Showing 9001 words to 12000 words out of 244445 words

Chapter 4 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16419

d’in ka’’

Numfashi ya fesar kafin yace’’Jikina Alhamdulillah dasauk’i kafin ki zo
amman yanzu kam na san in kika tafi kika barni a haka
akwai matsala.Hak’uri da godiya sannan tsautsayi da k’addara ne ya janyo hakan
sai mu yi adduar Allah ya kare gaba’’ya k’arashe maganar tasa yana mai zaro wayarshi daga aljihu ya fara daddanawa
shi ala dole yayi fushi da ita
watakil in ta ga hakan ya san za ta yi masa yadda yake so.
Yana addua Allah yasa maganarta ta zama positive dukda bashi da tantama akan itama tana sonshi.

‘’Allah ya ji k’an musulmi,Allah ya baka lafiya,Allah ya kare gaba’’ tace da shi kamar yadda shima ya jero mata kafin ahankali ta fara tafiya towards k’ofar zata fita.
D’an d’agowa yakeyi yana satar kallonta yana kallon wayar tashi ganin tana shirin fice wa ne yasa yayi sauri ya mik’e yace’’au ba za ki tambayeni
me zai dawo min da ciwon nawa bayan kin tafi ba ko??’

Duk yadda ta so daurewa sai da murmushi mai had’e da y’ar siririyar dariya ya sub’uce mata a ranta tace’’Mutumin da ya had’e rai shi ala dole yayi fushi yayi zuciya
amma kalli shine ya mik’e yanzu yake wannan batu.’’

Sarai ya ji sautin murmushin nata dan haka ya k’araso ya tsaya a gabanta yace ‘’Dariya ma kike yi min ko??’’
Ya fad’i hakan cikin b’ata fuska
kamar wani k’aramin Yaro.


Wani d’an siririn murmushi
wanda ya sanya Yash ya ji kamar zai suma ta saki kafin a hankali tace’’na san mecece amsar da za ka ba ni shiyasa ban tambaya ba’’

Cikin tarar numfashin ta yace
‘’Mecece amsar??’’

Sai da ta d’an kalleshi kad’an tukunna ta sunkuyar da kanta tace ‘’Cewa za ka yi saboda ban fad’i abunda kake son jiba,kuma ai na ga ma fushi ka yi da ni yanzun.’’

A hankali cikin yin k’asa da murya yace ‘’ni na yi fushi dake??’’ bai jira jin amsartaba yace ‘’Never’’
kafin ya d’aura da cewa’’Kin san rashin amsar taki ce za ta k’aramin rashin lafiya amma shine kika zab’i ki tafi ki barni a haka??saboda kin tsane ni,ko?.Wannan sarkin nacin.’’
Yayi maganar yana nuna kanshi

Dasauri ta d’ago ta kalle sa tashi d’aya tace ‘’A’a’’

Dukda yadda ya ji sanyi a ranshi amma sai ya dake ya sake had’e fuska yace’’to yaya ne?’’

‘’Ba sai na fad’a ba na san ka sani’’
Ta bashi amsar tana mamakin yadda sam ba ya gajiya da kallonta tun da ta shigo d’akin
ba ta jin ya d’auke idonshi a kanta in ba lokacin da ya yi fushi ya d’auko waya ba,ita
har tsarguwa da wannan kallon nashi takeyi….kullum in suka had’u kmr ranar ya fara ganinta…

Muryarshi ce ta katseta jin yana cewa ‘’i’ll love to hear it
ba ki san taimakon da za ki yi min ba in kika fad’a Manu’’
Kamar zai yi kuka yace’’so plssssss’’ ya ja plss d’in sosai har cikin ranta sai da taji
‘’If your answer is yes just say it yanzu I just need to hear it na garu dayawa a tausaya min
haka mana…….’’

A hankali cikin tarar numfashinsa ya ji tace’’Yes!’’

‘’Yes What?’’
Yayi mata tambayar yana kallonta yana murmushi
sosai

Turo baki tayi ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta da su dan kunya take ji sosai sanann ta yi tunanin da ta ba sa amsar zai kyaleta ne amma ta ga alama wannan so yake su kai dare anan ana abu d’aya

Yashjub kuwa tsabar murna ji
yake kamar ya zare hannun ya janyota jikinta ya yi hugging d’inta…..ahankali yace’’ pls mana,kin ce min yess kawai kin barni,elaborate mana,sannan na ce fa bana son wannan sunkuyar da kan a d’an rage wannan kunyar tayi yawa fa…’’


Knocking ya ji an d’an yi dan haka da sauri ya juya ya saka key sannan ya juyo gareta yace’’um’’alamun ita yake sauraro.

Zaro ido tayi kafin a rikice tace
‘’Dan Allah ka bud’e maybe su
Jidda ne suka dawo harda Ya Musbah muke tafe dan Allah ka bud’e kar su yi tunanin wani abun’’ ta fad’i hakan ahankali k’asa k’asa kmr wani zai jiyo ta sanann duk a rikice.

Ba k’aramin dariya ta ba sa ba ganin yadda ta tsure tashi d’aya a ransa yace ‘’perfect’’

amman ya dake ya mak’e kafad’a yace’’um um,ni kam ba zan bud’e ba’’
sai kuma ya d’an sake matsawa kusa da ita kafin ya ci gaba da cewa’’har sai kin fad’a min komai yau
tukunna babu ruwana ko waye ya zo to ya jira Queen ce take zuba mulki da jan aji dan haka shima ta shafe sa.’’

Dai dai nan aka sake yin wani knocking d’in,sai da ta d’an zabura kafin ta kalli k’ofar sannan ta kalleshi a gigice tace ‘’to me kake so ince??
ko waye fa a bakin k’ofar nan na san ya ji lokacin da ka saka key kuma kana bud’ewa sai a ganmu tsulum mu biyu kawai kaga ai hakan babu dad’i,na riga na ce maka yes ai dan Allah ka bud’e k’ofar nan’’

Cikin tarar numfashi ta yace ‘’waye zai bud’e k’ofar??ai in gaya miki muna nan ni da ke har abada muddin ba ki bani amsata ba,bari ma kiga in zare key d’in in cilla ta window’’
Ya fad’i hakan yana mai juyawa

Da sauri tace ‘’wait!’’
Sai da ya d’an yi y’ar guntuwar dariya tukunna ya juyo.
Kamar za ta fashe da kuka tace ‘’to me zan ce?’’

‘’Abinda yake a cikin zuciyar ki game da ni’’ya ba ta amsar kanshi tsaye.

Kallon shi ta yi ahankali ta d’aga kai tace’’Yes….’’
sai kuma ta yi saurin sunkuyar da kanta tace’’na ce maka yes tun d’azu…’’ta fad’i hakan kamar za ta fashe da kuka dan ita har ga Allah wallahi kunyar gaya masa complete kuma direct take ji.

Juyawa kawai ta ga yayi ya zare key d’in.

Still kuma har yanzu anata faman knocking k’ofar

Da sauri tace’’me kuma na sake yi?’’

Kallo ta yayi kafin yace’’Yess’’

Da d’an mamaki tace’’yes kuma?me kenan?’’

‘’Yauwa exactly my point,kin ga kema ai ba ki gane ba ko?dan haka ya kamata ki fahimci nima ban gane me yes d’in ki take nufi ba,if you want to express yourself all you have to say is ‘i love you Yashjub’ ni har ga Allah banga abun wahala a y’an waennan kalmomin ba…’’

Knocking aka yi da k’arfi sosai this time around, Manubiya ba ta san lokacin da ta fara bubbuga k’afafunta ba kamar wata y’ar yarinya tana cewa ‘’ni kam Allah A’a dan Allah kawai ka bud’e’’.

Shagala yayi kawai yana kallonta,sai da suka suka had’a ido sai kuma ta tsaya chak! tsabar kunya kasa ma cigaba da fuskantar sa ta yi dan haka sai ta yi saurin juyawa.

Murmushi yayi da sauri yace ‘’a’a pls don’t stop you look cute’’

Bugun da akayi da mugun k’arfi wannan karon ne yasa ta juyo tace’’dan Allah’’
Ta fad’i hakan hawaye suna s
taruwa a kyawawan idanunta wanda suka sanya idanun suka fara kyalli
wanda hakan ya sake d’imauta Yash

Ahankali yace’’Manu!
ba zan tab’a bud’e k’ofar nan ba idan har ba ki gayamin abunda nakeson ji ba,in ma bakya sona ne to ki fad’a min
Ni a ganina ke kika bari har aketa bugun nan,and just so you should know in har Doctor ne yake knocking d’innan to mutane zai je ya tattaro a b’alle k’ofar tunda patient ne a ciki
In su ka ji shiru yayi yawa za su yi tunanin ko wani abun ne ya sameni gashi jiya na sanya sun zare cctv d’in d’akin nan,kinga ana zuwa ba ma mutum d’aya ba mutum dayawa ne za su ganmu tsulum kuma Allah kad’ai yasan tunanin da kwakwalwar kowa za ta basa.
Dan haka it’s up to you ki yanke decision da wuri tun kafin a zo
a b’alla k’ofar nan saboda one thing is for sure ‘ni dai ba zan tab’a bud’ewa ba yau har sai na ji ishashshiya kuma gamsashshiyar kalma daga gareki’.’’
Ya k’arashe maganar yana murmushi k’asa k’asa yana kallonta

Dole ta ajjiye kunya a gefe
tun kafin ya janyo mata magana a cikin asibiti
A hankali ta runtse idanunta da k’arfi tukunna tace’’i love you’’

Ahankali Yash wanda tashi d’aya kasala ta rufar masa ya d’an matsa kusa da ita kad’an
ahankali kamar wanda baya so kowa ya ji yace’’how much’’

Direct daga zuciyar ta tace’’so
very much’’

Wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace’’za mu yi auren mu soon ko?’’

Jinjina kai ta yi still idonta
a runtse tace ’’inshaaAllah’’

‘’Ki haifamin ya’ya masu kama dake?’’

ahankali tace’’inshaaAllah’’

Wani bugun aka sake yi
wanda ya sanya Manubiya ta bud’e ido ta kalli k’ofar da sauri,tabbas yau kam ta san babu yadda za’ayi ta iya had’a ido da Yashjub dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa tukunna tace’’plss ka bud’e dan Allah’’


Lumshe idanunsa yayi ya bud’e yana mai ji kamar ya fita wajen ya je ya shak’e koma wanene a bakin k’ofar da yake musu wannan uban knocking haka me shegen naci…tashi d’aya ya ji ya tsani knocking zai rubuta a diary d’in shi shikam ‘ya tsani knocking ,forever!!’
This is the best moment of his life he needs to be all alone with her
sannan ya samu yayi expressing kansa more and deep amman kawai an kama an zo an dame su gashi ba ya so ya karya alk’awarin da yayi mata ta hanyar k’in bud’e k’ofar.

Da k’arfi aka sake yi dan haka Manu ta sake cewa ‘’dan Allah’’

A hankali ya juya ya zura makullin ya murd’a ya bud’e k’ofar yanajin kmr yana bud’ewa kawai ya fellawa wanda yake knocking d’in mari…………..MANNUBIYA
(Book 2)
Page 05
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Yana bud’ewa suka yi ido biyu da Yasmeen ahankali ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin yace’’i wasn’t expecting you!’’

babu Mommy da Daddy a wajen ballantana ta yi rashin kunya shiyasa ta yi shiruu ta d’an sunkuyar da kanta k’asa,kafin ta d’an d’ago ta kallesa tukunna tace’’Yau ne ranar da na ke shigowa aiki nan asibitin,shine na ce bari in lek’o in duba ka’’

‘’Nagode’’
kawai yace da ita daga haka ya fara k’ok’arin maida k’ofar.

Manubiya tana jin muryar Yasmeen zuciyarta ta fara wani irin tuk’uk’i….yanayin conversation d’in su ba kad’an ba ya d’aure mata kai gashi ta ji yarinyar sai wani kashe murya takeyi tana wani lallab’asa……


Da sauri Yasmeen ta sa hannu
ta d’an tare k’ofar kafin tace
‘’Those are for you’’
Ta fad’i hakan tana mai nuna masa allurar hannun ta.

This time around b’ata rai Yashjub ya yi cikin d’an
fushi yace ‘’i’m fine,na warke. And if necessary
go get the doctor’’
A ranshi yace ‘’lalle ma yaran nan rainin hankalin nasu ya yi yawa,su gama basa raini da attitude a gaban mutane shine yanzu dan ta maida shi d’an cikin ta za ta zo kuma ko bada hak’urin rashin kunyar da ta yi masa bata ma da shirin yi.Kamar ma bata yi komai bama’’


Ta ji zafi sosai amman sai ta
dake ta d’an yi murmushi
kafin a hankali tace’’nima ai Doctor ce,kuma shi ya shiga surgery,just let me in i…..’’

Cikin fushi sosai yace
‘’Ke!ina miki wasa??’’
Bai jira jin amsar ta ba yace ‘’b’ace min a gani,kafin in karya ki a wajen nan’’.


Dai dai nan Jidda da Siyama suka k’araso wajen dan ba su
samu lemo da ayaban a kusa ba shine Ya Musbah ya karb’a suka tafi nema shi da Muhsin bayan ya balbalesu a titi kamar zai rufesu da duka.

Ahankali Yasmeen ta d’an sunkuyar da kanta ta fara k’ok’arin maida kwallar takaicin da take shirin yin nasarar zubo mata.

Sai da Jidda ta d’an rissinar da kanta
tukunna ta ce’’Ya Yash,Ina wuni’’
Haka ma Siyama

Jinjina kai ya yi kafin a hankali yace ‘’Alhamdulillah’’

Daganan ya juya ya shige bayan ya bar musu k’ofar a bud’e.
Kamar ba za su kula Yasmeen ba sai kuma jidda tace mata
‘’Sannu Ina wuni’’tunda koda dai ace likitarsa ce(dan sun ganta sanye da lap coat)
but tare suka gansu suna magana.

Dakyar ta iya d’agowa ta kallesu….kyawawan mata ajin farko masu ji da asalin kyau da k’uruciya gashi sai wani kalar k’amshi sukeyi su duka biyun
sai dai tashi d’aya yanayin kayan jikin su zai sanya ka fahimci suna cikin yanayi na rayuwa,sanye suke da dogayen rigunan Abaya bak’ak’e amma
tsabar yadda kayan sukaji ruwa har bak’in ya d’an fara komawa kamar kalar dark ash
sannan rabin stones d’in jiki duk sun goge,tashi d’aya ta ji gabanta ya yanke ya fad’i,kallon
da taga suma sunayi mata ne
yasanya kawai dakyar tace’’fine’’a cikin zuciyar ta tana tunanin’’to wacece budurwar Yash d’in a cikinsu’’
Sai da suka tura k’ofar suka
shige tukunna ta samu damar yin ido biyu da Manubiya
wadda itanma Allah Allah dama takeyi a d’an bud’a k’ofar ta samu ta ga wacece take magana da Yash d’inta haka yake disga ta.
A bud’e su Jidda suka bar k’ofar dan a tunanin su shigowa za ta yi

Har manubiya ta d’auke idanunta daga kanta amma
ita Yasmeen din ta kasa,kallonta kawai take yi tana sakewa….sanye take da dark army green din jilbab har k’asa,yanayin yadda ta yi parking gashinta ta d’aure igiyoyin jilbab d’in ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba….…’’Hi Yasmeen’’d’in da sir Najeeb yace mata ne ya dawo da ita daga duniyar k’arewa Manubiya kallo,da sauri ta kawar da kanta ta mayar gareshi kafin dakyar ta samu ta d’an k’ak’alo murmushi tace’’Najeeb,
Ina wuni!’’
Ta fad’i hakan tana d’an murmushi.
D’an lek’awa ya yi,ya hango Yash suna gaisawa da su Jidda bai ga fuskokinsu ba
dan sun bashi baya ne iyakar
gefen fuskar Manubiya ya samu ya gani.

Juyowa ya yi ya kalleta kafin yace ‘’ya na ganki a bakin k’ofa?’’ya yi mata tambayar yana tsare ta da idanuwa

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace ‘’ko da na zo ma na kusan 20 minutes tukunna da kyar aka bud’e min,ashe madam ce a ciki shiyasa,Itace yayar tamu ko?’’ta yi mishi tambayar tana kallon Manu.
Direction d’in da yaga tana kallo ya kalla tukunna ya d’anyi murmushi ya juya ya kalli Yasmeen d’in sannan yace’’Yeah itace!ba ku gaisa ba ne?mu je cikin mana..’’

Girgiza kai kawai ta yi kafin tace ‘’Yace ma in ban bar nan ba sai ya karya ni,ma gaisa wata rana bara in wuce’’

Ta fad’i hakan tana d’an yin gaba sai kuma ta juyo tace ‘’am d’azu na ga miss calls d’inka sorry ina driving ne shine na saka wayar a silent’’

Ajiyar xuciya ya sauk’e kafin yace‘’it’s about Ya’isha!kin dai san halinta.Anyways na ga kamar kina sauri ki je kawai za mu yi magana anjima’’

‘’Ok’’kawai tace kafin ta juya ta yi gaba….

Shiruu Najeeb ya yi yad’an bita da kallo har ta b’ace ma ganinsa a ransa yana tunanin menene yake damun Yash haka ne,shi shi kad’ai iyayenshi suka haifa he always wish inama ace yanada siblings
shiyasa har gobe yake mamakin Yash ya rasa dalilin da yasa baya appreciating gift d’in da Ubangiji ya basa.

Girgiza kai kawai ya yi kafin ya shige cikin d’akin bakinshi d’auke da sallama,ahankali
duk suka amsa kafin Manubiya ta d’ago cikin girmamawa ta gaidashi

Murmushi yayi yace ‘’Lafiya ya
gida ya mai jiki?’’


‘’Alhamdulillah’’ta ce
daganan ta sunkuyar da kanta

Kusa da Yash ya d’an matsa tukunna yace masa’’Ya jiki?’’

Kamar ba zai amsa shi ba sai kuma yace ‘’Alhamdulillah,ai
na d’auka ba za ka shigo ba’’

Murmushi Najeeb d’in ya yi
kawai ya girgiza kai kafin ya mayar da idanunsa a kan su Jidda da suka ce masa ‘’ina kwana’’a tare,sai da numfashinsa ya yi sama
sakamakon ido biyu da sukayi shi da Siyama.Dakyar ya samu ya iya ce musu ‘’lafiya Alhamdulillah’’
sannan ya yi sauri ya d’auke idanunsa daga kan Siyama wadda ita bama ta san yana yi ba dan suna had’a ido ta sunkuyar da kanta.

Manubiya ya kalla kafin yace’’ya na ganku duk a tsaye?ku zauna mana
Itan ma sistern ki ce?’’

Ta san sun had’u da Jidda ranar a asibiti shiyasa ta fahimci Siyama yake nufi dan haka tace’’Eh,k’anwata ce,cousin
sister’’

Ahankali yace’’MashaaAllah’’
Sai kuna ya sake cewa’’ku zauna mana’’

‘’Tam’’
Jidda tace
daganan suka juya suka nufi sofa ita da Siyama suka zauna

Shi kuma ya zauna a gefen Yash kan gadon.
Manubiya ya sake kalla yace
‘’Amaryar mu ba za ki zauna ba ke??’’
Da sauri Yashjub ya juya ya na mishi wani irin kallo
Dariya Najeeb yayi kafin yace
‘’Sorry!’’sai kuma ya kalli Manu yace ‘’Amaryar Yashjub shi kad’ai!ki taimaka ki zauna’’

Ahankal ta juya da niyyar zuwa inda su Jidda suke amman sai
ya sa k’afa daidai inda za ta bi ta wuce,dukda k’afar ba ta wani kafeta sosai ba amma ta fahimci sarai abunda yake nufi
zuwa yanzu ta riga ta san halin Yash ta san ba k’aramin abu bane a wajensa yanzunnan sai ya ja mata ta ji kunya a gaban su Jidda muddin ta k’i yin abunda yake so
shiyasa kawai sai ta nemi waje ta zauna a kujerar mai jinya
tana mamakin sa a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma
tana mamakin Sir Najeeb
mutumin da da ko kallon kirki baya yi mata daga frowning face sai ciccin magani
amman yanzu wai shine haka kamar zai goyata.

D’an zungurin Yash sir Najeeb d’in yayi ganin yadda yake kallon Manu
K’asa k’asa yace masa’’kar ka
cinye ta da ido mana..’’

Dariya Yash d’in yayi shima k’asa k’asa kafin kawai ya d’auke kansa daga kan Manubiya ya maida kan Najeeb yace’’wanne munafurcin Yasmeen ta shirga maka d’azu’’

Shiruu Najeeb yayi yana kallonshi kafin ya mik’e tsaye yace ‘’za mu yi magana dakai anjima sai kuma ya kalli Manu yace’’bari in bawa bak’in mu ruwa’’…tun lokacin da su Siyama suka koma chan gefe suke zauna yake ta so ta juyo ya sake kallonta amman tak’i
Suna zaune abun su hankalinsu na ga wayar Siyama…ya san hakan bai dace ba bai kamata ba sannan ko a ta b’angaren sa shima sam double dating ba ya cikin tsarinsa dad’indad’awa kuma ga Yashjub a wajen abun zai yi kamar cin fuska sannan ya san yana yin wani move Yash d’in zai gano sa shiyasa tun d’azu yake ta tausar kansa amman duk yadda ya so sam ya gagara hak’ura….dan haka ya yanke shawarar kai musu ruwa
he don’t mind

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login