Showing 84001 words to 87000 words out of 162658 words

Chapter 29 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42987

Figar motar ya yi da guda sannan ya soma jan giyar ta na gama ta na bayan kamar ta na jacking.
Hannun shi ta kai wa cizo shikuma ya saki k'ara ta re da fad'in,
"Auuch! Wallahi sai dai ke ki yi driving, idan ba haka ba kuma mu kwana a nan". Hamdan ya fad'a ta re da folding hannunsa ya na kallonta.
"Driving ko? Zan ko yi". Fad'in Sabrin ta re da fitowa daga cikin motar ta zagaya, shikuma ba ta re da ya fito ba ya koma inda ta tashi.
"Ka tabbatar ka saka belt". Fad'in Sabrin ta re da saka belt a jikinta, shi ma Hamdan ya saka.
Key ta yi wa motar ta re da figar motar da uban gudu. Da ba din Hamdan ya saka belt ba, sai ya yi tsalle ka na zai dawo wajan zaman sa.
"Ki yi wa girman uban giji ki yi parking zan koma gida a k'afa". Fad'in Hamdan saboda irin uban gudun da Sabrin d'in ta ke yi, don motarsu har karkacewa ta ke yi kamar b'arayi y'an sanda sun biyo su.




*________________*
............Gaba d'aya y'an aiki sai kai wa da komowa ake yi sakamakon babban d'an mai gidan da zai dawo yau daga k'asar *CANADA*.
Anna da kanta yau ta shiga kitchen ta na had'awa shalelen na ta abuncin da ya fiso, gefe kuma Fanan da Binty na ta ya ta da wasu abubuwan.
Wayar Bintyn ce ya yi k'ara, fiddo da wayar ta yi daga cikin aljihun apron d'in da ke jikinta.
Text message Yousouf ya turo mata, murmushi ta saki ta re satar kallon Anna ta ga Sam hankalinta bai kan ta. Sak'on ta shiga karantawa ta na sakin murmushi har hak'oranta sai da su ka bayyana. Sai da ta gama karantawa tsaf, ka na ta shiga yi masa replay da dad'ad'an kalamai kamar yadda su ka saba.
"Amma ban yi maku warning akan shigo da waya kitchen ba? Na fad'a maku ba'a zuwa da waya a in da akwai gas amma Sam ba kwa jin magana". Fad'in Anna ta na kallon Binty da ta yi saurin mayar da wayar cikin aljihun apron d'in gabanta na fad'uwa kuma ta na addu'ar Allah ya sa ka da Anna ta ce ta ba ta wayar ka da ta ga abunda ta ke yi.
"Anna ita dai, don ni kam ban shigo da waya kitchen". Fad'in Fanan ta na yi wa Binty gwalo.
"Keep quite, ai halin ku d'aya. Thank God Yayan ku na hanya, duk zai gyara maku zama ai". Fad'in Anna ta na hararar su duka.
Dariya Binty ta yi ta re da yi wa Fanan gwalo kamar yadda ita ma ta yi mata.
"Anna ki na ganin ta ta na min gwalo ko. Ki fad'a mata ni yayarta ce fa. Zan zane ta". Fad'in Fanan.
Kallon Binty Anna ta yi ta re da fad'in,
"Maza ki je ki aje wayar nan ki dawo. Ban son in k'ara ganin Ku da waya a hannun Ku in dai za Ku shigo kitchen. Idan kuma ba za Ku kiyaye ba, to zan kwace wayar".
"Anna ki yi hak'uri za mu kiyaye". Gaba d'aya su ka fad'a saboda kwace waya da su ka ji Anna ta ce, don sun san hakan ba k'aramin aikin ta ba ne.

Fitowa daga kitchen d'in Binty ta yi ta re da saurawa sama da sauri. Ta na shiga d'akin su ta k'arisa typing message d'in ta re da tura masa.
Cikin second minti d'aya ya sake turo mata da wani message d'in. Ita ma ta sake masa replay. Kamar wasa su ka yi ta wa junan su musayan kalamai, su Binty har da kwanciya a kan gado, shaf ta ma manta da batun girki da su ke yi.
" *_Mai yasa ka fiye son aiko min da sak'o fiye da ka k'ira ni a waya? Kwata-kwata sau biyu kawai mu ka tab'a yin magana ta waya_*". Ta na gama typing ta tura masa.
Karan message ne ya shigo wayar ta. Bud'e message d'in ta yi.
" *_I preferred message than talk, that the reason_*".
Murmushi ta yi ta re da typing message.
" *_Muryata ba dad'i ko? Na san haka ne ai_*".
Wayar ta ce ta so ma k'ara. Sai da gabanta ya fad'i da ta ga shi ne ke kiran ta a waya. Kasa picking ta yi har wayar ta gama k'ara. Wayar na yankewa, ya tura mata message.
" *_Ban tab'a jin murya mai dad'i kamar ta ki ba. Golden voice gare ki. Mai ya sa ki ka k'i picking call d'in? Are you angry?_*".
Dad'i ne ya mamiye zuciyarta, message ta shiga yi masa typing.
" *_Haka nan na ji na kasa d'aukar wayar. I'm not angry with you_*".
Message d'in da ya sa ke turo mata ne ya sa k'irjinta bugawa. Kallon message d'in ta yi ta re da k'ara karantawa.
" *_Idan ba matsala, mu had'u a wonderland by 4:00pm_*"..
Ta karanta message d'in ya kusa sau goma. Wani message d'in ne ya sa ke shigowa.
" *_Still waiting for your replay_*".
Ta na gama karantawa ta kashe wayar gaba d'aya ta re da sauka daga kan gadon. Apron d'in da ta ga ni a jikinta, shi ya tuna mata abunci su ke yi a kitchen.
"Wayyo Allah na". Shine abunda ta fad'a ta re da fita da gudu. Da gudu-gudu ta ke saukowa daga steps d'in, aikuwa tsautsayi ya sa ta yi missing step ta dunga gungurowa har ta fad'o can k'asa.
K'aran ihunta ne ya fito da Anna da Fanan da ke kitchen da gudu.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!". Anna da Sabrin su ka fad'i ta re da nufar in da ta ke.
A dai-dai lokacin ne kuma, motar Barrister Fu'ad ta dannawa Oga Solomon horn, dawowar shi kenan daga airport ya je ya d'auko ya Bibi.

Kasancewar bai son magana da hayaniya, shiyasa jama'a da dama su ke zaton shi d'in mai girman kai ne. Wannan k'aron ba sai da ya yi wa Fu'ad warning akan ya tabbatar motar da zai zo d'aukar shi ta na da tinted. Hakan ne ya sa jama'ar gidan ba su san da shigowar sa ba.
Ya Fu'ad na parking ya yi saurin fitowa, cikin tafiyar shi na ingarman namiji ya nufi side d'in Anna saboda bai k'aunar gaishe-gaishen nan sa y'an aiki su ke yi.
Sallamar ya yi cikin siririyar muryansa ta re da kutsa kai cikin parlour ya na sakin ajiyar zuciya.
Ita kuwa Anna ko sallamar shi ba ta ji ba, ta na duk'e a in da Binty ta ke kwance ta na fad'in,
"Inna lillahi, wayyo Anna ta". Da ma ga ta da shegen raki.
Anna kuwa cike da tausayawa har ta fara hawaye.
Idanuwan Julaibib ne ya sauka akan Anna da ke sharan hawaye. Gaban shi ne ya ba da sautin dam, domin adunya ba ya k'aunar kukan mace, musamman ma a ce abun k'aunar na da duk duniya babu kamar ta ce ke yi.
"Subhanallah!". Julaibib ya fad'a a hankali ta re da nufar wajan da su ke.
Duk'awa ya yi ta re da ka mo hannun Anna ya ce,
"Anna what's the problem? I'm here". Julaibib ga fad'a in a very cool voice da ke bayya tashin hankalin shi.
Saurin kallon fuskan shi Anna ta yi ta re da fad'in,
"Thanks God! Julaibin du ba min marainiyar Allah don Allah. Fad'owa ta yi daga sama". Fad'in Anna.
Kallon gefen da ta ke ya yi sau d'aya ta re da saurin kau da kansa ya mai da kan Anna ta re da narke fuska kamar wani k'aramin yaro ya ce,
"Anna zuwa na fa kenan, ko ruwa ban sha ba sai in fara aiki".
"Do as I said now". Anna ta ba shi umarni cike da tsare gida don sarai ta san halin d'an nata abu mai sauk'i ne a wajan shi ya ce ba zai yi duba ta ba.
"Wash, wash, wash! Wayyoooooh Allah na, Anna hannu na". Fad'in Binty da idamunta ke a kulle sai faman raki da kiran sunan Anna ta ke.
Ya Fu'ad da shigowar sa ke nan ya yi saurin k'arasowa wajan ta re da fad'in,
"Anna mai........". Bai k'arasa maganar ba idauwansa su ka sauka akan Binty da ke ya she a k'asa sai fad'in wayyo hannunta ta ke yi.
Fu'ad bai san sanda ya d'auke ta cak ya aje ta akan three sitter ba ya shiga fad'in,
"Beauty Anna lafiya? Mai ya same ki?". A rud'e ya fad'i haka ta re da kallon Anna ya sa ke fad'in,
"Anna mai ya sa me Binty?".
"Ta yi missing step ne". Anna ta fad'a ta re da kallon Julaibib ta antaya masa harara.
Hannu Julaibib ya sa ka ga dafe kan shi, don ihun ''wayyo hannu na'' da Bintyn ta ke yi har ya soma damun shi.
Ya Fu'ad kuwa kallo Binty ya yi ta re da fad'in,
"Sannu kin ji Binty, ga ya Bibi nan zai du ba ki".
Harara Julaibib ya makawa Fu'ad da bai ma san ya na yi ba. Yamutsa fuska ya yi ta re da nufar wajan da Bintyn ta ke a kwance ya d'an rankwafa ta re da rik'o hannun da ya ke mata ciwon.
Wani k'ara ta kwalla ta re da rik'e hannun Julaibib d'in da d'ayan hannunta. Don lokaci d'aya ta ji wani azaba biyu ya ziyarci hannun. Na farko zafin da hannun ya ke mata, ba biyu kuma wani irin k'aik'aci mai kama da k'unan wuta da ta ji yayin da ya rik'e hannun na ta.
D'an tsaki ya yi ta re da d'aure fuska ya ce,
"Sake min hannu ko in mazge ki anan wajan. Sai shegen raki da shagwab'ar tsiya. 'Anya wayyoo hayyunaa'. Dallah matsa can". Julaibib ya maimaita abunda ta ke fad'i kamar yaro na magana.
Duk irin tausayin da Fanan ke mata sai da ta dara saboda yadda Ya Bibi ya yi maganar.
"Ka rai na ni ko Julaibib?". Fad'in Anna ta na kallon shi.
"Anna ba laifi na ba ne. Y'ar ki za ki yi wa magana ta natsu in duba mata hannun. Kuma ma fa buguwa ce kawai ta yi tsabar raki ne kamar ta karye ko ta samu gocewar k'ashi". Julaibib ya k'arisa maganar ya na maka mata harara.
Zama a gefen in da ta ke Anna ta yi ta re da shafa kan ta ka na ta ce,
"Auta na ji tsaya yayanku ya duba miki hannunki kin ji ko, in sha Allah zai warke ya dai na miki zafi". Fad'in Anna a tausashe.
"Annan mu dan Allah ace masa ya min a hankali. Zafi na ke ji". Fad'in Binty cikin shasshek'ar kuka.
"To zan fad'a mishi, amma kar ki gardama kin ji Binty na". Fad'in Anna.
Gyad'a mata kai Binty ta yi ta ra da kallon Julaibib ta wani narke fuska.
Harara ya watsa mata ta re da kamo hannu. Wannan karan ba ta ji turirin azaba kamar ta k'one ba, sai azabar yadda yake murd'a hannun.
Wani irin ihu ta saki da k'arfi har ba ta san san da ta afka jikinsa ba ta re da ruk'unk'ume shi ta na fad'in,
"Wayyiooo Annah zai kashe mi ki ni. Dan Allah ki taimake ni".
Shi kuwa Julaibib, ihunta har cikin kwanyar shi ya ji shi, ji ya yi kunnan shi ya yi masa wani duummmm. A hankali ya b'amb'are ta daga jikinsa ya bar ta nan kwance k'asa ta re mik'ewa tsam ya saka hannun shi biyu a kan kunnansa ka na ya juya ya soma tafiya.
Da sauri ya Fu'ad ya bi bayansa Anna ta yi saurin dakatar da shi ta re da girgiza masa kai. Dawowa ya yi inda Binty ta ke ta re da sungumar ya mai da ta kan kujera.
Julaibib be ya juyo ta re da watsa masa harara kamar zai yi magana, sai kuma ya fasa ya fice daga d'akin.
"Fu'ad ina ganin gasa hannun za'a yi". Fad'in Anna.
"Gasawa kuma Anna?". Fu'ad ya fad'a a marairaice ya na kallon idanunta.
"Eh. Ba ka ji abunda ya ce ba. Ba karaya ba ce kuma ba tsagewar k'ashi ba ne. Buguwa ce. Saboda haka gasawa za'a yi sai a shafa mata maganin zafi".
"To Anna ina da maganin zafi a d'aki na, ba ri na d'auko". Ya fad'i hakane ta re da mik'ewa ya fice daga d'akin.
"Sister sannu kin ji". Fad'in Fanan kamar za ta yi kuka ta na kallon Binty da ke gunjin kuku.
"Ba ri ba d'ai bo ruwan zafi a kitchen, ki zauna da ita". Fad'in Anna ta re da nufar kitchen.

Fu'ad kuwa d'akin Julaibib ya so zuwa, nocking ya yi, sai da Julaibib d'in ya ba shi izinin shiga ka na ya shiga.
Zaune ya sa me shi a bakin gado ya rik'e kan shi da hannu bibbiyu daga shi sai dogon wandon jikinsa da kuma singlet.
D'ago jajayan idanuwan shi ya yi ta re da watsawa Fu'ad wani kallo sai da hantar cikinsa ya motsa. Mai da idanuwan shi ya yi ta re da lumshe su ka na ya mai da ya rufe.
"Kar tsautsayi ya sa ka k'ara d'aukar yarinyar nan, ka san dai ba muharramar ka ba ce. Ka ba ri Anna da Fanan su taimaka mata. Ka ji abunda na ce?".
Sai da Fu'ad ya had'iye wani bushasshen miyau har sai da Adams apple d'in shi ya motsa ka na ya ce,
"In sha Allah haka ba zai sa ke faruwa ba Ya Bibi".
Gyad'a kai kawai Julaibib ya yi ta re da mik'ewa ya nu fi toilet. Fu'ad na ganin haka, shi ma ya mik'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login