Showing 141001 words to 144000 words out of 162658 words
doka ta re da shi da mahaifiyarsa da kuma mahaifin mahaifiyarsa wanda dukkaninsu sun kasance zuri'ar amintaccan bawan wannan masarauta. Don haka yanzu za su fara fuskantar hukunci".
Gaba d'aya aljanun nan su ka shiga ihu su na fad'in,
"Hukunci! Hukunci!! Hukunci!!! Sai sun fuskanci hukunci".
Kallon wannan badakkare Oumul Sahwat ta yi ta re da jinjina kan ta.
Kaifaffiyar doguwar wuk'a ya zaro daga k'ugunsa ya saita k'eyar mahaifiyarsa Yousouf wacce ke hawaye ta na kallon Yousouf d'in ta re da girgiza masa kai ta na kuma furta "kar ka karaya ko sun kashe ni" a leb'anta.
Sai da ya d'aga wannan wuk'ar sama ka na ya aza da k'arfi bi sa k'eyar mahaifiyar Yousouf sai da jini ya yi tsartuwa ta re da wanke fuskan Yousouf ka na kan ya fita daga gangan jikinta ya gungura k'asa.
Gaba d'aya aljanun nan su ka d'au shewa da ihu ya yin da Sabrin da Binty su ka sa ke zubewa k'asa sumammu karo na biyu.
A gigice su ka farfad'o sakamakon wani irin ruwan sanyin da su ka ji a kan fuskokinsu da wannan badakkare ya zuba masu.
Yousouf kuwa wani irin zabure-zabure ya fara yi ta re sa fizge-fizge jijiyoyin jikinsa sun yi burd'un burd'un yayin da idanuwansa su ka koma kamar garwashin wuta.
Julaibib kuwa ji ya yi gaba d'aya tsoro ya fice a ranshi sai wa ni irin tsana da yaji ya na yi wa Oumul Sahwat na kisan gillar da ta yi wa mahaifiyar Yousouf.
"Ke azzaluma ce wacce ba ta tsoran Allah. Muguwa kuwa in Allah ya yarda k'arshan ki ya zo don sai na yi sanadiyar ajalinki". Fad'in Julaibib cikin fusata har jikinsa ya soma rawa.
Wani irin d'agowa Oumul Sahwat ta yi ta kalli cikin idanuwarsa ya yin da Badakkare ya yi kan shi don sare wuyansa.
Sai da wani tsawa da ta daka masa shi yayi saurin dakatar da shi.
Jikinta na b'ari ta mik'e cikin iska ta re da nufar in da Julaibib d'in ya ke babu kwayar zarra na tsoro a fuska da zuciyarsa.
"Ciro abunda ke wuyarka ka mik'o shi kan tafin hannu yanzu". Fad'in Oumul Sahwat cikin ba da umarni.
Wani k'ask'antaccan kallo ya watsa mata ta re da fad'in,
"Ba ki isa ba, domin ni ba kya mulkata. Wad'annan su za ki yiwa umarni su bi ba Julaibib ba". Ya k'arisa maganar ya na nuna aljanun da ke tsattsaye wajan.
Saurin dafe saitin zuciyarta ta yi saboda jin alamun k'arasowar Sarauniyar Daulatul Bahshan wato Bak'ayatul Mahruri da tawagarta.
Cikin sauri ta juya ta re da nufar in da Yousouf ya ke ta zaro wannan takobi a cikin naman hannunta da ke da tsini da tsawo ta soka shi a gefen cikin Yousouf sai da ya fito ta baya ta re da mik'a tafukan hannunta wanda ya yi dogo gar gaban Julaibib ta re da fad'in d'aura min sarkar nan a nan ko ya bar duniya".
Cikin sauri Yousouf ya d'ago su ka had'a idanuwa da Julaibib ta re da fad'in,
"Idan har cikin zuciyarka ka na k'aunar Rukhsana ina nufin Binty da gaskiya har zuciyarka to ka da ka ba ta abunda mahaifiyata ta ba ka, shi ne lagonta don da shi ba za ta tab'a iya cin galaba a kan ka ba, kuma ko da ta yi maka barazana da wad'anda su ke ta re da kai, ka da ka ji tsoro domin da wannan abun da ke wuyanka babu abunda za ta iya ma su". Fad'in Yousouf daidai lokacin da ta d'aga mashin nan ta so ke shi ta cikin ramin cibiyarshi sai da gudan jini ya fito daga bakinsa.............
🌹 *77-78*🌹
...............B'angaran Anna kuwa bayan sun ko ma gida hankali ta she ta re da tunanin halin da Binty ta ke ciki da kuma inda sauran y'ay'anta su ke.
Fanan kuwa da Anna ke shaida mata duk abubuwan da su ke faruwa, fitsari ta saki a tsaye ba ta re da sanin ta na yi ba saboda firgici da tsoro.
Alhaji Usman kuwa, komawa State CID ya yi don shaidawa DG ko mai za'a yi a yi don ganin y'ay'ansa sun dawo gare sa.
Hakan ne ya sa aka tsanantawa dukkannin su azaba mai gigitarwa da fitar hayyaci akan sai sun fad'i in da su ka kai su Julaibib, musamman Junaina wanda a gidanta su ka b'ace.
An kira Alhaji Saifullahi ta re da kunna masa wannan video na confessing da matarsa da sauran gaba d'aya su ka yi.
Kusan haukace masu ya yi a wajan nan ya na ihu ta re da fad'in duk in da y'ar shi ta ke sai an fito masa da ita.
Da kyar aka kwantar da hankalinsa ta re da shaida masa duk in da su ke za'a gan su.
Cikin hikima DG da alhaji Usman su ka shiga yi wa alhaji Saifullahi nasiha akan irin nu na banbanci akan y'ay'ansa da ya ke yi wanda haka na iya janyo muguwar rikici da tsana tsakanin y'ay'ansa ko da kuwa mahaifiyarsu d'aya.
Sosai nadama ta shigi alhaji Saifullahi domin ya san idan da laifin Junaina to tabbas da laifinsa.
Abu kamar wasa an yi bincike matuk'a amma ba'a ga in da su Julaibib su ke ba, kuma bincike ya nuna ba su fita daga gidan su Junaina. Wanda hakan ya k'arawa Junaina zargi da su kan su hajiya Mansura da Zuwairah tun da da ma su na cikin k'ungiyar asiri.
Tu ni aka tura mota biyar ta re da jagorancin Hajiya Mansura wacce aka ce ta kira meeting d'in gaggawa wanda hakan shi zai ba da umarnin kwamushe duka sauran members d'inta.
Sun yi nasarar kwamushe mata ak'alla za su kai guda Hamsin da uku, don motocin da su ka zo da shi ma bai isa ba sai da aka k'aro wasu duk aka watsa su kamar akuyoyi.
Anna alwala ta yi ita da Fanan ta re da yin sallah raka'a biyu su ka shiga yin addu'a akan Allah ya kare su a duk inda su ke.
*_____________________*
A matuk'ar razane da mugun tashin hankali Julaibib ya yi wani irin tsalle ta re da isa wajan da Yousouf d'in ya ke a d'aure. Ya na tab'a wannan kaca da aka d'aure Yousouf da shi kacan ya zube k'asa, Yousouf d'in kuma ya taho gaba d'aya jikinsa ya na wani tari mai fidda guda-gudan jini.
Tallabosa Julaibib ya yi idanuwansa sun cika da hawaye, jijiyoyin kansa sun yi burd'in-burd'in ya shiga k'ok'arin b'arke rigar jikin Yousouf d'in.
Caraf Yousouf ya rik'e hannunsa ta re da fad'in,
"Ka da ka yi k'ok'arin ceto na, ka d'auki Binty da sauran mutane ku gudu. Abun da ke wuyanka ba zai kare ka daga tsafi da takobin sarauniya Bak'ayatul Mahruri ba. Don Allah Ku gudu ka min ta shigo cikin masarautar nan". Fad'in Yousouf jini na b'ulb'ulowa daga hancinsa da kuma bakinsa.
Mik'ewa ya yi ta re da sab'a Yousouf a kafad'arsa, ka na ya nufi inda su Binty su ke jikinsu na rama, kama hannun Binty ya yi ta re da kallon sauran ya ce ku biyo baya na, kuma ko wanne a cikinku ya rik'a karanta ayatul qursiyu da duk addu'ar da ta zo bakinku. Ka da Ku yadda bakinku ya yi shuru ba ya ambaton Allah".
Gaba d'ayansu a tsorace duk su ka tsaya a bayansa. Ya yin da Oumul Sahwat ta tsaya a gaban Julaibib ta re da fad'in,
"Za ka ja ni ka yi nasara saboda abun da ke wuyanka, amma ka sani ba za ka tab'a iya ja da Bak'ayatul Mahruri ba".
"Allah ya fi ta domin shi ne mahaliccinta". Fad'in Julaibib ta re da yin gaba.
Wani irin ihuu Oumul Sahwat ta yi wanda ya yi sanadiyar mutuwar aljanun dubu biyu. Ta shi sama ta yi ta re da rikita ta koma tsuntsuwa, sai da ta yi nisa a sararin samaniya ka na ta b'ace b'at.
Tafiya kawai su ke yi ba ta re da sanin in da su ka nufa ba cikin daji.
Wani tsoho ne tukuf ya bayyana a gare su jikinsa duk jini idanuwansa na tsiyayar da hawaye.
Nuni ya yi da hannunsa izuwa gangan jikin Yousouf, ta ke Yousouf ya ko ma hannunsa, shimfid'ar da shi ya yi a k'asa ta re da shafa fuskanta.
Bud'e idanuwa Yousouf ya yi cike da azaba ya na kallon kakan na sa kuma ya na murmushi kamar bai jin azaba a jikinsa.
"Ya kai jika na, ka da ka tafi ka bar ni. Kai ka d'ai ka rage a cikin tsatso na. Y'ata ta mutu ta bar wannan duniyar duk a sanadiyar taimakon bil'adama. Ya Allah ka sa haka ya zama silar shigarta Aljanna".
Da gudu Binty ta isa in da Yousouf d'in ya ke a kwance ta na kuka ta re da fad'in,
"Ka da ka mutu ka bar ni masoyi, ka manta alk'awarin da mu kai wa junan mu ne? Mun yi alk'awari za mu ra yu da junanmu duk rintsi. Kalla zoben da ka saka min, kalli wanda na saka maka a hannunka". Fad'in Binty ta re da d'aga d'an yatsarsa wanda zoben ke mak'ale.
Murmushi ya sakar mata mai cin rai ta re da fad'in,
"Mai sona, tabbas ina k'aunarki kuma zan mutu da sonki. Sai dai idan har na kasance da ke Allah ba zai bar ni ba domin na cutar da ke. Wanna na daga cikin wasiyya na k'arshe da mahaifiyata ta bar min akan ka da na bari tsokar da ke k'irjina ta rinjaye ne. Ba zai yu mu rayu ta re ba saboda jinsin mu ba d'aya ba ne. Sai dai ina miki albishir don ki na da wanda ya ke miki k'aunar da na ke miki ko in ce fiye da ni ma". Ya k'arisa maganar ne ta re da kallon fuskan Julaibib ka na ya ce,
"Yaya Bibi ga ta nan ka amana, don Allah ka kula da ita fiye da yadda za ka kula da kan ka dan Allah. Ka ba ta soyayya ka da ta yi kuka domin ka".
Idanuwan Julaibib ya rine kamar gauta sabida tsabar jan da ya yi. Bai iya cewa ko mai ba sai juya baya da ya yi saboda bai son hawayan da ya ke mak'alewa su zuba.
Kuka sosai Binty ta ke yi ta na jijjiga Yousouf ta re da fad'in,
"Kar ka bar ni, Yousouf kar ka bar ni dan Allahhhhh". Ta k'arashe maganar da wani irin narkakken kuka mai narka zuciyar mai sauraro.
Sabrin ita kan ta kuka ta ke yi sosai ta re da jin tausayin Yousouf d'in da ita kan ta Bintyn.
"Su waye iyayena?". Fad'in Binty cikin kuka ta na kallon fuskan Yousouf da shi ma fuskan na ta ya ke kallo.
Kallo fuska kaka Yousouf ya yi shikuma ya jinjina masa kai.
Dawo da kan shi ya yi wajan Binty wanda a ta re su ka yi haka don Julaibib don jin abunda Binty ta tambaya. Shi kan shi ya na son sanin haka.
"Asalin sunan ki Rukhsana wanda haka na gani ajikin showel d'in da aka nannad'e ki da shi, kaka ya tsinci wannan a cikin jikinki". Ya fad'i hakane ta re da yink'uri ya girgiza jikinsa ya fiddo wani k'atotan kwarya wanda a cikinsa akwai kwalliyar d'awisu wanda aka yi sa kamar mafici da kuma wani awarwaro na zinari sai rigan sanyi na yara riga da wando.
"Sauran bayani kaka zai miki shi". Hannunta na rawa ta karb'i wannan kwarya idanuwanta na k'ara kwararar da hawaye.
Sai da ta d'ad'd'aga kayan ka na ta mai da dubanta izuwa ga kaka, kaka ya bud'e baki zai yi magana barrister Fu'ad ya ce,
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!". Da mugun k'arfi ya yin da ya yi wani tsalle domin isa wajan da kaka ya ke ya ture sa, sai dai ka min ya har mashin da Bak'ayatul Mahruri ta jefo ya caki bayansa ya kuma b'ullo ta cikinsa har sai da ya tab'a cinyar Barr Fu'ad da ya isa gaban Kakan.
Gaba d'ayansu mik'ewa su ka yi a razane ta re da ja da baya don ganin dandazon aljanun da su ka zagaye su.
Hamdan rik'e hannun Julaibib ya yi da k'arfi ya na karanta ayatul kursiyyu ya yin da Binty ta sume sakamakon jinin kaka da ya fallatso ya wanke mata fuska.
Barr Fu'ad kuwa k'afafuwansa ke wani irin rawa sakamakon tsoro da kuma azabar da ya ke ji a cinyarsa.
B'akayatul Mahruri ce ta k'araso wajan ta re da yin kwallo da gawar Kaka sai da ya lula can sama ka na ya fado bisa bishiyoyin da ke dajin.
Sai da ta saita takobinta ka na ta d'aga za ta cakawa Binty a zuciyarta, Julaibib ya yi wani irin tsalle don ture Binty takobin ya sa me shi amma sai Barr Fu'ad ya riga sa takobin ya caki k'irjinsa ta ke ya fad'i ko shurawa bai yi ba.
K'arar ballewar wuyarta su ka ji wanda tsabar zuciya Julaibib bai san lokacin da ya yi bismillah ta re da murd'e wuyanta ba. Ta ke ta fad'i k'asa ta na shuru-shuren mutuwa.
Yousouf gaba d'aya sauran jarumtarsa ya yi amfani da shi ta re da mik'ewa ka na ya d'auki takobin bak'ayatul Mahruri ya datse mata kai wanda ya yi sanadiyar rusunawar gaba d'aya dakarunta wa Yousouf d'in.
Cikin azama Oumul Sahwat ta k'ariso wajan ta re da fad'in,
"Lallai dole in mayar da kai matsayin kakan kakanka wato amintaccan bawan masarauta kasancewar jarumi wanda ya kashe azzalumar sarauniyar Daukatul Bahshan. Yanzu aljanun masarautar za su kasance cikin salama da.....".
Bai bari ta k'arisa ba ya yi amfani da takobin hannunsa ya fille mata kai saboda hango yadda ta fille kan mahaifiyarsa.
K'ok'arin fad'uwa ya ke yi Julaibib ya yi saurin taro shi ya fad'o jikinsa.
Magana ya ke son yi amma ya kasa saboda jinin da ke kwararowa daga hancinsa, bakinsa da kuma kunnansa.
K'ok'ari ya ke ta yi ka da ya kulle idanuwansa amma ya kasa.
Jikinsa ne ya yi nauyi sosai har Julaibib ya ji nauyin ya masa yawa sai da ya kwantar da shi a k'asa idanhwansa na tsiyayar da hawaye.
Wani irin guguwa ne