Showing 162001 words to 162658 words out of 162658 words

Chapter 55 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42931

d'ayan su su na da shigan k'aramin ciki.
Na Binty ya fi nunawa kasancewar laulayi ta ke yi mai zafi don jinin Julaibib na da k'arfi don O'negative ne. Genotype d'in sa kuma AA. O'negative sai ka tara mutane d'ari da kyar ka samu d'aya mai irin jinin.



AFTER 10TH MONTH
Sabrin ce ta fara haihuwa, ta haifi d'anta namiji Aahil, bayan kwana uku Rauhiyy ta haifi y'an biyu mace da namiji, su ka ci suna Aayad da Airah, tsakaninsu da Binty kwana d'aya ta haifo mace mai kama da ita sak ta ci sunan Anna Na'ima, su na kiranta da little Anna, Amrah ce k'arshan haihuwa ta haifi mace ita ma ta cire sunan mommah Rahima suna kiranta da khairat.
Lokacin an saka bikin Hanan da Hamdan wata takwas masu zuwa don har ya gama service kuma mai martaba sarkin Gombe da kan shi ya karb'i takardunsa ya nai ma masa aiki.
Soyayyar ruwa-ruwa ya ke gudana tsakanin Julaibibda da Binty, ba sa fushi mai tsayi da junansu. Sun shimfid'a rayuwarsu cikin fahintar juna, idan d'aya ya yi fushi, d'aya zai sauko ya taushi d'aya.

Ranar bikin Hamdan kuwa sun yi rawa sun cashe ka na su ka mik'a amarya Hanan gidan mijita wanda su ka b'oye su ka yi kuka sosai na rashin mahaifiyarsu akusa ta na can prison ta lalace don duk wata sai sun je ganinta.


Hajiya Kandala an yi shekara uku an fito daga gidan yari ta kod'e ta jeme. Kai tsaye Datu ta fara naima wacce gaba d'aya kud'inta na hannunta da ta k'arba da sunan juya mata kud'in.
Sai dai ta yi katari da abunda ya kusan tsayar da numfashinta domin kuwa Datu ta yi aure ta da d'an damfara ya damfareta ya kwashe komai ya gudu zuwa Dubai.
Kai tsaye Saminaka ta nufa, in da aka yi mata koran kare domin bayan tafiyanta matar Buba mai kwarankwatsi ta tona asirin komai wa Goggo Shatu.


Wannan tsoho kuma da su ka dawo duniyar aljanu da su Binty ba kowa ba ne fa ce alhaji mai tumbi da mahaifiyar Yousouf ta tafi duniyar aljanuda shi wanda tashin hankali ya sa ka ya yi loosing memory don iyalansa ma sun dad'e da gama Rabin gadon shi ta re sake sure don sun d'auka ya mutu, kuma bayan barin gida na tsawon lokaci su ka Shiga d'akin sirrinsa da bai bari a shiga su ka ga ne ya fad'a k'ungiyar asiri ne.







*TAMMATA BIHAMDULLAHI*

_NAN NA KAWO K'ARSHAN WANNAN LITTAFI WANDA BA HAKA NA SO TAFIYAR TA TSAYA NA, WALLAHI UZURI NE GARE NI BABBA DA FATAN ZA KU MIN AFUWA._
_KUSKURAN DA NA AIKATA YAYIN RUBUTA WANNAN LABARI ALLAH KA YA MIN, ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMAR IN ROK'I YAFIYAR KU WAD'AND'A NA B'ATAWA RAI, NI NA YAFE MAKU HAR CIKIN ZUCIYATA, ZAN TAFI OFFLINE WANDA BAN SAN RANAR DAWOWA TA BA, DAN ALLAH KU YAFE MIN WATAKIL WANNAN SHI NE BOOK D'INA NA K'ARSHE. ALLAH SHI YA SAN GAIBU._


_NAGODE NAGODE NAGODE DON KUN NU NA MIN AMANA, DON BA KU FITAR MIN DA BOOK BA, HAKAN YA TABBAR MIN DA KU D'IN YAN HALAS NE WANDA KU KASAN AMANA DA KUMA HUKUNCIN WANDA YACI AMANA. ALLAH YA K'ARA BA KU IKON RIK'E AMANA YA SA HAKAN SHI ZAI SAMO SILAR SHIGAR KU ALJANNA_

😭😭😭🤧🤧

_SAI MUN SA KE HAD'UWA IDAN DA RABON HAKA_






*MATAR SAYYADEE*🥰

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login