Showing 6001 words to 9000 words out of 269010 words
kwaso duk da tsofi ne amma bana taba barin su da dauda kullun na dawo sai na wanke muna su na sha idan sun bushe na buge nakai daki kafin mu wuce islamiya.
Do ba halin na barsu nazo na iske an masu ba daidai ba ko tukunya za a sauke dasu ake saukewa idan an tashi aiki in suna shanye a waje.
Mun gama shirin mu muka shirya zuwa islamiya mun fito ke nan yaya sani yana zaune a daban su na yan matasa yace dani ke Safiya zo nan.
Jiki na min bari na nufe shi sai naji yace dani kunci abinci nace eh yaya munci yace to ki saurareni kiji daga yau duk wanda kika ga zai daki ummin ki ki nemo sanda kema ki buga mashi ninace a mutu har liman.
Da sauri na dago kai ina mamakin kalamin shi yace eh don abin yai yawa daga magana sai duka irin haka itama Rabin na fada mata ta daina zama ana mata wanan cin fuskan tun bakuyi wayo ba har gashi kun tasa ana bu daya a gidan.
Yace baki ji may Nura ya fada bane kowa ma ai uwarshi ya sani don haka ninace ki rotsa mutum koma waye.
Yace maza ku tafi kada ku makara zance a gun yaya sani muka samu sauki dakin mu don yafi kowa zama tantiri a gidan mu.
Sai gashi kuma Allah ya dora mu a kan shi yana jin mu a gidan ko dan ladabin da muke mashi ne oho ?
Don zamu ganshi komai yawan abokan shi sai mun duka mun gaida shi idan kaya muka gani a hannun shi zamu karba a hannun shi mukai dakin su.
Shima idan yar dahuwar shi ya samo ni zai nema na dafa mai kuma ko ya bani bana karba nace ya bar shi, sai idan ya zare min ido zan karba naci ko na bawa kan ne na suci.
Tun wanan fadan da akayi gidsn mu ummin mu ta dan samu baki idan ana mata wanin abin cin fuska zata zage ta mayar da martani kamar yadda akai mata ba dadi din itama.
Abin dake ci mun rai shine irin yadda gamu da yawa a gidan mu amma kowa a ware yake ba mai hurda da wanin shi dan dama tsakanin yaran dakin mama dana Inna akwai dan shiri a tsakanin su.
Nice dai babu halin idan suna zaune ko suna wanin abin da ya shafe yara mata nace zanzo wurin yanzu zakaji sun fara hattarana.
Suna fadin ke kuma may kika zo yi nan munafuka kawai sai wata tace muguwa mai irin halin uwar ta kawai in ba gulma ba may kika zo saurare nan.
Dole zan bar wurin don zagi da hattara irin haka yasa ko suna abin su bana shiga shirgin su ina daki da ummi na ko ina wani aikin a waje sai dai abinka da yaro inayi ina sauraren su sai na manta na saka baki wata rana su kyale ni wata rana kuma nasha ba dadi garesu.
In kaji dariya na ko farin cikina muna tare da kanne na ko kuma na fita zuwa makaranta ne.
Idan baba ya shigo yaga bana cikin su yanzu zai fara fada dani wai ina tsabbare kaina a cikin yan uwana.
Sai kaji Inna tace mugun hali ya ci may idan batai hakan ba ko uwarta baka ganin komai nata a makidance takeyi shi don dai kawai duniya ta zage mu.
Ace muna gallaza mata ita da uwarta a gidan kasan mutum baida gadon ka amma yana da na maganan ka yanzu.
Sai kaji baba ya amsa da naga alama ai an koya mata halin tsiya ta iya itama.
To ba dole ba kullun suna daki ana mata hudubar tsiya a kai dabiar da ba zai amfane ka ba ko yau tana tsabbare sun hada kai da uwar ta a daki suna wance tayi min abu kaza don may bazata tashi da mugun hali ba kuwa ?
Abin yana ban mamaki don sai inga ai komai a baiyyane yake ai a gidan ni dai a iya sani wani fitina bai tasowa ace da Safiya a cikin sa.
Ko wani ya kawo kara daga waje yace ai Safiya tai mun wani abin suko ko yaushe cikin sallama mashi ake ana kawo karan su gun shi.
Sai dai abin mamaki wanan bai sa yayyena maza su kini ba a gidan namu don su basu matsa min kuma ba su yarda ai min sheri a gaban su yanzu zasu ce zasu daki yarinya idan tai masu tsiya tun dai yaya sani.
Kuma duk wanan abin idan sun dan samo kudin su gun Ummina zasu nufo dashi ta baye masu har ya kare.
Da haka har ummi ke dan samu tana basu shawaran abinda zasu yi wanda zai amfane su a rayuwan su, sai kuma iyayyen nasu suka koma cewa.
Wani sallon yaudara ne don ta raba su da yayan su ummi ta dauko sukai mata ahir da yaran su shikan yaya sani da ya samu labari tun a nan yau zaune tsakar gida yana fadin.
Oho wai ni za aiwa yau don a raba ni da mai taimaka min a dinga kwace min kudi to ban yarda ba babu wanda zai hanani bawa maman safiya a jiyan kudi na a gidan nan.
Ke mama da kike fadin haka ba nan Nura ya sayo akuya ba ku kai masa sheri aka sayar da akuyan akace mai ya bata.
Cikin tsawa mama tace dashi kai kada ka kawo min diban albarka idan kaje kayo shaye shayen kane kake son saukewa a kaina bazaka sha da dadi ba yanzu na saka yara na suyi maka tsinanen duka a gidan nan.
Wuf daya yayi ya yanko reshen darbejiyan dake baya gidan mu yana fadin yau naga shegen dan ki daya isa ya tabani a gidan nan idan ba a kwashi gawan shi ba shege nake.
Yau kuwa zan gwada maki halin mashayan da kika kira min aiko yai cikin su a kofan dakin ta da take tsaye da diyan ta a take suka watse.
Suna rige rigen shiga daki wani na ture wani daga kofan dakin wurin shiga dakin don yai masu mai ka uwa da wabi baki daya.
Ashe fadan bai kare ba sai ga Inna ta na cewa idan har yaron na yana shaye shaye ke ko diyan ki barayin kororo ne da karuwai, waye bai san abin da suke a gari ba har akuyan da kike fadin an sace dake da diyan ki kuka sace shi ai.
Nan fada ya kaure tsakanin ranan dai gidan mu babu dadi tonon asiri zalla suka dinga yiwa junan su har abin dake a boye saida kowa yaji shi gare su.
Baba na kasuwa dole aka kirashi shi yazo ya kashe wanan wutar fitinar da ya ruru a gidan don gaba daya yaya Sani ya haukace masu a gidan.
Iyakarmu kallo da saure sai washe gari da baba ya kira sulhu da safe kuma suka so su dora laifin gun ummi na mai farin jini a gare su.
A nan ma yaya Sani baiyi shiru ba yace may ye laifin ta a ciki kudi dai ne har gobe ko kaya ita zanbawa a jiya ni babu ruwa na da zancen kishin ku.
Dole inna tana ji tana gani suka saka mashi ido don ya riga da ya kangare ba mai iya lankwasa shi a halin yanzu.
Idan ya shigo gida har da gaiyya yake jan ummi na da hira a cewan shi haushin mama yake ji don itace ke kulla duk wani makirci a gidan.
Ita ko Inna bata tsayawa saurare sai ta hau ta zauna a kai daga baya kuma mama ta zamay jikin ta ta nuna bada ita akayi zancen ba ta bar Inna a ciki.
Mu dai a gun mu har gobe gaba dayan su a yan uwa muka dauke su ba mu banbanta a tsakanin mu dukkan su a yan uwa muke daukan su.
Sai dai su a gun su ba wani canji a gare mu dasu har gobe halin yana nan na yan ubanci da suke nuna muna a gidan.
Mun zama su shanun ware ko bare da suke kyankyamin mu daga cikin su suna bakin ciki su bude ido su ga dan dakin mu na wani abin ci gaban rayuwa yanzu sheri zai tashi a tsakani sai anga bayan abin an durkusa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , , , , ,
🧕🏿3️⃣ 🧕🏿
FREE PAGE, , ,
SEENABU MAKAWA, , ,
NA ROKE KI DAN ALLAH DON SON MANZON RAHAMA IDAN DA ZUCIYA BIYU ZAKI SHIGO GROUP DIN KADA KI SHIGA DON ALLAH DON BAZAN YAFE MAKI BA WANDA KIKA TURAWA HAKKIN YANA AKAN KI YAR UWA DON ALLAH KI HAKKURI DA DAUKAN HAKKI AKAN NOVEL DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE KIN SANI BA PUBLISH NOVEL BANE DA KI KE FADI KIN BIYA NE DON ALLAH MU SAHIRCE WA JUNA AKAN HAKA YAR UWA KAN ABINDUNIYA DAFATAN ZAKI KU FAHINCE NI.
Yau alhamis bamu shiga islamiya don haka na ke son zuwa ziyara gidan yan uwan mahaifiyar mu dake a cikin gari.
Zaune nake ina kwaliya a kofan dakin mu yayin da mutane gidan mu ke ta aiyu kan su na yau da kullu a cikin su har da ummi na wacce ke wanke kofi.
Sallama aka shigo dashi gidan dashi shi ne ya dauki hankalin kowa a gidan baki daya tare da amsawa.
A, a mutanen lagos yau she agarin abinda su maman mu ke fada ke nan mu yara muka shiga sannu da zuwa.
Ta dan tsaya a tsakar gida suna gaisawa sama sama da mutanen gidan da ga nan ta kwasa tai dakin mama,
Daya bayan daya ake shiga gaida ita tana amsawa don sanin muhinmanci ta ga iyayye mu baki daya.
Gwago kulu ke nan kauna ne ga mama kuma yar uwa ga mahaifin mu don mama da mahaifin mu yan uwane dukkan su auren gida ne sukayi irin matar fari zabin iyayye din nan.
Haka yasa mama ke shimfida mulkin ta yadda taso a cikin gidan daga ita har yaran ta ko magana ake a gidan wanda ya shafi gida zakiji mama tace mu din kujera ne dole a bi mu.
Don da mijina aka samay ni ko anki ko an so dole ne a gan mu a gidan babu yadda za yi damu dan mu yandagi ne.
Watarana idan tana irin wannan habaicin Inna takan biye mata suyi tayi sai sun gaji har ta kan ce ban ga macen da zato tace zata shifida min doka ba a gida na.
Sai dai duk wannan haukan ga may wayau da hankali yasan Inna ce ke shimfida mulkin ta a gidan don baba a can hankalin shi yafi karkata.
Ni dai nakan ce tsoro ne don wani lokaci zaka ga ya juya gun wata da zaran inna taga haka yau zata birkice mashi da masifan dare daban na rana daban saiya dawo a kan ta.
Duk wani dan uwan mahaifin mu da zai za gidan wirin mama zai yadda zangon shi ba zai tafi wani daki ba sai in wani dalili ya kawo mai shi.
Wannan abin yana kona wa inna rai don ita mace ce mai son taga komai ita ne a kan gaba a gidan namu.
Saida na kanmala kwaliyana na saka hijjab dina na karasa kofan mama ina fadin sannu da zuwa gwago alokacin sun hade kai da mama suna magana a hankali kasancewan su biyu ne a dakin ki.
Cikin dan hanzari ta amsa min da yawwa na juya zan tafi sai take cewa wa nake gani kamar sai tai shiru can tace ba yar wurin Rabi bane ?
Mama tace itace tace, mana tace ikon Allah girman dan mutum baida wuya har yaushe yaushe aka haifi yarinya nan diba yanzu yadda takai da girma.
Sai naji mama tace ta biyo tsawon kafan uwar tane kisan Rabi ba baya ba wurin tsawo shine suka kwaso ai duk haka yaran suke in kin gansu.
Nidai na tafi ba abina ban tsaya jin sauran abinda zasu fada ba don dai zancen bai kare ba na bar su akai.
Dariya naji sun kwashe dashi wanda nasan wani sheri aka fada wanda yai dadi har sukayi hakan .
Mu Huda muka fita da kannena gidan gwagon mahaifiyar mu muka fara zuwa inda muka samu taro na arziki ta rasa ida zata saka mu.
Haka mu ke gani idan munje gun ta muna samun taro yadda ya kamata sabanin dagin mahaifin mu, wanda basu ma san da zaman mu ba nake gani.
A binci ta shiga girka wa don idan muje wuni muke a gidan ta, nafito na kama mata aiki yadda ya kama ta har muka kan mala yin komai.
Abinda bamu saba ba gidan mu an cika muna kwano da shinkfa da mai da yaji sai ci muke yi hannu baka hannu akushi.
Ga zobo mai sayi data sayo muna mu sha dashi mun kai kat na kwashe kayan da mukai aiki da amfani dasu da wanda mukaci abin ci akin sa.
Na gyara mata gida sai nace da ita zamu mu gaida su mama watau diyan ta ke nan dake aure a cikin uguwa.
Tace kada mu dade don mu koma gida da wuri mun tafi inda can ma muka samu taro yadda ya kama ta sun bamu alheri su man shafi da sabulu da omo da dan kudi muna ta murna mun samu kyau ta .
Gwago ma tai muna abin arziki muka dawo gida bayan sallah la, asar cike da zudin kyautan bajin ta da muka samu.
Muna tajin dadi muka nuna wa ummi alherin da tan uwanta suka kai muna ta sani tare da fadin shine abin dayasa bani son kuna zuwa gidan su don dawai niya kuke kai masu.
Kani yai caraf yace ummi cewa sukayi fa mu dinga zuwa ko yaushe kuma kikece damu kada mu koma abamu .
Gaba daya dariya muka sa mai ummi tace damu tare da dubana nida nake da wayo a cikin su yawan zuwa zai sa su gaji daku ne ku zauna matsayin da Allah aje ku Allah zai dube mu.
Jikina yai sanyi don na fahinci may ummi take nufi din a sanyaye na ce in sha Allahu ummi baza kara zuwa mu kai masu nauyi ba haka.
Dan abinda muka samu ummi ta ware min wani abu acikin sa waina kara jari dashi na sana, a na da nakeyi kada mu kashe a baki daya.
Wanan kudin shine sillar da har takai mun da samun sauki a dakin mu don a hankali na fara sarrafa kudin biyar na kamowa goma gama na zama ashirin ashirin ya koma wazo har zuwa sama.
Idan baka raina sana, a tau watarana sai ya koma maka babba don tun ina dan madara har na koma ina soya ruwa ana saye a gida.
Sai gashi har nawaje suna shigowa saye na hada da aya da sauran makulasa sai sanaa ya koma na ummi na.
Sannu sannu ina sana,ar har muka koma mangyada da sauran abin amfani kudi na shigo muna.
Sai hassada da kyashi ya shigo a cikin wa yan gidan mu nan kuma bamu da sauran shakat gare su zasu ce damu ganin muna dan sana,an dake kawo mu kudi ya muke son yi masu gani gani.
Sai suka da habaici ya tashi har zance yakai gun baba na magana kadan yanzu zai yo cikin ummi da zagi yace wai mutane suna shigo mai gida don su din ga lekan may asirin gida suna fita waje suna fadi.
Nan mama ta turza don kan taki yarda da zancen baba na wanga karon ta ko hankace mashi da fitina tana cewa ai da takoma in irin halin da ta fito gara ta hankura dashi ta tafi inda ake son cigaban ta yafi mata don ta ganne cigaban ta akewa hassada bakomai ba.
Inda watane ke wanan sana, ar aiba za hana ba amma don anga tana samu za ai mata bakin ciki ga sana,an ta, kowa na dan sana,an shi cikin gida bai yi magana ba, sai nata ne za ia wa bakin ciki.
Da haka zancen ya mutu karshe mama ta ce ya kyale ta taita sana an ta tunda kowa na saman sanaar ashi badon aina tasa ba dole ta kyale ummi ta ci gaba da sana, an ta tana na kallo ba yarda zata yi a gidan.
Wanan ke nan ya wuce saura wani kama don ummi ta kyatare wanan karon daga kaidin ta.
Wanan abin da akeyi ina yar shekara goma sha uku da haihuwa amma duk idon gidan mu na ga kaina gaba dayan su kamai yan yazu ace safiya ce.
Koban ji ban gani ba don dai kawai ai min fada suji dadi yanzo zasu jawo abinda za ai min fadi din .
Duk wani aiki aike yi mai dadi da akasin sa duk ni zan yi amma duk wanan ban tsira akan shi ba don cewa suke wai lalaci da raggaci yai min yawa.
A haka jebawan mu shiga secondary yafito inda naci makarantan kwana aiko