Showing 237001 words to 240000 words out of 244445 words
ko namiji saboda Ina matuk’ar son abuna.
Magiya kuka da kuma nuna mini alfanun yin hakan da yadda za mu taimaki juna da Kausar da Yassir suka yi ne ya sanya na chanja ra’ayina na amince idan na haihu Kausar sai ta karb’a ni kuna sai in dawo gida gareku ba tare da kowa ya san abunda ya faru da ni ba in yi rayuwa ta kamar farko.
Tunda na haihu na ji ba zan iya bata d’ana ba….da mugun kyar na amince bayan Yassir ya lallab’ani amma a jiya da na ji yana waya ana sanar masa abunda Kausar d’in ta yi wa Yarona ya sanya na fahimci bayarda shi a Kausar is the worst thing I can do
dan haka na dawo kawai ku karb’i Yarona ku bani inason abuna wallahi ba zan iya rabuwa da shi ba ba zan iya bar mata shi ba,daganan ku yafe mini ku yafe min na san na yi muku laifin da ni kaina ba zan iya yafewa kaina ba.”
Cikin kuka Kausar tace”Wallahi k’arya take yi”
itama Munirat cikin kuka tace”
Wallahi gaskiya nake fad’a….”sai kuma ta kalli Yash tace” and again cikin ta ba 12 days bane ba tun asalin farko k’arya ta yi muku suka had’a Baki da Junior akace naka ne amma a lokacin da tace tanada ciki,cikin jikinta watanninsa biyu na ji komai kuma na ga komai a wayar Yassir!!!”.
Damk’ar wuyanta Kausar ta yi cikin ihu da kururuwa ta hau cewa “wallahi k’arya take yi mini sharri ne Munirat waye ya turo ki??”
K’arasowa Junior ya yi da kyar ya kwace wuyan Munirat daga hannun Kausar kowa su yake kallo…kunya kamar k’asa ta tsage ya shiga hakanan ya kallesu yace”da gaske Munirat take!cikin Kausar da na duba a wanchan lokacin ya ma haura 2 months amma na ce muku bai wuce 12 days ba saboda……………”
Tiryan tiryan ya zaiyyano musu komai da yadda Yassir ya yi tricking d’insa komai bai b’oyeba kafin ya juya ga Yash ya had’e hannuwansa biyu yana kuka Yash d’in ma yana hawaye yace”ka yafe mini dan Allah kar ka rik’eni a rai ka taimaka ka yafe mini…..”
……
Tuburan!!haka Kausar ta kafe ta dinga rantse rantse k’arya Munirat da Junior suke yi…
….
Scannning d’in da yayi aka nemo Yasmeen ta duba ta tabbatar sannan ya nuna musu messages d’in da Yassir ya dinga yi masa a wannan rana amma still Kausar tana tsaye tana kuka tanata faman rantse rantse Itafa k’arya aka yi mata…Yashjub bai san lokacin da ya k’arasa ya damk’i wuyanta ba kamar ya samu k’ato haka ya kaita bango yadinga gwara kanta sai da jini ya fara fitowa ta kunnenta…da mugun kyar su Daddy suka kwaceta daga hannunsa tana ganin haka ta fita da gudu….ta riga ta san asirinta ya tonu kuma a halinda Yash yake tsaff zai iya kasheta shiyasa kawai ta nufi gidan Mommy a hargitse,ta san idan ta je za su nemi mafita!!!dan she ain’t giving up wallahi.
Hakanan ta nufi titi kowa yana kallonta(dan daga ita sai riga da wando manya na barci,da hula.)
ita kam sam bata damu ba..da kyar ta samu napep ta hau ta yi masa kwatancen gidan Mommy suka wuce a haka sanyi yana kad’ata kamar zai d’auke ranta.
Tana fita Yash ya rushe da wani irin kuka ya juya ya rungume Daddy fad’I yake”Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah”ba bu k’ak’k’autawa….Allah kad’ai ya san adadi da kalar dad’i da fatincikin da ya tsinci kansa da nutsuwar da ya samu da akace d’an Kausar ba nasa bane ba,kuma yanzu ya sake tabbatarwa babu abunda ya shiga tsakaninsa da ita.
Shima Daddy kukan yake yi,a ransa cewa yake”Astaghfirullah Astaghfirullah how did I end up
With a son like Yassir!!!…total shame….”
Daddy da Hajiya Mama where very disappointed in Junior amma kuma he has his own reasons kuma yanzu ya fito ya fad’i gaskiya shiyasa suka yi masa fad’a suka nuna masa illar k’arya a ko wanne hali!!!
Yadira ma da yake tunanin zata yi wani abun bata yi komai ba ta dai ji zafin al’amarin kasancewarsa da wata sosai dukda abun ba yanzu baneba amma ba komai..inshaaAllah,zata rungumi mijinta su zauna lafiya ta kula da shi yadda ya kamata.
Sosai Junior ya sake luntsumawa kogin dana sani da ya san haka zasu karb’i al’amarin da bai zalinci Yashjub har haka ba.
Hakanan aka d’auko Yaro a sama yanata tsala
Ihu aka bawa Munirat,sai a sannan Yash ya yarda ya kalli fuskarsa….
Har ta juya zata tafi Ummi ta ruk’o ta ta rungumeta tace kar ta sake tafiya ta barta..ta yi laifi amma itama da laifinta,bai kamata ita da yayarta su yi dogon fushi da ita ba ta rasa abokin shawara sannan ita kanta ta san bata paying attention a kanta sosai dan inda wata uwarce da ya ci ace ta gane y’arta tana d’auke da ciki ne tun a karon farko!
Ta yi hak’uri ta yafe mata su yafewa juna su gyara mistakes d’insu…
Sai da su Daddy suka saka baki tukunna Munirat ta sake neman yafiyarsu ta yarda zata zauna…a nan parlourn gefe kad’an Ummi ta zaunar da ita tace”ta bawa Yaron nono dan ba a tab’a basa ba”
Ai kuwa tana saka masa a baki ya kama yana sha a haukace duk sai da ya basu tausayi.
Ummi da Daddy basu so samun shege a cikin zuriarsu ba amma zasu rungumi k’addara su karb’i Yaron hannu bibbiyu inshaaAllah da su cinye wannan jarabawar….
Suna tsattsaye ana koke koke da neman yafiya su Yasira suka shigo ita da Yusra.
Da gudu Yusra ta tafi jikin Daddy ta fad’a ta fashe da kuka hakama Yasira ta je ta rungumesa….cikin kuka Yusra ta fara neman Yafiyarsa tace”ya yafe musu they have been wrong yanzu sun gane gaskiya…basu san inda Ya’isha take ba…Mommy tace ta aiketa k’auye har yau ba ta dawo ba…ya taimakesu a nemota tabbas sun san akwai abunda Mommy take b’oyewa…..
Sosai kan Yashjub ya fara juyawa…da kyar ya yi gyaran murya duk suka kallesa tukunna tiryan tiryan ya shiga zaiyyano musu yadda ya ga Mommy ta fito daga gidanta da yadda ya bi bayanta har zuwa inda suka hak’a rami ta saka Ya’isha….
Sannan ya d’aura da cewa
“A gani na bai kamata a binneta a haka babu sutura ba shiyasa na d’aukota to kuma ina gama sakata a mota sai na ji labarin rasuwar Inna….”
Manubiya ya kalla wadda take kuka kamar ranta zai fita yace”Ina zuwa gwaggo Suwaiba ta nemi ganina….tashi d’aya Ina shiga ta sanar da ni Inna fa ba mutuwa ta yi ba amma ita kanta bata gama sanin mai ya faru da ita ba..saboda da suna yi mata wanka ta ga babbar yatsarta ta hannun dama
ta yi motai alamun akwai rai a tare da ita amma kuma ba ta numfashi kuma Likita ma ya tabbatar da ta mutu…a wannan lokacin ta ce mini bata so ta ce bata rasu ba ta saka wa su Manubiya rai kuma a zo daga baya aga ta rasu d’in saboda ta tabbatar mini aikin asiri ne ba na asibiti ba to komai zai iya faruwa a gaba ta yiu ta tashi ta you kuma ta wuce…shiyasa tace mini za ta wuce da Inna k’auyensu a taru a yi mata addu’a suna da manya manyan hafizai a k’auyen masu tsoton Ubangiji da sani daga nan sai a ga abunda Ubangiji zai yi Idan bata tashi ba zasu binne ta a chan idan kuma ta tashi za su dawo da izinin Allah….
Zannuwa da cottons kawai da kara muka had’a aka saka a makara aka je aka binne dan bama so kowa ya san maganar……inajin batun Gwaggwo Suwaiba tashi d’aya na fahimci komai sharrin Mommy ne wani abun suka yi shiyasa take ta nuk’u nuk’u da rasuwar Ya’isha musamman ma da na tuna yadda na ji Ya’isha ta je gidansu Manu a day before shiyasa na had’a har da Ya’isha aka kaisu k’auyen su Inna a tare da zummar ayi musu addu’ar tare dan itamana yi tunanin watak’il asirin ne ya shafeta amma sai dai ita Ya’isha suna zuwa aka tabbatar ta rasu dan har ta fara kumbura shiysa na je aka yi mata sutura aka binneta a chan……..
Gaba d’aya parlourn kaurewa ya yi da koke koke…da kyar Manu ta k’araso gabansa ta tsaya jikinta yana karkarwa tace”inna fa?”
Murmushi ya yi yace,kwana talatin ta yi ta warke,yanzu haka ma suna hanyar dawowa tun jiya gwaggo Suwaiba tace mini sammako zasu yi yau inshaaAllah,yanzu haka da ma da shirin muna gama abunda muka fita yi sai mu wuce……”
K’amewa Manubiya ta yi ta kasa motsi sai da su Yasira suka zo suna kuka suka rungumeta tukunna ta dawo cikin haiyyacinta…
Share mata hawaye Yasira ta yi ta fara k’ok’arin durk’usawa a gabanta…da sauri Manu ta tarota ta shiga girgiza mata kai tace”na ji na san me kuka yi…Yasira tun Ina cikin mahaifiyata Allah ya k’addara hakan zata faru da ni ,idan na haihu Alhamdulillah idan ban haihu ba haka Allah ya tsara kawai inaso ki san cewa kome kuka yi na yafe muku na rungumi k’addarata….let’s just start a fresh…..”
Rungumeta suka yi gaba d’ayansu har Yasmeen da Yahanasu suna wani Irin kuka….
Dai dai nan Gwaggo da mai aikinsu suka fito,tana sunkuyar da kai tace”itama tanada magana!”
Ashe ranar da Mommy suka yi magana ita da Yahansu ta ji komai har ta yi recording tace”tanata so ta kunnawa Daddy amma bata san ta Ina zata fara ba….nan ta kunna musu muryar Mommy tarr suka ji duk wasu bayanai da ta yiwa Yahanasu a wannan rana……
Hajiya mama ita dai k’arashe k’afafuwanta kasa d’aukarta suka yi dan haka ta nemi waje ta zauna a naan kan kujerar.
Kowa kuka yake yi a parlour..suna gama jin recording d’in Gwaggo tacewa Yashjub a wachchar ranar ma
tana gani kamar Kausar Abu ta zuba masa she’s not sure though amma ta lura da ita nan ta zaiyyane masa yadda suka yi da ita…..numfashi ya fesar ya share hawayen sa ya nemi guri ya zauna yana mai jinsa kamar wani sabuwar halitta,kasancewar sa ba d’an Mommy ba yana daga cikin abu mafi dad’i da ya tab’a faruwa da shi a tarihin rayuwarsa shiyasa wani sanyi nutsuwa annashuwa suka mamaye sa……
da kyar ya iya bud’e bakinsa yace wa gwaggwo”yanzu kam babu batun Kausar ta bar cikin rayuwarmu forever….halinta ya bita.
Duk parlourn Ameen suka ce kafin Daddy ya kalli Yaha yace mata”meyasa kika yi shiru,wannan gagarumin al’amari haka???”
Sabon kuka ta fashe da shi ta ta k’arasa ta ruk’o hannun Yashjub tace”I’m so sorry….”
Lumsassun rinannun idanunsa ya d’ago ya zuba mata kafin yace”Yaha ba zan b’oye miki ba sam ban ji dad’in yadda kika yi shiru game da wannan al’amarin mai matuk’ar mahimmanci a rayuwata da ke ba har iyau kuma na fahimceki na fahimci uzurinki dan haka karki damu komai ya wuce..”
Su Yasira ya kalla waenda suka matso garesa suma yace”kuma abunda kuka yi mini ba komai ba zan ce na manta da shi kamar bai faru ba amma kar ku d’au hakan a ranku inshaaAllah ba zai zamo silar shiga tsakani na da ku ba..rashin walwala da shak’uwata da ku ya sanya Mommy ta samu damar shiga tsakanina daku ta yi poisoning mind d’inku kuka yarda cewa bana sonku wanda ni hakan nature d’ina ne kuma kasancewarku mata da kuma yanayin rawar kan Yassir ya sanya na ga dacewar in sake zama mai tsauri a kanku saboda kyautuwar tarbiyyarku amma inshaaAllah daga yau zan gyara zan jaku a jikina mu zama abu d’aya ta yadda babu wanda zai sake shiga tsakaninmu kasancewata step brother a gareku ba wai yana nufin zumuncin zai samu rauni ba sai dai ya k’ara k’arfi InshaaAllah…”
Rungumesa gaba d’ayansu suka yi cikin kuka sukace kar ma ya sake cewa shi step brother d’insu ne har abada zasu zama d’aya babu y’an ubanci inshaaAllah…..”
Da kyar suka iya had’a ido da Yahanasu suka nemi gafarar ta,they really can’t believe wai Yaha cikinsu d’aya suka dinga yi mata wulak’anci ta yi shiru sannan itama Mommy ta sani amma ta yi shiru duk dan cikar burinta tabbas Allah ne kad’ai zai yiwa Mommy hisabin da ya fi dacewa da ita….
Hajiya Mama ma tun d’azu ta fara hawaye fad’i take”Alhamdulillah Alhamdulillah”
Ta godewa Ubangiji da ya bata Aron rai ta ga wannan rana…Alhamdulillah da ya fallasa rub’abb’en irin gidan Imam a gabn idanun kowa,matsalar gidansa ta zo k’arshe.
Cikin sharar hawaye Yash yace”hak’ik’a yau tana daga cikin ranakun da suka kai k’ololuwar dad’i da farin ciki a cikin ranakun rayuwata…Hak’ik’a Ubangiji mai kun faya kun ne!ya kan yaye damuwa ya chanja al’amari ya kawar da matsala mai girman gaske a cikin k’ank’ani lokaci…
Mu dai kawai abunda ya kamata mu yi a ko da yaushe shine mu yi trusting d’insa mu saka gaba d’aya fate d’inmu akansa mu mik’a dukkannin al’amuranmu garesa daga nan komai zai yi falling into place cikin sauk’i…..in da Rabbana ba wahala….
Alhinina d’aya a halin yanzu rasuwar Ya’isha da mahifiyata da bama ta san tanada ni ba…..”
Ya fad’i haka cikin zubar hawaye..
Cikin sharar hawaye shima Daddy yace”Tabbas Khadija ta dad’e tana zaluntata tun asalin farko…da ace Ubangiji zai bani da ma da na koma baya na janye abunda na yiwa Mahaifiyar ka Yash…da na gaya mata na yarda da ita d’ari bisa d’ari kuma na san sharri akayi mata…how I wish Khadija bata rasu da bak’in cikina da takaicin na yarda da ita ba…inama ace tana raye da na sauk’e wannan nauyin na nemi gafararta…..”
Yahanasu ta san ta yiwa Mama alk’awari amma kuma an riga an linke Daddy ta baibai ba zai tab’a fahimtar Mama tanada rai ba muddin ba nuna masa ita akayi ba….dan haka ta goge hawayenta tace”tanaso kowa ya biyota tanada surprise d’in da zata nuna musu kar wanda ya tambayeta kawai kowa ya biyota…”
Daga haka ta shiga d’aki ta kwaso key sannan ta Kira Mama tace mata”tana Ina?”
Maman tace”Tana gidansu Manu tun jiya Gwaggo Suwaiba ta kirata tace su had’u a gidan da sassafe gasunan yanzu haka ita da su Ammi suna shiga gidan….”
Tana fitowa suka tsara akan za a d’auko y’an sanda su tafi da Mommy su mik’ata kotu a yanke mata hukunci…daganan suka nufi gidansu Manubiya akan sai sun gama da nan d’in tukunna zasu je a tafi da Mommy dan bayan Inna dake hanya Yaha tace musu nata surprise d’inma yana gidansu Manu.
Kausar bata tarar da su Yasira a gidan Mommy ba dan ko da ta yi knocking ma Mommyn ce ta zo ta bud’e mata wanda ganinta a hakan ya yi matuk’ar d’aga mata hankali dan haka ko shiga bata bari sun yi ba tana gama rufe gate ta shiga tambayar ta “mai ya faru?!.”
Sosai Kausar ta zama emotional dan haka ta fashe da kuka cikin kuka ta shiga zaiyyane mata abunda ya faru…
Har wani irin huci Mommy take yi tsabar b’acin rai!!!
Enough is enough fa wallahi zata yi fito na fito da mutanen nan komai ta fanjama fanjam!!!
Ba ta kai ga bud’e bakinta ta yi magana ba suka ji knocking…
Ko da Mommy ta lek’a da
kyar ta iya gane Yassir dan sanye yake da kayan sanye ga hula ta rufe masa kai goshi da kunnuwa sannan ya sanya bak’in gilas,da sauri ta sa Hannu ta bud’e masa ya shigo….
Wani Irin sanyi ya ji a ransa sakamokon idanu biyu da ya yi
da Kausar…saboda dama zuwa ya yi akan ya d’auki Yusra su je ta je ta fito
masa da Kausar saboda shi an hana masu gadi barinsa ya shiga sannan yana ta kiran wayarta ba ta d’auka.
Mommy tana shirin yin magana ya sa Hannu ya rik’o hannun Kausar yace mata “Mommy d’an bamu mintina goma zamuje mu dawo”
“To” kawai ta ce masa ta bisa da kallo tana jin wani irin yanayi….har ya juya zai fita sai kuma kawai ya dawo ya sa Hannu ya rungume Mommy sosai a jikin sa tukunna ya cikata ya ja Kausar suka fice suka bar Mommy a nan tsaye kamar statue.
Sosai k’irjin Kausar yake dukan uku uku dan a yadda ta shirya komai ta tsara komai bai kamata ta ga Yassir free har yanzu ba!!!
A ranta tace
“Ko dai ya fahimci abunda ta yi ne?”
dan kayan sanyi ne a jikinsa ga bak’in glass amma she can tell’ransa a masifar b’ace yake’!.
Sai da ya zaunar da ita tukunna ya zagaya ya shiga ya zauna ya kunna motar ya saka lock ya bata wuta!!!!
..
Wani irin uban gudu yake tsulawa wanda tun daga nan Kausar ta fara data sanin biyosa da ta yi….gashi tace masa”Yassir”
Daga fitowarsu zuwa yanzu ya fi sau talatin amma ko kallonta bai yi ba!
Sai da ta ga sun d’auki hanyar barin Kano tukunna ta fashe da kuka tace”Yassir baka da hankali ne?ina zaka kaini??”
Ba tare da ya kalleta yace”mutuwarki!!”
Sosai ta firgita gashi ta fara ganin sun dumfari wani mahaukacin k’aton rami,jikinta yana wani irin karkarwa ta sa hannu ta zare key d’in da sauri ya taka burki kafin ta Ida cirewa….
Cikin kuka sosai tace”Baka da hankali ne?”
Sai kuma ta juya ta fara k’ok’arin bud’e k’ofa ta samu ta fita amma inna sam ta gagara….
Komawa ya yi ya kwanta a jikin seat d’in har ta k’araci bige bigen ta ganin bafa za ta iya escaping bane ya sanya ta juyo garesa ta fara yi masa magiya…
Zuba mata ido ya yi ta cikin glass d’in kafin ya furzar da huci yace”Kausar su grenade sun tura mini duk wasu chat d’inki da su,saboda suna so in san who is behind it all…..kamar yadda kika so an saki videos d’ina a wajen hukuma yanzu haka nemana ake yi dead or alive…sannan last week a gidan Abokina muka yi raping wata y’ar minista to death wanda mu kanmu bamuyi tunanin zata mutu ba shiyasa muka b’oye gawar muka saka ta a fridge kwatsam kuma yau da aka zo arresting d’ina sai aka ga gawar!!
Ba su samu sun kama ni ba shi kuma Abokin nawa ba ya nan…
Da kyar da mugun kyar na samu na yi escaping amma kuma sai da na gudu d’in tukunna na ga guduwar tawa ma ba ta da amfani dan dole sai an nemo ni kuma hukuncina kisa ne!!!
Bani da mai bani shelter yanzu kam..saboda Abokina da yake bani hatta abinci da kayan sakawa da motar hawa shima ta kansa yake kuma laifukana sun fi k’arfinsa,bani da gatan da wani zai tsaya mini ko ya yi defendin d’ina ko ya taimaka mini in