Showing 153001 words to 156000 words out of 162658 words
Julaibib kuwa da ya san ma'anar babi d'in jinjina ya yi mata da babban d'anyatsarsa wanda ya sa ta zaro idanuwa don ba ta tab'a tunanin zai yi mata hakan ba a yadda ta san ya Bibi mara wasa.
"Ba gida mu ka yi ba daga nan mun tafi shan ice-cream". Fanan ta sa ke fad'i ta re da shigewa motar Fu'ad.
Langwab'ar da Kai ta yi ta re da fad'in,
"Please yaya Bibi in bi su?".
"Please Hayatiey ka da ki bi su ni ma zan kai ki wajan shan ice-cream d'in". Fad'in Julaibib kamar yanda ita ma ta yi maganar.
Zaro idanuwa ta yi ta re bud'e baki ta na kallonsa.
Hannu ya saka ya rufe mata bakin ta re da nuna mata cikin motar.
Shiga ta yi ta na kallonsa har kan ta na buguwa da saman motar.
"Aauch!". Su ka fad'a a ta re kamar wani shi ya bige.
"Ki yi a hankali ka da ki jimin ciwo ki jawo min aiki Kin ji Nuriyyah".
"Biyu kenan". Fad'in Binty cikin zuciya da ba ta san ma ya fito fili ba.
"Ai idan dai sunaye ne za ki ji fiye da d'ari ma". Fad'in Julaibib ta re da rufo motar ya zagaya ya shiga mazaunin driver.
Kallonsa ta ke yi ko kyaftawa ba ta yi sabida tsantsan mamakinsa. Hura mata iska a idanuwanta ya yi ta re da fad'in,
"Ya dai? Wannan kallon fa Khairiyyah".
"Na shiga uku". Fad'in Binty ta re da saurin saka kan ta tsakanin cinyoyinta gabanta na fad'uwa.
Dariya ya yi ta re da jan motar bai tsaya a ko ina ba sai wani park d'in da duk yawonsu da Barr Fu'ad ba su tab'a zuwa ba. Wajan ba hayaniya sosai irin wajan da manyan mutane su ke zuwa ne.
Wajen wani shukoki flowers ma su kyau ya kai ta. Sosai wajan ya burgeta har ba ta san lokacin da ta fara murmushi ba.
Jin mutum kawai ta yi a bayanta ya na fad'in,
"Wajan ya k'ayatar da ke ko? Zan rik'a kawo ki bayan auran duk weekend". Ya fad'i hakane har ta na jin sautin fitar numfashinsa a wuyanta.
Wani irin saurin juyowa ta yi ta re da zaro idanuwa sabida kalmar bayan mun yi auran da ya ce har sai da ta bugu da k'irjinsa kasancewar ya na gab da ita sosai.
Wayarsa ya yi saurin d'agawa ta re da yi masu salfie a hakan yadda su ke.
Saurin ja baya ta yi nan ma ta yi baya da yawa saura kad'an ta kai k'asa ya yi saurin rik'o hannunta ta re da jawota jikinsa gaba d'aya.
Waro idanuwa ta ta yi ta re da rasa inda za ta saka kan ta don wani irin kunya, tsoro da mamaki da su ka taru mata lokaci guda.
Juyata ya yi ta kalli gabanta yayin da ya rungumo waist d'in ta ta re da d'aura Kansas a kafad'arta sai da ta waro idanuwanta.
"Ina son kin tun ranar da na fara ganinki. Ke ce farin ciki na. Ban tab'a son wata mace a rayuwata ba sai ke, ina son ki kasance matata sirrina kuma uwar y'ay'ana. Ki ba ni soyayyar ki dan Allah ba don wanini dalili ba Binty. Ka da ki cuci kan ki, ki soni dan Allah ba don wata alfarma ba kin ji". Ya fad'i hakane ta re da sake mata nauyin Kansa a kafad'arta sai da ta yi kamar za ta zame a hannunsa ya yi saurin k'ara damk'o waist d'in ta.
Ita kuwa kunyace mai tsanani ta dabaibayeta ta re da jinta a wani yanayi daban ga kuma wani abu da take ji tun daga kwakwalwar kan ta wanda ba ta tab'a jin sa ba.
Sakinta ya yi jin yadda jikinta ke rawa sosai. Aikuwa ya na sakinta ta yi saurin yin gaba ta re da b'oyewa a jikin wata bishiya da ke gabansu kad'an ta re da dafe k'irjinta ta na sauke numfashi.
D'an lek'o da kanta ta yi, karaf su ka had'a idanuwa ya na sakin murmushi, saurin komawa ta yi ta na k'ara dafe k'irjinta ta re da zaro idanuwa.
"A'a wannan ba yaya Bibi ba ne Allah. Mafarki na ke yi". Ta fad'a k'asa-k'asa. Can kuma ta kai hannu ta re da tsungulin hannunta don tabbatar da mafarki ne ko gaske.
"Aauch!" Ta fad'a sabida zafin da ta ji.
Saurin isa wajan ya yi ta re don sanin abunda ya sa me ta.
Su na had'a idanuwa ta yi sauri rufe idanuwanta ta re da juya baya ta rungume bishiyan.
Sosai ta ba shi dariya. K'arasawa wajan ya yi ta re da juyota ka na ya ce,
"Ke dan Allah tun 1888 aka dai na wannan gulmar da kinibibi. Idan ki na sona kawai ki fad'a babe".
Ba ta san lokacin da ta fad'a k'irjinsa ba don kunya ta rufe fuskanta da k'irjinsa ji ta ke kamar ta nitse.
"Mu tafi gida?". Ya rad'a mata a kunne said da ta ji tsigar jikinta ya ta shi har ba ta san lokacin da ta d'aga masa kai ba.
Hannunta ya kama ta re da nufar parking space, sai da ya sakata a mota ka na ya zagaya ya shiga.
Kanta ta saka tsakanin cinyoyinta ta b'oye fuskanta. Dariya ya yi ta re da reverse su ka bar wajan. Sai da ya hau titi ka na ya kunna wak'ar Umar M Shariff *CIKIN D'AYA*. Hannunta ya rik'o ta yi k'ok'arin kwacewa amma ta kasa, bin wak'ar ya shiga yi kamar haka,
🎻 _Cikin d'aya a cire d'aya, zai zamo ba ko d'aya ni da ke mu zan d'aya ba mu fatan rabuwa. In za ni ba da labari, wa ke saka ni annuri, sunanki zan kira farii, lallai ki da da alkhairi. Kyawun halinki ne ya Jani, ga natsuwa da kyan tsari, auran ki shi na sa buri daga ke ba ni yin k'ari, gun ki kai na sunkuyar, hankali na na tsayar, ke na baiwa ajiyar zuciyata bai d'aya. Ku kalleta kyakkyawa, gu na ta wuce kowa, Idan gaki, idan gani, ni dai ba ni son kowa. Ko da ba ni motsawa, ko da na zamo gawa, da ke zan yi kwantawa ajinina kin ka narkewa. So da k'auna kin shigar, ba bu kowa kin kawar, ke kad'ai ce mallakar zuciyata guda d'ayaaa. O'o'oohh! Lokaci na bak'in ciki, ke ki ka sani na yi darawa, kin sa ni farin ciki duk damuwata na yi mantawa, komai daki-daki na ke a yanzu ba ni rud'ewa, in an yi farmaki gare ki dole na yi karewa. Wajibi in tabbatar, masoyiya na tseratar, ko da rai za na salwatar za na yi maki kariya. Cikin d'aya a cire d'aya, zai zamo ba ko d'aya, ni da ke mun zan d'aya ba mu fatan rabuwa_🎻
Rar cikin jinin jikinta ta ke jin wak'ar, ba ta tab'a tunanin yaya Bibi ya na sauraran wak'ok'in Hausa ba balle ma har ya ita rerata haka ba. Mamaki duk ya gama kasheta. Ta san da za ta baiwa Fanan wannan labarin sam ba za ta yarda ba sai dai ma ta yi mata dariyar k'aryar da ta shararo.
Haka ya dunga mata kalaman soyaya cikin wak'ar Umar m shariiff kala-kala ga shi ba gudu ya ke yi kad'an-kad'an ya ke tafiya don ka da su isa gida da wuri.
Bayan sun isa gida ya yi locking motar ta re da fuskantarta ya zuba mata idanuwa ita kuma ta k'udundune cikin cinyoyinta.
"Ba ki ce komai ba Ruhiey, kin amince da ni a matsayin mijinki na gobe". Fad'in Julaibib.
"Wayyoo dan Allah ka bud'e min in shiga gida dan Allah". Fad'in Binty a marairaice.
"Dan Allah ki fad'a min ki na sona". Shi ma ya fad'a kamar yarda ta yi cike da shagwab'a.
"Wayyoooo Allah". Binty ta sa ke fad'i.
Dariya ya yi sosai saboda ya fahimci kunya ta ke ji sosai. Bud'e lock d'in ya yi. Ai kuwa cikin sauri ta bud'e motar ta fice da gudu saura kad'an ta fad'i har da wani zabura ya yi kamar irin shine zai fad'i.
Da gudu ta wuce su Rauhiyyah da Fanan da ke ciye-ciye har da Fu'ad.
Gaba d'aya dariya su ka fashe da shi kasancewar tuni sun harbo jirgin ya Bibi.
"Babi!" Fanan ta kwala mata kira cike da tsokana.
Ko juyowa ba ta yi ba ta haye sama da gudu. Sai da ta turo k'ofar d'akin ta rufe ta re da jinginar da jikinta a jikin k'ofar ta shiga mai da numfashi.
Tun daga ranar su ka soma wasan b'uya, ba ta yadda ta tsaya in da zai ganta. Shikuwa har ya shiga wani hali na rashin ganinta kwana biyu.
Rauhiyyah kuwa ita da Fu'ad kamar da wasa soyayyah ta shiga tsakanin su, tuni Fanan da ma su Sabrin su ka canza masu suna zuwa Babi (matar yaya da yaran Hindi).
Mas'ud kuwa tun da ya kyallara idanuwansa akan Sabrin ta tafi da shi, shi ma bai cuci kansa ba ya fito masa da manufarsa, kuma said Allah ya had'a zuciyoyinsu, gidan Anna dai ya koma gidan masoya, don kullum Mas'ud na can su na shan soyayyarsu da Sabrin ya yin da Fu'ad su ke shan na su da Rauhiyy. Mai gayyar ne dai har yanzu ba ta ba shi had'in kai ba.
Ta fito daga kitchen kenan cikin sauri ta na son guduwa zuwa sama ka da ya ganta. Sai da ta isa tsakiyar parlour caraf ta ji an damk'i hannunta.
*PAID BOOK 08128755583*
🌹 *85-86*🌹
...........Juyawar da za ta yi idanuwansu su ka had'u da na juna. Ji ta yi kamar ta kurma ihu saboda kunyan da ya lullub'eta.
"Mai ya sa ki ke guduna Habibty? Kin san yadda hakan ya ke min zafi ana kuwa?". Ya k'arasa maganar ta re da nuna saitin zuciyarsa.
"Dan Allah wallahi kunya na ke ji". Fad'in Binty har da wani karyar da wuya irin marainiyar nan.
"Dan Allah wallahi na k'osa in ji kin fad'a da bakin ki kina sona". Fad'in Julaibib cikin shagwab'a shi ma.
Kallonsa ta yi na second biyu ba ta san lokacin da ta bushe da dariya ba saboda yadda ya yi da fuska kamar d'an two years.
Ka mo hannunta ya yi ta re da matsota kusa da shi ka na ya d'aure idanuwata da hanky ka na ya rik'o hannun su ka fita, can garden su ka nufa.
Sai da ya kawota tsakiya ka na ya kwance idanuwan na ta tare da tsayawa a bayanta.
A hankali ta fara bud'e idanuwan har ta bud'e su duka. Zaro idanuwa ta yi sakamakon arba da ta yi da wasu flowers multi colours da aka shimfid'a a filin. Ga wasu balloons ma su shape d'in love a jiki kuma an rubuta I love you Rukhsana, wani kuma an rubuta I love you Bintyn Anna, wasu kuma a jiki an rubuta can't live without you. Du ka balloons d'in ba bu wanda ba kalmomin k'auna a jiki.
Duk'awa ya yi a gabanta ta re da kamo hannunta ya ce,
"Will you be my wife? I mean will you be the one and only mother of my children?".
"Yyy.. Yes". Fad'in Binty in a very cool voice ta re da rufe fuskanta da d'aya hannunta".
"Na yi alk'awarin zama da ke cikin aminci da soyayya in sha Allah har k'arshan rayuwarmu. Zan kula da ke fiye da yadda zan kula da kai na, zan shayar da ke zallar zuma da madarar soyayyar da ba ki tab'a ga ni ba. Wallahi Salis na son ki irin sosai d'in nan".
Gaba d'aya maganganunsa sai su ka tu na mata da Yousouf lokacin da su ke musayar zobe. Kwal-kwal ta yi da idanuwa kamar za ta yi kuka sai ta yi saurin shanye hawayanta.
Fu'ad da Rauhiyyah da ke mak'ale can cikin garden d'in su ma su ma shan na su soyayyar su na kallon su.
Rauhiyy ce ta fiddo wayarta k'irar iPhone 13pro max ta soma yi masu video tun sanda ya kwance mata hanky a fuska.
"Kin ga love ko?". Fad'in Fu'ad ya na tallabe k'eyar Rauhiyy.
Shafa k'eyar ta yi ta na dariya ta re da fad'in,
"Kwarankwatsi na ga ni, ni ma ai min irin haka ko inyi rejecting". Fad'in Rauhiyyah.
"Ke kin ma isa? Ni da ke ai mun zama hatta da jini". Fad'in Fu'ad.
"Allah ya sa su hango ku yasin". Fad'in Sabrin wacce su ke yowa inda su ke ita da Mas'ud.
Dariya su ka yi gaba d'ayan su ta re da nufo in da ya Bibi da Binty su ke su na tafi.
Binty na ganin su ta yi ta rud'e ta rasa in da za ta saka kan ta, bayan ya Bibi ta yi da gudu ta b'oye fuskanta a bayansa.
Aikuwa nan ma su ka k'ara kwashe da dariya ta re had'a baki su ka soma yi mata wak'a kamar haka,
🎻 _Binty! Ayaya_
_Binty! Aya_
_Binty Binty Binty! Aya_
_Binty mai miji Ayayah_🎻
Balloon d'aya ya d'auka ya bi su da shi da gudu, gaba d'aya su ka dare su na dariya.
Tun daga wannan ranar aka shiga soyayyah ruwa-ruwa tsakanin Binty da Julaibib, abinci daban ta ke dafa masa gidan kuma sai abunda ya zab'a ta ke yi masa ta kai masa har d'aki. Raba dare su ke yi suna waya. Kasancewar idan ya fita tun safe sai dare saboda yanayin aikinsa kuma gashi dama daddy ya sayan masa wani makeken fili ana gina masa asibitinsa a wajan. Yanzu haka asibitin ya kai linta.
..........Kwanansu Anna goma su ka dawo daga bauchi ci ke da farin ciki, sai dai ba su cewa kowa komai ba.
Washa garin ranar da su Anna su ka dawo, su Binty su ka d'ugunzuma sai gidan Maman Fakri (uwar rik'on Rauhiyy). Har da su Sabrin da