Showing 120001 words to 123000 words out of 244445 words

Chapter 41 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16494

ta dawo abu guda da inna ta fara noticingm shine Yaa Musbah mugun mugun tsoron ta yakeji.Gashi baka Isa ka ce abunda ta yi bai kamata ba tashi d’aya zai hau kumbure kumbure
Tun a kan issue na tashin su da Innaa ta so ta hana tashi d’aya ya nuna hakan fa ba zai yiu ba!.
Muhsin kuwa da ya yi alk’awarin d’auka ko kalar k’ofar gidan sa na Na’ibawa bai sani ba.

Ya Nafi’u kuwa ko waya basa yi,tun lokacin da ya dawo da Baraka dama ya fice a harkar sa,ko da ya zo tashi ma bai gaya masa ba dan ya san zai hana shi shima kuma ya Nafi’un har yau bai ce masa
Musbahu Ashe ka tashi ba,
K’ark’ari ya kan je ya duba su Inna shi da Aisha da Khairat duk bayan kwana biyu amma shi da Ya Musbah kam ko a waya sun daina gaisawa,Baba ne dama ya kamata ya tsawatar ya dawo da Abotar tasu to shi kuma Baba tun lokacin da Inna ta amince a dawo da Baraka tashi d’aya ba tare da ta shawarci kowa ba
Ya ce “case in dai na Musbahu da Baraka ne to ba zai bada shawarar komai ko ya ce zai saka baki a kai ba…”
Gashi issue na Baba da su Baba Habu abun ba dad’i
Kaka mallan ma ya fara gulmace gulmace wai Baba ya bi kud’i ya aurawa mai kud’i y’arsa amma gashi ya barsu a talauci har yau bai tab’a ganin an kawo ko kwayar shinkafa k’ofar gidan ba.!”

Inna tana wannan tunanin Yashjub ya dawo d’akin yanata faman sussunnar da kai,
so yake ya tambayi Manubiya mai take so ta ci dan tun yoghurt d’in safe sai d’an malelen Mama da ta ci daga su bata sake cin komai ba gashi Doctor yace “ana so ta dinga cin abinci sosai saboda lafiyar ta da lafiyar Babyn”…to kuma shi har ga Allah kunyar Inna yakeji
dan d’azu ma sai da Ummi ta sa ya ji kunya
Haka nan ta tisa shi a gaba tana tsokanar kalar zumud’in da yake ta yi a gaban su Innar…

Yana wannan tunanin ya ji wayar sa ta d’au k’ara kamar ba zai d’auka ba dan da ya zaro bak’uwar number ya gani sai kuma ya d’auka ya kara a kunnen sa yace ‘’Assalam alaikom,’’
A gigice ya ji wata murya kamar ta security d’in sa yana cewa”Sir wuta!wuta!! ya kama a estate na kano ka zo
da wuri…….’’yana gama fad’in haka ya kashe wayar daga background d’in in banda hayaniya da k’arar y’an kwana kwana ba abunda yake tashi.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”ya shiga ambata a fili.
Da sauri Yasira ta matsa tace ‘’mai ya faru?’’
Cikin karkarwar murya da kyar ya kalleta yace
“Estate d’ina ne ya kama da wuta’’
Salati gaba d’ayan su suka saka suka mik’e tsaye.

Cikin tsananin gigita Yasira tace “subahanallah!!
mu je mu je da sauri…”
Ta fad’i haka tana yin gaba.

Da sauri ya ruk’o hannunta yace
‘’noo it’s not safe kar ki damu zan je ni d’aya zan kira Yassir a hanya sai mu had’u a chan.
A hankali ta d’an dawo ta tsaya kafin tace “Allah zai mayar da alkhairi inshaaAllah’’

Jinjina kai yayi yace”inshaaAllah”sannan yace”ku yi addu’a Allah ya sa mutane ba su mutu ba!”

Jin jina kai ta yi,daga haka ya zare hannunsa a nata ya k’arasa inda Manubiya take zaune a kan gadon ya ce “bara in je ko?”
sai kuma ya d’an sunkuya yace
“Dan Allah kar ki d’aga hankalin ki I’ll be back soon okay?”

Ba ta san lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba,ita ya kamata ta lallashe sa amman kalli shi yake lallashin ta.
Da sauri ta sunkuyar da kanta tana jin jina kai…
Murmushi ya yi yai sallama da su Innaa daganan ya juya ya fita gaba d’aya suna jajanta masa tare da adduar alkhairi.

Yana fita ta sake sakin kukan ta tana jin wani iri a cikin ranta

A hankali Innaa ta koma kusa da ita ta zauna ta shiga lallashin ta tana bata baki,Mommy kuma ta shiga kiran Daddy domin ta sanar da shi halin da ake ciki.

Cikin rashin jin dad’i Ya’isha tace
“Ai dama matsalar had’a jini da mai farar k’afa kenan!
Dama ace a iyaka aure aka tsaya to da na san abun zai zo da sauk’i”.

Shiruu duk suka yi d’akin ya d’auki shiruu
Kafin Ya’isha ta sake cewa “Allah dai ya rufa asiri ya kuma tsayar a iya nan’’
Zuwa yanzu Manubiya ta ji ba za ta iya jurar cin fuska a gaban ahalin ta ba Ashe dama jiya da suka dawo saboda a gaban Yashjub ne shiysa suka yi mata kissa kenan suke wani nan nan da ita…
Shiyasa kawai cikin wani irin fushi da ba ta san tana da shi ba ta mik’e ta cewa Inna “ta zo su tafi”

Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Kamar ya ku tafi?
Me kike nufi?
Idan tafiya kike son yi ai mu za mu tafi da ke ba Innaa kad’ai ba ko?”

“A’a inaga tana nufin za ta koma gidan ubanta ne!
Ai ta shafa farar k’afar tata yadda ya kamata shiyasa ta ga ya ci ace ta tafi…”

Ba k’aramin mamaki Innaa ta yi ba ganin yadda ko gezau Mommy bata yi ba balle asa ran za ta cewa Ya’isha tayi shiru wadda ta cigaba da fad’o zafafan maganganun kamar tab’ab’b’iya.

Cikin nutsuwa Innaa ta mayarda Manubiya ta zaunar da ita tace”kar in je zance mara dad’i ki zauna ki yiwa mijinki addu’a ki jira dawowarsa”
tukunna ta kalli su Jidda wadda har ta fara kwallah tace mata ‘’ku tashi mu tafi’’
Sai da suka mik’e tukunna Innaa ta juya ta k’arasa in da Mommy take tace mata ‘’Hajiya mun tafi,Allah ya k’ara sauk’i’’
Daga haka ta fice ta na jin yadda kukan Manubiya yake dira a cikin zuciyar ta kamar dalma…..


Sam ba haka Mommy ta so ba so ta yi ace Manubiya ko k’anwarta ko Innar tasu wani ya biyewa Ya’isha daga nan ayi kacha kacha su yi zuciya su tafi da y’ar su ta yadda za ta raba auren ta kuma ga bayan cikin ta kowacce hanya hankali kwance…..
Yanzu haka ji take yi kamar zuciyar ta za ta kama da wuta ita kad’ai ta san halin da take a ciki tsakanin jiya da yau..shiyasa ko Baba larai ba ta gayawa ba ta taho asibitin dama opportunity irin wannan kawai take nema ta samu a yi ta ta k’are dan ta riga ta kai peak.Sai dai
Kash!Inna ta lalata mata komai…


Su Inna suna fita Yasira ta yi tsaki ta juya itama ta fita Daddy da Yassir ta fara kira suka yi magana tukunna ta kira wata k’awar ta wadda bata dad’e da yin aureba a nan estate d’in Yashjub d’in suke haya,dan haka ta kira ta ji ya abun yake sun samu sun fita safe ko?.

Ta ji matuk’ar mamakin yadda k’awar tata ta amsa wayar hankali kwance har da y’ar tsokana a ranta tace”to ko dai ta fita ba ta gidan ne dan haka a hankali a fili tace mata “kina ina?”
Sai da gaban Yasira ya yanke ya fad’i da ta ji k’awartata ta ce mata”Ina gida mana za ki zo ne?”

Zaro wayar ta yi ta kalla ta tabbatar da k’awar tata ta kira tukunna ta mayar kunnenta kanta tsaye tace’’ji na yi ance gobara fa ya tashi a estate d’innaku!yanzunnan aka kira Yash aka ce masa ga wuta yanata ci an gagara kashewa”

A rikice matar ta rafka salati kafin tace “to inaga gaskiya mak’iya ne, wani ne yake so ya yi luring nashi out a samu ya fita a kama shi ko dai wani Abu makamancin haka dan mu kam nan ko k’aurin wuta babu a nan gaskiya ki yi maza ki kirasa kice ya juya…..”
ai tun kafin ta rufe bakin ta Yasira ta yi maza ta kashe wayar a gigice ta shiga kiran Yashjub…ta jera masa miss calls sun fi takwas amma bai d’auka ba shiyasa hankalinta ya sake tashi dan zuwa yanzu tabbas ta gama gasgata maganar wannan k’awa tata,
tashi d’aya ta fashe da wani Irin kuka a ranta ta gama sakawa ‘shikenan an kashe Yashjub’……..
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
MANNUBIYA
(Book 2)
Page 29
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

..Ko kuma an yi kidnapping d’in sa!.

A rikice ta afka d’akin,suna nan a yadda ta bar su su uku Manubiya a gefe tana ta faman hawaye.
Cikin rikice Yasira ta k’arasa gaban Mommy tukunna tace
‘’Mommy Ina ga magauta ne suka kira Ya Yash!dan yanzunnan na kira frnd d’ita ta estate d’innasa,tace “babu wani gobara,shi kuma yanzu haka inata kiran sa a waya ba ya d’auka!inaga sun sace shi ko sun yi masa wani abun….’’
Ta k’arashe maganar tana mai sake fashe wa da wani irin kuka.

Manubiya kawai tsintar kanta ta yi a gaban Yasira a rikice tace
‘’Ki sake gwada kira InshaaAllah babu abunda ya same sa bara nima in kirasa idan bai d’auka ba mu yi message,na san in ya gani zai ki kiramu” ta fad’i hakan tana mai juyawa ta nufi wayarta.

Sai a sannan tukunna Mommy ta tashi ta tsaya a d’an rikice tace ‘’ikon Allah to Allah dai ya sa lafiya…babu komai ma ki kautata zato….”


Kafin minti sha biyar gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi
dan babu kalar kira da sak’onnin da ba’a yi an tura masa ba amman sam ba ya d’aukar waya kuma bai yi responding messages d’in ba.

Banda kuka babu abunda Manubiya take yi tana kuka tana aikin kiran waya ba’a amsawa abun tausayi…

Suna a haka Daddy ma ya kira wayar Yasira yace “da shi da Yassir sunata kiran sa suma amma baya d’agawa but ga su yanzu suke barin gida za su je su duba estate d’in na sa..”

Yassira ce ta yanke shawarar ta sake kiran friend d’in tata inyaso ko mai gadin su ne ta sanya ya tayasu ya bincika ko Yashjub d’in ya k’arasa chan…gaba d’aya ta gigice haka ta shiga kiran k’awar tata.

Matar tana d’auka tace ‘’ya ake ciki Yasira?kun yi magana da shi?”
A tare da matar da Yasira suka fara jiyo hayaniya da ife ife…ta cikin background d’in Yasira take jiyo k’ara ta ban mamaki kamar ana fasa abubuwa da kuma na bindigu da ihun bayin Allah suna neman ceto….
A hankali jikinta yana wani irin karkarwa ta ji matar tace”Innalillahiwa innalaihirrajiun,Yasira kina jin abunda nake ji?bara in duba…”
Sai kuma a rikice taji tace”y’an bindiga ne suka shigo mana sun fi mutum d’ari…..”
K’arar harbin da Yasira ta ji ne ya tabbatar mata da k’awartata aka kashe dan a tare ta ji k’arar wani abu ya fashe kamar k’ofar aka fasa da kuma harbin….
K’amewa ta yi ta kasa cewa komai,tana sauraron yadda mutanen suke magana suna cewa”a sake duba gidan sosai idan babu kowa su yi sauri su kunnawa wannan ma wuta su tafi next house they don’t have much time…su yi su yi su tafi,yanzu Grenade ya yi masa waya yace su yi retrieving sun riga sun kashe gayen sun k’ona motarsa tun a bakin gate….“

K’afafuwan Yasira ne suka shiga kakarwa tashi d’aya ta gagara ci gaba da tsayuwa dan haka ta durk’ushe a wajen ta fashe da wani irin kuka.
Daidai nan Manubiya ta matsa kusa da ita kusan a tare ita da Ya’isha suka ce mata “m-m mai ya f fa rru!??’’
Suka yi mata tambayar a tsorace dan yanayin ta ya yi matuk’ar sake firgita su.
Da kyar ta iya d’agowa ta kalli Ya’isha ta yi mata bayanin abunda ta jiya faru sannan ta d’aura da cewa”na ji yana cewa gurnade ya ce sun kashe sa sun k’ona motarsa tun a gate,Ya’isha Ya Yash suke nufi shi ake so a kashe dama shiyasa aka yi k’arya da gobara aka ja sa wajen saboda su b’adda track d’insu kar a gane manufarsu.Ba y’an fashin gaske bane Ya Yash d’inmu aka shirya kashewa dama Wallahi…”

‘Sululululu’ haka Manubiya ta tafi ta fad’i a wajen sumammiya…

Mommy ce ta kira Daddy
a rikice ta ji muryarsa yana cewa“gasu nan sun zo shiga layin motocin sojoji suka taresu wai y’an fashi sun kaiwa estate d’in hari an hana su shiga sun ma rufe gate d’in layin gaba d’aya but gasu nan dai ana ta k’ok’arin shiga motocin sojoji biyu sun kutsa kai yanzunnan…”
Yadda su Yasira suka ji muryar Daddy yana yiwa Mommy bayani ta wayar yana kuka ne yasanya suma suka fashe da wani irin kuka.

Sun san Daddy ba lalle ya so su je wajen ba shiyasa ba su ce masa za su je d’in ba instead suna gama wayar da shi suma suka fice dan hankalinsu gaba d’aya ya yi wajen….a nan suka fice suka bar Manubiya a yashe a k’asa suka nufi estate d’in suna kuka gaba d’aya su ukun..

A Chan suka tarar da Daddy da Yassir suma duk hankali a tashe lokacin har an bud’e gate d’in layin wajen taff cike da sojoji da y’an kwana kwana dan kusan kaff gidajen sai da suka cinna musu wuta tukunna suka gudu ba a kama ko d’aya ba.! Yadda estate d’in ya k’one ya koma wani abu daban dole ya bawa mutum al’ajabi sannan ya sanya ka sake ka’daita Allah ka kuma tabbatar da cewa abun duniya da duniyar kanta ba a bakin komai suke ba.Su Yasira suna hango su Daddy suka k’arasa wajen su suna kuka shima Daddyn hawaye yake yi cikin sharar hawaye yace “akwai hope! ga dai motarsa chan a k’one da mutum a ciki amma gaskiya ba shi bane inaga kamar driver d’insa ne kuma shi har yanzu wayarsa tana shiga,amma wayar mutumin ciki ta k’one da na duba ba ta aiki.
Sannan munata dubawa har ciki amma kamar ma shi d’in bai zo nan ba kwata kwata.

Cikin jinjina kai Yasira ma tace “Nima Inada hope Daddy
dan yanzu ma na kirasa wayar tasa tana shiga,Allah dai ya sa ba wani abun ne ya same sa ba
dan gaskiya bai zo nan ba.”


Daddy ne ya kira asibiti
dama ga polisawa da sojoji a wajen dan haka ambulance suna zuwa aka fara fitar da deceased da injured abun ba dad’in gani dan mutane sunfi talatin waenda suka mutu
injured kuma wajen mutum goma……



Bayan kamar awa d’aya wajen ya cika taff da jama’a dan har su Baba larai duk sun k’araso suma kowa in ka kalla hankalin sa a tashe.
Dukda cewa zuwa wannan lokacin sun tabbatr da cewa Yashjub ba ya wajen dan kaff jama’ar dake yashe a harabar wajen da gefen gefen titin a lokacin da abun ya faru an shaida identity d’insu amman kuma rashin amsa wayar ta sa ne ya fi komai d’aga musu hankali a halin yanzu.
Dan haka Daddy ya kalli Yasir wanda duk hankalin sa ya gama tashi da rashin ganin gawar Yashjub…cikin dafa kafad’arsa yace ‘’ka kwantar da hankalin ka Yassir inshaaAllah babu abunda ya samu d’an uwanka,ka nutsu ka yi addu’a ka ji ko? dan ni kam zuwa yanzu inda hope ‘’
Ahankali Yassir ya had’iye wani k’ululun tashin hankalin da ya toshe masa mak’ogwaro kafin yace ‘’To Daddy’’.
Cikin fesar da huci Daddy yace ‘’d’an sake gwada kiran sa mu gani”
Still yanzu ma a hankali ya sake cewa “to Daddy”
Daganan ya matsa gefe k’irjinsa yana dukan uku uku dan baya k’aunar ya kira a yi rashin sa’a ya ji muryar Yashjub safe and sound!..Hatta seconds da komai sai da aka k’irga from inda yake to the estate sannan ya bada numbobin motocinsa duka incase ma
Idan ya chanja mota,kuma sai da suka yi waya da mutanen suka ce masa gashinan ya shiga estate d’in yanzu tukunna suka fara aikin amma bai ga alamun sa a wajen ba!sai driver d’insa wada yanada tabbacin bai cika yawo da shi ba,mai ya faru???where is he????adduarsa d’aya Allah ya sa a wani wajen suka danna gawarsa shiyasa ba a gani da wuri ba!…Allah ya sa a nemota yanzunnan a duk inda take a cikin estate d’in a fito da ita dan tabbas zuciyarsa za ta iya tarwatsewa idan akace Yashjub ya yi getting out of this one alive and safe…
Da kyar ya samu ya d’an nutsu tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu,hannunsa har karkarwa yake yi haka ya danna kiran Yashjub..bugu biyu a na uku ya d’auka yace ‘’Yassir! kuna Ina??’’
A hankali Yasir ya lumshe idanuwansa wasu zafafan hawayen bak’in ciki da na tashin hankali suka shiga silalo masa…
Sai da Yashjub ya sake cewa ‘’Yassir ba ka jina ne?kuna Ina??”
tukunna da kyar da mugun kyar ya samu ya iya had’a kalmar ‘’ga mu nan duk a estate d’in ka’’
‘’Okay gani nan zuwa but bawa Manubiya wayar first Inata kiran ta ba ta d’auka!is she fine??”

Shiruu ya yi ya d’an kalli Daddy wanda ganin kamar waya yake yi ya sa ya tunkaro sa
Cikin tsananin rikici Daddyn ya ce “shine??ya amsa?”Sai kuma ya sa hannu ya karb’i wayar.
A take ya lumshe idanuwa wasu hawayen farin ciki suka zubo masa jin muryar Yashjub safe and sound yana cewa ‘’Yassir,ka yi magana mana!Ina Manubiya take?ka bata wayar”
Dai dai nan su Mommy ma suka k’araso wajen,suna masu tambayr su “shi ne?ya d’auka?”.
Sai da Daddy ya jin jina musu kai yace ‘’eh’’ tukunna ya maida hankalinsa ga Yashjub wanda ya rikice ta waya yana tambayar ‘Ina Manubiya?’ya ce
‘’Yash Manubiya ba tana asibiti ba? ka nutsu mana she’s fine ai ko?….”
‘’Daddy tare na barsu ita da su Mommy na fita,and she was very worried a time d’in,sannan yanzu na ji Yassir yace duk kuna estate meaning har da su Mommy kenan kuma ita ban ji ta ba sannan Ina ta kiran wayar ta bata d’agawa..”
Yashjub

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login