Showing 9001 words to 12000 words out of 269010 words
take yan gidan mu suka nuna bakin cikin su ka zancen.
Suke cewa makaratan kwana ko lalacewa may zaki koyo banda lalacewa a makarantan kwana bokon diya mace ko lalacewa.
Kai komai sun fada akan wanan zuwa karatun nawa karshe dai baba sha zuga sai cewa yayi abar zancen karatu don shi bai ga amfanin yin karatu ga ya mace ba.
Ina ji ina gani aka watsar da zancen karatu na ganin da gaske baba keyi na sulale jiki na tafi wurin gwago na fada mata komai.
Batai sanyi ga gwiwa ba ta sami babana a kasuwa don magana bai yi a gida nan dai gwago ta shawo kan shi har ya yarda amma da sharadin .
Baba hannun shi a ciki ko kwadalan shi ciki gwago tace taji ta dauka akwai Allah zakawo mafita.
Amma yace ba zai yarda da batun zuwa makarantan kwana ba gwago tace taji zasu samo jeka ka dawo na tafi.
Wannan shine dalilin zuwa na makaranta da nayi mutane gidan mu dai sun ga ina shirin ba su san komai ba.
Ranan da zan fara zuwa hankalin kowa a gidan ya tashi don sai suke zargin mahaifin mu ne yai min ko mai.
Nan ko ina ta saka shi a gaba da cewa munafucin banza da wofi idan an tanbaye shi kudin yace bai dashi amma ya dau ki yar gwal ya saka a makaranta don ran uwar ta yai dadi.
Ba dole ba yana gudun bacin ran uwar ta kada ta hana shi kwana da ita ya rasa jin dadin shi.
Da abin ya ishi baba yai ratsuwa har ya gaji shi ba dasanin shi bane baiba ma san wanda yai samo min makaranta ba amma nasu yarda ba.
Sai cewa yayi ya biya min din suda yake wa dayan su lalurori fa saiko fada dashi da inna har takai ga yin ya ji a gidan.
Yaya sani yace safiya ki shirya da kaina zan kaiki in ga wanda ya isa ya hana ki zuwa na gane yan bakin ciki ne mutanen gidan nan.
Da yaya sani muka tafi makaranta sai da yaga komai ya kamala ya dawo gida.
Tun wanan lokacin aiki ya rage man agidan namu saboda ban da lokacin zama a gida har su ganni suce in ma su aikin.
Sannu a hankali girma ya shi gana yanzu na fara ganewa bawai son ummi ne mahaifin mu ba yayi ba kawai dai shakun matan shine yake ji.
Na gane hakane ta yadda idan ya fakaici idon matan shi yake nuna kulawan shi kan ta har nama yakan dan ja ta da wasa ko da ba, a.
Sai dai idan matan shi sun gani ya kan dan yi kamay kamay kamar bashi ne daga karshe dai ya koma fada kamar bashi ba.
Kadai muke zaman mu da dadi ba dadin a gidan watarana mu kwana da farin ciki watarana akasin sa.
Sannu tashi na kamal aji uku zan shiga babba ajin aga da secondary sai ga gwago tazo daga lagos nan mukai ta murna da zuwan ta sai awan kararon bata ita kadai tazo muna ba.
Ita da zurian ta da maigidan tazo ganin mu nan aka shiga ina aka saka da ita da diya ta da maigidan ta don dai ba karamin son ta yan uwa keyi ba, in zata zo takan sayo abubuwan anfani tajo ma iyayyen mu da shi.
Nikan ina saurin naje makaranta don haka tsayawa nayi daga kofa na gaida su dan suna dakin mama ne zaune har mijin nata da yaran ta.
Take cewa wanagani kamar yar wurin Rabi haka koyaushe za a gan ki kamar ke kadai ke kiwo a gidan gaki tsatsab dake kamar wata wayyayiya.
Murmushi kawai nayi zantafi sai naji tace wanan ai takar ita koke kiyawu agidan.
Ta juya tana magana da mama bandaiji abin da suka fada ba nai tafiyana don ina saurin in tafi makaranta.
A kofan gida muka tarar da wani matashi yana shan taba zaune saman mota kallo daya nai mashi na kawar da kaina daga gareshi.
Sauri nake na wuce don da gani tare suke da gwago mu sai naji yace ke shiga ciki ki dabo min ruwa nasha.
Na dauka badani yake ba ina kokarin wuce wa naji ya sake cewa dake nake fa na juya baya na ko zanga wace yake magana da ita.
Sai naga babu kowa a tare dani na dan tsaya kadan yace ruwa nace ki debo min a ciki.
Juyawa nayi nakoma na debo mashi ruwan nakawo mashi ya kurba sau daya yake cewa wanan wani irin ruwa ne mara dadi.
Nace shi muke sha a gidan mu don haka shi ke gare mu, oho i see waya kaleni sama da kasa yake cewa karbi ki mayar .
Haushin sa ne yakama ni lokaci guda don ya rena muna wayau da arzikin gidan a haka dai na karba na wuce shi don warin taba duk ya isheni da hamami.
Na dawo zan wuce yake cewa dani ke yana kokarin kuna wani taban a bakin shi shigo kice wa su mum sufito haka nan dan Allah.
Kamar nace bazan tafi ba sai dai na juya zantafi sai gasu sun fito daga cikin uban na gaba suna biye a bayan su.
Nikan nawuce abina ban tsaya kara sauraren su ba don dama nakara zuwa islamiya duk da nasan bawai buguna za ayi ba amma ya kamata ace na isa a cikin lokaci.
Har na isa makaranta ban dana jin warin taban da aka sha a jiki na ba gani nake duk jikina warin taba yake kamar nice nashi taba din .
Mun dawo na debi kayan mu na wanke don ban samu wanke wa da rana ba aka raba tsaraban gwago ko wani daki aka bamu.
Saida na shigo dakin mune na samu tsaraban da gagwo ta kawo muna a gefe, na samu wuri na zauna gefe ina cewa da ummi.
Wanan mutumin dasu gwago suka zo dashi dazun baida tarbiya zama fa yayi kofar gida yana shan taba a gaban ko wa.
Ummi tace dani wa kina nufin ubale aishine dan gwago kuna fari duk sain an ni shi sunyi aure amma shi, shashanci ya na shi yi wai shi dan fari yana takama da zama cikin kabilu ya saje dasu.
Nace Allah ya kyauta amma kan wallahi bai yi ba wallahi mutun sakace wani ibom can.
Muna cikin magana mukaji fada ya kaule a tsakanin mama da inna kan kayan da gwagon mu ta kawo tsaraba inna ke cewa da mama wai tarage kayan ta basu abin da taga dama.
Mama ta bata amsa da cewa yar uwarki konawa ina yar uwa nane dai ko kaya kuma abinda naga dama kenan na bayar inkina so ki karba inbaki so zaki iya mayar.
Mama tace idai kayane je ki ta ci saukin abindai muma muna da yan uwa bake kadai keda su ba balla ki kawo muna bakar magana.
Muna daki da ummi muna sauraren su har suka sude bamu leko ba sukayi suka kare ba mu leka waje ba.
Washe gari kuma da safe suka aza sabon fitina a gidan baba na dakin inna ya fito yake cewa daga yanzu indai rabo zai kawo fitina kowa ya rike abin sa a zauna lafiya.
Da haka karshen fitinan ya mutu kowa in yaga dama ya rike kayan shi ba dole araba wa saura inna tace yafi nono fari.
Mu dai namu dasu ido don sun fi kusa wanda yace zai shiga fadan su a ciki zai kwana minti goma yai kadan aga sun shirya tsakanin su.
A yau asabar bamu zuwa makaranta don haka na shirya cikin kayan da mama lami ta ba ina son zuwa gaida kawata da bata da lafiya.
Wanan ne karo na farko da na sa kayan a gidan mu don basu san ni da kayan ba nan sukayo mani ca da idanuwan su naji mama tana fadin.
A yau kwaliya akaci haka yau sai ina da wanan adon nai murmushi kawai ba tare da na bata ansa ba sai naji inna na fadin ke ma dai yaya da wani zance ki.
Yarinya kekaga tana wanan irn kwalliya haka ai kin san abinda take yi inba mashin shine ai banza ya kai zomo suwa ke ma kin san aida wallakin wai goro cikin miya.
Muka hada ido da ummi na sai taimin da alama da ido na kyaleta na kara shiryawa nake cewa zan tafi tare da yi masu sallama.
Inna tace dama diya mace inta dadani namiji ai ba tafiba hankalinta bai taba kwanciya yawon gantalin za, a ake sallaman mu.
Kai akwai ki da wani zance wallahi ina safiya da ga wani saurayi kyalle ta dai da nacin son karatu a rayuwan ta inji mama ke fada mata haka na.
Ta ja tsaki tace ai ku ke kara zugata wanda baida lokacin kan shi a gida kulun boka watafi son karatu adaiyi shaani kawai wai an cuci na kauye.
Na fito gida ina tunanen kallamin inna ba zaka taba jin kalman alheri abakin ta ba in ba yayan ta bane sai na sheri.
Ita da bakin ta take fadi wata rana yarinya ga kyau ga wanka amma babu saurayi yau kuma ta can za ta kuma ce maza naka bi.
Naje gidan su Amina na samu bata da lafiya sosai amma ta samu sauki na dan zauna da ita mukai hira nawani lakaci na mike zani gida don kar na dade Inna tace sai da ta zubar nadawo kuma.
Mun fito tare da Amina donta dan taka ta walwale jikin ta muna tafe muna hira inda muke tafiya a hankali ina bata labarin text din da kayi muna, bata nan yadda ya kaya.
Hon din motane ya damay mu daga bayan mu da kara daga ni har ita ba wanda ya juya dan gani ko wa nene mai mator kuma bai daina hon din ba.
Ganin ba zamu tsaya ba yasa shi fito wa a motar ya biyo mu, sallama yai muna duk muka juya a lokaci daya muna kallon shi.
Nikan a zato na sun san juna ne sai kawai na fara tafiya na barsu tare ban tsaya ba kada naja wa kaina magana ban yiba ance nayi ina ga na tsaya.
Sai naji yace don Allah malama ko zaki taimaka taimaka min da yar uwar ki ta saurare ni min ti biyu in ba damuwa.
Safiya dake ake magana inji Amina, na juyo nace wani a cikin mamaki yace nasan badaidai ba ne na tare ku a hanya.
Amma kuma dole yasa na tsada ku a hanya yanzu don idan kun tafi ban san ina zan kara haduwa daku ba.
Nace gaskiya bazan tsaya ba sunana ya baci ga ban za a saman hanya sai yai murmushi yace naga alama ai amma don Allah kibani dan lokaci nasan wani abu gare ki.
Allah daya ke hada mu dashi har da Amina din yasa na tsaya badon na so ba ya ce sunana sulaiman ni dan garin nan ne saidai ba anan nake ba.
Ina fatan zaki bani amsa ga tambaya a wurin ki don Allah ida bazaki damu ba zan so nasan gidan ku don na gabatar da kaina.
Gaskiya malam kayi hakkuri saboda karatu nake yi sai an jima nan nabar su tsaye awurin na wuce.
Ya dan rintse idanuwa shi tare da sauka da ajiya zuciya yana mai sauke num fashi , ya dan yi murmushi tare da duban Amina dake gefen shi tsaye yace.
Idan ba damuwa ki tai makeni da noba ta kokuma gidan su zai fi sauki a gare ni nan dai yabawa Amina tausayi tabashi addresen gida yai mata godiya ta tafi.
Ban da lafiya da fatan zakuyi hakuri da mistake din kuka gani anan kwana uku ina typing ban iya hadawa ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , ,
🧕🏿4️⃣ 🧕🏿
SEENABU MAKAWA
DON ALLAH NAMIJI KAYA SHIGA DON MATAN MUTANE MUKA KA TARA ANAN INKA KA SHIGA ALLAH YA SAKA MU NA
DON ALLAH YAR UWA ABIN DUNIYA KAR YA JAKI GA HALAKA IN KI BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYABA DON BAZAN YAFE MAKI HAKKI NABA, , , ,
Dare ne kowa na zaune a tsakar gida saboda zafi da duhu da akwai yaro ya shigo yana kwala sallama a kofa.
Baba na gida ya amsa yaron yace wai ana sallama a waje sai baba yace yaya Nura ya duba yagani.
Zuwa can ya dawo yace wai wani wai wurin Safiya yazo amma ya ba son ganin ka.
Inna tai caraf tace Safiya kodai Ainau, Safiya ina taga saurayin da zai mata sallama, ga wayannen ta tanan wake maganan ta.
Yace nidai abinda ya fada min kenan na fada yasamu wuri ya zauna yaci gaba dacin abincin sa.
Inna tace tashi maza Ainau jeki ki gani wake sallama dacewan Ainau yar wurin Mama taje ta ga ba wurin ta bane tadawo kafin Ainau ta dawo ta shige da yar ta mairo daki.
Sukayi ku ku ku da ita saiga Aina tadawo tana fadin Inna ba wurina bane wannan fa dangaye ne ke sallama a waje.
Saiga Mairo ta fito zata har takai kofa taji ance ke dakata wurin ki aka zo ko kuwa tace zan duba na gani ne.
Maza koma ki zauna yaya sani ne ke wannan maganan da mairo daga dakin Inna ta daka mashi tsawa tace kabari tafita ta duba mana ko ita akewa sallama.
Ya ce yaushe mairo ta koma Safiya a gidan nan ne ke bana son rainin woyo maza kidawo wurin nan tun ranki bai baci ba.
Sanin hali yasa ta juwoyo simi simi ta da dawo cikin gida ta zauna ya mike ya fita zuwa kofan gida wurin bakon da kansa.
Duk wanan kace nacen magana da suke faman yi kunnen mu nida ummi sukeyin sa, kallo daya zai kayi min kagane a rikice nake.
Ummi dai batai min magana ba don tsaban tsoro duk jikina ya dauki rawa a lokaci daya can najiyo muryan yaya sani yana kwala min kira.
A rikice na fito daga dakin na rabe gefe guda a tsugunne lokaci guda yake cewa dani, akwai wanda kukai magana dashi zai zo gida ne ?
Gaba daya hankalin yan gidan mu ya dawo gare mu suna sauraren mu a hankali na bude bakina zanyi magana .
Naji Inna tace dani ke yan zuwa har da masu mota kike tsayawa don tsaban miskilan da munafunci irin naki na gado.
Nasoma rantsuwa baki na rawa ina fadi wallahi tallahi na rantse da Allah inna bantaba magana dakowa waye ba
Ji nayi yaya sani yace Safiya na amsa da sauri da naam ya ce tashi kije inda ake maki sallama waje.
Ai gara dake daza ki jawa mai mata kika jawo muna su diyan su da kara da doki duk zuwa yake wurin su fa.
Maza tashi tafi kada yaga an tsaida shi kin dade baki fito ba ya dauka bakya nan ne.
Na mike gwaiwa da sanyi da ce tau yaya nufi kofar gidan wurin wanda aka ce din yana min sallama wanda yaja min zagi da zargi agida uwurin mutanen gidan mu.
A kofan gida nahango shi tsaye ya jingina jiki da mota hannu daya kuma ya dafa motar shi dashi ya tsura wa kofar gidan mu ido.
Yana gani na ya dan muskuta tsayin shi yagyara da kyau har na iso kusa dashi.
Fuskana kamar zanyi kuka a lokacin nazo na tsaya sai yace dani ba gaisuwa yan mata kamar baki na na ciwo nace dashi Ina wuni ?
Shima cike da yanga yace min lafiya lau yan mata,
Wai halan ba ke kadai bane Safiya a gidan naku sai naga wasu yan mata nata fitowa da sunan safiya mana.
Saida na dan bata lokaci kafin nace ni kadai ne mana kawai da sun fito ne sun dauka wiri su aka zo yaron yai matuwa yace safiya don sun ga ba wanda ke aikowa kirana sai yau.
Ya nisa tare da cewa "kai, kice ni din nazo a sa, a ke nan nine zan bude fage in bar tarihi.
To amma naso naga baba ne da kaina koda yake ai naga yayan mu ya bani go ahead naci gaba da zuwa .
Kallon sa nakeyi ta gefen ido ya yagyara tsayuwar shi da kya yace na samu goyon baya kai tsaye ke na kinga duk lokacin da nake son ganin ki ina iya zuwa.
Na turo baki ina cewa indai na amince da hakan ko nifa na fada maka karatu nake son yi ban da lokacin tsayawa soyayya.
Ba zabin ki nake son ba illa yaka ki bani hadin kai shikaratu nufi ne na Allah.
Don haka ki bar Allah yai maki zabi kar ki raja, a a bangare daya don kinfi son karatu kice gareshi zaki tsaya.
Kunya bakin ciki da takaici suka sauka min a lokaci daya na rasa amsa da zanbashi kawai sai hawaye suka dinga zubo min .