Showing 78001 words to 81000 words out of 244445 words
Yash ya k’araso wajen yana cewa”Baby ya kuka tsaya a waje su shigo man.. “
Da sauri Ya’isha ta ja ta tsaya
sai kuma ta koma gefe ta had’e rai ta tamke fuska.
Kallon su ya yi d’aya bayan d’aya kafin yace”Ina Yahanasu?”
Sai da Yassira ta d’an fesar da iska tukunna tace”May be tana hanya”
Shiruu ya yi kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya yi shiru.Sam bai yi tunanin suna da audacity d’in da za su zo inda yake kwana kusa ba after what they did,sannan har da wata Kausar,ba ya so ya yi musu wani abun a gaban Manubiya kamar yadda Daddy ya fad’a shiyasa yake k’ok’ari wajen ganin bai bada k’ofar da Manubiya za ta ga wani abu na sab’ani tsakaninsa da y’an uwansa ba.
Dakyar ya danne zuciyar da ya ke ji tana taso masa dan yana ganin fuskokinsu komai ya dawo masa sabo.
A hankali yace “baby mu je” yayi maganar yana rik’o hannun Manu kafin ya kalli Yassira yace mata”bismillah”
Daga haka ya ja hannun Manu,kamar wata Yarinya haka ta juya ta bisa suka
nufi cikin parlourn wanda hakan yasa Kausar ta ji kamar ta kurma uban ihu!..dama sai da ta cewa Yasira “ba za ta zo ba!kar ta zo ta ga tashin hankali”amman suka tilasta mata a cewarsu “ba za su bar Manu ta sake ta shak’i iska a cikin gidan dai dai da na kwana d’aya ba,sun dinga zuwa kenan daga yau har zuwa lokacin da zata koma mansion d’insu da zama su samu su fitar da ita daga rayuwarsu gaba d’aya.
A kan one seater Manubiya ta zauna dan taga suna da yawa sannan bata buk’atar zama kusa da d’aya daga cikinsu.
Tana jira taga shima ya zauna a d’ayar one seater d’in kawai taga ya nemi guri ya zauna a kusa da ita kamar
zai shige cikin jikinta dan kujerar ta yi musu kad’an sosai.Ahankali su Kausar suka k’araso cikin parlourn duk suka nemi guri suka zazzauna,Kausar ta sunkuyar da kanta k’asa sosai kamar zai karye.
Tun d’azu Yash ya lura da yanayin Manubiya kuma bashi da tantama a zuwan su ne kafin ya k’arasa k’ofar akayi mata wani abun
maybe Kausar ce ta harare ta ko ta fad’i wani abun….
Yana wannan tunanin ya ji sun fara gaida shi cike da mutuntawa,jimullah ya yi musu yace “lafiya”
Daganan ya koma ya fara kallonsu one by one yana jira ya ji sun gaida Manubiya amman sai ya ji shiru,
Minti d’aya ya ware musu
yana cika kuwa ya gyara zama yace “ba za ku gaisa da matar gidan ba?”.
Ba iya ka su ba ita kanta Manubiya sai da ta ji wani iri
dan ba ta yi tunanin zai iya ce musu hakan ba.
Ganin yadda ya tamke fuska kamar bai tab’a dariya bane
ya sanya Yusra cewa “Ina wuni”
Ta fad’i hakan ba tare da ta kalli Manubiya ba,dakyar Yadira ma ta gaida ita.
Ahankali Manubiya tace
“Lafiya Alhamdulillah”kanta a k’asa ba tare da ta d’ago ba,
daga haka parlourn ya d’auki shiru kamar babu halittar mutane a ciki kafin Yashjub ya mik’e tsaye kawai ya wuce sama bayan ya cewa Yassira “ta biyosa”.
Suna hawa,a nan parlourn saman ya ja burki ya tsaya ya juyo ya ce “Kun zo
Gidana!kuma na gode,amma ba zan d’auki iskanci ba!
dan haka na baku 3 minutes ku tattara ku tafi duk lokacin da kuka san abunda ya kamata u guys are free to come back.”
Kamar za ta fashe da kuka tace”Ya Yash ni ce zan gaida ita??”ta yi masa tambayar tana mai nuna kan da yatsa.
Cikin takaici yace
“Yassira gidan ta fa kuka zo!a
gaban ta kuka gaida ni,
a matsayinta na matata ya kamata ace kun gaida ita ko da kuwa kun girmeta, idan ma kuma kuna ganin kun girmeta ai ko ‘Hi’ da ‘ya gida’ ya kamata ace kun ce mata.
Na ga take taken ku na lura fitina kuke nema da ita wanda ban san ribar ku a kan hakan ba, sarai na san abunda kukayi a gidansu Daddy ne ya ja min burki shiyasa na d’aga muku k’afa if not Wallahi da sai kun gane kuranku!na yi masa alk’awarin ba zan yi muku komai ba akan wanchan abunda kuka yi amma hakan ba wai ya na nufin zan zuba ido ku taka min mata ba,dan haka be warned!…kin riga kin san wat i’m capable of but for now!kar ki bari in sauk’o in same ku a cikin gidan nan.”
Yana gama fad’in haka ya wuce ya barta anan a tsaye zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Ta so ta shiga d’akin Manubiya dayake a nan saman ta zuba abunda Baba larai ta bata ta ce ‘ta zuba’ amman sai akayi rashin sa a ko taku biyu ba ta yi ba Manubiya ta hawo saman
dan Yashjub yana tashi su Ya’isha suka fara yada mata da maganganu marasa dad’i! dan dama a wuya suke da ita ji sukeyi kamar su rufeta da duka.
Tana d’aga kanta dake dama kana iya hango parlourn sama daga nan k’asan ta ga Yashjub ya wuce ya sake hawa bene ya nufi d’akinsa Itakuma Yassira tana tsaye a nan parlourn shiyasa ta mik’e da sauri ta wuce su ta nufi saman ba tare da ta ce musu uffan ba.
Takaici da bak’in ciki da rashin jin dad’i duk sun kanainayeta a lokaci guda,zuwa yanzu ta riga
ta gama sanin Allah ya had’ata da dangin mijin da ba su san darajar d’an Adam ba sam kuma ba sa k’aunarta.
Ita ko a labari bata tab’a jin labarin jahilan dangin miijin Irin nata ba.
Tana wannan tunanin ta hayo sama idanunta taff da kwallah,
Yassira ta ji motsinta tun a stairs shiyasa ta jiyo….ta na juyowa kuwa su ka yi ido biyu,da sauri Manubiya ta d’auke kanta dan sam bataso Yassirar ta ga idanunta shiyasa tashi d’aya ta kauce ta nufi d’akinta ba tare da ta nuna ta ma ga Yasirar a wajen ba…dai dai ta zo wucewa kenan kawai Yasira ta sha gabanta ta ja ta tsaya,lumshe idanu kawai Manubiya ta yi kafin ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya tana mai k’ok’arin rik’e kanta dan tabbas in ta d’ago a yanzu da wannan temper da take ji ta na taso mata to ba Yaseera ba ko wacece sai ta d’auke ta da mari.
Sun kusan second ashirin a haka kafin Manubiya ta kauce ta chanja hanya amma sai Yasira ta sake shan gabanta ta tare mata hanya…a hankali Manubiya ta d’an d’ago still tana mai k’ok’arin danne zuciyarta tace”Anya ba daga gidan mahaukata kuka gudo ba kuwa?”.
Murmushi mai had’e da dariya Yassira ta yi kafin tace “eh to tare da tsohon da ya d’aura miki aure muka gudo!
Anyways
dama I just want to see your eyes,Ina so inga how strong u can be kuma na riga naa gani..yadda idanuwanki suka cicciko ya tabbatr min da cewa ‘u are weak!’
shiyasa a take a yanzu wallahi har kin bani tausayi saboda bakiga komai ba!there is a lot coming your way!”
Sai kuma ta kalleta sama da k’asa tukunna tace
“Da ni da y’an uwana ba ma yin ki!ba ma sonki ba ma k’aunarki!
Kausar ita mukeso ta auri d’an uwan mu amma kika shiga kika fita,amma karki damu dan wallahi idan sama da k’asa za su had’e sai Kausar ta auri Yashjub
Mark my words!”
Tana gama fad’in haka ta wuce fuuu cikin tsananin takaici da bak’in ciki….dukda maganganun da ta gayawa Manubiya sun d’an rage mata takaici amma ji takeyi kmr ta mutu…wai ace yau itace ta zo gidan yayanta for the first time amman ya koreta saboda ba ta gaida matarsa ba,ga shi ba ta zuba maganin da ta ci burin barbad’awa ba kuma Yash yace su tafi ta tabbatr ko sun zo gobe ko da ace su Mommy sun shiga maganar tou it’s either ya ki sake musu ko kuma ma ya sake ce musu su tafi gaba d’aya!.Ga kuma takaici da tsantsar tsanar Manubiya da ta ke ji tana ratsa ta…ta ya ma Yashjub zai kalle ta ya ce ta gaida wannan Yarinyar,saboda Allah idan shi ya yi lowering class d’inshi ya zubar da kansa ya zubar da mutuncinsa ai bai kamata ya yi expecting same thing da ga garesu ba…ai ita Manubiyan ce ya kamata ta gaida su after all ta auri Yayansu an rufa mata asiri ta shigo cikin family dinsu y’ar talakawa da ita.Amman ba ta san na gaba da ita ba wato daman zaman da ta yi da kuma tare k’ofar da ta yi tun farkon zuwan su jira takeyi su gaishe ta kennan shi
kuma Yash ya biye mata dake bai san darajar su ba…saboda giyar amarci tana d’ibaar sa shine zai ci musu tuwo aka a gabanta ya wulakanta su saboda ita.
Waennan tunane tunanen ne suka sa duk dauriyar Yassira ta kasa daurewa dama har yau akwai takaicin dukan da Daddy yayi mata saboda su shiysa ta na sauk’a k’asan da suka had’a ido da su Yasmeen kawai sai ta fara sakin hawaye.
Gabad’ayansu kanta suka nufa suka shiga tambayar ta “mai ya faru?”
Dakyar ta iya controlling kanta tace musu “Ku d’auko handbags d’inku mu tafi”
K’asa k’asa da murya Yasmeen tayi kafin tace
“Kin zuba ,har kin gama?”
Girgiza kai kawai ta yi kafin ta sake ce musu “ku taho mu tafi!”
Cikin rashin jin dad’i Yasmeen tace “Kamar ya mu tafi?ba tare da mun yi abunda ya kawo mu ba?”
Ahankali Kausar wadda ta fi kowa nad’ar takaici ta d’an dafa Yasmeen d’in tace “mu je kawai ma dawo wata rana”
Saida Yasmeen ta kalli Yassira tuukunna Yassirar tace mata “ku taho mu tafi kafin ya sak’k’o”
Cikin fushi Ya’isha tace
“Ba dai shi ya ce mu tafi ba??”
Bata rai Yassira ta yi kafin tace
“Shikenan!ni dai kunga tafiya ta…idan ya sak’k’o ya same ku ba bu ruwana”
Ta fad’i hakan tana mai yin gaba ta nufi k’ofa.
Cikin tarar numfashinta Ya’isha ta ce”Ai yau sai dai ya kashe ni wallahi amma babu dalilin da zai sanya in fita a cikin gidan nan!aikin banza ku kuke jin tsoronsa…za a ga ikon Allah yau a cikin gidan nan!”
A hankali Yasmeen wadda itama jikin ta yayi sanyi ta matsa ta shiga bawa Ya’isha baki.
Itakam Kausar juyawa kawai ta yi ta bi bayan Yassira suka nufi k’ofa dan tunda uwarta ta kawota duniya ba ‘a tab’a mata disgi irin wannan ba
Yashjub bai aureta ba
sannan tunda ta shigo ko kallonta baiyi ba kuma saboda ba ta gaida matarsa ba yace
su fitar masa daga gida.!
Dakyar da mugun kyar Yasmeen ta lallab’a Ya’isha
tukunna ta yarda za ta tafi.
Su Yassira suna bakin k’ofar dan a yadda sukaga Ya’isha ta burkice sun san idan har Yashjub ya sak’k’o ya tadda ita ba za su k’are ta sauk’i ba.
Tana zuwa ita ta bud’e k’ofar da k’arfi dan a wuya take
tana bud’ewa suka yi ido biyu da Siyama wadda ta d’aga hannun ta da niyyar yin knocking…tun jiya take kiran sir Najeeb a waya amman ya’ki ya d’aga kuma bata da tantama saboda wannan shegiyar Yarinyar ne.
Hannun nata ta kalla wanda ta dunk’ule da niyyar yin knocking d’in tukunna ta kalli fuskarta tace “Er mallan Shehu bell ake dannawa ba kwankwasawa ba!”
Murmushi kawai Siyama tayi kafin ta matsa gefe ta tsaya ta hard’e hannuwanta akan kirjinta,kawai.
Zuwa yanzu Ya’isha ta fara bawa Yassira haushi dan ta ga alamun ta rantse sai ta janyo abunda ransu zai kuma b’aci
dan haka tayi gaba kawai ta barta a wajen hakama su Yasmeen suka wuce aka barta daga ita sai Yadira.
Ya’isha so tayi ta hana su Siyama shiga dan ba zai yiu ita ta gidan yayan ta ace bata samu zama ba amma wasu kuma su zo su shige a gaban
idanun ta!
amma kuma ganin da tayi su Yasmeen duk sun watse sun barta sai kawai itama ta watsawa Siyama tsaki ta wuce tana jin tsanar Yarinyar tana ratsata!ji takeyi kmr ta koma ta yi mata illa.
A harabar gidan suka tarar da Aisha ita da su ya Musbah da ya Nafi’u sunata faman sauk’e kayan gara daga motar ya Nafi’u da d’ayar y’ar k’urk’urar da suka zo da ita.
Takaicine ya sa tunda su Yassira suka yi musu kallo d’aya ba su yarda sun maimaita na biyu ba….tsabar tsiya kalli kayan garar da aka kawo gidan d’an uwansu kamar an rok’o!
A haka wai amma har wani so yake a gaida ita
Inaa da sake wallahi
dama sunsan ba za su barta ta rayu a cikin gidan ba amman dukda haka dole ta gane kuranta ta san matsayinta kafin ta fita a gidan dan ruwa ba sa’an kwando bane ba.
Dama tunda suka tunkarosu
Aisha tace wa su ya Nafi’u kar ma su kula su kar su ce musu komai basu da mutunci.
Haka kuwa suka zo suka wuce bayan sun sake tamke fuska tamau kamar ba su tab’a dariya ba.
Ba k’aramin tashi hankalin Ya Musbah ya yi ba tashi d’aya ya shiga tunanin tayaya k’anwar sa za ta yi rayuwa a tsakanin waennan Yaran….
Tashin motocinsu ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka,a hankali ya Nafi’u ya matso kusa da shi ya d’an dafa sa dan shi dama tun ranar da aka kaita Aisha ta basa labarin iskancin da su Yassira suka yi.
Sai da ya fesar da iska tukunna yace “InshaaAllah komai zai yi dai dai ka kwantar da hankalinka”
Cikin rashin jin dad’i ya Musbah yace “Nafi’u kaga d’aya daga cikin illolin yin aure ba tare da anyi kwakkwaran bincike ba ko?
Abunda na ke gudu kenan shi kuma Baba….”
Da sauri ya Nafi’u ya katse shi ta hanyar cewa “Karka ce haka!babu ruwan bincike da abunda Ubangiji ya riga ya tsara kaida kawai mu taya ta da addu’a”.
Lumshe idanuwa ya yi ya bud’e daganan suka fara jidar kayan suna kaiwa bakin k’ofa
Siyama kuma ta fara kiran Manubiya a waya dan ya Musbah yana zuwa yace “kar su shiga kai tsaye su jira Yashjub ya zo ya shigar da su tukunna.”
Tun lokacin da Yassira ta wuce ita kuma ta shige d’akinta ta zauna ta fashe da wani irin kuka,zuwa yanzu ta riga ta gama amincewa babu ta yadda za ayi su zauna lafiya ita da sisters d’in Yashjub - Yahanasu.
Wanann wacce irin k’addara ce ace wai k’annen mijin ka ne zasu fito k’iri k’iri su ce maka “ba sa sonka”
Kuma sai sun aura masa y’ar uwar su!tayaya za ta yi rayuwa a cikin su taya y’ay’anta za su rayu a tsakanin su?……
Tana cikin wannan tunanin ta ji an bud’e k’ofar an shigo dan haka ta yi saurin juyar da kanta gefe ta fara k’ok’arin share hawayen ta.
Murmushi ya k’ak’alo shima dakyar tukunna ya k’arasa in da take ya tsaya ya shiga k’are mata kallo kafin chan ya fesar da iska ya zauna a gefen ta yana mai ruk’o ta izuwa jikinsa cikin sigar lallashi yace
“Wanne d’an gangancin ne ya tab’a min matata?ko Inna kike missing?”
Shiruu ta yi ba ta ce k’ala ba kuma bata daina sauk’e ajiyar zuciya akai akai ba.
Murmushi ya sake yi ya d’ago da fuskarta yana kallonta kafin yace
“Ki yi hak’uri”
Girgiza kai kawai ta yi ta fara k’ok’arin mik’ewa…a hankali ya ruk’o ta yace “Ki yi hak’uri!ko..na baki hak’uri ai,next time idan sukazo za su yi miki magana,it’s only a matter of time za ku fahimci juna da su inshaaAllah
Yanzun akwai abunda ya d’an faru ne….”
Ba tare da ta kalle sa ba kanta a k’asa tace “saboda kak’i yarda ka auri Kausar?”
Sai da gaban Yashjub ya yanke ya fad’i ba na wasa ba dan sam bai yi tsammanin jin hakan daga gareta ba, bai so ace ta ji wannan maganar ba!maganar da yake rok’on Allah Ubangiji kar ya tab’a nuna masa ranar tabbatuwar ta ko da a cikin mafarki ne.
Besides waye ma ya gaya mata sannan ai shi ba saboda yak’i yarda ya auri Kausar bane yaushe ma aka tab’a maganar auren sa shi da Kausar??
Ya yi tambayar a cikin ransa.
Shiruu yayi ya fad’a duniyar tunani….sai yanzu kansa ya d’au chaji! wato hatta su Yasira sun san zancen maganar Kausar tana son shi kuma sun so ya aureta ne,abunda shi da kansa bai sani ba….shiyasa kenan suke fushi suke wannan haukar.To amma Mommy ma a bayansu take itama ba ta son aurensa da Manu!ba ta son farin cikin sa kenan?! ita da y’an uwansa duk so suka yi su manna masa Kausar saboda ba su damu da farin cikin sa ba ko ya abun yake ne???
Tashi d’aya ya ji kansa ya d’aure……
Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin yadda yayi shiruu ya sha jinin jikinsa,a hankali tace”Ba ka tab’a cemin Kausar family d’inka sukeso ka aura ba,ko a ranar da muka fara had’uwa da ita cemin ka yi she’s just a sister”
Ahankali ya fesar da numfashi ya kamo hannayenta tukunna yace”Wallahi Allah nima yau na fara jin zancen nan
Wai ‘Kausar family d’ina suke so na aura!’ban san maganar ba
In da na sani kin san da zan fad’a miki,but a Ina kika ji zancen?”
Girgiza kai tayi tace “Shikenan”
daga haka ta fara k’ok’arin barin wajen
A ranta kuma tana mamakin yadda still yake k’ok’arin b’oye mata zancen bayan ga mamaki nan k’arara a kwance a kan fuskar sa wanda hakan yake tabbatar mata da ya san da maganar.
A b’angaren Yashjub kuwa
mamaki yakeyi…shi dai ya san ya ji lokacin da Kausar tace tana son shi ya san dama Mommy za ta iya goya mata baya amma bai san abun ya kai har haka ba kuma harda su Yassira ma sun san maganar kuma suna so ya aureta bayan sun san ita d’in budurwar Yassir ce,
to me yake faruwa ne a cikin gidan nasu wanda shi bai sani ba dan ko Manubiya bata gaya masa ba ya fahimci a zuwan su na yau ne aka samu wata ta gaya mata wannan maganar domin a shiga tsakanin ta da shi!me yasa su Yassira za su zama haka ne!wannan wacce
iriyar halayya ce suka k’irk’iro da ita sabuwa…..
Ji yayi kawai ta bud’e k’ofar ta fita har ga Allah bai san lokacin da ta mik’e ta isa k’ofa har ta fita ba…tana fita wayar ta ta d’auki k’ara dan haka ta d’auka ta kara a kunnenta
Jin Siyama ce yasa ta yi iyakar bakin k’ok’arinta ta tsayar da hawayen ta d’an share ta