Showing 195001 words to 198000 words out of 244445 words

Chapter 66 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16462

kam ta tabbatar da suna k’aunarta duba da yadda suke taya ta murna.Kowa in ga kalla baki a washe Yasmeen ce kawai babu a wajen.
A ranar har Baba larai suka yi alk’awarin had’e kansu guri d’aya su taimaki Kausar su tsaya mata ta yak’i Yashjub
su ga bayan Manubiya.

Cike da farin ciki Mommy take kallon y’an matan nata batasan lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba
Ahankali Baba larai ta kamo hannun Mommy tace
“Kar ki damu, na san hawayen me kikeyi inshaaAllah family d’inki ya kusan zaman complete.“
…..
Yassir so yake ya je wajen Kausar amma ya san tana tare da su Mommy dan tun d’azu da ya hawo da niyyar sake dubata ya ga su Yasira sun shiga bai ga sun fito ba.shiysa ya hak’ura ya d’aga musu k’afa dan ya san yana shiga a haka akwai matsala kuma ya riga ya gama yi mata alk’awarin ba zai fallasa plan d’insu a kowa ba za su yi komai cikin sirrine.

Kishi da tashin hankali da bak’in ciki sun rufesa,ya san Kausar ba ta haramta a garesa ba kuma ya san a yau idan ya ce a warware auren ba shi da matsala da ita sai dai Mommy dan haka ya tsara za su zauna shi da Kausar da Yashjub gobe inshaaAllah a warware ba tare da su Momy sun ji ba ,tunda duk su ukun ba so suke yi ba.
Sai da ya yi reaching to this conclusion tukunna ya d’an ji sanyi a ransa..amma fa dukda haka kishi sai da ya sauk’ar masa da wani zazzafan zazzab’i..dan idan ya tuna cewa yau fa Kausar matar wani ce sai ya ji kamar ya cinnawa gidan wuta.
Shiyasa kawai ya wuce side d’insa bayan ya tura mata message yace”ta kirasa idan ta zama free.”
Yana shiga d’akinsa ya ware ac ya rage kayan jikinsa
ya kwanta akan tiles flat
daga shi sai boxer yanajin yadda kansa yake wani irin sarawa.
Assurance yake ba wa kansa yana sakewa cewa”Yashjub ma ba zai yarda da wannan had’in ba dan haka ba shi da matsala ta koina InshaaAllah a gobe za a ware auren daganan duk abunda su Daddy za su yi wannan daga baya kenan! kuma ko sun yi fushi ya san za su huce.”
Yana waennan tunane tunanen
zazzab’in jikinsa ya nunku!….ya dad’e yana fama kafin ya samu ya d’an ragu, daga haka wani bacci mai nauyi ya yi gaba da shi………..


Yashjub Yana fita gida ya nufa…har yanzu kwakwalwarshi ta k’i ta bashi kwakkwaran dalili kwaya d’aya wanda ya sanya su Daddy suke tunanin ya kamata ya auri Kausar saboda shi duk wannan bayanin da Daddy ya yi sam baiga ta inda hakan ya zamo hujja akan ya auri Kausar ba.

Zai iya kula da ita da ‘danta ba tare da ya kalli inda take bama
Idan kuma tafiya takeso ta yi
ta na iya wucewa ta tafi duk inda takeso ita ta sani!Abu d’aya that is for sure shine idan ta riga ta haihu duk inda take indai a cikin duniyar nan ne to zai nemo ta kuma ya karb’o d’ansa daganan kuma ita da shi har abada wallahi.

Maganar b’ata suna kuma ta je ta yayata dan shikam tunda har ya sab’awa Ubangiji sannan Iyayenshi y’an uwanshi da Manubiya kowa ya san abunda ya aikata to tsoro ko kunyar ubanwa kuma zai ji??
Wallahi ba ya shakkar ta d’auki loudspeaker ta hau helicopter ta yi Yekuwaaa! sam hakan ba zai damesa ba,bai damu da mutane da abunda za su ce ba…kawai dai ya san duk shekarunsa da k’arfin tunaninsa bai Isa ya hango abunda su Ddaddy suka hango ba shiysa ya yi putting maganar su into consideration.

Tunda ya taho yake addu’a Allah Ubangiji ya sa kar Manubiya ta amince dan wallahi ba ya jin zai iya shak’ar numfashi muddin akace Kausar ta zama matarsa…ya ma san manu ba za ta yarda a yi mata kishiya ba ta na son shi ba zata amince ya auri wata ba no matter what,kuma zai yi ta nuna mata hujjoji har ya yi convincing d’insu.

Tunda ya taho ya ke jin yadda wayarsa da ke a aljihu take ta faman vibrating…
Ganin an jera masa misscalls sama da ashirin ne yasa ya hak’ura ya zaro wayar zai amsa shi a tunaninsa ma daga gida ne amma sai ya ga bak’uwar number…tana katsewa yana shirin mayarwa aljihu dan driving yake yi bayaso ya rik’e wayar a Hannu gudun samun distraction kamar gizo haka yaga message ta notification bar an rubuta”ka duba watsapp an turo maka evidence akan wanda ya saka aka kaiwa Estate d’inka hari duk dan a kashe ka.”

Sai da sitiyarin motar ya kufcewa Yashjub da mugun sauri ya rik’e Allah ya rufa asiri bai bugu ba bai bige kowa ba dan haka ya yi sauri ya yi parking a gefen kwalta yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa zuciyar sa take tsinkewa kansa yana juyawa.
Wata zuciyar tana hana sa bud’ewa dan bai san mai zai gani ba wa zai gani ba Yayinda wata zuciyar take azalzalarsa da ya hau ya gani.
Sai da ya yi addu’o’i ya ce Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi tukunna ya danne zuciyar da ta ke hanasa bud’ewa..tashi d’aya ya kunna data ya hau Online k’irjinsa yana wani tafarfasa,yana tunanin to waye wannan mai turo evidence haka ko dai pulling legs d’insa ake so a yi to amma ai ba kowa bane ma ya san a na binciken.

Sai da messages suka gama shigowa tukunna ya hango number da ta kirasa d’in a ta chan k’asa ga kuma video nan alamun an turo tun d’azu, da messages wajen ashirin a cikin chat d’in.
Yanzun ma sai da ya yi da gaske tukunna ya shiga chat d’in ya yi scrolling chan sama ya fara daga farko inda aka turo abubuwa har wajen guda biyar aka goge,kafin a sake turo bayanai da pictures da videos.
Maganar farko da idanunsa suka fara yin tozali da ita itace”K’aninka jininka Yassir Imam kura shine ya yi hiring d’inmu ya bamu hoton ka ya bada bayanan ka ya tsara mana yadda komai zai tafi a tsari mu samu mu kasheka.
A k’asa idan ka yi downloading za ka ga komai za ka ga yadda ya bamu kud’i da duk wani shiri da muka yi tare da shi.”

Wani irin jifa Yashjub ya yi da wayar jikinsa yana wani irin karkarwa!!ba dan kan kujerar mai zaman banza wayar ta fad’a ba da tuni ta tarwatse!!!!

Wani irin karkarwa da huci ya shiga yi yana jin yadda numfashinsa yake shirin d’aukewa!

Da kyar a hankali a fili ya shiga cewa”innalillah wa inna ilaihirrajiun ya Allah kasa hakan ba gaskiya bane ba!”.

Ba shi da wani option d’in da ya wuce ya sake lalumo wayar ya yi downloading ya bud’e ya kalla saboda yadda aka taso masa da tashin hankalin nan idan ba ganin ya yi ba ya tabbatar ko kuma akasin haka tou ya san tsaf nan da y’an mintuna zai iya samun heart attack……..

Hakanan ya lalumo wayar ya bud’e ya shiga downloading hannnunsa suna wani irin mugun karkarwa da kyar ya danna play yana addu’ar Ubangiji ya sa kar ya ga Yassir amma sai dai kash!videon yana fara tafiya fuskar Yassir ce farkon abunda ya fara gani ya fahimta,tare da mutumin da yake custody d’insu da wasu guda biyar Yassir d’in ya na yi musu bayani dalla dalla yana jaddada musu kar fa a samu matsala su tabbata ya mutu.

D’ayan videon kuma inda yake basu mak’udan kud’ad’e ne sai ragowar kuma call recoding ne wanda ya k’unshi yadda suka dinga communicating, har wayar da suka yi d’azu yace su goge suka yi negotiating akan zai basu 3m duk sai da suka tura da receipt d’in 2 da 1m d’in da ya turo daga baya……..

So yake yi ya yi kuka hawaye su zubo daga cikin idanunsa amma k’aff!!yau kam babu hawaye sun k’afe sun k’are…
Wani Irin jaa!idanunsa suka yi jijiyoyin kansa duk suka baiyyana…so yake ya k’aryata amma babu hanya dan idan ya ce fuskar Yassir aka saka bai Isa ya ce muryar ma sakawa aka yi da yanayin maganarsa ba…..

Ya fi awa biyu a cikin motar dan har sai da Manubiya ta fara waya sakamokon daren da ta ga yayi,tukunna ya kira driver d’insa ya kwatanta masa inda yake.ya zo ya d’auke sa suka nufi gida dan kwata kwata ba zai iya yin driver d’in ba.

Shi kansa driver d’in sai da yanayin Yash ya bashi tsoro!Kamar wani zombie d’in robot haka ya zama da kyar ma ya chanja waje ya koma mazaunin mai zaman banza.

Ko da suka isa gida ma bai sani ba har driver d’in ya zagayo ya bud’e masa ya ce masa”mun iso” har sau hud’u tukunna ya yi firgigit ya d’an kallesa kafin kusan bayan mintunan uku ya samu da mugun kyar ya motsa ya fito ya nufi k’ofar entrance.
Ba zai iya komawa ya d’auko key a cikin mota ba dan haka ya tsaya yana danna doorbell..



Lokacin da ya dawo Manubiya tana kitchen tana k’arasa soya wainar fulawar da suke yi ita da Siyama kafin su Ya Nafi’u su zo su d’auketa ta tafi.….jin door bell ya sa ta yi tunanin ko dai su Siyaman ne suka dawo maybe sun yi mantuwa dan basu dad’e da tafiya ba.Da wannan tunanin ta fita dan sam ba ta kawo Yash bane da kansa ya tsaya yana knocking instead of ya bud’e kawai ya shigo.

Manubiya tana bud’e k’ofar suka yi ido biyu da shi a hargitse..dan fuskarsa ta yi jaaa idanunsa ma haka jijiyoyin kansa sun fito sannan gaba d’aya babu nutsuwa a tattare da shi.

Yana ganinta sai ya sake karaya tashi d’aya ya zama emotional cikin tsananin damuwa da neman agaji ya fad’a mata a jikinta ya fashe da kukan da ya nema ya rasa d’azu!jikinsa yana wani irin karkarwa har abun tsoro.

Duk k’ok’arinta kasa rik’esa ta yi dan ya yi mata nauyi…a wajen suka zube nan bakin k’ofar ko rufewa ba su yi ba….tsoro da al’ajabi ne suka sanyata fashe wa da kukan itama tana yi tana tambayarsa “me ya faru??”

Shiruuu bai ce komai ba dan ya kasa magana ya kasa cewa komai kawai ya k’ank’ameta yana kuka bilhakk’i da gaskiya.

Sun jima a wajen sosai kafin ta ji ya shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere yana wani irin numfashi.
Cikin sake fashewa da kuka tace”Ya Yash dan Allah ka fad’a mini koma menene kana dad’a tsoratani fa!”

Ahanakali ya d’an cikata har yanzu jikinsa bai daina karkarwa ba…da kyar suka mik’e da taimakon juna,ya tura k’ofar ta rufu tukunna suka k’arasa cikin parlourn suka zauna ya ruk’o hannuwanta duka biyu ya runtse su a cikin nasa…..

Sau biyar yana bud’e Baki da niyyar yin magana amma sam sai ya kasa,
Ajiyar zuciya ta sauk’e k’irjinta yana dukan uku uku tace”i’ll always stand by you!no matter what!
Ka yi mini magana Mijina dan Allah ka fad’a min ko ma menene.Mu nemo mafita mu magance matsalar tare.”

Da kyar ya samu ya iya bud’e Baki ya shiga yi mata bayani daki daki a kan case d’in Kausar komi abunda ya faru yau sai da ya zaiyyane mata.
Kafin yace”duk abunda kika ce hakan za a yi amma dan Allah dan Annabi kar ki ce in aureta,wallahi ba zan iya rayuwar aure da ita ba!”

Manubiya ba ta iya cewa uffan ba tsabar matsanancin tashin hankalin da ta shiga…is she dreaming??da gaske wata ce take d’auke da cikin Mijinta a jikin ta!kuma ake shirin aura masa ita?!!
Yashjub d’inta fa!inaa!!!duk kawaicin ta ba zata iya ba wallahi ba za ta iya ba!!!!
Ashe dama haka mata suke ji idan za a yi musu kishiya?ashe kwanakin baya da ta ji kishi da haushin Kausar duk wasa ne!!
Dan sai yanzu ne ta san menene kishi ta san zafin sa ta kuma san yadda ake ji…wani irin feeling take ji feeling d’in da ko mak’iyin ta ba za ta so
ya ji ba!
Ji take yi kamar ta yi hauka!!!
ji take kamar za ta mutu!!
Hatta b’argo da tsokar dake a jikinta yau kam tabbas sun san tana cikin masifa….


Yanayin da ta shiga ya isa ya sanya Yashjub ya fahimci amsar ta ‘no’ce dan haka cikin tsananin farin ciki ya rungumota yace”na ji dad’in wannan decision d’in naki,na ji dad’i….”

A hankali jikinta da kwakwalwa da zuciyarta har yanzu suna kan karb’ar azaba tace”a yi mata adalci,na yarda ta zo nan ta zauna da mu har zuwa lokacin da za ta haihu…daga nan idan Babyn ta ya yi wayo zan rik’esa kamar ni na Haifa da zuciya d’aya,ba na son Kausar amma na yarda ta zo
ta zauna da mu zan jure!zan jure komai banda kasancewar wata mace matarka Ya Yash!!!”
Ta k’arashe maganar cikin fashewa da kuka…

Wani irin sauk’i Yash ya ji dan ya san su Daddy idan suka ji wannan shawarar da Manubiya ta bayar Hatta Mommy duk za su ji sauk’i kuma an yiwa Kausar adalci tunda har za ta zauna a gidansa ya d’auki d’awainiyar ta har ta haihu ai kuwa an yi adalci kuma itama Kausar d’in ya san tunda ba ta riga ta san su Daddy suna shirin had’asu aure ba tsaff za ta yarda da shawarar Manubiya….ko dan ta zo ta zauna gida d’aya da shi,ya san za ta so ta yi abubuwa da dama idan ta zo d’in amma InshaaAllah shi kuma ba zai bata fuska ba kuma zai taka mata burki ba zai bata dama ba.


Cikin samun sauk’I ta b’angaren case d’in Kausar ya sake rungumo Manu ya yi kissing forehead d’inta ya share hawayenta yace”inshaaAllah ke kad’ai ce mace d’aya tak
Matar Yashjub,inshaaAllah.”

Ajiyar zuciya ta shiga sauk’ewa kafin ta d’aura kanta a k’irjnsa ta yi shiruuu.
Dukda tana jin tsananin tashin hankali idan ta tuna Kausar tana d’auke da ciki amma ba
ta kishi da da Yaro ko
Yarinyar da za ta haifa tunda ba laifin sa/ta bane ba,InshaaAllah zata rik’e da zuciya d’aya dan ba ta Isa ta tsani d’an Yash ba ta san ba xa at iya ba….amma Kausar kam!wani kalar zafin kishinta ne yake azalzalar zuciyar ta ji take yi kamar ta je ta sameta ta shak’eta!.


Sun jima a haka kafin ta ji yace”na san da maganar binciken da kuke yi ke da Yaha a kan case d’in estate d’ina…na gode sosai Allah a saka muku da alkhairi na ji dad’i matuk’a da na ji batun kuma na yi farin ciki amma daga yau ku dakatar da komai ku daina.”
Ya k’arashe maganar muryarsa tana kakkatsewa kamar zai fashe da wani kukan.

A hankali ta d’ago ta kallesa tace”meyasa?”

“Saboda na riga na san waye”
Ya bata amsar hawaye suna masu saukk’o masa kafin ya zaro wayarsa ya shiga chat d’in ya kunna mata ya mik’a mata ta karb’a ya sa hannu biyu ya dafe kansa yana mai zubar da hawaye….da d’an sauk’i da ya kasance ba Mahifiyarsa Mommy bace behind ita,amma fa dukda haka masifa da tashin hankalin da ya shiga da ya fahimci Yassir ne babu sauk’i.

Tabbas dama Manubiya tunda akace insider ne Yassir ta zarga amma dukda haka itama sai da ta shiga shock ba na wasa ba.

Kasa ma magana Mannubiya ta yi gaba d’aya tausayin Yashjub ya rufe ta tun bama da ya fara magana cikin d’acin zuciya abun tausayi ba!”amma ni kad’ai ne mai irin d’an uwan nan ko?babu wani d’an uwa da na tab’a jin labarin ya aikata hakan ga d’an uwansa uwa d’aya uba d’aya!!babu shi.
Ji nake kamar zuciyata za ta fashe!!shiyasa fa case d’in farko na k’i yin bincike saboda inyi avoiding wannan pain d’in!!!
It hurts it sucks ace naka ne yake son ganin bayanka!
me na yiwa Yassir haka!ya za a yi ya tsaneni to this extent???me ya yi zafi har haka?.”

A hankali Manu ta rungumesa itama tana hawaye ta shiga shafa bayansa alamun rarrashi.
Suna zaune a haka wayarsa ta d’au k’ara!!
Sai da aka kira sau uku tukunna ya zaro wayar Da kyar! ya iya karanta sunan Ummi tsabar masifar da yake ciki,a hankali ya amsa ya kara a kunnensa yace”Hello Ummi”
Cikin hargitsi da b’acin rai ya ji Ummin tana cewa
“Yashjub kana Ina?ka zo yanzunnan,Daddynku yanzu suka gama d’aura maka aure da Kausar.”
Kashe wayar kawai ya yi ya ajjiye a gefe ya runtse idanunsa da mugun k’arfi yana jin kansa kamar ba a jikinsa ba!

Yana cikin wannan yanayin ya ji k’arar fad’uwa…
A mugun rikice ya bud’e ido yana kallon Manubiya da ke yashe a k’asa kan kafet.
Sai da numfashinsa ya d’auke da kyar ya dawo jikinsa ya d’au wani mahaukacin karkarwa.
Tabbas ya san abunda aka fad’a ta ji dan wayar tasa tana da murya sosai!!shiyasa tashi d’aya wani sabon tsanar Kausar ya lullub’esa…haka kurum Yarinya ta bi ta d’aga musu hankali babu gaira babu dalili!!!!
bai san lokacin da ya shiga tsinewa Kausar albarka ba!.

Da hanzari ya rufarwa Manubiya…sai da ya k’ura mata ido sosai ya lura Ashe ba suma ta yi ba tsabar tashin hankali ne ya sanya ta yanke jiki ta fad’i.

Shafa fuskarta ya yi a hankali ya mik’ar da ita ya rungume ya ce”kar ki bari hakan ya d’aga miki hankali dan Allah saboda Abu ne wanda ba zan tab’a aminta da shi ba”
Daga haka ya sa hannu ya d’auki wayarsa da kyar ya nemo number Kausar a wani group na y’an gidan nasu ya tura mata message daga garesa mai d’auke da saki guda biyu kwarara!
Ta watsapp da ta sms duk ya tura mata da niyyar gobe da safe zai ce ya mayar da ita sannan atake ya sake sakinta,shikenan!!!
Ya san idan ya yi uku lokaci guda tsaff za a mayar da shi d’aya.


Lokacin da Yashjub ya yi sakin su Kausar suna zaune ita da su Yasira suna zab’ar gado a wayartata messge d’in ya shigo,ta sama duk suka gani amma ba sosai ba dan kad’an suka gani…cikin tsananin tashin hankali Yasira ta amshe wayar ta bud’e gaba d’aya dan Kausar ta kasa bud’ewa…da kyar ta lek’a suka karanta a tare su duka tashi d’aya ta zube a kan gadon ta fashe da wani irin kuka.


Salati duk sukayi Yasira ta mik’e ta k’arasa ta nunawa su Mommy da suka mik’e tsaye a tare sakamokon salatin da suka ga suna yi da kuma kukan Kausar da rikicewar da suka ga sunyi.
Suna gama karantawa Mommy ta kalli Ya’isha da Yasira tace su biyo ta kafin ta kalli Baba larai tace”bari mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login