Showing 267001 words to 269010 words out of 269010 words

Chapter 90 - Bahagon Rayuwa By Makawa

04 Dec 2025

13344

har ya fara karatu a can .
Ranan da muka dawo gida da yamma yaya Saadu yazo gidan yake fada min an bugo mai waya jikin gwago ya tsanan ta sosai don haka gobe zai tafi.
Na jajanta mashi tare da fatan Allah ya bata lafiya yadan dade wurin uncle suna fira ya tafi don dare yayi a lokacin .
Yaran ke rikice a gaban mu akan remote din tv nace wa Abba ya bar ma Azahabi kallo na uncle yayi cikin tsawa yace ma yaron ya kawo mashi remote din ya kora su zuwa dakin mommy wai suje ai masu shirin barci su kwanta dare yayi.
Bayan sun wuce ne don suna matukar tsoron shi ta juyo gare ni dama nasan ba zai barni ba sai na samu rabona a gurin kan hukuncin da na yanke din ga yaran.
Yace yanzu kinga kinyi wa Abba adalci ke nan a hakan shine babba fa ama kika ce karami ya rike remote din yanzu ne kike son sulaiman din fiye da Abba.
Uncle ba hakana bane nace gani nayi shine ya fara dauka shiyasa nace ya bar mai kai ya girgiza min yace ina lura dake kin fison shi akan Abba din don kirikiri yanzu a gabana kuka zalunce shi.
Nace cikin dago kaina ina kallon shi Zalunci uncle akan may zamu zalunce shi kuma wai ke baki san hakan da kike yi ba zalunci ne maimakon ki karbe duk a hannun su sai kice yabarwa kanin shi.
Shiru nayi kada zancen yayi nisa a tsakanin mu ya mike yana fadin irin haka sai ya kawo raini a tsakanin su balle yana ganin ya cin mashi da girma yanzu uncle har wanan yasan wanj abu raini a yanzu.
Yace a haka ake tasowa dashi ki taimake ni ki hada kan yayan nan don Allah kada ko bayan mu su samu matsala idan kan su yana hade babu wanda zai iya shiga tsakanin ko gaba.
Nasan inda maganan shi ya nufa yadda ya taso da yan uwan shi ne baison hakan ya faru da diyan shi daki ya wuce ni kuma na mike na shiga dakin nasu don in ga kwanciyan su.
Na samu mommy har ta shirya su ana rikici wurin kwanciya nace su kwanta su rike junan su sai suyi barcin a tare ba tare da sun rungumi mommy ba da suke ma fada.
Kwana biyu muka shirya muka tafi bauchi ganin hajiya taji dadin wannan ziyaran don mun dade bamu zo gida ba irin haka.
Banzo da kanne na badon makaranta da suke zuwa nan na barsu da mommy Abuja da yaran kawai nazo garin.
Mun dan zaga wurin dagi da sauran yan uwa mun gai dasu muna bauchi kwana hudu da zuwa bauchi sai ga sakon daddy sun yi nutsu a cikin ruwa inda suke aiki.
A ranan uncle da wasu yan uwa suka wuce lagas sun barmu hankali a tashe a gida sai zuwa safe muka samu labarin rashin dadddy din da akayi.
Hankali ya tashi sosai dole uncle yace mu biyo jirgi mu dawo Abuja in gari ya waye mu nufi lagos din don har wasu sun tafi ko.
Yadda yace haka mukayi hankali a tashe muka iso gida nike fadawa mommy abinda ke faruwa hankalinta ya tashi matuka da jin labari mara dadi daya dawo damu ba shiri.
Mun isa Abuja washe gari har lokacin ba a kawo gawan shi gida ba suna abinsu na yan kaki da gawan .
Mun shigo anty suna falo zaune gani na yasa ta sake wani kuka mai tsuma rai nima rungumay ta nayi ina kukan rashin da mukayi na daddy mutumin arziki.
Sai yamma suka bada gawan su nan aka shirya masu bi harda mu don zamu dafa ma anty baya.
Mun kwasa mun koma bauchi da gawan a jirgi guda da yan uwa isar mu da gawan ya tayar da hankalin yan uwa da abokan arziki.
Zuwa safe aka kaishi gidan shi na gaskiya har rana ban samu ganin uncle ba mu zaune a dakin anty cikin tashin hankali don ni na zamay mata kamar yar uwarta na jini a wurin duk da ga yan uwan nata a kusa da ita.
Shigowan yan uwan daddy maza a cikin su har da uncle sukayi gaisiwa tare da addua ga mamacin nan sukai dan bayani akan gobe zasu koma lagos dan ana son ganin su acan akan komai na daddy din.
Suna fita nabi bayan shi dole ya dan tsaya min na iso kallo daya nayi mai naga a lokaci daya duk ya sauya min a idona uncle kako ci wani abu na iya fadi.
Kai ya girgiza min yace yanzun dai nake son in karya magani fa nace dashi da sauri yace ban sha ba safiya ji nayi ina son in kebe dashi don ya samu ya karya yasha maganin shi kada ai biyu babu.
Su hajiya baaba ma suna gidan don haka na karbi makulli a hannun ta na fito muka wuce gida a sai da na zuba mai abinci na dauko mai maganin mu na bashi.
Yana zaune ya dafe kan shi a hankali na iso gare shi na zauna a gefen shi kuka yake yi nace uncle kayi hakkuri kowa yayi rashi amma ansan kai da anty akafi yi ma wanan rashin .
Yace safiya daddy mutumin kirki ne ya tafi ya barni a lokacin da nafi bukatan shi a tare dani rugumay shi nayi don maganan kara mashi bakin ciki yakeyi.
Sai da naga ya natsu sosai naji yace kinyi waya da mommy yaran na lafiya nace lafiya suke sai dai Abba ne tace yau ya tashi da mura ta bashi maganin shi.
Gobe zamu tafi lagos kuma da madam zamu tafi ina ga gida zaki koma don yaran sai ke tsaya Abuja ya kamata ki huta yanzu jigilan yayi maki yawa hakana.
Nace uncle ai kai keda jigila ga rashi ga ba hutu a tare da kai yace yaya za a yi dole nine zan bi komai nashi yanzu har komai ya daidaita.
Hari aka kawo masu na bazata shine ya zama ajalinsu haka su goma sha bakwai suka rasu a lokacin .
Allah dai ya jikan daddy nace yace amin yanzu ban san plain din madam ba nasan dai a can lagos din zata zauna saboda aikin ta ko kuma ta dawo arewa da aikin ina ganin zaifi mata sauki kusa da gida.
Haka dai sukai ta jigilan akan alamuran daddy har komai ya kammala ya dawo gida bayan wasu watanni aka nenawa anty trasfer ta dawo Abuja da aiki tare da yaranta.
Jikin gwago ya kiya baba yace a dawo da ita gida ayi na gargajiya a gani gashi basu jittuwa da Samira duk kokarin da take mata gwago bata gani sai zagi kawai ke shiga tsakanin su.
Haka yasa hankalin yaya Saadu yafi kwantawa da akaita gida don yawan fitinan da ake samu da samira duk da kokarin samira din.
An kaita gida ba afi wata biyu ba Allah ya amshi ranta muka je gida gaisuwa nan na samu zance aure yaya Sani ya tashi sai gina yake tayi inda zai saka matan shi.
Don yace bai son zama ko kusa da gida don gudun samun matsala da inna duk da inna yanzun tayi laushi sosai da fitina har in nazo takan dauki su Abba tayi masu wanka da sauran su.
Uncle yazo da ma, aikatasu sai dai basu kwana ba suka juya ranan mu sai da mukai kwana biyu muka dawo gwago ba karamin dukiya ta bari ba wa yayan ta.
Yaya Saadu yace yabarwa kannen shi mata idan sun samu mazan aure ai masu aure dashi sadiya ta dawo da zama wurin yaya Saadu.
Tare da mama da inna muka sauke farali inna ta saka hakora uku a bakin ta inda mama ta saka biyu sunyi dani in saka nace uncle yace baya so sai suka kyale ni.
A wurin jefa inna ta tashi mutuwa da kyat muka cetota wanan abin ya kara tsorata inna duk inda na jefa kafana tana biye dani.
Mu dawo lafiya saida suka kwana biyu a wurin mu suka wuce gida don ta Abuja suka tafi sai da muka dawo muka je gida bukin yaya Sani da yar wurin mai unguwar mu.
Abubuwa da yawa suna faruwa inda girma kuma ke kara shiga uncle da nauyi na yan uwa da abokan arziki idan aka kwana biyu kuma ya debe mo zuwa waje mu huta.
Bayan shekara hudu na sake haihuwa yar budurwa taci sunan hajiya baaba muna kiranta da baaba din sai na dakatar da haihuwan jikin kan dan motsa muna wani lokaci wani lokaci kuma sai ka gan mu kamar ba mu ba.
Yanzu nasan cuta baya kashi sai kwana ya kare do ga daddy mai lafiya ya tafi ya barmu gwago na ta tafi ta barmu muna rayuwan mu a cikin salama.
Yarana suna nan duk lafiyayun su basu da wata matsala a tare da su sun girma sun zama kyawawa dasu gwanin ban sha awa.
Ina kula da yan uwana da yan uwan miji nice na zama jigo a gidan mu inda ake girmama ni kamar wata babba a cikin zurian mu komai za ayi sai da shawarana.
Yanzu inna taba kai bori ya hau sai bi da lalami a tsakanin har in wani yaron ta yayi wani abin tana kawo min kara in yi mashi fada.
Rayuwan mu sosai yaci gaba don uncle ya bunkasa sosai ni da anty mun dinke sosai dawowan ta Abuja mun zama kamar uwa daya da ita.
Uncle ya dawo daga dubai bamu san da zuwan shi ba sai ganin shi mukayi ya sagalo jaket din shi a kafada Azahabi ya fara ganin shi .
Lokacin ina zaune dasu a dining suna cin abincin safe daddy daya ce yasamu duban kofa da gudu yaran suka nufe shi ya rugumay su duka ukun a jikin shi sai da ya gama sun batan su ya dago yana kallo na ina tsaye na taso taron shi na harde hannaye na wuri guda.
Yace madam Family yaya kuke nadan lumshe idona tare da yowa inda suke nima na rugumay su kit naji maimu ta dauke mu hoto daga inda take tsaye.

Alhamdullahi nan na kawo karshen labari na bahaggon rayuwa wata rana baki wataran fari haka rayuwan bawa yake tafiya har lokacin da naba da labarina gare ku muna nan raye da yaran mu lafiya lau cutar jikin mu bai nakasa mu ba.
Muna rayuwan mu normal kamar kowa ana bin mu kuma don baiwan arzikin mijina da muke ci tankar babu wani cuta a tare damu babu mai kyaman mu a cikin alumma komai daidai mukeyi da yan uwa.
Nima mai rubuta labarin na kare da cewa cuta ba mutuwa bane sai kwanan bawa ya kare uban giji yasa mu cika da imani a tare da mu.
Wanda na batawa ya yafe min don Allah.

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login