Showing 57001 words to 60000 words out of 244445 words
nuna halin ko in kula a garesu da Mommy kanta!ta san cewa yanada matsala kuma bai san ciwon kansa ba amman bata tab’a sanin cewa shi mahaukaci bane sai yau.
Yanzu nan ya zo?ashe dama
akan wadda ta fito a wannan gidan Ya Yash ya ke abubuwan da yake yi da uban rawar k’afar da yake ta faman yi kamar wanda zai auro y’ar gwal!?.
Sannan su kansu k’annenta ashe daga nan suka fito amman har suke da guts d’in wani ciccin magani a gabansu?ba laifin kowa bane laifin Yash ne da ya had’asu da su..tabbas Yash ya janyo musu babban insult da abun kunya a rayuwa….wallahi ko gidan su gwaggwo mai aikin su ya fi wannan kyan gani…….”
Yasira ta zaiyyane hakan a cikin ranta. Same thing suma su Ya’isha duk lissafin da suke yi kenan.
Yasmeen kam ji takeyi kamr ta fashe da kuka dan ba kad’an ba wannan insult ne,ta ya
Yash zai had’asu family da Irin waennan mutanen,what has
gotten into him?”cikin bawa kanta amsa tace”tabbas wannan aikin asiri ne babu tantama,amman za ta gane inda ta zo ne!……dan ba ta jin za su iya tolerating Yarinyar nan na 1 month ma wallahi,gwara da Allah yasa ba su yi gaiyyata ba yau da sun kwashi abun kunya!.
Yassira bata iya fitowa a mota ba sai da ta kira Mommy a video call ta shiga nuna mata gidan.
Mommy ta san Yash ya wulak’antasu kuma ya k’ask’antar da su da shi kansa amman kuma ta d’an ji dad’i dan a yadda Manubiya take bata da gatan nan tabbas ta tabbata k’aramin alhaki a hannunta,shiyasa har Kausar wadda take ta faman lallashi tun d’azu ta nuna wa video call d’in da Yassira takeyi sannan
ta sake tabbatar mata da cewa’ba su da wata matsala dan Yarinyar da ta fito daga wannan gidan ba za ta zame
musu jidali ba InshaaAllah’.
Har waje Yassira ta fito tana video call d’in tana nunawa Mommy gidan da layin ba tare da damuwa ba wanda hakan ba k’aramin d’aurewa mutanen da suke kai kawo Kai ya yi ba,why!?for what reason za ta fito tana yin video d’in da kowa ya fahimci layin da gidan kawai take d’auka dan in da ace videos d’in d’aukar Amarya za ta yi ai kowa ya san
sai an shiga ciki tukunna ake farawa
besides yanayin yadda take yin video d’in nata kana gani za ka san gidan kawai take d’auka ba komai ba. Waenda
suke kusa da ita sosai ne suka fahimci video call ne ragowar
kuwa sam ba su fahimta ba…..
Girgiza kai kawai Ummi ta yi ta fito da ga motar ta,kafin ta k’arasa inda su Yahanasu suke tsaye ita da su Jidda…
Da farko Siyama da taga abunda Yassira takeyi har za ta kula ta su yi,amman kawai sai ta basar da ita gudun kar su yi creating scene ta jawa Manubiya abun fad’a kuma tana juya wa suka had’a ido da Ya’isha,ta san idan ta biye su to tsaf za a yi ta ba dad’i dan ta lura kamar yarinyar fad’a take nema da ita dan yanzun ma tana juyawa ta zabga mata harara shiyasa kawai ta rabu da su amman wallahi ba dan
yau ranar Manubiya bace da sai ta koya musu hankali gaba d’ayansu.
Kallon duk su biyun Ummi tayi kmr ta san me ke a cikin zuciyarsu tace”ku yi hak’uri,ku yi komai saboda yar uwarku,kar ku bari ayi abun fad’a a ranar aurenta ku danne
zuciyar ku kunji y’an albarka”
Murmushin k’arfin hali Jidda tayi dan ba k’adan ba itama zuwa yanzu ta hau dan har wata dariya take jiyo su Yusran sunayi
Irin dariyar rainin hankali da k’ask’anci d’innan,a hankali tace”inshaaAllah Ummi”
Daga haka suka sake gaisawa suka gaida k’awayensu kafin su ce musu “bismillah”
Su Jidda a gaba su Ummin kuka a baya haka suka nufi gidan.Dai dai su Siyama sunzo wucewa kenan Yusra tace”Am Yasmeen ni kam anya ba kejin kaji da tumaki aka mana kwatance ba kuwa?inaga
gara fa mu kira mu sake confirming….”
Wani irin tafarfasa zuciyar Siyama ta shiga yi,inda ace iyakar i su iskancin nasu ya tsaya to da dasauk’i amman kejin kaji da tumaki da Yusra ta ambata it means tana referring har da iyayen su kennan,shiyasa duk yadda Siyama ta yi alk’awari ta kuma so ta kyale su sam sai ta kasa,ta san tana juyawa za ta iya kifa wa Yusra mari shiyasa still sai da ta kuma tausar zuciyarta tukunna ta juyo tace
“Group leader d’in ‘rashin sanin yakamata‘
kuna iya shigowa kuma idan kun so,ku d’auki Amarya
kamar yadda aka umarceku ku yi daga gida”
Tayi maganar tana kallon Baba larai dan Babba bai fi Babba ba.
Tana gama fad’in haka ta wuce ciki.
Shiruu duk suka yi dan ba su yi
tunanin za ta kulasu ba
saboda sun lura kamar yaran sunada d’an tsoro,amman fa sun ji dad’in kulasun da ta yi hakan ya nuna ta ji zafin maganar tasu kuma wallahi sai sun nuna mata ba su san ya kamatan ba kuwa!.
Yasmeen ce tace”mu je ciki mu d’auki Amaryar”daga haka duk suka yi ciki suma.
Sam Ummi ba ta so Siyama ta tanka musu ba dan ta san za su yi mata shirme ne a gaban dangi da y’an uwa,kamar
ta san haka suka shirya d’in kuwa!….
Siyama ta yi zaton za su tanka mata amma sai ta ga ba su ce komai ba,kusan tare ma suka shiga parlourn nasu kafad’a da kafad’a ita da su Ya’isha ba wadda ta kalle ta a cikinsu.
Parlourn cike yake taff da mutane…dukda k’amshin turraren wutan da yake tashi tunda ga k’ofar gidan hakan bai hana su yatsine fuska ba
sannan suna tafiya kamr kar su taka k’asa sai kace masu tsallake kwata….Lace ne a jikin Yassira wanda a k’alla ya kai naira dubu d’ari hud’u,haka itama Ya’isha dan nata da na Yassira kala ce kawai ta bambanta na Yassira blue na Ya’isha kuma brown,mayafi 3D suka rufa a kansu y’an k’anana suka zagaye wuyan su da shi,
Yassira bubu ne a jikinta
Ya’isha kuwa fitted gown.
Iyaka zobuna da
awarwarayen gold d’in dake a hannayensu kad’ai sun isa su gigita mutum.
Su Yasmeen kuma super ce a jikinsu itada Yusra,su kam har d’auri suka yi suka rufa mayafansu a wuya,
amman suma dank’ara dank’aran gold d’in jikinsu hannu wuya kunne da y’an yatsu kad’ai abun kallo ne.
Yadira ce kawai mai material
d’inkin fitted gown amma
itama kana gani kasan yadin yaji kud’i,a kunneta kawai ta saka gold sai agogon ta na gold ko zobe ba ta saka ba ita.
Maganar gaskiya
kaff gurin kayansu ne ya haskaka ko Ina dan tun a waje kafin su shigo babu mai kyallin su!kana shigowa layin in ka kalli kowa zaka ga su ne pronounce,ga wayoyin hannun su irin wadda ake yayi ta shekarar.Shiyasa suka zama abun kallo sannan
behaviour d’insu ya zama
kowa ya gani saboda idanun
kowa a kansu yake….
Suna shiga parlourn wata mata tace”Allahu akbar!ga dangin ango!”
Dakyar Yassira ta d’anyi murmushi tace”na jini ma kuwa”
Ta yi maganar tana kallon Munirat wadda ta fito daga d’akin da Manubiya take ciki d’auke da kaskon turaren wuta a hannunta”.
Murmushi Munirat d’in ta yi kafin tace mata”ina wuni,har kun iso?”
K’ura mata ido kawai ta d’an yi kafin ta d’auke kai ta maida dubanta ga matan da suke karkad’e kan kujeru duk sun rikice sun ga gwalagwalai da sutura,dan tashin mutane ma akayi akan kujerun aka shiga karkad’e musu inda za su zauna.
Ba wani datti a wajen
amman dukda haka sai da matar da ta karkad’e wajen tace musu “bismillah” ya fi sau biyar tukunna dakyar Yassira ta d’an zauna ita da Yasmeen da Baba larai,su Yusra kuwa a tsaye suka tsaya akan kafet da takalman su!sam ba su damu da yadda suke tattaka abincin
da aka ci aka zuzzubar akan
kafet d’in yana mammannewa ba,wayoyin su kawai suke daddannawa.
Ita Yassira abunda yafi damunta shine kar ta je ta kwashi infection a jikin kujerun
dan har wani danshi danshi ta ji da ta d’an d’osana bombom d’inta ta zauna…jin yadda danshin yake sake ratsata ne yasa ta ga inaa!ba za ta iya ba!dan haka tashi d’aya ta mik’e ta zare d’an kwalinta dama a ka ta rufa mayafin shiyasa ta zaro sa ta shimfid’e
akan kujerar tukunna ta koma ta zauna wanda hakan da ta yi sam bai yiwa rabin matan parlourn da suka san ciwon kansu dad’i ba.
Dariya k’asa k’asa Yasmeen ta yi wanda hakan ya sake k’ular da su Siyama waenda suka dawo daga d’aukowa su Ummi fararen kujerun zama suka shigo yanzun.
Ba tare da sun kalli su Yasmeen d’in ba suka wuce suka ajjiye wa su Ummi kujerun fuskokinsu tamau.Suna ajjiyewa Ummi tace”Siyama ki barshi ba sai kun yi wahala ba ai,”
Murmushi kawai Siyama ta yi tace”ba komai Ummi,bismillah”
Dai dai nan Inna Iya ramma da Maman Siyama suka fito daga d’akin.
Su Inna basu damu ba suka zauna a chan gefen carpet yayinda su Yasira suka hahhatd’e k’afafu akan kujera, su Ummi ma inda su Innar suke suka k’arasa suka zazzauna aka shiga gaisawa cikin mutunta juna
ana introduction.
Yahanasu ce ta yi introducing tun daga kan Baba larai har izuwa kan Yadira,su kuma suka nuna Inna farar bafulatana mai k’aramin jiki kkyakkaywar gaske a matsayin mahaifiyar Manubiya
Maman Siyama kuma a matsayin gwaggon ta.
Ummi ce tace musu”Ita Ummin sa ce step mom,Mahifiyarsa tana gida bata samu zuwa ba”.
Kamar jira Yasmeen take ta
tari numfashinta tace “Yeah!tanada allergy duba da yanayin arean nan ne yasa ba ta zo ba”.
Rabin matan ba su gane me take nufi bama sai y’an kad’an
ne suka fahimceta.
Shiruu Ummi tayi haka ma kowa kafin Yahanasu ta d’anyi murmushi ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa”ko za’a
fito mana da Amaryar mu wuce!na ga magariba har ta gabato”
Sai a sannan maman Siyama tace”da ikon Allah,bari in je in kawo muku ita”
daga haka suke mik’e su biyu ita da Iya ramma
sannan sukace Ummi ta biyo su.
Idan ka kalli Baba larai
kai kanka Babba sai ta baka tsoro,ta had’e rai ta yi tamau da fuska ta kumbura.A nata lissafin wai tsabar an rainasu ko including d’insu ma ba a yi itada su Yassira!su Ummi da Yahanasu kawai suke komai sam su ba a d’aukesu da mahimmanci ba,ga kuma takaici da tsanar Manubiya da ahalinta baki d’aya,ga shi ba su samu sunyi abunda suka yi niyya d’azu za su yi a gidan Amaryar ba..Shiyasa gaba d’aya ranta ya b’aci ta kumbura ta yi suntum!tana mai jin kamar ta d’aura hannu aka ta yi ya zabga uban ihu….
Ba a yi mintuna shida ba suka fito da Manubiya sanye cikin fara k’al d’in alkayabba sai
kyalli da tashin k’amshi takeyi.
A gefen Ummi suka ajjiyeta,tana zama Ummi ta rungomo ta izuwa jikinta sannan tace”Allah ya yi miki albarka,Allah ya sa ki zame mana sanyin idaniya”
“Ameen” gaba d’aya kowa ya ce ana raha daga nan aka bawa Ummi amanar ta,suka karb’a hannu bibbiyu ita da
Yahanasu,aka yi addu’a aka shafa kafin a fara shirin mik’ewa…..Yassira ce tace
“Yauwa Inada magana
saboda akwai al’adar da muka saba da ita mu y’an gidan mu!”
Runtse ido Yahanasu ta yi
kafin ta kalle Yassirar tace
“Yassira inaga gara mu wuce kawai,yamma ta yi”
Murmushin rainin hankali Yasirar ta yi mata kafin tace
“Nop!It won’t take long.”
Sannan ta kalli Inna tace”and first of all inaga ya kamata in d’an yi muku clarifying wani abu”
ta yi maganar idanunta cikin idon Inna kafin ta ci gaba da cewa “Ita wannan wadda kika bata amanar y’ar ki!
Matar Baban mu ce,itama
kamar uwa take a wajen mu
amman ba ta san cikakkiyar A’adar gidanmu ba dan ko
shekara d’aya ba ta yi a gidan ba.
Wannan itace yayar mahaifiyarmu wadda aka turo ta wakilceta”ta yi maganar tana nuna Baba larai kafin ta ci gaba da cewa”Actually!,
a al’adar mu!’mu da muka zo d’aukar amarya,to tun daga kan Baba larai har izuwa kan Yadira dole ne sai Manubiya ta bi mu one by one ta durk’usa a gaban mu sannan ta gaishe mu a matsayinmu na dangin mijin ta,daga nan ne idan mun ga muna so za mu karb’e ta mu yarda da ita tukunna mu d’auke ta mu tafi da ita’.”
Cikin tarar numfashinta Ummi tace “Yassira wanne irin shirme ne wannan???”
Da d’an murmushi kwance a kan fuskar Yasmeen tace
‘’Ai gaskiya ce Ummi,kuma
ai ba abun zafi bane
kamar wasa ne hakan game ne
you just watch…it will be fun.”
Ta k’arashe maganar tana murmushi.
Yusra ce ta d’aura da cewa”ai yakamata ta san mu ta san matsayin mu na siblings d’in mijinta tun yanzu,ta san cewa idan ta shigo zata girmama mu ne ta bamu girman mu,a garinmu hakan shine main purpose na b’ullo da wannan al’adar.
As it is banga alamun haka daga gareta ko wani a cikin parlourn nan ba dan na lura
it’s like ba ma a san da mu ba
ko irin y’ar amanar ta ma ba a bamu ba Ummi kad’ai aka bawa
So yakamata ta yi gaisuwa ta yi durk’uso kafin mu d’auke ta
mu kaita gidan ya Yashjub d’in mu mai tsada…
Ku duba fa kuga yadda zamu d’auke ta daga nan!”Yusra ta fad’i hakan tana kallon parlourn tana nunawa da hannunta kafin ta ci gaba da cewa”mu kaita chan aljannar duniya gidan Yash”
“A ganina ko cewa mukayi ta kwanta ta gaida mu bai kamata ace kunyi jayayya ba.
Besides ba wai mu muka tsara ba Al’Ada ce ta Mahaifiyarmu sannan Mahaifiyar ya Yash,mune wakilanta dan haka a gaskiya babu inda amarya za ta je ba tare da an gwada kuma anyi da one thing d’in da zai yi nuni da an darajata an daraja mu sannan an karrama Al adarmu ba……”
Ganin kowa yayi tsit an kasa magana ne yasa
Siyama cewa “Tou inaga za ku iya kwasar motocin ku ku koma saboda an samu babban misunderstanding anan
ta inda mu muke ganin munyi muku alfarma na baku one in town din y’ar uwarmu da mukayi kuma kuma naga kuna ganin kamar kunyi mana alfarma ne…”
Da sauri iya ramma tace”Siyama ya Isa haka!”
Ba dan Siyama ta so ba ta yi shiru tana mai rama hararar da taga Baba larai tana yi mata.Bayan Ya’isha
Baba larai ce second halittar da Siyama ta fi tsana a cikin su,Ita wallahi tunda take bata tab’a ganin babbar kwabo babbar banza irin wannan matar ba…
Matsawa Iya ramma ta d’an yi tukunna ta kalli Ummi
tace “y’an uwan sa ne kika ce ko?”
Jinjina kai Ummi tayi tana shirin yin magana
Yassira tace”Daga Yashjub!sai ni da d’an uwana twin brother d’ina Yassir!sai wannan Yasmeen! sai wachchar Ya’isha!
sai Yusra sai y’ar autar mu
Yadira!”
Tana dasa aya ta d’aura da cewa”ku ne fa kuke ganin kamar cin fuska ne yin hakan ko wani abun na daban alhalin mu al’ada kawai muke so mu raya
kuma munaso mu samu good beginning da ita
that’s all Amaryar.
Ku ne kuke ta complicating abubuwa,you guys should just
let her bow down!a yi a wuce
wajen.”
Jin jina kai tsohuwar tayi
kafin tace “na ji na fahimceki!”
Sai kuma ta kamo hannun Manubiya ta mik’ar da ita tsaye dakyar tukunna tace”y’ar albarka!mu je ki gaidasu”.
D’iff!
Haka parlourn yayi tsit ba wanda ya iya cewa uffan!
Ummi tana so ta yi magana amma ta san idan ta yi magana abun sai ya fi haka zafi dan tanada tabbacin maganar da Siyama ta yi ne ya sanya su yin wannan haukar..
Ahankali Ahankali sheshek’ar kukan Manubiya yake tashi a cikin parlourn…cikin rarrashi Iya ramma tace”ki yi shiru kiyi hak’uri ki je ki gaidasu ki tafi d’akin ki,aure fa ibada ne dama haka abun yake sai kinyi hak’uri da duk wasu k’alubale da zaki fuskanta,ki yi hak’uri ki yi ta hak’uri ki rungumi hak’uri dan yanzu kika fara hak’uri
Indai har zaman auren kike son yi kuma aljannah kike nema…”
Kamar Siyama za ta fashe da kuka tace”Iya ramma,ta Ina gaida su ya zama ibada??”.
Cikin fushi da d’an fad’a fad’a
Iya ramma tace “za kiyi shiru ko sai na hamb’are ki?”
Cikin kuka Manubiya ta cewa iya ramma “ba zan fa gaidasu ba,ku maida ni d’aki ka…”
Cikin katseta Iya ramma ta girgiza kai kafin tace
“Manu ki yi hak’uri,kar ki ce haka dangin mijinki ne su..ki
kauda kai kawai kar ki biyesu”.
Dariya Ya’isha ta yi kafin ta matso tace
“Au wai itanma cewa tayi A’a?.
Wow!this is gonna be fun…dan mu kam yau sai an yi Al’ada,bari ki ga ta kaina ma za ki fara”
Ta fad’i hakan tana matsowa
kusa da Manubiyan ta tsaya daff da ita.
Kowa shiruu yayi kawai yana kallon ikon Allah…tabbas waennan sun tabbata dabbobi!
Wanne irin cin mutunci da cin fuska ne wannan haka a gaban mak’ofta da y’an unguwa saboda Allah…
Kuka ne ya tahowa Jidda dama a high take shiyasa ta yi sauri ta juya ta shige d’aki.
K’ok’arin juyawa itama Manubiyan ta fara yi…a hankali cikin tsananin mutuwar jiki Inna ta mik’e ta k’arasa inda take tace…………..MANNUBIYA
(Book 2)
Page 19
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
K’ok’arin juyawa itama Manubiyan ta fara yi…a hankali cikin tsananin mutuwar jiki Inna ta mik’e ta k’arasa inda take dai dai ta gama juyawa,sai da ta juyar da ita tukunna ahankai murya cike da rauni tace”durk’usa!”
Shiruu Manubiya ta yi ta k’i motsi sai da Innaa ta sake cewa”durk’usa!”
Tukunna a hankali ta durk’usa a gaban Ya’isha tana wani irin kuka.
Jin jina kai Inna ta yi kafin tace
“Allah ya yi miki albarka”
Gaba d’aya parlourn a tare aka amsa da “Ameen”har su Yahanasu.
A hankali Innaa ta cika ta
ta kalli Iya ramma tace”ki kaita ta gaida ragowar.”
Mik’ar da ita Iya ramma ta yi suka nufi Baba larai,suna
wucewa Inna ta yi sauri ta fice
daga parlourn.Tana fita ta saki
hawayen da take ta k’ok’arin rik’ewa….
Hatta Yadira sai da Manubiya ta je ta durk’usa a gabanta.
Tukunna Yassira tace “Alhamdulillah,muna iya wucewa da Amarya yanzu tunda ta nuna zatayi biyayya.
Once again,sorry fa!idan na b’atawa wasunku rai,Al’ada ce ta zo da hakan.”
Daga haka ta mik’e ta kalli Ummi tace “za ku iya fitowa da ita,ni na gama nawa.”
Tana gama fad’in haka ta d’auke d’ankwalinta da ta shimfid’a ta zauna a kai ta yi gaba,a take Yasmeen da Baba larai suka