Showing 81001 words to 84000 words out of 162658 words

Chapter 28 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42969

Da ma ya gama tsara komawar shi k'asar shi Nigeria ji bi, saboda wannan abun da ya faru ya b'ata masa rai shiyasa ya ke son barin k'asar.
Ya na zuwa airport ana kiran passenger. Cikin tafiyar shi sauri-sauri kuma cikin natsuwa ya soma tafiya.
Ko da ya shiga jirgi air phone ya saka a kunnan sa ya na saurara karatun Al'qur'ani.
Su na sauka a Dubai, hotel ya nai ma ya kama, ka na ya yi wanka ta re da kwanciya kasancewar bacci ya ke ji sosai. Don gobe ne ya ke son ya sauka a k'asar Nigeria bayan shekaru masu yawa.

*NIGERIA*
"Anna, Ya Bibi ya min text d'azu wai gobe zai diro Nigeria, abunda ya sa ban kira shi ba, na san tun da ya min text bai son magana ne kuma ma a wajan su dare ne". Fad'in Ya Fu'ad.
Wani sanyi Anna ta ji na ratsa zuciyar, don fisabillahi duka y'ay'anta ta na son su, amma Julaibib ne favourite d'in ta duk da ta na danne hakan a gaban sauran y'ay'an amma su kan su sin shan shak'uwar ta daban ce. Don takanas Anna na yankar ticket tun ya na *US* ta je wajan shi har ya koma *CANADA* ta na ziyartar shi ta yi kwana uku ta dawo. Don shi Alhaji Usman bai ci ka samun lokaci ba saboda kasuwancin sa, sun fi yin waya a kai a kai.
"Kira min gaba d'aya ma'aikatan shashin nan right now". Anna ta fad'a farin ciki kwance a fuskan ta.
"Aifa, su shalele za'a dawo. Har na ji tausayin su Binty, don fa Annan su za ta aje su gefe". Fad'in Fu'ad ta re da nufar maid quarters.
Anna kuma wayarta ta d'auka ta kira Binty a waya ta ce su sauko k'asa ita da Fanan.
Ta re su ka sauko, Binty ta kalli Fanan ta re da fad'in,
"Me y'an aiki su ka yi wa Anna yau a kan ta ra su du ka a parlour?".
"Ta re fa mu ka sauko, ma ji idan mu ka k'arasa". Fad'in Fanan.
Ganin fuskan Anna k'umshe da farin ciki ya sa su ka ga ne ba laifi y'an aikin su ka yi ba. Nai man waje su ka yi kusa da Anna su ka zauna. Binty har da kwanciya a jikin Anna.
"Hhuhmmm, yarinya na yau ne kawai, daga gobe idan ma ance ki zo kusa da Anna da k'afarki za ki gudu". Fad'in Barrister Fu'ad.
"Anna kin ji shi ko, ba ni ce autares d'in ki ba. Wai haka ne abunda ya ce?". Fad'in Binty ci ke da shagwab'ar da ya k'ara mata kyau.
"Rabu da shi kin ji, tsokanar ki ya ke yi. Wa ya isa ya hana ki zuwa jikin Annan ki".
Gwalo Binty ta yi Wa barrister Fu'ad, shi kuma ya yi dariya ta re da kwafa.
"Na ta ra ku anan ne domin in shaida muku babban d'a na ya na kan hanyar shi gobe in sha Allah, na san wasun Ku a nan sun san shi, wasun kuma ba su tab'a ganin sa ba. To magana ta gaskiya ya na da wani murd'ad'd'an hali. Sam ba ya san hayaniya da yawan magana a kan shi. Ga wanda bai san shi ba, zai d'auka kyamar mutane ya ke yi ko kuma shi d'in mugune saboda ya na sama da ku, amma ga wanda su ka san shi kuma su ka iya zama da shi, za su ga ne kyawawan halayen shi na wai dan ya na d'ana ba. Sannan ya na da matuk'ar zuciya sosai wanda a wasu lokutan ni kai na da na ke mahaifiyar sa, ba na iya shawo kah cikin sauk'i. So dan Allah ko wacce ta kiyaye ta tsira da aikinta". Fad'in Anna ta na kallon y'an aikin na ta.
Cike da girmamawa su ka ce,
"In sha Allah za mu kiyaye Hajiya".
"Za Ku iya tafiya". Fad'in Anna.
Ga ba d'aya su ka mik'e su ka fice.
"Annah, ya Bibi ne zai dawo? Wayyo Allah dad'i kuma haushi". Fad'in Fanan.
"Mi ye dad'in, kuma mi ye haushin?". Anna ta tambaye ta.
"Anna dad'in na yi shekaru ban ga ya Bibi ba. Haushin kuma zai hana mu sak'at a ciki n gidan nan.
"Ai abun ba wuya, sai Ku kiyaye shi". Fad'in Anna.
Ita kuwa Binty hankalinta ma ya bar wajansu ya koma kan screen d'in wayarta ta na karanta daddad'an text d'in da Yousouf ya turo mata. Don kafin ya kira ta ya na jimawa, sai dai fa kullum sai ya mata dad'ad'an texts, na safe da ban, na rana da ban na dare da ban. Ku ma ba ta tab'a yin k'urin yi masa replay ba sai yau kawai ta ji ta na son ta yi masa. Sau uku ta na rubutawa ta goge, a na hud'un ne kuma ta daure ta tura.

Yaya Fu'ad da ke kallon ta ba ta re da sanin abunda ta ke yi a cikin wayar ba, ya na jin son ta na k'ara huda ko wani sashe na jikinsa.
"Fanan ki d'auko key d'in part d'in ya Bibi Ku je ke da Binty ku gyara masa tsaf, kin san bai san y'an aiki na shigar masa d'aki. Maza ku ta shi yanzu". Fad'in Anna.
Ta shi Fanan ta yi ta re da kallon Binty da ke kallon sak'on da Yousouf ya sake turo mata yanzu sakamakon replay d'in da ta masa.
Fizge wayar Fanan ta yi ta re da yin sama da gudu, sai a lokacin Binty ta dawo cikin natsuwarta ta re da bin bayan Fanan d'in da gudu ita ma.
Har kan gado Binty ta ni ta ta re da fizge wayar ta maka mata harara, ka na ta cigaba da karantawa message d'in Yousouf d'in ta re da kwanciya a kan gado har da wani lumshe idanu.
"Idan za ki ta shi ma gwara ki ta shi muje mu gyara d'akin ya Bibi". Fad'in Fanan.
"Ki je ki yi ke d'aya, ni love na ke yi. Aikin ne ba za ki iya yi ke d'aya sai na ta ya ki?". Fad'in Binty.
"To ba ri na je na fad'a wacce ta ce mu yi ni da ke, idan ya so sai ki ke da kan ki ki fad'a mata ke ba za ki yi ba". Fad'in Fanan ta re da sauka daga kan gadon.
Rik'o hannunta Binty ta yi ta re da fad'in,
"Ke fa muguwa ce, to na aje wayar muje. Kill joy kawai saboda ta ga ba ta da mai tura mata hot messages". Fad'in Binty.
Tab'e baki Fanan ta yi ta re da fad'in,
"Ni ma nawa Prince d'in ya na kan hanya".
Fitowa su ka yi su ka nufi side d'in ya Bibi da ya kusan sumar da Binty saboda tsaruwarsa, da ta d'auka ba za'a samu d'akin da ya fi na Daddy kyau ba, sai ga na Julaibib ya ninninka na daddyn.
Mai makon su tsaya su gyara d'akin da kyau, sai su ka b'ige da masa bincike a d'akin su na kallon old picture d'in sa. Hoton sa Binty ta ga ni lokacin da ya kammala degree d'in sa na farko hannunsa rik'e da award.
"Kaiii ku kyawawa ne Fanan, yayan ki kyakkyawa ne sosai".
"Ya su ke da Yousouf d'in ki?". Fad'in Fanan.
Saurin ajiye hoton Binty ta yi, ka na ta kalli Fanan d'in ta re da fad'in,
"Ko kusa ba bu had'i, wallahi Yousouf d'i na ya fi shi kyau".
"Beauty is in the eyes of the beholder". Fad'in Fanan ta re da soma kakkab'e gadon.
Haka su ka yi aikin ba cikin natsuwa ba, don su na yi sai su aje su ko ma kallon wani abun. Daga k'arshe ma haka su ka gama su ka manta ba su wanke bayi ba.

Haka su ka yi aikin ba cikin natsuwa ba, don su na yi sai su aje su ko ma kallon wani abun. Daga k'arshe ma haka su ka gama su ka manta ba su wanke bayi ba......

..............."Haba besty na, idan ki ka guje ni ina za ni. Dan Allah ki yi hak'uri mu shirya beauty". Fad'in Hamdan tsugunne a gaban Sabrin da ta had'a k'afa d'aya a kan d'aya ta na shan ice-cream ko kallon shi ba ta yi ba.
"Dan Allah ki min magana Love, idan ki ka yi fushi da ni zan fad'a wancan sweeming pool d'in can in mutu". Fad'in Hamdan..
"Really? Mu je wajan to mu ga ni". Fad'in Sabrin ta re da hararar sa ta re da mik'ewa ta yi wajan pool d'in.
Bin ta ya yi a baya ta re da cigaba da magiya. Sai da ta tabbar ya zo kusa da pool d'in ka na ta daddage ta tura shi ciki ta na masa dariya da gwalo ka na ta ce,
"Beautyn ta ka ta zo ta cece ka. Ta yi tsuntsuwa daga kan bola ta zo ta ciro ka".
"Haba ai Ke ce beauty na. A kwai wacce ta kai best friend d'ina kyau kuwa, ina tunanin fa ko Beauty a wajan ki aka sammata".
"Hmm, sweet mouth. I hate you". Fad'in Sabrin da k'arfi.
"And I love you besty". Fad'in Hamdan da k'arfi.
Ko juyawa ba ta yi na ta so ma tafiya.
Da sauri-sauri ya fito ruwa na d'iga a jikins ya nufi wajanta da har ta bud'e mota. Shi ma bud'e gaba ya yi ta re da shiga.
Kallon shi ta yi ta re da yamutsa fuska ta ce,
"Disgusting, please out".
Ruwan goran da ke gyefan shi ya bud'e ya watsa mata a jiki ya na dariya.
Ihu ta yi ta re da soma kukan shagwab'a ta na fad'in,
"I hate you, I hate you, I hate youuuuuuuuuu".
Fitowa ya yi daga motar ya jawo ta daga driver seat ya mai da ita in da ya tashi ta re da rufe mata k'ofa ka na ya ko ma driver seat d'in ya ja motar su ka bar park d'in.

*PAID BOOK 08128755583*
🌹 *45-46*🌹

*Bonus*✋🏻😂 ( *BARKA DA SABUWAR SHEK'ARA. YA UBANGIJI HALITTA, SA DA MU DA ALKHAIRI WANNAN SABUWAR SHEKARA DA MUKA SHIGA, SA'ANNAN KA KORE MANA FITINTINU DA BALA'IN DA KE CIKIN TA ALFARMAR FIYAYYAN HALITTA (AMEEN)*)

............."Besty dan Allah ki dai na saurin fushi haka, ki ga ne ke d'in ta daban ce. Amma fa ita ma Binty..."
"Enough! Za ka saka in bud'e motar nan in fita idan har ka cigaba da kururta y'ar bolan ka a gaba na. Ka ba ri idan za ka fad'i kyawunta sai ba na wajan dan zan shak'e ka ka mutu in kuma canza besty". Fad'in Sabrin.
"Da kad'an Binty na ta fiki kyau". Fad'in Hamdan ta re da yi mata gwalo.
Shak'e shi ta yi ta ta re da fad'in,
"Sai na kashe ka, sai na kashe ka, mai kan goruba kawai".
Dariya ya shiga yi ta re da k'ok'arin kwace wuyar rigarsa da ta rik'e. Saura kad'an su yi karo da wata mota ya yi saurin juya steary ta re da ta ka burki.
"Kin ga abunda ki ke so jawo mana ko?". Fad'in Hamdan ta re da dungure mata kai.
"Drive jo! Sanyi na ke ji in yi ina son canza kaya". Fad'in Binty ta re da ja masa hancinsa.
"Sannu ni kuma in ce me da kika tura ni cikin pool. Du be ni gaba d'aya na a jike na ke har d'iga na ke yi". Hamdan ya fad'a ta re da kunna motar ya soma tafiya a hankali.
"Ai kai ka ja, idan za ka rik'a maganar beauty a gaba na zan to she ka yasin-yasin yaro". Fad'in Sabrin.
"Ke wanene yaron? Na fasa miki baki".
Turo bakin ta yi ta re da fad'in,
"In ka fasa".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login