Showing 96001 words to 99000 words out of 244445 words

Chapter 33 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16426

nasa tukunna ya kalli Ya Musbah ya ci gaba da cewa”shikenan, tunda ka nace…sai ka je ka samu Inna ka ce mata kanaso za ka dawo da Baraka.”

Da d’an zafi Ya Musbah yace
‘’Ya za ka ce in je in samu Innaa?bayan abunda Baraka ta yi mata taya kake expecting in je ince mata zan dawo da ita?ai wannan aikin ka ne
Kai ka san ta inda za ka b’ullowa al’amarin Kai ne za ka taimaka mini shiyasa na ke gaya maka,saboda ka taimakeni‘’

Shiruu kawai Ya Nafi’u ya yi yana nazartar sa…bayaso ya zargi Baraka amma kuma kana ganin Ya Musbah da zantukan sa tashi d’aya zaka fahimci tabbas aikin asiri ne ba haka ta bar sa ba.
Ya taso masa da maganar Inna ne saboda yanaso ya tuno masa da abunda Baraka ta yi wa mahaifiyarsa ya ji zafin abun ya daina tunanin dawo da ita
amman it’s like kamar ma an yi deleting takaicin da wannan ranar ta k’unsa dan kwata kwata bai hango haushi ko takaicin Baraka a idanunsa ba
bayaga zazzafar soyayyarta da tausayinta dayake hangowa a tattare da shi.

“Ba laifinta bane itama,sharrin shaid’an ne amma ta yi mini alk’awarin ba za ta sake ba har hak’uri tace za ta zo ta bayar,ka yarda da ni Nafi’u Baraka ta shiryu tun ba yau ba”
Ya sake jin muryar Ya Musbah.

Kallonsa ya yi da kyau kafin yace”Tun ba yau ba?kenan tun ba yau ba kuke waya kake zuwa???”
Bai basa damar cewa komai ba yace”Am Musbahu…
ba zan baka goyon baya ba sannan ba zan hanaka ba.As far as I can remember na san kanada hankali da sanin abun da ya kamata dan haka ka yi
duk abunda ka ga dama.”
Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice ya wuce cikin gida ya bar Ya Musbah a nan zaune shi kad’ai.

Ya jima sosai a cikin motar tukunna ya zare makullin ya rufe motar shima ya nufi cikin gidan.
A zaune ya same shi suna raha wasa da dariya shi da su Inna,
yana shigowa Ya Nafi’u ya mik’e ya yi wa su Inna sallama suka wuce shi da iyalinsa…ko ba a fad’a ba tashi d’aya zaka fahimci Ya Nafi’u haushin Ya Musbah yakeji shiyasa dukkan su suka shiga al’ajabi dan abu ne wanda bai tab’a faruwa ba.
Suna fita Baba ya kalli Ya Musbah yace
“Tashi ka bi sa ku sasanta.”
Zai yi magana yace
“Jeka”
Saboda dama shi tunda aka ce masa suna waje suna magana ya san akwai wani abun,yanzu kuma da ya ga hakan sai ya fahimci tabbas sab’ani suka samu…maybe ma shiyasa kwana biyu yake ta ganin Musbahun a cikin damuwa…

Ba su jima da fita ba Baba ma ya mik’e ya fita bayan an tabbatar masa da cewa su Manubiya suna lafiya,daganan Muhsin yace “bara ya je d’akin su”Jidda kuma ta tafi raka Siyama…
Suna fita Siyama tace “ni kam ina ma ace Ammi za ta
hak’ura wallahi…kinga d’azu fa dakyar ya iya jan motarsa ya shiga gida!,ko ba ki lura da shi a time d’in da muke shirin shigowa gida ba lokacin shima yana k’okarin shiga gida.
Kinga yadda ya rame kuwa a cikin kwana hud’u gask…..”

Kukan da Jidda ta fashe mata da shi ne yasanya Siyaman yin shiru,kafin da sauri tace “Innalillahi yi hak’uri Jidda mai ya yi zafi??”

Cikin kuka tace
‘’Siyama dan Allah ki daina min maganar Al‘Ameen dan Allah!kin san Ammin sa ba za ta tab’a amincewa ba ko ta amince ma su Ya Musbah suma yadda suka zuciya na san ba za su bada goyon baya ba.
Ki daina yi min zancen sa ki taimaka min in samu in fitar da shi a raina dan Allah.”

Shiruu Siyama ta yi tana mai jin tausayinta yana sake rufeta…
rana d’aya tak ta d’an samu moment da Najeeb ta kuma fahimci k’udirin sa a kanta amman ba k’aramin Namijin k’ok’ari take yi wajen dannawa calls d’in sa reject ba.
Shiyasa ta ke ganin k’ok’arin Jidda na hak’ura da Al’ameen bayan shekaru wajen hud’u da suka yi a tare kawai yanzu tashi d’aya an raba su,tabbas abun da ciwo.

Rarrashin ta ta shiga yi tare da bata baki dakyar Jiddan ta d’an dawo dai dai dan a kwana biyun nan ita kad’ai tasan halin da take ciki..kwanakin baya ta ji haushi ta ji takaici amman kuma tun da ta gansa gaba d’aya sai ta ji ta yafe masa.
Kuma tabbas a yadda ta ga ya yi ta san yana da uzuri sannan uzurin na sa mai k’arfi ne…she just wants to hear him out,forgive forget and be with him….
Tana wannan tunanin suka fara takawa towards wajen su Siyama kowa ta yi shiru da abunda yake damunta a haka suka k’arasa Siyama ta zaro makulli daga jakarta ta bud’e
Parlourn dan maman nata
bata nan ta tafi gidan suna.

Suna shiga ko gama zama ba su yi ba
Siyama tace
“Kina ganin mu kira Manu mu yi magana ko mu je gidanta bayan kwana biyu?”

Shiruu Jidda ta yi kafin tace
“Sai dai zuwa anjima mu kirata dan kinsan tafiya za su yi tace jibi ne da asuba.
Amman zakice na gaya miki dangin mijin nan nata ne suka sakata kuka ba ruwan Ya Yash
kinga yadda jikin sa yayi sanyi
ai ba laifin sa bane.”

A hankali Siyama ta nemi guri ta zauna sannan tace
“I hope so dan ba na so su fara samun matsala da shi.Allah dai ya sa ta gaya mana.”

Cike da assurance Jidda tace “za ta fad’a inshaaAllah..idan na bayar da shawara ne sai mu bata idan kuma munga ya fi k’arfin mu sai mu sanar da su Innaa dan ba zai yiu mu zuba ido ba…kwata kwata fa yau ne ta yi 4 days a gidan.

Ahankali Siyama tace
“InshaaAllah ma k’aramin abu ne Allah ya sa ba wani babban issue bane ba.”

Ya Musbah yana fita daidai motar su Nafi’u tana tashi,sarai ya san ya gan sa amman haka ya murza giya ya ja sukayi gaba.
Shiruu ya yi kawai ya fad’a duniyar tunani a hankali ya nema waje ya zauna akan d’an dakalin k’ofar gidan ya buga uban tagumi…Bai tab’a samun matsala da Nafi’u ba tunda yake sai a kan Baraka,shiyasa ya ke jin tsoron tunkarar su Baba ma da maganar dan ya san suma akwai matsala
shi kuma a yadda yake jin Baraka in har aka hana sa ya maida ita to tabbas akwai matsala Babba.
Ya jima sosai yana tunani a wajen ya ga motar Yashjub ta yi parking a daidai k’ofar gidan.Dama tunda suka nufo sa ya gane su dan haka ya d’an k’ura wa motar ido kafin ya mik’e tsaye bayan sun gama parking d’in.

Murmushi ya yi ganin yadda Manubiya ta fito har tana d’an tuntub’e shi kuma Yash d’in yana cewa ta yi a hankalin yana mai zagaya wa da sauri inda take.
Yana gani Yadira ta bud’e k’ofa ta fito dan haka ya d’auke kai ya maida hankalin sa ga Yashjub yana mai ce masa “Ashe kuna tafe barka da zuwa mu shiga daga ciki mana”
murmushi Yashjub ya yi yana mai jin dad’in yadda ya Musbah ya amshesa sam bai rik’e kukan da ya baro Manubiya tanayi a rai ba.
Cikin jin dad’i ya cewa ya Musbah “ya gajiyar ku”

“Alhamdulillah”yace kafin cikin yanayin sigar zolaya yace”Yashjub!a k’aida fa sai mace ta yi wata uku take zuwa ganin gida daganan kuma ita da ta dawo sai ta haihu”
Wani kallo Manubiya ta yi masa kamar za ta yi kuka
sai kuma ta fara bubbuga k’afa tana cewa “dan Allah kar ka fad’a ya ji,Allah ba zai d’auka da wasa kake ba”

Da sauri ya tsare gida yace
“Au ke a naki tunanin wasa ne?”
Sai kuma ya kalli Yash yace
“Dagaske Yash ba a zuwa sai bayan wata uku”

Jin jina kai Yashjub ya yi shima in a serious way yace
‘’ai ban sani ba,yanzu kam mun riga mun zo dama kuma shima saboda za mu yi tafiya ne shine muka zo yi muku sallama,amman daga wannan zuwan kam inaga sai in ta haihu d’in kenan’’

Kan Ya Musbah Manubiya ta yi ta na cewa”Allah bana so ka daina”
Ganin ta na shirin fara kuka ne yasa duk suka saka dariya wanda hakan ne ya sanya ta fahimci zolayar ce dan haka ta koma gefe ta chuno baki gaba.
Murmushi Ya Musbah ya yi yace”yi hkr mana”ya fad’i hakan kamar yana lallashin wata y’ar Yarinya.Yadda ya yi d’in ne ya sanya murmushi sub’uce mata ba tare da ta shirya ba.
Daganan ita da Yadira wadda ko kallo Ya Musbah bai isheta ba balle ta gaida shi sukayi cikin gidan Ya Musbah da Yashjub kuma suka nufi masallaci…ba ya son case ko ta kawo masa raini a gaban mutane shiyasa kawai ya rabu da ita,yana addu’a a cikin ransa Allah ya sa in sun shiga ta gaida su Inna a d’ayan b’angare na zuciyarsa kuma yana mamakin how Daddy failed to see how wrong and rude behavior d’insu Yadira yake.
A fanfon masallacin sukayi alwallah duk da masallacin yanada matuk’ar kyau amma yana alwallar yana aiyyana yadda zai sake gyara masallacin duk da inshaaAllah ya san su Baba sun kusan tashi dan ya gama siya masu gida amman yanaso kawai ya gyara masallacin saboda yana daga cikin tarihin rayuwarsa.

Ba su dad’e da shiga ba Baba ya shigo kusan a tare shi da su Baba Habu
Da mutuntawa Yashjub ya gaida su ba yabo ba fallasa suka amsa shi daga haka suka koma gefe shi kuma da shi da Baba suka d’an gaisa sama sama suma dan ba su wani tsananta magana ba sakamokon a masallaci suke kuma Allah ya taimakesu babu Kaka mallan wanda kwana biyu yake fama da zazzab’i da sai gaisuwar ta fi haka.Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar Magrib d’in
Ko da aka idar bayan an gama gaishe gaishe.
Yashjub a masallacin ya zauna dan yana son ya yiwa Ya Musbah magana…..sam bai ji dad’in yadda Ya Musbah shima ya k’i amincewa da maganar tashin nasu ba dan kamar yadda Manubiya tak’i yarda ya chanja musu gida hakanan shima yak’i amincewa amman dai ya ce zai sanar da su Innaa su saka masa albarka but ya san suma bazasu tab’a yarda ba.
Sun jima suna kai ruwa rana kafin daga baya Yashjub ya hak’ura kawai ya rabu da shi ba wai dan ya hak’ura ba sai dan ya basa time ne ya yi nazari kafin ya sake zuwa masa da zancen.

Sai da aka yi sallar isha tukunna Yashjub ya shiga ya gaida Inna.
Tsaraba ya so ya siya musu amman babu lokaci kuma ya lura kamar C I D aka turo Yadira dama shi kuma ba ya son case a halin yanzu,shiyasa sai da ya bari su Manubiya sun dawo daga wajen Aisha dai dai sun zo tafiya kenan tukunna ya damk’awa Muhsin kud’i yace da shi da Siyama da Jidda naira dubu hamsin hamsin
Ya so ya basu wanda ya fi haka amman ya lura ba lalle su karb’a ba idan ya fi hakan
Dan dubu hamsin hamsin d’in ma sai da ya yi dagaske tukunna Muhsin ya k’arba musu…dan shi Yaron kud’in ma tsoro suka basa gashi saida Yashjub d’in ya ga su Jiddan sunyi gaba su da Manubiya tukunna ya basa.

Har mota suka rakasu kuwa Manubiya ta so ta shiga ta ga Mama amman sai Yashjub yace mata “ta bari taa ganta next time yanzu dare yayi,ya na so su yi sauri su je su had’a kayayyakin su saboda gobe siyayya za su yi na tafiya jibi kuma 6 za su bar k’asar…”

Ba dan ta so ba ta bari akan za ta kira ta ta yi mata sallama,cikin share kwallarta ta shiga motar ta zauna dan tunda aka zo tafiya ta k’ank’ame Inna da kyar ta cika ta su Jidda suka raka ta har mota suka wuce.

Su Jidda sunso su yi maganar da suke son yi da Manu d’in su samu su tambayeta menene matsalar ta amman Yadira ta kafa ta tsare….da kyar aka ci sa’a ta gaida Inna, k’iri k’iri da aka zo yin alwallah ta k’i shiga toilet tace wa inna “idan suka k’arasa gida za ta yi”
Babu bak’ar magana babu rashin kunya amma yadda ta dinga wani d’ari d’ari tsaf kana gani ka san kyankyamin gidan take yi kuma kamar gadin Manubiya take yi tana nad’ar zance dan idanuwanta kyar a kan kowa…

A b’angaren Yadira kuwa,tsoron Yash ne kawai ya hanata yiwa su Yasira videon d’akin…ashe daman a inda suka d’auki Manubiya ba nan ne asalin d’akin su ba,ashe dama Babanta gurgu ne??..

Shiyasa ta na zama ta zaro waya ta hau watsapp hatta kalar k’ofar band’akin su Manubiya da komai sai da ta zaiyyanewa su Yasira a group…..

Washegari da sassafe Ya Musbah ya gagara gane kansa ko aiki ma ya kasa zuwa,ganin
yana neman mutuwa ne ya sa ya mik’e ya fad’a toilet ya yi wanka dama Muhsin ya dad’e ta tafiya makaranta.
Da kyar ya samu ya kimtsa dan kamar muryar Baraka ya ke ji a duk wata kusurwa ta d’akin…a daddafe ya fito ya sakawa d’akin nasu key ya nufi
d’akin su Inna..ya san inna za ta ga kamar ya yi mata tsaurin ido amma kuma hakan shine kad’ai option d’insa…

A zaune ya sameta tana nad’e kayanta da na Baba tana gyara musu wajen kayan dan Jidda ma bata nan ta tafi makaranta dan har sun koma, gaba d’aya tashi d’aya duk sai ya ji kunyar Innar ta rufe sa amman kuma ya kasa hana kansa abunda zuciyar sa ta ke so…….MANNUBIYA
(Book 2)
Page 25
Na
Humayrah Bulama

Ganin ya koma ya zauna ya yi shiru bayan sun gaisa ne ya sanya Inna ta ajjiye kayan dake hannunta ta mik’e ta k’arasa inda yake ta zauna.A hankali tace”Da!na ce ba zan yi maka magana ba nima,amma kuma na ga abun naka kullum k’aruwa yake yi.Jiya dai Baba ya ce mini yana tunanin matsala kuka samu kai da Nafi’u kwana biyu duba da yadda kukayi jiya kai da shi a gabanmu,sai dai kuma ni ina kokwanto.
Dan haka inaso Musbahu ya gaya mini meye ne yake damunsa kwana biyun nan?ko ya fara b’oyewa Innar sa abu ne bata sani ba?”.

A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa kafin yace
‘’Inna kunyar ki nake ji shiyasa kika ga na kasa gaya miki,”
da sauri ta kamo fuskar sa da hannu biyu ta d’ago da shi kafin tace”kunya ta kuma Musbahu?ni ce ma kenan silar damuwar taka?.Gaya mini kar ka d’auki lokaci, Ina sauraron ka, ka gayamin ko ma menene yanzunnan.’’

Ahankali ya Musbah ya kama hannayen nata duka biyu yana jin wani nauyin ta da kunyar ta
tukunna da kyar kamar wanda dama chan jira yakeyi a tambayesa yace
“Idan na ce inaso in dawo da Baraka inna za ki iya yafe mini?’’
Ya fad’i hakan kwayar idanun sa suna kallon k’asa.

Ahankali ta zame hannunta daga fuskar sa ta kawar da kanta gefe.

Da sauri yace
‘’ki yi hak’uri inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba‘’

Ahankali ba tare da ta kallesa ba tace
‘’Musbahu mai ka d’auke ni?”

Da sauri ya sake cewa
‘’Ki yi hak’uri Inna inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba har abada,dan Allah ki yi hak’uri’’
Ya fad’i hakan yana mai k’ok’orin mik’ewa.
A hankali ta ruk’o hannunsa ta d’ago da fuskarta ta kalle sa kafin tace‘’Ba ka bani amsata ba!.
Mai ka d’auke ni?”
Ganin ya yi shiru ya sunkuyar da kansa k’asa ne ya sa tace”A tunanin ka idan uwar Mijin Jidda ko Manubiya ta bayar da gudunmawa wajen kashe musu aure murus zan ji dad’i?.
Sannan kana tunanin dama chan Ina farin ciki ne saboda ka hukunta Baraka a ta dalilina?
Bari kaji..Baraka ta yi mini k’ololuwar rashin mutunci amman a ko da yaushe idan na tuna da mai sunan baba na tuna cewa a ta dalilina iyayen sa suka rabu gaba d’aya sai in ji babu dad’i.
Dukda na ji dad’i kuma ka zame mini abun alfahari Musbahu saboda yadda ka nuna b’acin ranka a lokacin da aka wulak’anta ni,na ji dad’i!na ji dad’i matuk’a! kuma har gobe Ina sanya maka albarka amma kuma idan ka ce za ka dawo da matar ka ba zan ji haushi ba dan Babban burina a yanzu shine in ga kai da k’annenka zaune lafiya a gidajenku..”

Hawayen farin ciki da k’aunar mahaifiyar tasa ne suka shiga sintiri a kan fuskarsa bai san lokacin da ya rungumeta ba yace”Amman Innaa sai nake gani kmr ban kyauta miki ba…”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta saki murmushi ta d’ago ta kallesa tace
‘’ ka dawo da ita na san yanzu ta ku san fita daga idda ma ko?”
Ba ta jira jin amsar tasa ba ta d’aura da cewa”ni kaina ba son zaman nan naka nake yi a d’aki gabjeje da kai ba.Ka dawo da ita ku koma gidan ku ku ci gaba da rayuwar ku Allah ya yi maka albarka.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e ta fice daga d’akin ta nufi kitchen bayan ta d’auki mayafin ta.

Ya Musbah bai tashi a wajen ba sai da ya maida Baraka
Cikin tsananin jin dad’i ya mik’e ya fice…wajenta ya fara zuwa ya sanar mata ta yi masa iso cikin gidan su ya sanar da Mamanta aka kira kawunta a waya dake ba a garin yake ba shima aka sanar masa…tukunna ya wuce aiki daga baya,suna ta murna shi da Baraka.

Sai dare tukunna Innaa ta samu Baba ta gaya masa yadda sukayi da Ya Musbah.
Dama ta san zai yi fad’a shiyasa ta bari sai dare..ai
kuwa ta sha fad’a dan rabon da Baba ya yi mata irin haka har ta manta.
Jidda kanta ba ta ji dad’i ba
dan ita har ga Allah a tunanin ta Baraka ta tafi kenan..wacce iriyar zuciya ce da Inna haka?ta ya za ki bayar da goyon baya d’anki ya dawo da matar da ta yi miki wannaann kalar wulak’ancin….
Kuma ta san Innar ta san Baba ba zai yarda ba shiyasa ta k’i tsayawa a yi shawara da shi ta yanke hukuncin ita kad’ai.

A b’angaren Baba kuwa….ya san idan har zama bai k’are ba to ko yankasu Baraka take yi a da! sai ta dawo.
Dan haka dama shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login