Showing 57001 words to 60000 words out of 162658 words
isa ta re da shafa man shafawar sa ya kuma feshe jikinsa da turare don shi ma'aboci turare ne. Ya na matuk'ar k'aunar k'amshi a rayuwarsa.
Wannan karan ma jeans ya saka ta re da t-shirts vneck. Ta je kan sa ya sake yi ka na ya sauko zuwa parlour. Kitchen ya shiga kasancewar kitchen d'in na a parlour ne. Tea ya had'a ta re da d'auko biscuit ya na had'awa da shi ya na sha kasancewar shi mara son cin abinci sosai idan ba na k'asar sa ba.
Sai bayan ya gama ne ya fito daga gidan, kai tsaye *Mount sinai Hospital* ya nufa.
Tun daga parking motar da ya yi a harabar asibitin mutane su ka zagaye motar kamar za su tsuguna masa.
Ko da ya fito daga cikin mutar, manyan likitocin asibitin nan da kan su su ka fito suka taro shi su na gaisawa da shi kasancewar babba kuma kwararra doctor a fanni daban-daban.
Domin dai degree biyar ga re shi, ya na kan na shidda yanzu.
Farkon degree d'in sa shine ya karan ci fannin Gynaecology and obstetrics (Fannin cutukan mata da haihuwa), na biyu kuma ya karanci Paediatric (Fannin rashin lafiyar k'ananan yara), na uku kuma Oncology (Fannin ciwon sank'ara (Cancer)), na hud'u kuma, Nephrology (Fannin k'oda), na biyar Cardiology (Fannin Zuciya), Sai na shidda wanda ye kan karanta yanzu wato Orthopaedic (Fannin k'ashi).
Sosai ya ke da kwarewa a wajajan nan. Booking ake yi idan za'a gan shi. Har da ga k'ashashe da dama ake zuwa ganin sa. Wanda Sai mutum ya na da sa'a ya ke samun hakan.
Kai tsaye wani had'ad'd'an office ya nu fa ta re da sauya kayan jikinsa izuwa na tiyata saboda tiyatar da zai wa wata a zuciyarta.
Fitowa ya yi daga cikin office d'in na shi ya yi theater room d'in, wasu daga cikin doctors su uku suka rufa masa baya da nurses hudu.
Kayan aikin su ma kawai abum kallo ne. Hatta aikin da akai wa wannan mata ba tsagata aka yi ba, ko mai da machine aka yi mata. And the operation was successful.
Cikin da godiyar ubangiji ya fito daga theater room d'in doctors su na congratulating d'in sa. Murmushi kawai ya ke ma su, don shi bai cika dariya ba.
Bayan ya fito ya canza kayan sa, kai tsaye masallaci ya nufa ta re sa sa ke alwala kasancewar a cikin theatre d'in nan sallar magriba ta sa me shi, kuma abunda ya fi tsana a rayuwar sa shine sallah ta wuce sa.
*NIGERIA*
Hmm abun zai ba ku mamaki idan na fad'a maku cewar Binty yanzu ta kware a yaran fulatanci. Turanci kuwa ko wani d'an da ya je makaranta ba zai nu na mata turanci ba. Ba laifi ta na yi kuma ta na mayarwa.
Gyefe guda kuma Malam Suhail ya fita sha'anin Binty, amma ba gaba d'aya ba. Don cewa ya yi kura na yawo, zabo na yawo, wata rana za'a had'u.
Hajiya Mansura kuwa sai k'ara haukacewa ta ke yi, don yanzu ji ta ke yi ko ido hud'u ne kawai su yi da Binty ko ta samu ta ji sauk'i cikiin zuciyar ta. Tu ni ta tsiri zuwa shashin Anna duk da kasancewar da zan ba zuwa ta ke yi ba. Kuma Anna na karb'ata hannu biyu duk da a k'asan zuciyarta ta na mamakin yawan zuwa shashin na ta da ta ke yi. Sai dai duk zuwan ta, Allah bai tab'a sawa ta ga Binty ba. Haka za ta k'ariki zamanta ta tashi ta fita. Kuma ba ta so ta tambayi ina Bintyn ta ke ka da ta yi suspecting wani abu.
Yanzu haka su Fanan sun na hutun third term ne. Sai farin ciki ta ke yi ta re za su koma makaranta sa Binty. Ta k'osa wannan ranar ta yi. Da ma tuni Ya Fu'ad ya je har makarantar ya ga ma wa Bintyn komai. Za'a saka ta primary 3 kasancewar ya yi wa principal d'in ba ya nin komai kuma yq shaida masa Bintyn ta na da saurin fahimta kuma sun d'aukar mata lesson teacher. Hatta uniform sun ba ta da kaf writing materials. Sai dai ya Fu'ad d'in bai shaida mata ba saboda surprise ya ke son ba ta.
Kwanci tashi ba bu wuya wajan Allah. Nan da kwana uku dai Binty za ta so ma zuwa *LEAD BRITISH* a matsayin d'aliba.
Ana gobe za su je makaranta, ya Fu'ad ya kwashe su ya yi masu shopping mai uban yawa har da su school bags da kuma takalman makaranta ba d'aya ba ba biyu ba.
Tsabar murna, tun saura sati d'aya Binty ta fara zuwa makaranta, ta dai na ishashshan barci. Har mafarki ta ke yo ga ta a cikin school d'in.
Daran ranar kuwa ba ta yi baccin kirki ba. Asubar fari ta tashi, ko da Anna ta zo tashin su, idanun Binty biyu ta ga ta. Dariya ta yo cikin harshan fillanci ta ce,
"Wato Binty ba ki yi bacci ba saboda zumud'i ko? To ai sai ku ta shi ku yi wanka ta re da d'auro alwala".
Binty ce ta fara saukowa daga kan gadon, ka na ta tada Fanan da ke bacci.
Wanka ta soma yi ka na ta d'auro alwala. Doguwar riga ta saka ta re da hijjab ta tada sallah kasancewar ta iya sallah sosai yanzu.
Bayan ta idar ta isa gaban madubi ta d'auko man shafawa ta soma shafawa a jikinta, dai-dai lokacin Fanan ita ma ta fito daga bayi.
"Heeey! Kar ki wa fuskan ki komai. Ki ba ri in idar da sallah da kai na zan gyara miki fuska. Ai yau kwalliyar ki ta musamman ce". Fad'in Fanan ta re da kabbara sallah.
Binty jiran ta ta yi har ta idar da sallah ka na ta zo ta yi mata kwalliya. Ba wani kwalliya ta mata ba, powder kawai ta shafa mata ta re da lipstick. Sai ta gyara mata gashin kan ta ta yi mata parking a tsakiyar kai ta kuma nannad'o gashin ta yi ma ta donut da shi.
Anna ce ta shigo hannunta rik'e da uniform d'in Bintyn a hannunta.
"Laa! Anna da ma an bata uniform?". Fad'in Fanan.
"Eh, Barrister ne ya je ya karb'o mata a makaranta har da ID d'in ta ga shi nan". Fad'in Anna ta re da aje kayan a kan gado.
D'aga kayan Fanan ta yi ta re da nuna wa Binty tana dariya.
Skirt d'in ta mik'a mata ta saka, ka na ta ba ta shirt d'in ciki mai dogon hannu ta saka ta re da d'aura mata coat d'in ta kuma b'alle mata mab'allin rigar. Ba k'aramin kyau ka yan suka yi wa jikinta ba. Kamar dan ita aka yi su. Hular ta saka mata ta re da baby hijjab d'in.
"Binty na kin gan ki kuwa? Kin yi kyau sosai". Fad'in Anna.
Dariya Binty ta yi ta na jujjuyawa ta re da kallon kan ta cikin madubi dad'i ya gama kashe ta yau za ta makaranta.
"Ga socks d'in ki nan ki saka ku fito ku karya ka da ku yi latti". Fad'in Anna ta re da fita daga d'akin.
Safar ta saka, ka na ta saka dark purple shoe kalar kayan mai matuk'ar kyau.
Cikin sauri Fanan ma ta shirya su ka fita parlour. A dinning su ka tara's da Daddy da Anna su ma su na karyawa. K'arasawa su ka yi su ma ta re da jan kujera su ka zauna. Gaba d'ayan su su ka gaida daddy da Anna. Ka na su ka had'a tea.
Daddy ya kalli Fanan da Binty ta re da fad'in
"My twins, dan Allah idan an je makaranta, a natsu a yi abunda ya da ce. Ban da fad'a da students. Sannan ke kuma Fanan ki kula da Binty sosai ta re da k'ara ko ya mata abubuwan da ba ta iya ba tun da ke kin san kan makarantar".
"In sha Allah daddy". Fad'in Fanan.
"Allah ya ma ku albarka". Fad'in Daddy.
"Ameen". Su ka amsa gaba d'ayan su.
Ta shi su ka yi kowacce ta d'auki jakar makarantar ta su ka sauko k'asa ta re da fita daga d'akin.
As usual driver na nan a nesa da part d'in kad'an ya na jiran isowar su.
Ya Fu'ad ne ya fito cikin shigar suit bak'ak'e ya nufo inda su ke. A tare su ka had'a ba ki wajan fad'in,
"Ina kwana ya barrister?".
"Lafiya k'alau autares d'in Anna. Binty kin gan ki kuwa cikin uniform d'in nan? Looking more beautiful". Ya Fu'ad ya k'arisa maganar ya na kallon Binty.
"Thank you ya Fu'ad". Fad'in Binty ta na dariya har sai da kyawawan hak'oran ta su ka bayyana ta re da lotsewar kumatukan ta.
"Mu je ni da kai na yau zan kai ku makaranta". Fad'in ya Fu'ad.
Tsallan murna su ka yi dukan su ta re da nufar motar yaya Fu'ad d'in da gudu.
Bayan su ya bi ta re da isa wajan motar ya danna key su ka bud'e. Binty ta shiga gidan gaba kasancewar ta na son zaman gaban mota saboda ta ga komai da komai ta na kuma tambaya abunda ba ta ga ne ba. Fanan kuma ta shiga gidan baya.
Shiga motar ga yi ta re da kunnata ya yi reverse ya nu fi gate.
Oga Solomon da ya dad'e bai ga Binty ba, da ya gan ta yau a gaban mota ba k'aramin mamaki ya sha ba, domin ta k'ara girma da kama kyau. Don gaba d'aya watan ta takwas a gidan.
A hanya sai k'ara ja masu kunne ya Fu'ad ya ke yi a kan su dage su yi karatu musamman Binty.
A k'ofar gate d'in ya sauke su ta re da jan kumatun Binty ya ce,
"Binty na ki yi karatu sosai kin ji?".
Gyad'a masa kai ta yi ta na murmushi.
Fanan ita ma ta kai kumatun ta ta re da fad'in,
"Ya Fu'ad ni ma"
Ita ja kumatun na ta ya yi ta re da fad'in,
"Rigimatu maza a shige makaranta".
Isa wajan gate d'in makarantar su ka yi ta re da nu na ID d'in su su ka shige ciki.
Gaba d'aya students d'in da su ke harabar makarantar su ka juyo ta re da zubawa Binty idanuwa su na fad'in
"Wow!".
*Ku yi min afuwa masoya. Ku yi hak'uri da wannan. In sha Allah za ku ji ni anjima da yamma*
*paid book 08128755583*
🌹 *33-34*🌹
.........K'awayan Fanan da gudu su ka zo su ka zagaye su. Rukayya wacce su ke kira da Saje ta kalli Fanan ta re da fad'in,
"Wannan ita ce surprise d'in da ki ka ce za ki taho mana da shi idan mun dawo first term. Lallai kam zuciyar Sabrin sai ta buga. Ba bu shakka sai an cire ta a sarauniyar kyawun *Lead British*, please sister will you be my friend?". Saje ta k'arishe maganar ta re da kallon Binty a marairaice.
Murmushi Binty ta yi ta re da mik'awa Saje hannu ta ce,
"Friend".
Ka min Saje ta ce wani abu, gaba d'aya k'awayan Fanan su ka rik'e hannun binty ta re da fad'in,
"Friends for rever and ever". Sun fad'i hakane ta re da d'aga hannun sama su na dariya.
Dai-dai lokacin tawagar k'awayan Sabrin su ka k'araso in da su Binty su ke a tsaye.
"Ku matsa mu na son ganin fuskan newcomer da ta zo yau". D'aya daga cikin k'awayan Sabrin mai su na Rufaida ta fad'a.
Gaba d'ayan su su ka dare su ka bar Binty a tsakiya ta na kallon Rufaidan.
Gaban Rufaida ne ta buga da k'arfi. Domin yadda students su ka zo su na fad'i masu irin kyawun newcomer d'in sai ta ga ta fi haka sosai.
Juyawa Rufaida ta yi ta re da kallon sauran k'awayan da su ma tsananin kyawun Bintyn su ke kallo da mamaki.
Ba ta re da fad'in komai ba, su ka juya su ka bar wajan ta re da nufar class inda Sabrin ke zaune idanuwan ta jazur, ga dukkan alama ma kuka ta ci.
"Yana yin fuskokin ku kawai ya tabbatar min da abunda students su ka zo su ka fad'a. Ke nan ku na nufin kuma kyawun yarinyar ya haukata ku haka? Ku na nufin yanzu za'a samu wacce za ta done ni a kyau a cikin makarantar nan? Ba zai yu ba. Wallahi ko fuskan yarinyar ba na k'aunar ga ni. Ba na son in san ta ko in ga fuskan ta har in bar makarantar nan yau". Fad'in Sabrin ta re da rushewa da kuka.
"Haba Ella. Kin san Allah, duk yadda ake fad'in kyawun yarinyar nan ko, kururutawa ne kawai amma ko k'unban ki ba ta kama ba. Kawai hasken fata ne irin bauu d'in nan kamar zabaya. Amma kin san Allah, kin fi ta komai, ba ma had'i". Fad'in Shamsiya Uba.
D'ago kai Sabrin ta yi ta re da fad'in,
"Duk wacce ta yi adoring yarinyar, ku ma idan har cikin team d'ina ta ke, a cire ta kuma za ta fuskanci hukunci". Fad'in Sabrin ta re da mik'ewa kasancewar an danna bell d'in assembly.
A cikin k'aton hall d'in da ake gabatar da assembly, bayan kowa ya natsu, an gabatar da addu'a da kuma assembly. proprietor ya fito ya yi jawabi da kuma yi ma su barka da dawowa first term. Sanna ya k'ara da karanto wasu dokoki kamar haka cikin harshan turanci.
"Kamar yadda ku ka sami, wannan makaranta ce da ake koyar da ilimi da kuma tarbiya. A kwai wasu dokoki da ni shugaba na shimfid'a sakamakon wasu abubuwa da su ka faru a shekarar da ta wuce. To hak'ik'a wannan karan idan haka ta k'ara faruwa, to za mu d'auki hukunci tsatstsaura akan ko wanenen. Ba ruwa da ko baban ka shine shugaban k'asa, idan ki/kai laifi, to hukuman makaranta za ta yi hukunci akan ko waye. Na farko, ba bu d'aukaf hukunci a hannu, duk abunda wani ya maka, ka kai k'arar shi, ba biyu ba'a yarda wani d'alibi/d'aliba ya takurawa wani ba, sannan ba a yarda ko waye ka d'auki bulala ka da ki wani ba ko da kuwa malami ne, sannan kuma duk house d'in da ka/ki ke, ba a yadda do ba ka san house d'in nan ka canza ba. Sannan duk abunda malami/malama ta saka ki/ka, wajibi ne ki yo idan har abun nan bai sab'awa dokar makaranta ba. Ina fatan kowa yaji bayani na". Fad'in proprietor.
Gaba d'aya students d'in nan su ka amsa da,
"Yes sir".
Sallamar su ya yi kowa ya soma mik'ewa zuwa ajujuwan su.
D'agowar da Sabrin za ta yi, su ka had'a idanu da Binty. Gaban ta ne ya buga da k'arfi ta wa ni zaro idanuwan ta.
K'awayan ta da su ka ga abunda ke faruwa, da sauri su ka zagaye ta ta re da fad'in,
"Ella ka da ki firgita, wallahi ba bu abunda ta fi ki da shi".
K'ank'ance idanuwa Sabrin ta yi ta re da fad'in,
"Da ma ita ce. Makarantar nan ta shigo kenan. Wallahi sai na saka ta gudu da k'afafun ta. Sai na d'aura mata k'ullin da ba za ta tab'a iya warware shi ba billahi".
Fanan hannun Bintyn ta ka ma ta re da fad'in,
"Mu je in nu na miki ajin ku, kin san amana Anna ta ba ni ke".