ka na ta ce,
"Relax my daughter, tabbas yarinyar nan sai ta duk'a a gabanki, za ki juyata fiye da tunaninki. Sai dai ina so ki nutsu mu yi komai cikin natsuwa. Yau ta zo gidan nan, mun d'ana mata tarkon da dole ne ma ta duk'a miki, ke dai ba ni daga nan zuwa kwana uku". Fad'in aunty Junaina.
Ajiyar zuciya Sabrin ta saki, ba ta re sa ta sake cewa komai ba ta d'auki wayarta da ke kan gadon ta fice daga d'akin.
Ko da ta sauko k'asa, sai da ta watsawa Binty wani irin kallo wacce kan ta ke duk'e a k'asa ta ba sak'e-sak'e cikin zuciyarta.
Kwata ta yi ta re da fita ta buga k'ofar wanda k'arar k'ofar ya firgita Binty da ta lula duniyar tunani.
Binty ta kusa awa biyu a zaune ka na Amrah da Hanan su ka shigo wanda dawowansu kenan daga gidan kakarsu da ke suleja.
Kallonta su ka yi ka na su ka juya su ka kalli juna. Tab'e baki Hanan ta yi ta re da shigewa side d'in su. Ya yin da Amrah ta ke kallonta ta re da fad'awa kogin tunanin maganganun kawar mummyn na su da su ke tattaunawa. Ajiyar zuciya Amrah ta yi ta re da bin bayan Hanan zuwa d'aki ba ta re da sun ce mata k'ala ba ita ma kuma ba ta masu magana ba don a ganinta su ya ka ma ta su yi mata sallama tunda su su ka shigo su ka same ta.
............"Sister wai ki na ina ne?". Fad'in Fanan da ke ta faman kwalawa Binty kira ta re da duba lungu da sak'o na part d'in na su.
K'ofar bayi ta nufa ta re da kwankwasawa, nan ma shuru. Tura bayin ta yi, nan ma ta ga wayam.
Fita ta yi daga part d'in ta nufi garden, nan ma ta duba sak'o da lungu ba ta ganta ba.
"To ina ta ke? Ba dai ta sake fita sun don had'uwa da mayaudarin nan ba mai k'arya da sunan wani?". Fad'in Fanan cikin zuciyarta.
Komawa part d'in su ta yi da gudu ta haura sama ta re da d'auko wayarta ta re da kiran numbern Bintyn amma sai ta ji wayar na k'ara a d'akin.
D'auko wayar ta yi da ke k'ark'ashin pilo gabanta na fad'uwa.
Wani gudun ta kwasa ta re da yowa k'asa. Kicib'isa su ka yi da Barr Fu'ad hannun shi d'auke da kaya, sai ya Bibi hannun shi rik'e da hannun Anna da ta warke sumul ga kuma Daddy a bayansu ya na murmushi.
"Annaaaaaah!". Fad'in Fanan ta re da nufarta da gudu ta rungumeta ta na hawayan murnar ganin Anna ta warke.
"Kin ga Annar ki kamar mai cutar jinnu ko, gobe fa muke shirin fita k'asar, cikin hukuncin ubangiji sai ga Anna sumul k'afa sun sace har ta na takawa da kafarta ko ina, shi ne fa ta kafa k'ahon zuwa dole sai an dawo gida kuma na san saboda ku ne, ta yi kewarku". Fad'in Daddy.
Rungumeta Fanan ta kuma yi ta re da fad'in,
"Anna munyi kuka kamar idon mu zai fita".
Anna da ke murmushi ta ce,
"To gani nan ai, kuka ya k'are naji sauk'i. Ina autata?".
Sai a lokacin gaban Fanan ya buga ta shiga zare idanuwa ta na kallonsu.
"Ta na ina?". Fad'in Julaibib tashin hankali bayyane a fuskan shi.
"Yaya Bibi wallahi ni ma ban sani ba, tun d'azu na ke ta nai man ta har garden ban ganta ba. Kuma na kira wayarta na ji ta na ringing a d'aki". Fad'in Fanan.
Da gudu Julaibib ya nufi upstairs ta re da bubbud'e ko ina amma wayam.
Anna kuwa ji ta yi cikinta ya wani irin murd'awa yayin da Barr Fu'ad ya nufi wajen gida domin dubo ta.
Daddy kuwa hankalinshi bai wani tashi ba don a tunanin shi Binty ba za ta b'ace ba ta na gidan sai dai idan wani wajan ta shiga.
Abu kamar wasa har dare ba Binty ba labarinta. Julaibib ya yi wajan su Oga Solomon ta re da tambayansu ko Binty ta fita, amma su ka shaida masa cewar ko wajan first gate Binty ba ta je ba balle ta fita.
Tun alhaji Usman na d'aukar abun da sauk'i har shi ma hankalinsa ya ta shi don shi ma ya soma tunanin ko Binty ta bi saurayin da ya yi mata karya da sunan Yousouf d'an gidan abokinsa.
Anna da Fanan kuwa kuka kawai su ke yi.
Ranar dai gaba d'ayansu babu wanda ya yi bacci don wani irin bincike a ka shiga yi har d'akin Suhail in da aka ci karo da manya-manyan kwalaye guda arba'in na cocaine da kuma ticket na zuwa k'asar hongkong guda hamsin.
Hatta d'akin Hajiya Mansura bai tsira ba wajan bincike, don Julaibib haukace masu ya yi kamar zaki.
🌙🌙
.............Kuka Binty ke yi sosai tsugune a gaban Junaina da Hajiya Zuwairah ta re da fad'in,
"Mai yasa za ku yi min haka? Ban cutar da ku ba ka da ku cutar da ni ba, don kun ga *BA NI DA GATA* shiyasa Ku ke gwara rayuwata kamar kwallo? Duk abunda Ku ke buk'ata da in yi maku abu d'aya kawai zan iya yin sa shine rayuwa a matsayin baiwar Sabrin har k'arshan rayuwata in dai har Anna ba za ta cutu ba. Ka da ku cutar da bayin Allahn nan don soyayyar da Allah ke wa manzon my SAW. Na rok'e ku". Fad'in Binty ta na kuka sosai ta re da had'e hannayanta biyu.
"Mu dai kin ji abunda mu ka ce miki don abunda Mansura ta yi kad'an ne a kan Wanda mu za mu yi mata. Mun ba ki nan da wata d'aya ki yi shawara". Fad'in Hajiya Zuwairah ta re da mik'ewa ta kalli aunty Junaina ta re da fad'in,
"Na yi nan, sai kin ji daga gare ni". Ta na gama fad'in haka ta fice daga parlourn.
Aunty Junaina kallon Binty da ke durk'ushe ta yi ta re da fad'in,
"Ki zagaya ta baya, ta na can wajan garden ki je ki tab'a k'afafuwanta ki nai mi gafararta". Ita ma ta na gama fad'in haka ta haye sama.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!'. Fad'in Binty ta re da mik'ewa ta nufi waje.
Amrah da ke mak'ale jikin labule ta na hawaye ta fito da sauri ta yi d'akinta.
"Besty ka ba ni shawara ya zan yi da wannan guy d'in dan Allah. Wallahi ina matuk'ar son shi sosai". Fad'in Sabrin da ke kallon Hamdan hannun shi rik'e da smoothie ya na sipping.
"Hmm, ni dai idan da za ki ji shawarata, to ki fita harkan shi tun da ya nu na miki shi ba son ki ya ke ba". Fad'in Hamdan.
"Ni ba zan iya rayuwa babu shi ba". Fad'in Sabrin ta re da marairaicewa.
"Da ai da babu shi ki na rayuwan ki, saboda haka yanzu ma za ki iya rayuwar ki ko ba bu shi". Fad'in Hamdan.
Sabrin ta bud'e baki za ta yi magana ta hangi Binty na zuwa. Wani murmushin jin dad'i ta yi saboda yanayin Bintyn ka d'ai ya isa ya fallasa abundan ta zo yi.
Binty na k'arasowa wajan ta rik'e kafafun Sabrin ta na hawaye ta re da fad'in,
"Ki min aikin gafara da yin sa'in sa da ke, kuskure ne da kuma sharrin shaid'an amma ko kusa ke ba tsara ta na ce. Kin min fintinkau a komai. Ke d'in cikakkiyar d'iya ce ni kuma ba komai ba ce face *MARA GATA* wacce ta ke ba ta da kowa sai bolan da ta ke rayuwa a kai. Ta yaya kamar ni zan had'a kai na da cikakkiyar d'iya kamar ki, don Allah ki wa Binty y'ar bola aikin gafara da yau za ta kasance a matsayin baiwarki har k'arshan rayuwarta".
Wani irin mik'ewa Hamdan ya yi bakinsa na rawa ta re da fad'in,
"Binty! Binty na. Bintyn Hamdan. Ki ce min ke ce dan Allah ba mafarki na ke ba
Binty na k'arasowa wajan ta rik'e kafafun Sabrin ta na hawaye ta re da fad'in,
"Ki min aikin gafara da yin sa'in sa da ke, kuskure ne da kuma sharrin shaid'an amma ko kusa ke ba tsara ta na ce. Kin min fintinkau a komai. Ke d'in cikakkiyar d'iya ce ni kuma ba komai ba ce face *MARA GATA* wacce ta ke ba ta da kowa sai bolan da ta ke rayuwa a kai. Ta yaya kamar ni zan had'a kai na da cikakkiyar d'iya kamar ki, don Allah ki wa Binty y'ar bola aikin gafara da yau za ta kasance a matsayin baiwarki har k'arshan rayuwarta".
Wani irin mik'ewa Hamdan ya yi bakinsa na rawa ta re da fad'in,
"Binty! Binty na. Bintyn Hamdan. Ki ce min ke