Showing 108001 words to 111000 words out of 162658 words

Chapter 37 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42935

buk'atarta. Ai saura kwana hud'u su dawo". Fad'in Anna.
"Ni babu abunda me b'atan rai kamar rashin network a garin. Ba dama ka kira ka ji wani hali su ke ciki". Fu'ad ya sake fad'i.
Tsaki Julaibib ya ja ta re da d'aukar key d'in motar shi, dama abinci ya gama ci ta re da kallon Anna ya ce,
"Sai na dawo Anna". Ya na gama fad'in haka ya fice daga parlourn.
"Anna dan Allah ki bari na je na d'auko su".
"Kai ta shi ka ban waje tun da ba ka da hankali". Anna ta fad'a ta re da hararar shi.
"Na yi shuru to". Fu'ad ya fad'a ta re da gyara kwanciya a kan three sitter.


..............Yaune su ka cika kwana hud'u a Saminaka, kuma yau ne su ke shirin komawa Abuja. Kwana hud'un nan kawai Binty da yi bala'in ramewa saboda tunanin abunda Kandala ta fad'a mata.
Mak'ota sai kawo tsaraba su ke su na basu dangin su kalwa, kub'ewa, kuka, barkono, da shambo har da su goruba da taura. Sai da su ka cika babban bako na kayan tsaraba.
Goggo Shatu kuwa har da matsar kwalla ta re da musu alk'awarin in sha Allah za ta zo.
Shatar mota Kandala ta yi masu har garin Abuja.
Kasancewar fitar sassafe su ka yi, k'arfe hud'u a Abuja ta musu, kuma da ya ke mota ce golf mai kyau kuma driver ya san hannunsa.
Gaban Binty fad'uwa ya ke yi sosai duk san da ta tino da maganar Kandala.
A k'ofar tank'ameman gate d'in ya yi parking su ka fito. Kandala ta biya shi kud'in sa lokacin tuni har Fanan ta isa gate ta re da kwankwasa gate.
"Who be that". Fad'in Oga Solomon.
"It's me, open the gate". Fad'in Fanan a gajiye saboda zaman motar da su ka yi".
Bud'e gate d'in ya yi ta re da washe hak'ora.
"Welcome back madam". Fad'in Oga Soloman.
"Welcome". Fanan ta fad'a a gajarce ta re da shiga ciki Binty na biye da ita a baya.
"Ah'ahhh beauty, beauty. Welcome home". Solomon ya fad'a ya na washe ba ki.
Murmushi kawai Binty ta masa ta re da wuce sa.
Kandala kuwa sai k'ik'i k'ik'i ta ke da k'atuwar bakon hannunta.
Tab'e baki ya yi ka na ya juya ya kalli Baban Haruna ta re fad'in
"Helf that human carry her load".
Tasowa Baban Haruna ya yi ta re da d'aukar jakar ya d'aura a ka ita kuma ta shige ta na hararar Solomon.
Kasancewar akwai nisa tsakanin first gate da ainahin cika gida, Binty da Fanan kamar za su fad'i don gajiya.
Barrister Fu'ad ne ya fito daga part d'in sa sanye da kaftan kasancewar yau juma'a ce kuma bai je aiki ba, yanzu ne ya ke son ya fitan. Idanuwansa ne ya sauka a kan Binty da ke tafiya da kyar kamar an tilasta mata tafiyar.
"Bintyyyyyyyyyyy!". Barrister Fu'ad ya fad'a da k'arfi kuma cike da jin dad'i.
Cikin sassarfa ya nufi wajansu ya na washe bakin jin dad'in dawowar ta su.
Ita kuwa Binty sai ta k'ara shagwab'ewa ita alan dole ta gaji.
"Wannan wani irin surprise ne mai dad'i haka? Gaskiya na ji dad'in dawowar ku. Dubi tantabarun gidan nan, su kan su dad'in dawowar ku su ke ji gasu nan sai oyoyo su ke maku". Fad'in Barr Fu'ad ya na nu na tantabarun da gaba d'ayan su su ka sauko k'asa gwanin sha'awa.
"Yaya we miss you irin lodi-lodi d'in nan". Fad'in Binty.
Fanan kuwa d'aura kanta ta yi a kafad'ar shi ta na fad'in,
"Yaya garin akwai nisa, we're very tired".
"Ai ni ma na fasa fita, muje ciki". Fad'in Barr Fu'ad ta re da rik'o hannunsu.
Kandala kallon bayansu ta yi ta re da tab'e baki ta na harararsu.
Ba bu kowa a parlour gaba d'ayansu sama su ka yi su na kwad'a kiran sunan Anna.
Anna da ke zaune a parlour ta na tunanin autares d'inta ta jiyo muryansu. Cikin sauri ta mik'e ta re sa nufar k'ofar parlourn.
Kicib'is su ka yi da juna, aikuwa gaba d'aya suka daka tsalle su ka d'are jikinta.
Rungume su ta yi ita tana jin dad'in ganinsu.
"Ya aka yi ku ka dawo yau? Ai na d'auka sai kun yi sati ka min ku dawo". Fad'in Anna.
"Anna kewarku ce ta hana mu sukuni wallahi". Fad'in Binty.
"To ku dawa ku ka dawo?" Fad'in Anna.
"Mu da Baaba Kandala, ta na parlourn k'asa". Fanan ta fad'a.
"To maza aje ayi wanka ayi sallah azo aci abinci". Fad'in Anna ita kuwa ta sauka zuwa wajan Kandala.
Barr Fu'ad ku ma wani tsallan murna ya yi na jin dad'in dawowar sahibar shi.
Su Binty kuwa bayan sun yi wanka sun yi sallah, ko bi ta kan abinci ba su yi ba su ka bi lafiyar gado don yin baccin gajiya.
Ko da Anna ta sallami Kandala wacce ta yi da ita a kan ta kwana gobe ta juya amma ta yi ta kawo mata excuses akan akwai buk'atar komawarta yau.
D'akin su Bintyn ta shiga ta tadda su su na ta sharar barcin gajiya. Ta da su ta yi ta re da fad'in,
"Ku ta shi daga wannan barcin haka, haramun ne bacci bayan la'asar".
Haka nan ba don sun so ba su ka tashi. Abincin ma zai ciwu musu ba sai after isha'i lokacin cin abincin dare Wanda su ne na k'arshan zuwa kan dinning d'in.
Kallo d'aya yaya Bibi ya yi masu ta re da d'auke kan sa ya na mamakin yaushe su ka dawo amma ya basar don bai son raini.
"Yaya Bibi ina yini?". Su ka had'a baki wajan fad'i.
"Lafiya". Ya fad'a a tak'aice ta re da cigaba da cin abincinsa.
As usual shi ya riga su ta shi ta re da goge bakinsa da tissue ya fita.
Kai tsaye d'akin Suhail ya nufa. Key ya saka ya bud'e ta re da shiga ka na ya mai da k'ofar ya rufe.
Har k'uryan d'akin ya shiga inda Suhail ya ke a k'ulle da kaca a k'afarsa har hannu.
Key ya saka ya bud'e kwad'on ta re da kwance masa hannun ya kuma yage seletep d'in da ke bakinsa ka na ya ce,
"Ka shirya yin magana ko mu cigaba a haka?". Fad'in Julaibib.
Tsabar taurin kai irin na Suhail ya k'i magana.
"So be it". Fad'in Julaibib ta re da fiddo burger a cikin aljihunsa ya mik'a masa. Cikin sauri ya karb'a ya cinye ya na hawaye.
Mai da kwado ya yi ta re saka masa seletep d'in a baki ka na ya juya zai fita.
Ni shi sosai Suhail ya soma yi alamar ya na son yin magana ta re da girgiza kansa.
Dawowa baya Julaibib ya yi ta re da yage seletep d'in bakinsa ya ya na kallon shi.
"Dan Allah ka yi hak'uri yaya Bibi, wallahi zan yi magana, zan fad'a". Fad'in Suhail.
Duk'awa ya yi a gaban Suhail d'in ta re kallonsa alamar ina jinka.
"Kusan kaf yaran da ake kawo wa daga k'auyan don su yi aiki a gidan nan, sai na yi amfani da su duk k'ank'antarsu. Akwai wata ma da har ta baya na ke amfani da ita, yarinyar da ke wajan Anna ma sau biyu ina yunk'urin keta mata haddi amma Allah bai ba ni nasara ba"...
"What?". Julaibib ya fad'a a matuk'ar k'ausashe ta re da d'auke shi da wani magigicin mari sai da jini ya fito daga ramukan hancinsa. Ta ke ku ma ya ji d'au sautin sa ya dod'e na wucin gadi.
"Fad'a min, ka yi mata wani abu ko baka yi ba? Na ce fad'a min ko in kashe ka a d'akin nan". Julaibib ya fad'a ya na haurin ko ina ya samu a jikinsa, har a gabansa da ke a kumbure saboda dukan da ya masa wancan lokacin.
"Wallahi wallahi wallahi ban mata komai ba, na farko Fu'ad ya kawo mata d'auki, na biyi kum.....".
Wani naushi da ya kai masa a ciki ne ya saka ya yi saurin shanye maganar da zai yi saboda azabar da yaji.
Da gudu Alhaji Usman da ke kallon duk abunda ke faruwa daga d'akinsa na side d'in haijya Mansura, kasancewa a kowa ni part ya na da computer da ku ma CCTV a wajan, ya fito da gudu ya hajiya Mansura ma ta biyo bayansa kasancewar ta ga fitowarsa.
D'akin Fu'ad d'in su ka nufo hajiya Mansura na biye da shi a baya, hankali ta she kasancewar d'akin tilon d'anta namiji wanda ta kuma kwallafa rai a Kansa.
Shigansu d'akin ya yi dai-dai da lokacin da Julaibib ya saka k'afa ya take gaban Suhail d'in. A take kuwa ya numfashinsa ya tsaya cak, idanuwansa su ka kakkafe.

















Please manage za mu had'e gobe.















🌹 *59-60*🌹
............."Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Julaibib mai yasa ba ka amfani da hankali idan za ka yi hukunci ne? Yan zu idan ya mutu fa? Ka san jagulewa zai yi ya dawo kan ka ko. Ka rik'a abu da natsuwa mana". Fad'in Alhaji Usman rai b'ace ta re da nufar in da Suhail d'in ya ke a kwance ba ya numfashi.
Kuka Hajiya Mansura ke yi kamar za ta shid'e na ganin halin da tilon d'anta namiji ya ke ciki.
"Ya mutu ko Alhaji? Wani irin mugunta da azaba ne haka? Ai ko kisan kai ya yi sai haka. Dubi irin yadda aka k'ulle shi da kaca sai kace k'asurgumin b'arawo". Hajiya Mansura ta fad'i ta na sharar hawaye.
"Umarni na ke ba ka a matsayina na mahaifinka idan har na isa kuma ina da wannan matsayin. Ka duba d'an uwanka ka na shi taimakon gaggawa yanzu haka".
Tsabar zuciya Julaibib ya shiga taune harshansa jikinsa na wani irin rawa kamar yana k'asar Moscow ba suwaita a jikinsa.
"Ba ka ji abunda na ce ba ne Salis?". Alhaji Usman ya fad'a a tsawace ya na kallon cikin idanuwan Julaibib da su ka rine kamar gauta kuma still ya na taune harshansa.
A hankali ya ta tawo har inda Suhail d'in ya ke a kwance ya duk'a ta re da d'aura d'an yatsansa biyu a wuyansa da kuma k'ofofin hancinsa. Ka na ya mik'e ya isa in da goron ruwa a kan center table ya bud'e ta re da tsiyayar ruwan ya dawo wajan Suhail d'in ta re da shafa masa ruwan cike da mugunta.
A matuk'ar razane ya farfad'o ta re da wawwaro idanuwa ya na fad'in,
"Na tuba, wallahi ba zan sakewa ko wacce yarinya fyad'e ba. Wallahi ita ma ban mata komai ba". Fad'in Suhail.
"Wani magana ya ke yi haka? Wa ya yiwa fyad'en a cikin gidan nan?". Fad'in Hajiya Mansura a birkice.
"Fito da mota mu kai shi asibiti, ba ka ganin yadda gaban shi ya kumbura". Fad'in Alhaji Usman ta re da k'ok'arin warware sark'an da ke jikinsa.
Mik'a masa key d'in da ya kulle kacan Julaibib ya yi ta re da ficewa daga d'akin ya nufi side d'in Anna rai b'ace.
Ganinsa kawai su ka yi a kansa. Ba su kad'ai ba hatta Anna sai da ta tsorata da yanayin sa. Barr Fu'ad kuwa wani k'undunbala ya yi kasancewar ya na kan kujera ne ya na facing su Binty da har yanzu su ke kan dinning duk da sun gama cin abinci su na baiwa Anna da Ya Fu'ad d'in labarin k'auye.
Kau kau kau! Julaibib ya tsinke fuskan Binty da mari hagu da ya sa ta ji tsigar jikinta ya tashi ta re da jin wani shocking na bin jikinta saboda azabar marin da ya sauka akan kuncinta.
"Ubbbban... Me yya kkai ki d'd'aakin Suhhaiil har ya nai mi rrraping d'inki?". Fad'in Julaibib cike da in'ina.
Daga Anna har barrister waro idanuwa su ka yi ta re da fad'in,
"Raping kuma?".
Binty kuwa hanyar nai man wajan b'uya ta ke yi amma ba hanya don ya yi fankan-fankan a kan hanya. Jikinta sai b'ari ya ke yi ta ma kasa kuka sai fiki-fiki ta ke yi da idanuwa.
Hannu ya k'ara d'agawa zai wanketa da mari ta saki wani gigitaccan k'ara don ta tabbatar wannan karan idan har ya samu fuskanta to babu shakka sai ta kurmance.
Caraf Anna ta rik'e hannun ta re da tura shi gefe amma ko motsi bai yi ba, sai taunan harce ya ke yi da har ya soma jini.
"Kar ka sake tab'a ta Julaibib. Wallahi ka sake tab'a y'ar nan sai ranka ya mummunar b'aci. Sakarai kawai wanda wanda bai iya controling fushin sa ba". Fad'in Anna, amma can k'asan zuciyarta dad'i ta ke ji saboda wani abu da ta hango a fuskan d'an na ta.
Huci ya ke yi kamar za ki, can kuma ya juya ta re da ficewa daga d'akin kamar zai fashe. Hanyar gate ya nufa.
Fitar shi ko minti d'aya bai yi ba, Alhaji Usman ya shigo ta re da fad'in,
"Maza Fu'ad fito mu kai d'an Uwanka asibiti bai da lafiya, d'an uwanka ya masa mummunan illa". Fad'in Alhaji Usman.
Saurin bin bayansa Fu'ad ya yi, Anna ma ta bi bayansu hankali ta she.
Numfashin Suhail sai sama da k'asa ya ke yi kamar zai tafi gaba d'aya. Ya yin da Hajiya Mansura ke tsugunne ta tallabe da kansa ta na kuka sosai.
Ita kan ta Anna ganin yadda gaban Suhail ya wani irin kumbura sai da ta na da baya ta dafe k'irji ta na salati da sallallami.
Ciccib'arsa Fu'ad ya yi har wajan mota, Alhaji Usman ya shiga gidan gaba, Anna da Hajiya Mansura su ma su ka shiga. Kan Suhail na kan cinyar Anna sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login