Showing 147001 words to 150000 words out of 162658 words

Chapter 50 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42921

dai lokacin Julaibib ya yi sallama a k'ofar d'akin.

Amsa masa sallamar su ka yi ta re da ba shi izinin shigowa.
Shiga ya yi ta re da mai man waje ya zauna, sai da ya gaishe su ka na ya ce,
"Daddy zan je gidan baba Muhammad in kai wa Yousouf maganinsa".
"Alhamdulillah! Da na tun tuni na ke son yi maka magana ka hanzarta ka kai masa don yaron na jin jiki sosai. Allah ya sa dai k'arshan wahalar kenan".
A ta re Alhaji Usman da Anna su ka amsa da "Ameen".
"Julaibib yaushe za ka fito da matar aure? Na gaji da ganin ka haka wallahi". Fad'in Alhaji Usman.
Sosa k'eya ya yi ta re sa sunkuyar da kai ka na ya ce,
"In sha Allah nan kusa daddy". Fad'in Julaibib.
"Ka bar shi ga shinan ai har k'anwar shi za ta yi ta bar shi ai". Fad'in Anna.
"Anna wata k'anwar ta wa ce za ta yi aure?" Fad'in Julaibib.
"Binty ce ta samu mijin aure". Fad'in Anna.
"Binty kuwa? Yaushe? Waye shi wannan mara kunyar? Kuma kun yarda Anna. Ni wallahi ban yarda ba yasin". Fad'in Julaibib hankali ta she.
Anna da Alhaji Usman gimtse dariyarsu su ka yi, ya yin da Anna ta ce,
"Kai a wa kenan da za ka ce baka yarda ba".
"Auranta zan yi, wallahi ina son ta tun ranar da fara ganinta. Anna dan Allah Ku taimake ni ka da in rasa Binty".
Anna da Alhaji Usman sun kasa rik'e dariyarsu su ka bushe da dariya.
Sai alokacin Julaibib ya ga ne tsokalarsa su ye yi. Saurin mik'ewa ya yi ta re da ficewa daga d'akin.

Kai tsaye gidan Alhaji Muhammad Ahlam ya nufa. Kasancewar ya kira alhaji Muhammad d'in ya shaida masa da zuwansa.
Ya na isowa aka shiga da shi d'akin da Yousouf ya ke a kwance kamar gawa.
Sai da yi addu'a sosai ka na ya bud'e bakinsa ta re da tsiyaya masa cikin bakinsa dakyar kasancewar ya dates bakinsa.
Cikin hukuncin ubangiji ko minti d'aya ba'a yi ba k'afafuwansa su ka fara motsi. Daga bisani ya d'aga hannunsa na dama. Can kuma ya juyo da kansa bakinsa na motsawa ya na karanto salati ta re da mik'ewa ya zauna digirgir.
Gaba d'aya gidan nan ya haukace da ihun murnan Yousouf ya dawo cikin hayyacinsa.
Ya na mik'ewa ya yi sujjada ta re da fashewa da kukan murna.
Nan aka yi ta murna da koke-koke.
Sab'ule jikinsa ya yi ta re da guduwa don barin y'an uwa su yi murna da kyau.

A hanyarsa na dawowa wajan traffic kasancewar an dakatar da shi. Juya kansa ya yi ya kalli gefe ta re mayar da kan shi ga titi. Cikin sauri ya k'ara kallon gefen da ya kalla. Tabbas ita ce dai dai lokacin kuma aka ba su umarni su wuce.
Da wani irin gudu ta figi motar, shi ma kuwa da gudu ya bi bayan motar kamar.
A wani katon gate ta yi horn mai gadi ya wangale mata gate d'in. Ta na danna hancin motar shi ma ya na biye da ita a baya.








*PAID BOOK 08128755583*
🌹 *81-82*🌹
...............Har zai tura motar cikin gidan sai kuma wani zuciyarsa ta hane sa. Dakatawa ya yi ta re da yin reverse ya yi parking ta re da fitowa daga cikin motar.
Wajan driver ya nufa da sauri wanda ke k'ok'arin rufe gate d'in.
"Bawan Allah dan Allah minti d'aya". Ya fad'a ya na d'an yin gaba.
Washe baki mai gadi ya yi ta re da fad'in,
"Ai na san mai ya kawo ki, ai Rauhiyya haka ta ke had'a go-slow a cikin gidan nan. D'aga kai gare ta ga yauk'i kamar kub'ewa. Amma ai na ga kai d'in ka had'u watak'ila kai ka yi da ce". Fad'in mai gadi ba ta re da an tambayesa ba.
"Nan ne gidan su kenan?". Fad'in Julaibib ya na kallon cikin gidan cike da tsananin mamakin kenan Binty twins ne.
"Eh nan ne gidan iyayanta". Fad'in mai gadi.
"Nagode da ma abunda zan tambayeka kenan". Fad'in Julaibib ta re da komawa wajan mota ya shiga.

Kai tsaye gida ya nufa cike da tunanuka cikin ran shi.
"Rauhiyyah!" Ya maimaita sunan cikin zuciyarsa ya na mamakin wannan wani irin suna ne. A duniyar aljanu Yousouf ya ce masa ainahin sunan Binty Rukhsana, sai ka ce wasu india, yanzu kuma ya ji wani wai Rauhiyyah.
Ya na isa gida ya haura sama. Anna na nan sai dai alhaji Usman bai nan.
Knocking bedroom d'inta ya yi, ita kuma ta ba shi izinin shiga.
"A'ah, har ka dawo?" Fad'in Anna.
"Anna ni fa ina tunanin na ga iyayan Binty na asali". Fad'in Julaibib.
Zaro idanuwa Anna ta yi ta na kallonsa ta re da fad'in,
"A ina kenan? Ya aka yi ka san su d'in iyayanta ne? Wani alama ka gani?". Fad'in Anna.
Nan ya kwashe labarin Rauhiyyah tun ranar da ya fara ganinta a wonderland har zuwa yau da ya bi ta a baya.
Anna har ta na watsar da kayan da ke hannunta wajan mik'ewa tsaye.
"Maza muje ka kai ni gidan yanzun nan". Ta fad'i hakane ta na lalubar wayarta a kan gado ta dannawa alhaji Usman Kira ta re da shaida masa abunda Julaibib ya fad'a mata.
"Ku jira gani nan zuwa yanzu mu tafi ta re". Fad'in Alhaji Usman.
Katse wayar Anna ta yi ta re da fitowa daga bedroom d'in Julaibib bi ye da ita a baya.
D'akin Binty Anna ta shiga ta re da fad'in,
"Binty fito za muje wani waje yanzu".
Caraf Fanan ta ce,
"Anna ni ma za ni dan Allah". To duk ku fito my tafi.
Gaba d'aya parlourn k'asa su ka sauko dai-dai lokacin da Barr Fu'ad ya shigo d'akin shi ma.
Nan Anna ta shiga shaida masa an gano iyayan Binty.
Sosai ya ji dad'in ya kuma ce ta re da shi za'a je. Fanan ma sai murna ta ke yi an gano iyayan Binty.
Binty kuwa ba za ka ce ka yanayin da ta ke ciki ba. Walau farin ciki ko akasin haka.
Cikakkiyar mintuna talatin ba'ayi ba Alhaji Usman ya shigo gidan.
"Ni fa duk na rud'e Na'ima, ya aka yi hakan to?". Fad'in alhaji Usman ya na kallon Anna.
"Shssssss! Muje ka wai" Fad'in Anna.
Gimtse sauran maganarsa ya yi, ya yin da Barr Fu'ad ya kalli Julaibib, shi kuma Julaibib ya kalli Anna da Daddy.
Anna d'aura fuska ta yi ta re da yin sama ta d'auko wannan kwarya da Yousouf ya baiwa Binty ka na ta fito. Fanan ta rik'o hannun Binty su ka fice.
Julaibib shi ne na k'arshan fita ya na son ga no abunda su Anna ke b'oyewa amma ya kasa kuma tabbas ya san da wata a k'asa.
Shi ya masu jagora har gidan da ya ga mai kama da Binty wato Rauhiyyah.
Horn ya yi mai gadi ya wangale gate su ka shi ga ta re da parking ka na gaba d'ayansu su ka fito.
Hannu Julaibib ya d'aga ta re da yafito mai gadi. Cikin sauri ya k'ariso wajansu.
"Ahh! Hajiya wallahi ban ga fitarki ba, ta ina ki ka fita to?". Fad'in mai gadi ya na kallon Binty.
D'auke kai Binty ta yi ba ta re da ta fahimce abunda mai gadin ya ke nufi ba.
"Dan Allah sallama za ka yi mana da mai gidan nan idan ya na nan".
Kallon Binty mai gafi ya sake yi ya na son cewa ga Rauhiyyah ai ba sai ya yi masu iso ba. Amma kuwa sai ya juya ta re da nufar cikin gidan.
Danna k'ararrawar k'ofar ya yi, second goma wani kyakkyawan yaro ya zo ya bud'e masa k'ofar.
"Fakarar yaron kirki kai ne?". Fad'in mai gadi.
"Ni ba sunana Fakahar ba Fakhri, understand?". Fad'in kyakkyawan yaron.
Washe baki mai gadi ya yi ta re da fad'in,
"To fakare, wasu bak'i ne a waje ke sallama da Babanka su na waje, amma fa har da auntynka Rauhiyyah".
"Aunty na na d'aki ta na wanka. Ba ita ba ce". Fad'in Fakhri.
"To je kira babanka ka ce ya yi bak'i". Fad'in mai gadi ba don ya yarda da abunda Fakri ya fad'a ba.
Zai juya kenan ya hango Rauhiyyah sanye da doguwar rigar material pitch colour kan ta sanye da hula mai kunnuwa hannunta rik'e da laptop ta na dannawa.
"Wa'innahu sulaimanu!". Fad'in mai gafi ta re da mitsittsike idanuwa ya na k'ara dallarosu ya na kallon Rauhiyyah da har ta zauna a kan kujera ta mai da laptop d'in bi sa cinyarta ta na danne-danne.
"Aunty Rauhiy, wai Bala ya ce wasu na nai man daddy kuma har da ke a wajan". Fad'in Fakhri.
D'ago da idanuwanta ta yi wanda ke d'auke da zara-zaran gashin idanuwa ta sauke a kan bakin k'ofar ta re da fad'in,
"Kai ban san shirme, zo ka wuce ka je ka fad'awa daddy ya yi bak'i awaje". Ta fad'i hakane ta re da mai da kallonta izuwa ga laptop d'in ta.
Cikin sauri mai gadi ya juya ta re da nufar wajan da su Binty su ke domin tabbatar wa idanuwansa abunda ya gani.
Har ya na tuntub'e saboda tsabar kallon da ya ke wa Binty.
"Matsowa kusa ya kamata ka yi sai ka k'are mata kallon da kyau". Fad'in Julaibib fuska a d'aure.
"Auu... Ummm amm yanzu zai fito in sha Allah". Mai gadi ya sake fad'i har ya na cin tuntub'e saboda kallon Binty da kuma mamakin kamannin da su ke yi da Rauhiyyah idan akwai abunda ya fi y'an biyu to sun fi haka. Tsayin, hasken fatan, kamannin da yanayin k'iran jikinsu duk iri d'aya ne.
Juyawa Binty ta yi ta had'a kai da mota dai-dai lokacin da wani mutum fari tass dogo siriri ya fito hannun shi sab'e da wata kyakkyawan yarinyar da ba za ta wuce 3years ba a kafad'arsa fuskansa fad'ad'e da farara.
"Assalamu alaikum, sannunku da zuwa". Ya fad'a ya na mai mik'awa Julaibib da Fu'ad hannu.
Daddy ma saurin mik'a masa hannunsa ya yi su ka yi musabaha. Anna ma ta yi saurin gaishe sa, dai-dai lokacin da Binty ta juyo kuma idanuwansu su ka had'u cikin na juna.
Yarinyar da ke hannunsa sai da ta kusa sub'ucewa Julaibib ya yi saurin taro ta.
Bakinsa na rawa ya ke nuna Binty da ita ma kallon na sa ta ke yi,
"Rauhiyyah! Wannan ai Rauhiyyah ce. Amma kuma ai a parlour na baro ta ta na danna laptop".
Dafasa Alhaji Usman ya yi ta re da fad'in,
"Kwantar da hankalinka, abunda ya kawo mu kenan, wannan ba Rauhiyyah ba ce, kamannin jini ka ke gani".
Shuru bawan Allahn nan yi jikinsa na b'ari ya na kuma k'ara kallon Binty da ita ma shi d'in ta ke kallo.
Da ky'ar ya iya bud'e baki ya ce,
"Muje daga ciki to". Ya fad'i hakane ta re da yin gaba su na biye da shi a baya. Amma duk tafiya sai ya juyo ya kalli Binty.
Parlourn bak'i ya kai su ka na ya fito kasancewar yarinyar da ya rik'o a ta na hannun Julaibib.
Har da gudu-gudu ya k'arisa gaban k'ofar part d'in cikin gidan ta re da murd'a handle d'in ya shiga. Da gudu ya haura sama. Rauhiyyah da ke danne-danne ta d'ago ta kallesa ta na mamakin mai ya faru ya saka Da-da gudu haka.
"Rahima fito fito ki zo muje ki ga abun al'ajabi da mamaki yau". Fad'in Da-da ya na mai ka mo hannun matarsa da ke bakin gado ta na warware wani zani.
Sakin zanin ta yi ta re da bin sa a baya. Su na saukowa parlourn ya kamo hannun Rauhiyyah da d'ayan hannunsa.
Aje laptop d'in ta yi ta re da bin sa ba ta re da ta ce ko mai ba.
Parlourn bak'in su ka isa gaba d'ayansu.
Numfashin Rahima kusan tsayawa cak ya yi sakamakon arba da Binty da ta yi. Yayin da Fu'ad, Binty, Fanan, da Anna su ka mik'e cike da zallar mamaki su na kallon Rauhiyyah da ke tsaye a bakin k'ofa.
"Inna lillahi!". Fad'in Fu'ad cike da wani irin mamaki kamannin Binty da Rauhiyyah.
"Binty! What am I seeing. Subhanallah! Wallahi komai iri d'aya". Fad'in Fanan.
Binty kuwa a hankali ta ke takawa har gaban Rauhiyyah ta re da kama hannunta hawaye na zuba daga idanuwanta.
Rauhiyyah kuwa kallon zallar mamaki ta ke yi wa Binty ko kyaftawa ba ta yi.
"Qalby da ma ba ni kad'ai ki ka haifa ba? Da ma mu twince ne? Ya aka yi haka?". Fad'in Rauhiyyah ta na kallon mahaifiyarta hawaye na ziraro daga idanuwanta.
Wani irin rushewa da kuka Rahima ta saki ta re da k'arisawa ta rungumesu duka a jikinta kamar ranta zai bar jikinta.
"Shikenan lokacin rabuwarmu ya yi Rauhiyy. Dan Allah ka da ku kwace Rauhiyy ku bar min ita har na aurar da ita". Fad'in Rahima ta na kuka sosai.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login