Showing 15001 words to 18000 words out of 244445 words
sannan gashi tana ganin an kusan auren su kinga ai komai mai iya wakana ne,yanzun fa Yasmeen
ce min ta yi ta fi minti talatin a bakin k’ofar d’akin da yake d’azu tana knocking amman basu bud’e mata ba
Me kike tunani???
Ina amfanin tarwatsa aure in ta riga ta samu ciki?? Dan na san kafin mu samu mu raba su ko mu san abunyi akan cikin asiri na ya gama tonuwa…..’’
‘’Tabbas ba mu yi wannan tunanin ba’’
Baaba Larai ta fad’a tana mai sake gyara zaman ta kafin ta d’aura da cewa ‘’zan san abunyi,matsalar shine sunan yarinyar da har yanzu bamu gama sani ba,Yassira tace kamar Manubiya ko Maryam ta ji Yahanasu tace ko?’’,sai kuma ta yi shiru kamar mai tunani kafin ta fesar da iska tukunna ta ce’’inshaaAllah komai zai yi dai dai’’.
Ruk’o hannunta Mommy ta yi kafin tace ‘’Baaba na gaji
zuciyata ba za ta iya sake nad’ar wani sabon bak’in cikin ba..’’
Cikin son kwantar mata da hankali Baaba Larai tace’’kar ki damu,komai zai tafi cikin tsari
InshaaAllah ba zan zuba ido Ina ganinki cikin damuwa ba…’’
Daga haka ta shiga lallab’ata tana bata baki tare da bata assurance tukunna da kyar Mommy ta samu ta d’an nutsu dan ba kad’an ba ta tsorata matuk’a kuma hankalinta ya tashi kwarai.
A bakin k’ofar shiga side d’in Yashjub Yassir yayi parking
shi da kanshi ya taya sa shigar da jakar computersa da kayan dubiyar da aka kawo mishi
tukunna yayi mishi sallama ya tafi.
Gwaggo da Ummi ne suka kai mishi abinci daganan suka tambayeshi ko akwai abunda yake buk’ata yace ‘’ba komai’’
dan haka suka mishi Allah ya kare gaba ya k’ara sauk’i suka tafi domin ya samu ya huta,ai kuwa bai huta d’in ba dan duk sai yau masu gadi suka samu zuwa dubiya saboda ta’aziyya da suka tafi na driver kuma
dama shima ya ce kar a gayawa kowa asibitin da ya ke.
Wannan ya shigo wannan ya fita haka masu gadi da drebobi har da mak’ofta aka dinga sintiri har dare dan haka ciwon kai ya sake turnik’e shi.
Ya na sane da su Mommy
Yadira ce kawai ta shigo ta duba shi itanma ya lura kmr fushi take dashi amman kana ganinta ka san ta damu sosai
dayake yarinyace ita shiyasa ya yi saurin b’aro jirginta.
Hakanan ta yi mishi ya jiki
harda d’an dessert d’inta ta had’o ta kawo masa.
Sam fuskarshi babu annuri haka ta yi ta tafi dukda kuwa ya ji dad’in zuwan da tayi amma ya kamata ya koya wa yaran nan hankali shiyasa d’azu yak’i sakarwa Yasmeen!ba zai yiu su yi fushi da shi a sanda sukaso ba tare da wani kwakkwaran daliliba sannan in sunga dama su kulashi a lokacin da suke so.Sam ba zai d’auki wannan iskancin ba,in the first place ma ba su Isa yin fushi da shi ba ko ma me ya yi ai shine Babba shine a matsayin ubansu ko da ace
shine bashi da gaskiya ba zai basu damar yi mishi wannan rashin ‘da’ar ba ballantana kuma shike da gaskiya,wannan tunanin ne ya sanya ciwon kan sa ya sake hauhauwa dan abun ya b’ata masa rai sosai especially ta b’angaren Mommy ya ji zafi kwarai a ganinsa bai kamata ta biyewa yara ta k’i zuwa duba sa ba,ya riga ya san halinta da
mugun tirjiya shiyasa kawai ya share ya yi k’ok’ari ya lallashi kansa da niyyar zuwa wajen ta anjima inshaaAllah ya bata hak’uri.
Daddy ya yi masa magana haka ma Manubiya sannan shima a karan kansa baya son irin zaman da suke yi da ita har cikin zuciyar sa amma ita take janyo komai,Mommy tanada wani hali sai wanda ya zauna da ita ne kad’ai zai iya sani
tanada shiru shiru tanada hak’uri amman kuma ba ta da dad’in zama kwata kwata
shiyasa duk wanda yaga irin zaman da sukeyi ita da shi sai ake ganin kmr shi ne ba ya kyauta mata bayan ita take tab’o sa.
Ahankali ya fesar da iska ya lumshe idanuwansa tashi d’aya tunanin dayake ta yi da rashin sanin abun da ya kamata ya yi game da rasuwar sa ya taso masa dan haka ya d’au waya ya kira Manubiya akaro na uku daga dawowarshi zuwa yanzu,dan tabbas yana buk’atar advice.
Bayan sun gaisa ne ya nemi ta bashi shawara akan ya yi bincike akan rasuwar driver d’insa ko kuma ya barshi,saboda ya san ba accident bane,dukda ya yi
alk’awarin d’aukar d’awainiyar family d’in mutumin daga nan har abada inshaaAllah to amma kuma yana gani kamar bai kyauta ba idan ya bari mutuwar sa ta tafi a banza saboda ya yi protecting kanshi
daga outcome d’in da binciken zai bayar wanda ka iya tarwatsa shi gaba d’aya.
Cikin son fahimtar da shi Manubiya ta yi masa nuni da yadda idan ya yi binciken kuma ya je outcome d’in ya yi destroying d’inshi to wa zai ci gaba da kula da family d’in mutumin??.the best thing da zai yi wa mutumin shine ya kular masa da family d’insa,shari’ah kuma su barwa Allah subahanahu wata’ala shi zai bi masa hakkinsa.
Ya ji dad’i kwarai kuma ya samu relief dan dama so yake a hanashi yin binciken.Sun d’an tab’a hira yau yaji dad’i dan babu mita babu complain haka suka sha soyayyarsu kafin su yi sallama ya katse kiran suna ji kamar kar su kashe wayar.
Suna gama waya ya mik’e ya nufi cikin gida.
Yana shiga side d’in Daddy ya wuce suka hau shirye shiryen gobe,ya dad’e sosai a wajen Daddy kafin su yi
sallama ya tafi,ba k’aramin dad’i Daddy yaji ba da ya ga hatta cokali Yashjub ya riga yayi order ya sayi komai
kuma gidan ma ya tsara komai
ya had’a komai ga lefe ma Yahanasu tana kan had’awa
ya san inda Yassir ne da zuba ido zai yi a yi masa komai….
Yashjub yana fita side d’in Mommy ya wuce sai dai yana zuwa k’ofar d’akinta ya ji a rufe ya so su tattauna ya bata hak’uri su fahimci juna amman yadda ya yi ta faman bugu ya ji shiru ne ya tabbatr masa da ta yi bacci,haka nan
ba dan ya so ba ya juya ya tafi ya barwa gobe.
A b’angaren Mommy kuwa a
lokacin da ya zo tana parlournta ta fara jiyo muryarshi yana magana da Yadira wadda take masa sai da safe
dan haka ta yi sauri ta afka d’akinta ta rufe da wuri dan ba za ta iya facing Yashjub a halin da take ciki ba ta san tsaf zata iya shak’e sa…tashi d’aya Yaro ya tsund’umata a cikin bal’ai da tashin hankali rabonta da ta yi bacci fiye da na awa biyu har ta manta,haka kurum yaje ya d’auko musu mayya!yo mayya mana idan ba mayya ba wacce irin yarinyace haka da za’a yi ta yin aiki a kanta amman a banza?.
Ba abun da yafi sake d’aga mata hankali kamar d’azu da ta lab’e ta ji Daddy yana waya da Abhi wai yana hanya ya taho,ta tabbata kenan gobe za a kai kaya a saka rana,dukda Baaba Larai ta ce ‘’ta jira taga goben tukunna in an kai shine sun yi failing’’
Amman ita a a yadda ta ga anata shirye shirye gadan gadan ta san an riga an kai ma an gama saidai su nema wani alternative d’in…and again ga maganar da Yasmeen ta gaya mata d’azu shiyasa duk take a gigice ta rasa inda za ta tsoma kanta ta d’an ji sa’ida.
Tun lokacin da Manubiya ta gama waya da Yash hankalinta yake a tashe bata nuna masa bane dan bata so ta sake assassa masa abun amma ba k’aramin firgita ta yi ba da ta ji yace’’ba accident bane wani ne ya so kashesa‘’.
Ganin ta a zaune tanata tunani ne yasanya Jidda matsowa ta shiga tambayarta….ai kuwa ita kanta Jiddan ba k’aramin firgita ta yi daga jin zancen ba amman sai ta da daure itama ta shiga kwantar wa da Manubiya hankali sannan ta d’aura da cewa’’kawai ta dage masa da addu’a Allah ya kare sa daga sharrin masharranta dama mutum kamar Yashjub dole yanada mak’iya.’’
Suna zaune suna d’an tattaunawa Baba ya shigo dan yau ya shiga busy shi da su Ya Musbah so suke su samu su gama shirye shiryen tarbar su Daddy da za su yi a gobe in Allah ya kaimu.
Sai da ya ci abinci ya d’an huta tukunna ya kira Manubiya ya zaunar da ita….nutsatstsiyar nasiha mai ratsa jiki ya yi mata,wanda sai da ta kai Manubiya ga yin kuka.
Murmushi kawai ya yi ya dafa kanta yace ‘’Allah ya miki albarka da ke da y’an uwanki Allah ya sa ki shiga gidan aurenki a sa’a.’’
Ahankali duk suka ce‘’Ameen.’’
Daganan Baba ya mik’e ya sake fita dan ba su gama ba ya shigo.
Murna a wajen su Jidda abun ba’a cewa komai dan yanzun kam maganar biki ta kankama tunda har suka ga Baba ya fara yiwa Manubiya nasiha .
Shiyasa suka yi ta murna suna cewa Allah ya sanya alkhairi’’kamar daga sama suka ji muryar inna tace’’Ameen’’cikin muryarta da suka jima suna mararin jin.Aikuwa duk d’insu rufar mata suka yi saida ta sake maimaitawa suka tabbatar tukunna Muhsin ya fita da gudu yaje ya kira su Baba a masallaci inda suke ta shirye shirye…..
A ranar murna wajen Manubiya da ahalinta ba’a magana dan har kuka sai da Baba yayi kukan farinciki da yaji muryar inna a zahiri,haka suma su Manu suka dinga kuka suna godewa ubangiji subahanahu wa ta ala.
Sun jima suna murna suna godewa ubangiji har da ya Nafi’u kafin su Baba suka fita domin zuwa su sanar da su kaka mallan maganar kawo kud’i da saka ranar Manubiya wanda za’ayi a gobe idan Allah ya kaimu……MANNUBIYA
(Book 2)
Page 07
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Su Baba suna fita daga d’akin ba da dad’ewa ba,su Jidda har ma da Manubiyan duk sai suka kaure da hawaye dan tashi d’aya suka tuno nan da kwana goma fa Manubiya za ta tafi gidanta ta barsu.
Da kyar ta samu ta share nata hawayen kafin ta samu ta shiga lallashinsu,tukunna suma suka yi shiru Muhsin ya yi bacci ita
da Jidda kuma suka cigaba da tattaunawa…y’ar uwar inna d’aya ce tak a duniya kuma Baba yace’’ya riga ya gaya mata d’azu’’dan haka sun san
inshaaAllah nan da kwana biyu za ta taho idan anci sa’a
mugun mijinta jatau ya barta kenan….Gwaggwo Furaira tana da son zumunci amman sai ta yi rashin sa ar miijin aure
Jatau sarkin yak’i,a chan k’auyen su inna take har yau,
Mijinta irin bokayen soron nan ne ya kafeta a gidan ko
kara ya ajjiye ba ta isa ta tsallake ta ba,dan tun lokacin da ya fahimci ta fara shiryen shiryen guduwa sakamokon ganowa da ta yi ba ya haihuwa ga kuma mugayen halayen shi da su ka yi yawa,ya kafeta a gidan.
Tun daga ranar ko waya sai ya so tukunna za ta yi da inna…..
Gwaggo Furairah sai Mama ta
ta gidan Ammi,su kad’ai ne waenda Manubiya za ta nuna tace za su yi mata uwa tunda
Inna tana kwance
Dukda ta so ace inna ta ga aurenta akan k’afafunta
amman bata isa jayayya da abunda ubangiji ya riga ya tsara ba.Ta san su Umma Kuluwa ba lalle su kulasu ba amma still za’a gaiyyace su watak’ilan in sunga dama su yarda mazajensu ma su yarda idan aka zo d’aukarta su rakata d’akin mijinta kmr yanda akeyi wa ko wacce ‘ya mace….
Siyama kam sunsan batada matsala za ta tsaya mata a y’ar uwa haka ma Aisha matar ya Nafi’u
Su kenan jama’ar Manubiya bata da wani dandazon Jama a sai ko mak’ofta,dan haka suka yanke akan ko gwaggwo Furairah ta zo tace a yi taro sukam ba za su yi ba iyakacin
abunda suke buk’ata suke kuma adduar samu
shine a yi auren a gama lafiya ta samu matan da za su rakata d’akinta,dama kuma ita Manubiya tun ba yau ba bata da buk’atar hayaniya a biki sam ba ta so.
Maganar kayan d’aki kuwa
Jidda tana sako zancen Manubiya tace’’Jidda babu wani kayan d’aki da za’ayi,Idan ma ya ce ayi jere nikam zan fito mishi k’iri k’iri ince ya yi hak’uri,
dan ba zan ma fara d’aga wa su Baba hankali da wannan batu ba,an samu da taimakon Allah da na ya Nafi’u da ya Musbah muna ci muna sha
hakan ma ya ishemu
Alhamdulillah,ke kanki kinsan yanzu ana fara maganar jere
Baba zai fara tunani,k’arshe na san bashi zai ci dan cewa zai yi sai ya yi,kuma na san k’arshen abun ba zai yi kyauba.’’
A take Jidda ma ta goya mata baya d’ari bisa d’ari dan haka suka yanke shawarar ana fara maganar jere ma za ta yi
kicin kicin tace ‘’bataso!’’.
Sun jima sosai da Jidda
kafin daga k’arshe Jidda ta yi barci ta bar Manubiya tana ta tunani,sai da ta ga shigowar Baba tukunna ta samu ta yi barci bayan kowa a d’akin ya yi.
Washegari..
A jiyan,dare ya yi kafin suka gama confirming shiyasa sai washegari da safe su Jidda suka tura Muhsin ya je ya gayawa Mama za a kawo kud’in auren Manu,ba k’aramin
dad’i matar ta ji ba dan haka bayan zuwan Muhsin da minti biyar sai ga ta,duk da ta san Inna ba za ta iya bata amsa ba amma haka ta zauna ta shiga yi mata ‘’Allah ya sanya alkhairi’’tana ta murna
aikuwa ga mamakinta ta ji Inna tace mata’’Ameen’’itama,
ba k’aramin dad’i Mama ta ji ba murna kamar za ta yi kuka
haka nan ta yi ta maimaita ‘’Alhamdulilla’’su Manubiya suna ta murmushi suna jin tsananin dad’i da annashuwa.
Mama ba ta jima da zuwa ba Sofia ta zo suka fara aikin su su kuma su Mama suka koma gefe itada su Manubiya daga nan ta shiga tsokanar Manubiya wai dama ashe tana da saurayinta amma shine bata tab’a ba ta labarinsa ba…..
Ahaka Sofia ta yi ta gama ta ce musu sai zuwa anjima da magrib za ta sake dawowa daga nan ta yi musu sallama ta tafi ita
kanta tana mai mamakin improvement d’in Innar.
Da Mama da Siyama sai Aisha
su hud’u ne har Jidda suka zauna har rana lokacin da aka kawo kud’in auren Manubiya daga b’angaren Yashjub.
Maama ta yi matuk’ar mamaki da ta ji sati biyu kacal aka saka
haka ma Aisha da siyama,haka su ma Baba Habu da kaka Mallan wanda da da farko ya cewa Baba ‘’Ba zai je ba ai an ja musu layi a tsakaninsu’’amma tunda ya lek’a ya ga zunduma zunduman motoci a bakin masallaci hankalinsa ya tashi
haka nan ya je harda zagin Baba Habu akan ya ce’’shi fa ba zai je ba’’,haka nan ya azalzalo Baba Habun yace’’ai shine Babba ya yi hak’uri ya turawa Baba aniyar sa ya je ko dan zumunci’’da fad’a da lallashi ya jijjib’oshi suka nufi masallaci yanata sauri
dan karsu makara,ai kuwa jama’ar wajen sun ga ikon Allah a wajen Kaka Mallan.
Daddy da K’anninsa(Abhi) wanda ya iso daga uk jiya around 3:00am
sai Yassir da wani babban Abokin Daddy ne suka zo suka kawo kud’in(naira miliyan biyu)
aka saka rana nan da sati biyu inshaaAllah…kaff cikinsu babu wanda Kaka Mallan bai bi ya karb’i numbersa ba,duk kalar disgin da Yassir ya yi masa da b’ata ran da yake ta yi sai da ya hak’ura ya kula sa ya bashi wrong number,ya tsani tsohon ya tsani layin gaba d’aya
shi tunda yake a rayuwarsa
bai tab’a tunanin akwai
tsukukun layi irin wannan ba karakakaf layin gida uku ne manya sai masallacin da yake da kyau shima amma gaba d’aya ragowar gidajen kamar kango a ransa yace’’me Yashjub ya gani da ya zo nan??’’yayi wa kansa tambayar ba tare da yasan wa zai ba shi amsa ba Kafin ya d’an tab’e baki a ransa yace ‘’anyways shi ya sani atleast zai k’ask’anta kafin ya mutu dama nan ne ya fi dacewa da shi shiyasa ya zo nan d’in ya d’and’an k’ask’anci daganan ya mutu’’
Ko gama tattaunawa ba a yi ba
Yassir ya mik’e ya fita daga masallacin
Kallonshi kawai Daddy da Abokinsa suka yi kafin suka d’auke kai aka ci gaba da tattunawa.
Dakyar Baba ya yarda da buk’atar da Daddy ya zo da ita ta inda yake cewa’’Dan Allah kar su zo da komai Yarinyar kawai ake so
basa buk’atar kayan d’aki’’
Daganan suka tsayar nan da kwana goma za a d’aura aure inshaaAllah bayan Baba ya nemi a d’aura a nan masallacin sun amince.
Su Yaa Musbah ne suka tartare
Pepper chicken da su cake da doughnuts da lemukan da ya Nafi’u ya kashe uban kud’i ya yi order dan a cewarshi bai kamata a ji kunya ta ko wanne b’angare ba,ya san ba za su yi
abunda ya kamata su yiwa mutane masu uban arzik’i kamar su Daddy ba amma atleast ya kamata su kamanta
Har mota suka kai musu suka jibge Daddy ya na ta faman saka musu albarka da shi da Abokin shi daga nan suka yi musu sallama suka shiga motocin su suka wuce suka bar su Baba suna mamamakin Yassir!ko da ya shigo fa sune
suka gaida shi,tunda ya zauna a cikin masallacin bai ce komai ba hakanan ya had’e fuska yana kallon mutane akan hanci,ko irin murmushin nan bai yi ba lokacin da Daddy ya gabatar da shi a matsayin d’an uwan Yashjub wanda yake bi masa
daga k’arshe ma tashi ya yi ya fice gaba d’aya yanzun ma da suke yi masa sallama bai ko kalli in da suke ba ballanta su sa ran zai amsa har hannu kaka Mallan ya mik’a mishi amman ya wuce da sauri ya shige motarshi…..addu’arsu d’aya itace’’Allah dai ya sa ragowar y’an uwan Yashjub ba haka suke ba’’dan yanayin Yassir da yadda sam Daddy ya kasa tsawatar mishi ko da da ido ne ya ba su mamaki ya tab’asu matuk’a.Daddy dai ba shi da matsala amma sun lura hatta k’aninsa bai yi wani farin ciki da wannan hadi’in ba,
Gudun kar ma su kawo wani tunanin su je su janyo abu da bakinsu ne