Showing 144001 words to 147000 words out of 162658 words
ya taso mai k'arfi ya lullub'e su na kusan mintuna goma ka na su ka b'ace b'attt.
A nan cikin garden su ka tsinci kan su kamar yadda anan aka kwamushe su.
Sabrin sakin wani tsumamman kuka ta yi yayin da ta yi kan Binty da ke yashe a k'asa ba ta numfashi.
Julaibib kuwa kan Fu'ad da ke zubda jini ta cikinsa ya yi kuma bai numfashi.
Daga Hamdan har Sabrin d'in an rasa wa zai bai wa wani hak'uri.
Wayarshi da ke aljihunsa ya ji ya na k'ara wacce ya ma mance da ita a jikinsa ya yi saurin fiddowa ta re da picking call d'in kasancewar daddy ne ya sake kira ko Allah zai sa ya dace.
"Ku na ina Julaibib?". Fad'in daddy.
"Daddy ka yi sauri akwai matsala mu na gidan su Sabrin". Fad'in Julaibib.
Kasancewar alhaji Usman su na ta re da alhaji Saifullahi ta re su ka nufo gidan a mota daban-daban.
Hankali ta she su ka nufo garden d'in.
Sabrin na ganin mahaifinta ta nufesa da gudu ta rungume ya yin da Alhaji Usman ya yi kan Fu'ad da gudu wanda ke zubda jini.
Fu'ad d'in ya fara sawa cikin mota ka na ya saka Binty ta re da kwantar da kan ta jikin motar.
Sam ba su lura da wani mutum wanda a k'alla zai yi sa'a da alhaji Saifullahi a gefe ba sai wawware idanuwa ya ke yi ya yi wani irin bala'in rama ta re da fita hayyacinsa.
Ko bi takansa ba su ba. Alhaji Usman ya shiga gaban mota ya yin da Julaibib ya zauna a baya ta re kwantar da kan Fu'ad a cinyarsa ya na jin tashin hankali cikin ransa.
Alhaji Saifullahin ma sai mota ya nufa Sabrin ita ma ta shiga ta re da kayan Binty da Yousouf ya ba ta cikin kwarya. Hamdan bi ye da ita su ka nufi asibiti.
Kai tsaye ICU aka nufi da Barr Fu'ad wanda Julaibib ya kasa shiga sai safa da marwa ya ke yi a ciki. Alhaji Saifullahi kuwa jikinsa rawa ya ke yi don idan Julaibib favourite d'in Anna ne, shikuma Fu'ad d'in ne fav d'in sa.
Cikin hukuncin ubangiji doctor su ka samu ceto rayuwar Barr bayan sun masa theater don sakamakon wannan wuk'a da ya soke shi ya b'ula masa hanji.
Lokacin da su ka fito daga theather nan k'arfe biyu da kwata na dare saboda sun matuk'ar dad'ewa a ciki tun magriba.
Binty kuwa dama suma ta yi sakamakon firgici ita ma dai sai da aka k'ara mata ruwa. Sabrin ke zaune da ita.
Hamdan kuwa ta re su ke safa da marwa da Julaibib.
............Can wajan Anna kuwa hankalinta ne ya tsananta tashi saboda ganin har biyu amma alhaji Usman bai dawo ba kuma ta kira wayarsa ta k'i shiga.
Fanan ta yi kuka har ta na sik'ewa.
Sai da Alhaji Usman su ka yi sallar asuba ta re da tabbatar da farfad'owar Fu'ad ka na ya kira Anna ya shaida mata bayyanar su Binty ta re da fad'a mata Fu'ad na kwance a asibiti.
Shi ma dai Alhaji Saifullahi ya kira Hajiya Sakna mahaifiyar Sabrin ta re da shaida mata halin da ake ciki.
*MANAGE PLEASE*
🌹 *79-80*🌹
................Hajiya Sakna ta fito ne ta ga wannan tsamurarran dattijon ya na tafiya da kyar kamar iska za ta hure shi.
"Bawan Allah, daga ina haka?". Fad'in mahaifiyar Sabrin ta na mai k'ara k'are masa kallo.
Shi dai da idanuwa kawai ya ke bin ta saboda kamar kwakwalwarsa ya tab'u.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Shafi'u! Shafi'u!!". Hajiya sakna ta saki salati ta re da kwalawa driver kira wanda ya zo da gudu ta re da d'an rusunawa ya ce,
"Ran ki shi dad'e ga ni. Wani wajan za'a kai ki ne? " Fad'in Shafi'u driver.
Nu na wannan bawan Allahn ta yi ta re da fad'in,
"Daga ina haka wannan? Yaushe ya shigo gidan nan?". Fad'in Hajiya Sakna ta na nuna shi.
"Hajiya gaskiya tun jiya bayan fitar alhaji da hajiya k'arama da kuma wani bawan Allah da su ka fita babu wanda ya sake shigowa". Fad'in Shafi'u.
Shuru Hajiya Sakna ta yi, can kuma ta d'auko wayarsa cikin jaka ta kira alhaji Saifullahi ta shaida masa komai.
Cikin mintuna talatin ya dawo gidan k'urawa wannan bawan Allahn idanuwa ya yi ya na son ya ga ne ko ya san shi, amma Sam bai ga ne sa ba.
"Bawan Allah daga ina?". Fad'in alhaji Saifullahi ta re da ware hannayansa ya na kallonsa.
Still shuru sai zare idanuwa ya ke yi.
"Ku fita da shi daga gidan nan yanzu" Fad'in alhaji Saifullahi.
Hannunsa Shafi'u da mai gadi su ka yi ta re da tura k'eyarsa zuwa waje ka na su ka rufo k'ofa.
Asibitin su ka koma, in da su ka taras Binty ta farfad'o sai kuka ta ke yi kamar ranta zai fita.
Julaibibi ya shiga d'akin har da turo k'ofa. Hanky ya ciro daga aljihun wandonsa ta re da share mata hawayan da ke zubowa ka na ya ce,
"Ki dai na kuka please, kukan ki a nan na ke jin sa" ya k'arisa maganar ta re da nu na zuciyarsa.
Mai makon ta yi shuru sai ta k'ara sautin kukan na ta.
Rungumo kanta ya yi zuwa k'irjinsa ya shiga bubbuga bayanta ya na mata magana cikin kunnanta.
Anna ne da Fanan su ka shigo hankali ta she. Cikin sauri Alhaji Saifullahi ya taro su ya na mai kwantar da hankalin su.
Sai washa gari aka ba su damar shiga d'akin da Fu'ad ya ke ciki wanda ta farfad'o sai wajan aikin da ke masa ciwo kad'an-kad'an.
Su na had'a idanuwa da Binty ya sakar mata murmushi. Da gudu ta k'arisa wajan gadon ta re da fad'in,
"Ya Fu'ad". Sai kuma ta fashe da kuka mai sauti Sabrin da ke gefe ita ma ta saki na ta hawayan.
Fanan kuwa k'arisawa wajan Binty ta yi ita ma ta shiga tayata kukan.
Da kyar Fu'ad ya iya lallashinsu wanda muryansa ke fitowa dakyar.
Satinsa biyu a asibiti aka sallamesa, kuma dalilin ciwona ya sa aka aje komai a gefe har da case d'in su hajiya Mansura wanda ake son tura su koti domin ta yanke masu hukunci.
Bayan sun dawo gida da kwana uku, mahaifin Sabrin da mahaifiyarta da ita kan ta Sabrin d'in da kuma y'ay'an aunty Junaina duk su ka d'ugunzuma state CID wanda tu ni Alhaji Usman da iyalansa sun isa can.
Videon su Kandala aka sa ke kunnawa, hajiya Sakna da y'ay'an Junaina da kuma Sabrin da ba su ga ni ba su ka sa ke gani.
Amrah ba ta gigice ba kamar yadda Hanan ta gigice ba sakancewar ita ta san abunda uwar ta su ta ke aikatawa.
Hanan kuwa ihun tashin hankali ta rik'a yi har sai da aka fidda ta zuwa mota.
Julaibibi kuwa ji ya ke yi kamar ya fiddo su Kandala ya kashe su.
Daga nan gaba d'aya gida su ka dawo anan side d'in bak'i da ke gefen side d'in Anna.
Barr Fu'ad shi ya zayyane ma su abunda ya faru a can duniyarsu Yousouf.
Gaba d'aya al'ajabi da mamaki ya gama kashe su wanda gaba d'aya sun ka sa magana.
Kwaryan da Yousouf ya baiwa Binty, Sabrin ta aje a gaban Anna.
Anna ce ta d'auki kwaryan ta re da fiddo kayan ciki ta shiga dubawa. Maficin d'awisun ta d'aga ta yi ta jujjuya shi.
Murmushi ta yi ta re da mai da kayan cikin kwaryan ka na ta ce,
"Allah ya bayyanar da iyayanki a duk in da su ke".
Gaba d'aya da amin su ka amsa ka na Anna ta shiga yi wa Binty fad'a akan b'oye mata wasu abubuwan da ta yi. Daga nan ma ta koma kan Sabrin ita ma ta yi mata fad'a akan duk abubuwan da ta ke yi duk da dai sun ji har da sharrin sammu.
Sosai ta ke kuka ta re nuna tsantsan nadama da kuma rok'ar gafarar mahaifiyarta. Shi ma alhaji Saifullahi ya rok'i gafarar mahaifiyar Sabrin.
Ta na kukan jin dad'in shiryuwar d'iyar tata ta ce,
"Na ya fe mu ku duka, Allah ya yafe mana baki d'ayan mu".
Julaibib kuwa hankalinsa ne ya tafi wani waje sabida kallon k'urillan da ya yi ta maficin d'awisun nan da kuma tuno tambarin d'awisun da ya ga ni a k'eyar Binty ranar da ta b'ace ba'a ganta ba.
"To wacece wacce na ke ga ni a wonderland?". Fad'in Julaibib cikin zuciyarsa.
Bayan Binty ta kasance ita d'aya a d'aki ta fad'a duniyar tunanin ta yadda za'a yi ta gano iyayanta da kuma dalilin yar da ita a bola.
B'angaran Fu'ad kuwa ya yi k'ok'ari sosai wajan cire Binty daga cikin zuciyarsa kasancewar ganin soyayyar Bintyn b'aro b'aro cikin idanuwar wan na shi. Sai ya shiga avoiding zama kusa da Binty gudun ta da mashi da miki. Gidan ma gaba d'aya ya dai na zaman sa kullum sai bayan isha ga ke shigowa.
............Kallon tafin hannunsa na dama ya yi ta re da k'urawa rubutun da ke hannun na sa don sanin abunda mahaifiyar Yousouf ta rubuta. Sai dai bai fahimci komai ba.
Kallan ruwan zam-zam d'in da ke gabansa ya yi ta re da d'auka. Sai da ya yi bismillah ta re da karanto ayatul kursiyyu ka na ya wanke tafin hannun cikin wani k'aramin jug sannan ya tsiyaye a cikin gora.
Aje goran ya yi ta re da shiga cikin bayi don yin kana ya tafi gidan Alhaji Muhammad Ahlam don kai wa Yousouf maganinsa da mahaifiyar Yousouf ta ba shi.
Cikin rabin awa ya gama kimtsawa cikin wata gezna dark blue ta re da hula bak'i sai takalminsa halve cover kalar bak'i wanda samansa ya sha stone masu walwali.
Kai tsaye fitowa ya yi ya nufi side d'in Anna. Sai da ya kwankwasa sannan ya tura ta re da shiga ciki.
Zaune Binty ta ke a kan 1sitter. Riga da straight skirt ne a jikinta irin na y'an kanti. Ba bu d'an kwali a kanta parking d'in gashinta ta yi a tsakiyar kan ta. D'an ramar da ta yi ya k'ara fito da haske da kyawunta earpies mak'ale a kunnanta ta na sauraran wa'azin Yousouf Guruntum mai su na (MAZINACIYA JAKAR GAYU).
Har ya iso kan ta ba ta sa ni ba sabida hankalinta gaba d'aya da ta tsayar a wajan wa'azin da ta ke ji.
Hannu ya kyasta a fuskanta ta re da zare earpiece d'in kunnanta.
Cikin sauri ta d'ago ta kalle shi ta re da saurin mik'ewa tsaye ta na rarraba idanuwa.
D'age mata gira ya yi ta re da fad'in,
"Mi ye na tsoran to? Ni dodo ne?". Fad'in Julaibib.
"Bbb.... Ba komai?". Fad'in Binty cikin in'ina.
"Za ki raka ni?". Fad'in Julaibib ya na matsota kamar zai had'e jikinsa da na ta.
"A'a". Fad'in Binty had da girgiza kai.
"Mai ya sa to?". Julaibib ya sa ke fad'i ta re da kuma matso ta kad'an.
"Zan yi aikin a kitchen ne. Zzan yi girki?". Fad'in Binty ta na mai zama jab'ar akan kujeran saboda k'ara matsowa da ya yi.
Sabrin da ke mak'ale a bakin k'ofar kitchen sai gimtse dariya ta ke yi sabida kan ya Bibi ya ganta.
D'aga k'afarsa ya yi ta re da d'aurawa a kan kujera ta re da fad'in,
"Baki ce na yi kyau ba. Na yi kyau??".
"Ka yi kyau!". Fad'in Binty da sauri don sabon yanayi da Ya Bibin ke mata kwanan nan.
"Ki kula da kan ki, idan na dawo za mu yi hira kin ji".
"Ttttt to". Fad'in Binty baki na rawa cike da mamaki.
Hura mata iska a fuska ya yi ta re da sauke k'afarsa ya juya ya nufi upstairs don zuwa wajan Anna.
Doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta re da murgud'a baki ka na ta mai da earpiece d'inta.
"Babi!". Fad'in Fanan ta re da nufota da gudu ta rungumeta ta na mai jin dad'i.
"Ke dalla menene kuma haka? Menene Babi kuma?". Fad'in Binty.
"Au duk kallon Indian ki ba ki san menene Babi ba? To ki je ki yi searching". Fad'in Sabrin ta re da nufar kitchen ta na fad'in,
"Kaho na pyar ri heee". Ta fad'i hakane ta re da rungume hannunta a kirjinta.
.............."Ummu Julaibib kin tabbata da abunda ki ke fad'amin kuwa?". Fad'in Alhaji Usman.
"Eh to, ban tabbatar ba, shiyasa na ke so na je na yi confirming. Shiyama ko a wancan lokacin ban ce komai ba. Amma gaskiya ban kaso sittin ina ji a jiki na ita ce". Fad'in Anna.
"To yaushe za mu tafi kenan?". Fad'in Alhaji Usman.
"Nan da sati d'aya idan an gama case d'in su Suhail". Fad'in Anna.
"Akwai fa abunda ban fad'a miki ba, na saki Mansura saki uku, domin ba za'a yanke mata hukunci da aure na a kan ta ba. Alhaji Saifullahi shi ma ya saki matarsa saki uku kuma ya hana y'ay'ansa ganinta. Na yi na yi da shi ya bar su su je su ganta ya ce su ma y'ay'an ba su son ganinta".
"To Allah ya kyauta". Shi ne abunda Anna ta fad'a dai