Showing 171001 words to 174000 words out of 244445 words

Chapter 58 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16449

wayarta a sama a parlournta”

Ta so ta lab’e amma sai ta yi gaba kawai but da ta dawo
tabbas taga kmr an tab’a flas d’in
Although ba ta ga Kausar ta zuba wani abun ba cake ma ta tarar da ita tana ci dan lokacin da ta dawo sai da ta d’an lab’e,amma kwata kwata
ita dai bata yarda da coffee d’inba kuma abunda ya sake saka mata zargin Kausar d’in yadda ta dinga cewa ta d’auka “ta kai masa” “ta d’auka ta kai masa”bayan ta dawo d’in.
Gashi ta ga ta ci uban kwalliya
dukda doguwar rigar abaya mai bottons ce a jikinta amma ta fahimci kamar k’ananan kaya ne ata ciki saboda har cinyarta sai da ta hango a waje
d’azun data zauna tana cin cake sannan ta gyara gashinta
ta sha jambaki
ga uban k’amshi………
Sannan har waje ta biyota
sai da ta ga ta shigo nan tukunna ta tsaya a wajen ta
fara wasa da flowers tana sinsinawa kmr irin dama abunda ta fito yi kenan……..



Yadda Yashjub ya ga gwaggon ta yi ne yasa yad’anji a jikinshi watak’il akwai abunda take so ya gaya masa amma tana jin tsoro…tashi d’aya lissafinsa ya basa ko dai akan case d’in Manu ne tunda ai tare suke a gidan har da ita shi fita yake yi dan haka dole ita ta ga wani abun…..ko kuma maybe taana so ta yi masa basaja ta kare kanta ne.!
Yana wannan tunanin yana sipping coffee d’in ahankali ahankali kafin ya d’auki maganin ciwon kai daga aljihun sa ya b’alle ya sha ya d’an had’a da cake kad’an daga haka yayi gyatsa yai hamdala ya fara k’ok’arin mik’ewa dan ya ji har an shiga sallah.

Yana mikewa ya ji kansa ya wani irin sarawa wanda har sai da hakan ya kaishi ga kaiwa k’asa ya durk’usa a nan bakin kujerar.
Jiri ya farayi had’e da wani yanayi na daban da ya shiga tashi d’aya abun har abun tsoro!
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”ya shiga maimaitawa dan tashi d’aya gaban sa ya fara fad’uwa saboda zai iya cewa bai tab’a tsintar kansa a irin haka tashi d’aya ba!

“Ya subahanaAllah
Ya furta a fili… ga Manu a asibiti a ransa yace”da na sani ban sha ruwan zafin nan ba na san duk shine sila
amman kuma tou jirin na menene??”
Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya san me bashi amsa ba.

Ganin abun fa gaba yakeyi
yasanya yayi sauri ya lalubo makullin motarsa….ya san Manubiya ba ta da lafiya but yana buk’atar kasancewa tare da ita ta hakan ne kad’ai zai iya tseratar da kansa daga fad’awa halaka….saboda this thing da ya ke ji is dangerous.

Dukda bayajin zai iya yin tuk’i
a halin da yake ciki ga kuma
jiri amma gara ya gwada…kar ya je ya yi abunda zai binne kan shi da ransa.

Da k’arfi ya mik’e tsaye…dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi dishi.

Yana mik’ewa ya ji an fara knocking…Addua ya fara yi akan Allah ya sa ba gwaggwo bace ta dawo dan ba gwaggwo ba ko Iya ce
Indai mace ce to fa akwai matsala muddin suka kasance waje d’aya a tashin hankalin nan da bala’in da yake a ciki.

Jin bai yi magana ba ya sa Kausar ta shigo a hankali ta mayar da k’ofar ta d’an tura ta
barta a bude ba tare da ta saka key ba.


Da farko dishi dishi ya fara ganinta sai da ta matso daff da shi tukunna ya fahimci ashe Kausar ce….tunda yake a rayuwarsa Kausar bata tab’a burgesa irin na yau ba…sanye
take da wata arniyar gown ta roba iya guiwa
Fitted
Red
ga stones a jiki sai walwali sukeyi,ta rambad’a jan jambaki
tasha kwalli!gashi ta gyara gashinta ta yi parking ta yi styling gaban da jel jelar
kuma tana reto a tsakiyar bayanta ga wani uban k’amshi da take zubawa.

Dakyar ya iya cewa”Kausar.”
Lumsassun idanunsa suna sake lumshewa.
Wata sabuwar k’aunarsa ce ta lullub’e Kausar a take a hankali ta matso ta sa hannunta a daidai saitin zuciyarsa tana shafawa kafin tace”Dukda kai da Daddy kunce a baka space amma na kasa yin hakan Ya Yash,i‘ve to come see you!(check on you),situation d’in da na ganka ya kasa barin brain d’ina.”
Ta k’arashe maganar cikin wata shuumar murya
sannan cikin shagwab’a da turo Baki kafin a hankali ta d’an matso jikinsa.

Karkarwa jikinsa ya fara yi dan haka ya tureta da dukkannin ragowar k’arfin da yake a jikin sa,cikin fushi yace mata
“Stay away!!!”
Ya daka mata tsawa.

Daga nan ya fara takawa
da niyyar fita amma sai k’ofofin suka juye masa,parlourn ma gaba d’aya
ya fara juyawa a kwakwalwarsa…ya ma kasa gane wacce ce k’ofar fita!.

Dasauri ta sake zagayowa
ta tsaya a gabansa tace”me ya sameka?In kira doctor ne?”

Tunani yayi tabbas idan doctor ya zo maybe ya bashi magani
dan zuwa yanzu ya san ba zai iya driving zuwa inda Manubiya take ba dan haka da sauri yace
“Yes pls ki kira harda Yasmeen”.ya fad’i hakan a hankali.

Dan sake matsowa jikinsa ta yi tace”Okay mu je in kaika
Bedroom sai in kirasa”
Daga haka ta matso sosai
batayi wata wata ba ta yi hugging d’insa.

Wasu tagwayen ajiyar zuciya ta ji yana sauk’ewa a jere jere kafin ya d’ago hannuwansa
gaba d’aya biyun ya rungume ta da dukkannin ragowar k’arfin sa.
Wani farin ciki ne ya lullub’e Kausar tashi d’aya hawaye suka fara ambaliya a fuskarta
tsabar farin ciki…a hankali ba don ta na so ba tace”Let me go
In kira doctor pls Ya Yashhh”
Ta fad’i maganar cikin sigar da ta sanya Yash ya sake rungumeta tsam a jikinsa…..
Shi dai daganan jin sa ganinsa da komai nasa suka d’auke
D’iff!!!
Ba shi ya farkaba sai……



Daddy ya yi tunanin zai ga Yashjub a masallaci amman shiru..
Dukdda ya san yana cikin damuwa amma ya kamata ace ya je Masjid ai….

Akwai maganganun da yake so su yi ya d’an kwantar masa da hankali tun d’azun amma sai ya hak’ura ya bari akan idan sun had’u a dinner sai su yi dan ya san maybe sai ya huta ya yi dinner tukunna zai wuce asibitin.

Shiruuu nan ma har aka fara dinner babu Yash babu alamun shi kuma wani abun mamakin babu Kausar.
Tunani ya yi ko dai ya wuce gidansa sai kuma ya tuna ai yanzunma kafin ya shigo Sai da ya ga motarsa.

Yassir kasa zama dinner d’in ma yayi saboda tashin hankali da kishi….ya yi trusting Kausar
amman the fact that
zata kwanta da wani na**d
a same bed and blanket yasanya gaba d’aya ya gaza
sukuni..babu damar ya yi magana yanzu sai tace bai yarda da ita ba!and hakan shine kad’ai mafitarsu ba su da
mafita sama da wannan!
Kai kawo ya dinga yi
har sai da 40 minutes d’in da suka riga suka tsara ya cika tukunna ya sauk’o k’asan lokacin ana tsakiyar cin abinci
shi a tunaninsa ma an gama…

Tunda aka zauna dinner Mommy da Baba larai suka sha jinin jikinsu dan kallar kallon tsanar da Daddy yake jifan mommy da shi sai da ya saka su a al’ajabi.


Da kyar Yassir ya dake ya gaida Daddy daga haka ya juya ya ja kujera ya zauna ya fara zuba abinci a ransa yana
adduar Allah yasa wani ya yi masa maganarta dan idan ya yi da kansa to ya b’ata komai.

Yassira ce tace
“Am Yassir Kausar tana sama ne?”

Kallon ta yayi yana jin wani sanyi a ransa a fili kuma sai ya sake tamke fuska kawai ya d’auke kai.

Mommy ce tace mishi “ba tambayar ka takeyi ba?”
Dan itama shirun na Kausar d’in ya d’an dameta saboda missing dinner ba aladar Kausar baceba babu abunda ta tsana irin ta kwanta bacci da empty stomach.


Ajiyar zuciya ya sauk’e ya ajjiye spoon d’in
tukunna yace
Mommy pls..kar ki yi mini maganarta ku rabu da ni kawai.
Ni da na san ma kuna nan da ba zan sak’k’o ba…”
Daga haka ya ci gaba da chin abincin sa.

“Hmm”kawai junior yace”daga haka ya d’auke kai bai ce komai ba.

Ajjiye spoon d’in sa Daddy ya yi daga nan ya gyara zama
ya yi gyaran murya ya kalli Yassir yace
“Kai!
Ina Yashjub?”


Ahankali ya d’ago ya kalli Daddy yace
“Yana side d’in sa”

“Okay ni kuma ka raina ni ko?”
Mommy ta fad’a.

Kamar irin an dameshin nan ya ajjiye cokalin gaba d’aya ya ture abincin sannan yace”Mommy Kausar ta tafi side d’in Yashjub dubo sa tun d’azu kafin magrib!”
Sai kuma ya yi shiruuu kamar mai tunanin wani abun kafin ya kalli Daddy yace
“Which is taking too long
Allah dai ya sa lafiya”
Sai kuma ya mik’e da sauri ya fita ya nufi side d’in Yashjub.
Gaba d’ayansu mik’ewa suka yi suma suka bi bayanshi har Yahanasu
……..
Tun a bakin corridor din da zai sadaka da babban parlourn gidan suka tsinci doguwar rigar Kausar…da k’arfi k’irjin Daddy ya buga dan haka suka tura k’ofar suka shige.
A tsaye suka tarar da Yassir a parlour ya k’urawa rigar Kausar ido wadda ke nan a yashe a tsakar parlourn.
Daddy yana gani tun kafin ragowar mutanen wajen su gani ya juya ya kalli Yadira da su Yusra yace musu
“Ku fita!”

K’urawa Yassir ido kawai Junior ya yi…a rayuwarsa wallahi ko tari Yassir ya yi ya san me yake nufi shiyasa tun d’azu da ya sauk’o ya san he’s up to somethin yanzu kuwa da ya ga sun fara tsintar kayayyakin kausar tun kafin a tafi conclusion ya fahimci komai…Tabbas Yassir ya tabbata d’an iska…but bari komai ya lafa zai titsiyeshi ya gaya masa reason d’insu shi da Kausar behind all of this if it’s lame Allah sai ya tona musu asiri,kasancewarsa best friend d’insa ba shi zai sa ya tsaya yana ji yana gani a k’ulla wa Yashjub sharrin da bai ji ba bai gani ba.

Yusra za ta yi magana Daddy yace”Fita nace!”
Da k’arfi…
Ficewa suka yi ita da Ya’isha da Junior, tun kafin ace wani abun Munirat ma ta bi bayan su Yusra hakama Yasmeen.

Da sauri Yasira da Ya’isha
dan karma a koresu suma suka shiga suka wuce suka nufi d’akin da ya ke a nan k’asan wanda suka ga k’ofar a d’an bud’e….



Kausar tana jin Yassir ya turo k’ofa ya shigo ta yi tsaki..
tabbas ta san Yassir da gangan ya bata k’ank’anin lokaci ta samu ta shirya komai iyakar wanda suka tsara..gashi yanzu ko gama hakin jan Yashjub ba ta yi ba har ya zo if not ai ba ta ga dalilin da zai hanata appreciating wannan expensive and special moment d’inba.
Ahankali ta yi kissing Yashjub for almost 5 seconds kafin
ta lalubo sachet water d’in dayake ajjiye a gefenta ta kawo dede setin fuskar su
ta matsa da k’arfin gaske
ya fashe da k’arfi toss!! A kan fuskarsa.


…..wata bagwariyar nannnauyar ajiyar zuciya
Yashjub ya sauk’e, tun lokacin da ya rungume Kausar
ya fara ganin dishi dishi
tace
“Zata kaisa d’aki ta kira Doctor tun daga wannan lokacin jin sa da ganinsa suka d’auke sai yanzu tukunna suka dawo

Abu d’aya ne ya basa tsananin mamaki d’ayan kuma ya firgita sa ya saka shi a tashin hankali….na farko yadda gaba d’aya wannan mahaukaciyar desire d’in da tsananin ciwon kai da jiri suka d’auke d’iff lokaci guda
Komai ya dauke
Garau yake jinshi…
Sai kuma abu na biyu wanda ya firgita sa dan indai ba mafarki yakeyi ba tou tabbas yau mummunar bak’ar rana ce a garesa saboda kamar naked ya ke jinsa daga shi har Kausar d’in wadda tashi d’aya ya fahimci da ita yake
tare tunda itan ce d’azu daga shi sai ita kuma har yanzu ga k’amshin turaren ta nan.

A hankali ya d’an fara k’ok’arin bud’e idanunsa domin ya tabbatar ya ji Yasira
tace
“Subahanallah!!”
Sai kuma yaji
Mutane sun taho
rututu!! gaba d’aya sun antayo cikin d’akin…


Runtse idanun naasa kawai yayi ya koma ya kwanta a kan
Kausar d’in dan bai ma san me zai yi ba!
In Banda sunayen Allah babu abunda yake karantowa yana ji kamar ya shak’e kansa!


Juyawa Ummi ta yi ta fita hankalinta a tsanain tashe ranta a masifar b’ace.
Tana fita Baba Larai ma ta fita…
Yahanasu kuwa kuka ta fashe da shi…..a ranta tace
“wannan wacce iriyar k’addara ce Yash da Manu suke ciki daga an toshe wannan sai wannan!waenna irin mugayen mutane ne haka Ubangiji ya taundumosu a tsakiyar su!!”
Ba za ta iya ci gaba da ganin wannan abun bak’in ciki takaici da tashin hankali ba shiyasa kawai ta juya ta fita dan tabbas idan ta ci gaba da zama to za ta iya kashe Kausar a take.

Kallonsu Yassira Daddy yayi kafin yace”kuma sai na ce muku ku fita!!!
Ba na kori kowa ba tun d’azu???”
Ya daka musu tsawa

Dasauri duk suka fice
d’akin ya rage daga Mommy Daddy Kausar Yash sai Yassir
wanda idanunshi suka kad’a sukayi jazir.
Suna had’a ido da
Kausar ta fashe da wani irin kuka sannan ta fara k’ok’arin tashi
Cikin kukan tace
“Yassir pls
Wallahi
Forcing d’ina ya yi.”

D’aga mata hannu kawai yayi,hawaye suna zirara daga idanunsa sai ya bud’e baki zai yi magana sai ya kasa
Yayi haka yafi sau uku
kafin kawai ya juya ya fita.

Tausayin shi ne ya lullub’e Daddy…ya fara ji kamar ya rufe su da duka…cikin tsananin b’acin rai yace”Ki tattara kayanki ki bar gidan nan!
kafin nan da awa d’aya tak!”.
Daga haka ya juya ya fice


Dasauri Mommy ta bisa har ya kai tsakaiyar parlour
ta rik’o hannunsa tace
“Wallahi babu inda za ta je!
Wai mai yake damunka ne?
Mai ya sa a ko da yaushe idan Abu ya faru sai ka huce a kan Kausar ne?
Laifin ta ne?
In dan ma tanada laifi shi kuma Yashjub fa?
Kuma fa kana ji tace forcing d’inta yayi a gabansa amman bai musa ba!”

Da mamaki Daddy yake kallonta kafin yace”Khadija ke wacce iriyar dabbar uwa ce???
Baki ganin abunda Yarinyar nan take mayar da ya’yan ki?
Ta lalata Yassir yanzu ta koma kan Yashjub mutum da aurensa!
Brothers fa
kuma
Ya’yan ki Khadijah
amman bakya gani???”
Ya yi mata tambayar kamar zai
rufeta da duka tsabar takaici da tsana!
Bai jira Jin amsartaba yace
“My decision is final!
Kausar za ta bar mini gida kafin nan da awa d’aya tun kafin ta fara bin y’ay’ana mata tana lalata musu tarbiyyar da na sha wahala wajen yi,tunda ta riga ta gama lalata mazan…ba ku Isa ba wallahi,da ke da Kausar ba ku Isa ku tarwatsa mini zuri’a ba.”
Daga haka ya juya zai fita ta sake ruk’o hannunsa
Ido cikin ido tace
“Nima bari ka ji decision d’ina!babu inda Kausar za ta je!idan kuma ka nace akan hakan
Tou
Tabbas nima zan bita.”

Dasauri yace”Alhamdulillah!!!
abunda na dad’e Ina son gani kenan!
Bari kiji in gaya miki
Khadija ranar da za ki bar gidan nan ki bar cikin rayuwata
Itace
Ranar da nake kwad’ayin gani all my life!!”

Duk yadda Mommy ta so daurewa sai da hawaye suka zubo mata,cikin d’aci da treat tace”shikenan zan tafi!da
Yassira
Yasmeen
Ya’isha
Yusra
da Yadira
sannan zan had’a har da Yahanasu tunda ni ce na zame mata uwa!
Yashjub da Yassir ma na san shekaru na suna yin gaba tare za mu zauna da su da matayensu,kaga wa gari ya waya?kai ne zaka k’are Kai d’aya kwal daga kai sai Ummi da agolar y’ar da wadda ba zata ji tausayinka idan ka tsufa ba!”
Cikin son fahimtar wani abu tace”kuma wallahi sai na ganka a prison tukunna hankalina zai kwanta dan sai duniya ta ji abunda ka aikata ga amaryar ka Khadija,ka ce Mallan Lawal yana raye bai dad’e da rasuwa ba na ji shi babu hakkinsa a kanka amma Khadijah kam wallahi sai ka yi paying for what you did!babu abunda zan b’oyewa duniya ko Yahanasu kowa sai ya san abunda ka yi.Tunda ka nuna saboda hakan ne kake tolerating d’ina a gidan nan ko?
To yau nima gashi na fito maka a mutum!
If you like ka cigaba da treatning d’ina ko Kausar akan barin gidan nan ka ga ikon Allah.Ka riga ka nuna mini babu so ko k’auna a tsakanina da kai dan haka nima ba zan
ji tausayinka kamar shekarun baya ba,fito na fito za mu yi da kai a cikin gidan nan daga yau!
It’s either ka hak’ura ka zauna da ni da Kausar
ko kuma ka sha mamaki!.”

Kallonta kawai Daddy yake yi zuciyarsa ta na tunzura shi da ya shak’e ta ta mutu kowa ya huta.
Tabbas duk abunda Babba ya hango Yaro bai Isa ya gani ba Hajiya mama ta yi gaskiya dan gashi tun yanzu ya fahimci tsaff Mommy zata rabashi da ya’yan shi kuma kamar yadda ta fad’a tsaff za ta kaishi prison
wanda shima abunda yake so d’in kenan amman ba zai tafi prison ya bar y’ay’ansa a hannunta babu wanda yayi aure ba,damage d’in da ta yi ma kad’ai ya isa shi ya kamata ya dage ya gyara ba wai ya bada goyon baya wajen bata k’ofa ta ci gaba da aikata b’arna ga ahalinsa ba….

Ajiyar zuciya Mommy ta shiga sauk’ewa a b’oye a yadda Daddy ya yi shiru bai tanka mata game da case d’in Khadija ba ta fahimci abunda take tunani ba haka bane dan yadda ransa yake a b’acen nan da ta yi maganar inda ace yana zargintane da ya yi mata zazzagar kwanyo…to amma me yasa ya yi hacking wayarta sannan me yasa yake yi mata kallon da kowa ya gani ya san kallon tsana ne tsagwaronsa!!.


Daddy kuwa ya riga ya tsara zai yi yadda Hajiya Mama tace ne shiyasa har zuciya ta ciyo shi zai yi ta ta k’are a take sai kuma kawai ya yi shiru ya danne zuciyar sa da kyar ya zuba mata ido kawai tsanarta tana sake shigarsa.
Suna tsaye a haka…suka fara jiyo ihun Kausar.

a minute before now.

Su Daddy suna fita Yashjub ya mik’e ya zauna,
Jallabiyarsa da ya gani a yashe a k’asa ya d’auka ya saka tukunna ya janye bargon daga jikinsa.

Ya daina jin jiri ya daina ciwon kai sannan desire d’in ma ya tafi amman fa dishi dishi yake gani tsabar tashin hankali.

Yan juyowa ya yi sauri ya d’auke kansa,saboda a yadda ya yaye bargon ya barta a haka take still tana nan a kwance ko kyalle bata ja ta rufa ba.
Wata kalar arniyar tsanar ta ce ta lullub’esa tashi d’aya!bai san lokacin da ya yi kanta ba ya hau kifa mata mari ba ji ba gani!
Bayason dukan mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login