Showing 33001 words to 36000 words out of 244445 words

Chapter 12 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16460

yi auren”.

A mugun furgice sannan da k’arfi Mommy tace “watt!!”

Jin jina kai Baba Larai ta yi kafin tace “Khadijah!ba ki kaini tsanar Yarinyar nan ba inaga
sannan baki kaini k’in auren nan ba amman ya zama dole mu hak’ura dan bazan b’oye miki ba bamu da yadda zamu yi,ba bu yadda zan yi dan babu abunda zan iya sake yi.Kuma ko ba ni d’in ba ko ina za ki je Wallahi sai dai a ci kud’inki…k’arshen basirata na k’arar amman ki duba ki ga jinkiri kawai aka samu,ki yi hak’uri tunda ta nace sai ta shigo gidan mu barta ta zo inshaaAllah sai ta fita da k’afarta,barin ma yadda muka samu Yash d’in ya fara jan mu a jiki ki duba fa ki ga yau har durk’usa miki ya yi sannan ya nuna miki girmanki da matsayinki a wajensa kinga kuwa wannan ai babban victory ne,dan haka daga yau inaso tundaga kanki har izuwa kan Yadira kowaccenku kawai ta nuna tana son auren bama so amma mu nuna masa muna so d’in,idan aka yi aka gama sai a san abunyi,daga yau inaso duk ku daina fushi da shi sannan ko goya su Yahanasu zai yi wannan ma ba ruwanku a tak’aice dai duk wani abun da zai janyo misunderstanding ko fushi a tsakanin ku da shi ku gujeshi,a iyaka maganar sa ta yanzu na lura kuma na fahimci
Idan har muka yi haka zamu samu kanshi cikin sauk’i,kinga kuwa idan muka samu kanshi komai zai zo mana da sauk’i dan inshaaAllah kafin ma amaryartasa ta gano steering da zata kama ta tuk’a rayuwar gidan nan da shi kansa Yash d’in tuni sai dai ta ji ta a waje.”

Sosai hud’ubar Baba Larai ta ratsa Mommy,dan haka washegari da safe suka tara su Kausar suka yi musu bayani,kowa ya yarda ya amince amma banda Kausar,babu yadda ba a so a fahimtar da ita ba amman furr ta birkice musu k’arshema barin d’akin ta yi ta banko musu k’ofa bayan ta cewa Mommy”ai dan ba ita ta haifeta ba shiyasa ta k’i bawa abun mahimmanci gashi yanzu har za a yi aure kuma a haka suke so ta kwantar da hankalinta,tana ji tana gani Yash ya auri wata su tare kenan ko ya suke nufi???…..”
Ganin duk sunyi mata shiru ne ya sa kawai ta fice ta bar musu d’akin.
………….
Abun har mamaki yake bawa mutane yadda jikin inna ya ware,dan tun wata biyu da suka wuce take tashi ta zauna da kanta wanka ma
Manubiya zata kama ta ta kaita band’aki ta sa mata kujera ta fito ta barta ta yi abunta,dukda ba fita take yi ba amma a wannan lokacin likitar tace”a barta ta dinga gwadawa shima wani exercise d’in ne”
Sannan magana d’aya biyu tana kwatantawa cikin ikon Allah,har waya ta karb’a dukda
maganar tata bata fita sosai haka ta yiwa Yashjub godiya dan ba kad’an ba ta jinjina masa akan yadda ya tsaya tsayin daka ba kowa zai
Iya abunda ya yi ba dan har wasu magunguna likitan ta rubuta ya siyo mata masu mugun tsada wanda akace ta dinga sha safe rana da dare!aikuwa ba ta sha na kwana hud’u ba
ta k’ara jin dad’in jikinta matuk’a,kafin wata d’aya kuwa tsaff inna ta ware gar kamar wadda ba ta tab’a samun stroke a rayuwarta ba,sai dai y’an abun da ba’a rasa ba.

Kowa in ka ganshi a gidan cikin farin ciki yake,abinci suna samu jikin Inna kam Alhamdulillah.
Jidda ma har ta fara first semester exams d’inta na level one a northwest yayin da Manubiya kuma ta gama first semester level 3 a buk.

A yau zasu karb’i lefen Manubiya wanda yayi dai dai da sauran kwanaki 7 d’aurin auren,shiyasa gaba d’aya suketa hada hada isu isu tun shekaran jiya…..MANNUBIYA
(Book 2)
Page 12
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ya Musbah ma ya samu aiki a wani company wanda Yash ya nema masa,har makaranta ya koma (ta manya) dan inda Yash d’in ya nema masa dole sai da karatu,dukda yana gane aikin ba wai ba ya ganewa ba amma yana buk’atar k’ari.
In ka gansa har ya murmure dan wajen ana samun alkhairi
sosai,a cikin watannin da basu kai uku ba har d’aki da band’aki ya gina musu a filin da ke jikin d’akin na su wanda yake mallakinsu,da shi da Muhsin suka koma ciki da zama dan mai sunan baba ya koma wajen mahaifiyar sa.
………..
Watanni uku da suka wuce su Mommy sun fi kowa farin ciki amma a yanzu kam sunfi kowa shiga cikin tsananin tashin hankali dan abun bai zo musu da sauk’i kamar yadda suka yi tunani ba.

A b’angaren Kausar kuwa gani takeyi kamar ta fi kowa shiga matsala da tashin hankali shiyasa take jin haushin kowa da komai especially ma su Mommy,a ganinta inda ace sun bar ta ta kashe Manubiya tun farko da ba’azo nan ba…k’iri k’iri suka hanata koda tab’a Manubiya ne hakanan ta amince ta yi yadda suke so bayan sun yi mata alk’awarin tsayawa by her side akan komai, amma kalli yadda yanzu tashi d’aya suka chanja tunani suke so ta bari a yi auren sannan tsabar cin fuska ita gani take ma kamar farin ciki suke yi da auren dan da su taga ake yin komai,ita kuma sun manna mata hauka sun tattara sun ajjiye gefe,
Bayan da farko plan d’insu’no matter what ba za su bari Manubiya ta shigo cikin gidan ba’ne,amman kalli yadda suka sauya shawara tashi d’aya,babu wanda ya damu da opinion d’inta.
Shiyasa gaba d’aya ta shiga cikin bak’in ciki! takaici da haushi tana jin kamar ta had’iye zuciya ta mutu ta rasa Ina za ta saka kanta ta ji sanyi.


A b’angaren su Yassira kuwa ba k’aramin k’ok’ari sukeyi ba wajen danne kansu da
nuna farincikin da take tunanin genuine ne.
Yau kam duk yadda suka so danne kansu abun na neman ya gagara,sakamokon akwatunan lefen Manubiya da su Hajiya mama suka jere a parlourn k’asa tun safe,shiyasa duk suka gaza sukuni.
Sun shirya tsaf tun d’azu amman kuma sun kasa sauk’a k’asan.

A karo na biyu Ummi ta yi knocking k’ofar d’akin Mommy,bata shiga ba ta tsaya a wajen tace”Hajiya mama fa tun d’azu ku take jira,an kawo sark’ar,ku fito mu tafi.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta koma k’asa zuciyarta fal cike da sak’e sak’e.

Bata dad’e da sauk’a ba su Mommyn ma suka sauk’o
gaba d’ayansu a shirye tsaf suna yak’e,tashi d’aya idanun Ya’isha suka sauk’a akan sir Najeeb wanda ya ke tsaye da shi da wani driver suna gyara d’aurin carpet,ya yi kyau ya yi fresh abunshi kud’i sun sake zama daram..har ga Allah dama chan ita tana son ya Najeeb kawai dai tana ja mishi aji ne saboda ita ta san tana da mutunci da daraja dan haka duk wanda zai sameta to sai ta wana shi dan ba zai same ta a b’agas ba.…amma tunda ta lura kamar Najeeb d’in yana shirin sub’uce mata ta yi sauri ta gyara ta daina duk wasu bad behaviors sai dai kuma gani take kamar ta makaro dan ta fahimci sam sam kamar ba ta gabansa kamar ya daina sonta,ko dan ya ga yanzu ya yi kud’i sosai ne maybe shiyasa yake ganin kamar ya fi k’arfinta….amma inshaaAllah za ta sake gyara komai za ta zage dantse za ta yi duk abunda yake so dan ita kanta ba ta san tana mahaukacin son shi kamar haka ba sai yanzu da ta ga yana shirin sub’uce mata….
Tana cikin wannan tunanin ya matso suka gaisa da Mommy da su Yasmeen kafin ya juya ya cewa Hajiya mama “zai jira su a mota”
daganan ya sa kai ya fice ba tare da ya kalli ko inda take ba.
Yasmeen ji ta yi kamar ta rufeta da duka idan shi bai kulata ba ai ita kamata ya yi ta gaidashi,shiyasa ta juya da niyyar ce mata “ta bishi motar”smman sai mom ta katsesu ta hanyar matsowa ta fara
nuna musu zabgegiyar sark’ar gold da bangles d’in da aka kawo yanzu…sark’ar Hajiya mama ce ta bada as gift da ga b’angarenta ita kuma mom d’in bangles d’in ne ta bada.
Shyasa Yasmeen ta ja bakinta ta yi shiru da niyyar in sun keb’ance za ta yiwa Ya’isha magana,dan ya kamata ta kama Najeeb da kyau tun kafin ya sub’uce mata.

Saida suka yi da gaske tukunna Yasira ta d’anyi
murmushi ta karb’a ta shiga yabawa,yayinda Hajiya mama ta yi shiruu kawai ta zuba musu ido ita da Ummi………


Tun safe yau Kausar bata lek’o ba ko breakfast ba ta yi ba jira take ta ga ko wani a cikin su Yassira zai lek’ota amman gashi har kusan yamma babu wanda ya lek’ota.Bak’in ciki tashin hankali fargaba k’unci da yunwa ne suka tuso ta a gaba, ganin tana shirin sumewa a d’akin ne yasanya kawai ta mik’e ta fita dan kanta.

Hankalin ta bai sake tashi ba saida ta sauk’a k’asan taga uban lefen da aka had’a sannan ta ci karo da sark’ar da ta gani a hannnu Yassira da bangles wanda tun kafin ta k’arasa sauk’k’owa ta fahimci d’anyen gold ne.

Babu wanda ta kula babu wanda ya kula ta haka ta wuce kitchen tana ganin dishi dishi,ta d’auki abunda zata d’auka ta zo ta wuce da sauri ta haye sama.
Tab’e baki kawai Hajiya mama ta yi ta d’auke kai tana hango ba’kin ciki da tashin hankali a idanun Kausar Mommy da su Baba larai
Ita fa wani lokacin har tsoro bayan mamaki Mommy take bata,anya kuwa mutum ce wannan matar?
wacce irin muguwar zuciya gareta haka?ta ya k’iri k’iri za ta k’i auren d’anta?
Kalli yanzu Allah kad’ai ya san mai da mai ta rad’awa su Yasira dan suma kaff d’insu da ganinsu kasan yak’e ne kawai sukeyi amman babu mai son wannan auren.


Kausar tana shiga d’akinta ta fashe da wani irin kuka
wato dai auren Yashjub za’ayi a cikin gidan nan sannan a gaban idanun ta kuma no body is willing to do anything about it.
Shin wai Mommy batasan idan ta bari aka d’aura auren nan tsaf za ta iya mutuwa bane ko yaya?!
Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta amince cewa ‘she’s alone all alone’.
Inda ace Yasira ce ko d’aya a cikin ya’ya’n Mommy ta san da tuni an nemi mafita amman da yake itace yau an fi sama da watanni nawa kullum ce mata akeyi ta yi hak’uri za’a san abun yi yau gashi har za akai lefe bata ga alamar tab’arb’arewar komai ba k’arshema sun b’ige da bin bayan d’an uwansu sannan
shima Yashjub d’in ta lura kamar ma rura wutar tsanar ta aka kuma yi a cikin zuciyar sa
ga kuma d’an kad’afe Yassir gaba d’aya ya hanata sakat ko numfashi in yananan da kyar take shak’a,dan ma ta samu ta yi masa wayo yanzu yana zuwa office yana d’an aiki ba laifi a cewarta “ya dage saboda shima aga ya zama serious kuma sai ya na da enough kud’i tukunna zai iya destroying Yashjub tunda yanzu komai na kud’i ne”
To dai an ci sa’a yana zuwa office d’in yanzu,ba dan haka ba ta san da tuni kullum yana nanik’e da ita. Kuma ta lura kamar su Yassira sun d’an fara jin haushinta akan Yassir d’in saboda suna gani kamar playin d’an uwan su takeyi tunda sunsan ba ta son shi amma kuma tak’i rabuwa da shi,maybe ma shiyasa suka k’i taimakon ta suka barta ita kad’ai kowa ya kyaleta take ta fama da tashin hankali day and night ……

wani sabon kukan ne ya kuma kufce mata,tashi d’aya ta fara ganin duhu duhu kafin daga k’arshe ganinta jinta da k’arfin jikinta ya tsaya chak komai ya d’auke daga haka ta tafi luuu ta zube a wajen kamar matacciya….


Duk yadda Mommy ta so ta d’an rabu da Kausar ko da na kwana biyu ne sam sai ta kasa dan tun da taga yanayinta ta gaza hak’uri kuma a yadda ta ga fuskar Kausar d’in ta kumbura ta yi jaa ta san akwai matsala dan haka ta mik’e ta bi bayanta domin taje ta lallasheta ta kuma sake bata hope….
Wata razananniyar k’ara Mommy ta saka daga shiga d’akin Kausar d’in sakamakon hangota da tayi wanwar a k’asa a zube.
A gigice ta fita ta tsaya a dai dai k’afar bene ta shiga rambad’awa su Yassira kira,dama suna hanya dan tunda suka jiyo ihunta Yassirar ta mik’awa mom sark’ar hannunta suka nufi saman gaba d’ayansu.
Har Ummi zata bisu dan batasan menene ba sai kuma kawai ta rabu da su dan ta lura kwana biyun nan wuyar ta su ga babu idon Hajiya mama kiri k’iri suke sauk’e mata maganganu!harare harare!da tsuka kamar masu jiran ta biyesu su dambatu.

Suna shiga d’akin suma duk suka
gigice,suka rufu akan Kausar,sai da Yasmeen ta tabbatar musu da ‘tana da rai’tukunna hankalin su ya d’an kwanta.
Sai dai kuma babu kalar dabarun da Yasmeen d’in ba ta yi mata ba amman tak’i yin koda motsi ne,dan haka suka kinkimeta suka sauk’o k’asa domin kaita asibiti.

A nan k’asan suka tarar da kusan kaff masu aiki da masu gadin gidan suna ta jidar akwatunan suna kaiwa cikin motocin da suke nan jere a compound d’in gidan.

A kan doguwar kejera suka shimfid’e Kausar kafin
Yassira ta k’arasa kusa da main driver d’in gidan tace”Baba sani yi maza ka fito da babbar mota zamu fita gaba
d’ayan mu Kausar ba lafiya”.

Shiruu yayi dan already babbar motar kusan a cikin ta aka jiide kayan su shinkafa carpet da tabarma da su randa,yana cikin tunanin mai zai ce mata ta daka masa wata uwar tsawa ta hanyar cewa”Ina maka magana ka yi shiru,ba ka ganin Kausar a kwance kamar gawa ne??..”

Cikin tarar numfashinta Hajiya mama tace “and so what??idan Kausar tana kwance kamar gawa?
Ai ita dama haka take,indai
aka zo abun farin ciki na ni da d’ana har ku kanku ma tou sai ta b’ata.
Maganar auren Yashjub kuwa idan a rami ake dannata wallahi sai an yi kuma sai mun yi farin ciki!
Ita ta sani ta yi ta kwanciya karta tashi daga nan har abada”

Ahankali Ummi ta matso tace”. Maama…...”
Cikin katseta Hajiya mama tace”Saddik’a kar ki wani damu makirci ne so sukeyi a fasa auren Yashjub
ni na gaya maki muna fita Kausar za ta mik’e dan lafiyar ta k’alau na riga na san duk acting ne takeyi”

Tana gama fad’in haka ta kalli mom da Yahanasu da Ummin tace musu “let’s go”
Tunda iya su ne yanzu za su tafi Munirat ba ta nan yayarta ta yi kira yau ta tashi bata da lafiya sosai shine ta d’an je ta dubota ta dawo.

Basu bar muusu driver ko d’aya ba gashi Hajiya mama ta sanya su Yassira sun rarraba makullayen motocin su a drebobin da za su kaisu tun d’azu.
Dan tashi d’aya ta fahimci basa san zuwa da motocin su
shiyasa ta karb’e tun da wuri dan so take ayi convoy.

Haka su Hajiya mama suka jera convoy d’in nan kuwa dan kaff motocin gidan sai da suka kwashe iya na Daddy Yassir Yashjub ne kawai babu suma kuma dan sun fita a ciki ne.

Motar Ya’isha kuma ta samu matsala balle su Mommyn su fita a ciki,gasu da uban yawa…..

Suna fita Mommy ta fashe da kuka tace “Baba larai na ce miki dama ba zan iya tolerating matar nan ba kalli wulakanci da rashin tausayi da isa da mallaka a cikin gida na!”

Shiruu duk sukayi zuciyar kowa a wuya,da kyar Yassira ta share kwallar da ta zubo mata ta wuce ta nufi dak’in Kausar…da kyar kuwa ta ga makullin motar Kausar d’in dan haka ta d’auko ta fito aka samu aka tafi kaita Asibiti daga Mommy sai Yassira da Yasmeen wadda ta zauna da Kausar d’in a baya dan motar ba za ta ishe su su duka ba…..



Kaff layin su Manubiya har ma da makwaftan layin sai da aka san yau an kawo lefe,dan convoy d’insu Hajiya mama sai da ya cika layin taff.
Suna zuwa Yahanasu ta kira Manubiya tace mata ga su sunzo,ita kuma Manubiya ta sanar da Ya Musbah,dama sun ji zuwan nasu.

Aisha da Jidda aka tura suka yi musu iso zuwa parlourn su Siyama inda yake nan a gyare tsaf sai tashin k’amshi yake yi.

Manubiya tana zaune a d’akin su ta ji anata wucewa da kaya ana hada hada shiyasa tashi d’aya jikinta ya yi sanyiiI,hakanan ta koma gefe ta rakub’e ta yi shiruuu,tana jin yadda gabanta yake ta fad’uwa.

Sai da suka gama shigewa tsaff tukunna anty Umma ta zo kiran su inna da mama domin su gaisa da surukan nasu,inna ce ta samu ta je yayinda mama ta ce”sa had’u next time,bari ta zauna da amaryar”
Su anty umma sun so ta je amma tace “ba komai,”dan haka suka fita suka barta ita da Manubiya wadda ta fara hawaye kad’an kad’an…cikin rarrashi mama ta shiga lallab’ata had’e da nasihar zamantakewar aure mai ratsa jiki.

Ba mom ba hatta Ummi ta sha mamakin gidansu Manu dan a tunaninsu Yarinyar y’ar manya ce,ba wai reni ko wani abun ba,kawai dai sun yi tunanin Yash ba zai zo nan ba,amman tunda nan d’in ya zab’a to Allah ya basu zaman lafiya inshaaAllah su kuma za su so ta su rik’eta amana.
Hajiya mama ma ba ta ji komai ba,sai ma sake ganin hankalin Yash da ta yi dan ta san tabbas tun da ya zo nan tou tarbiyya da hankali ya bi ba wai kyalkyalin duniya ba!,ai kuwa inna tana zuwa ta tabbatar da hakan,dan ba kad’an ba kawaici da nutsuwar matar suka sake tabbatar mata da hankalin amaryar tasu.

Cikin mutunta juna da barkwanci suka bada lefe akwatuna goma sha biyu da su taburmi da kayan al’ada.
Su kuma su inna suka basu tukuicin naira dubu d’ari da hamsin suna ta jin kunya amman yadda Yahanasu ta sa hannu ta karb’a cikin mutunci da karamci da kamala ne ya sanya suka d’an ji sanyi dan su kansu sunsan d’ari da hamsin ya yi kad’an a wannan uban kayan da suka cika musu gida da shi.

Hajiya mama ta so a kira mata Manu su d’an gaisa,amman kuma yadda parlourn ya cika taff da jama’a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login