Showing 228001 words to 231000 words out of 244445 words

Chapter 77 - MANNUBIYA COMPLETE HAUSA NOVEL PDF

24 Mar 2025

16485

kuma considering abunda ya faru ta ji ta gani a jiya ya sanya hankalinta ya kasa kwanciya hundred percent da Momyn tun lokacin da ta ji labarin rasuwar Inna…
Ta jima tana tunani kafin tace mata”I hope bakiyi komai ba Mommy”
cikin alhini ta d’aura da cewa”Mahaifiyar Manubiya ta rasu yau!,ki shirye mu je,mu yi musu gaisuwa.”
Daga haka ta mik’e da niyyar kimtsawa ta fito su tafi.
Shiruu ta ga Mommyn ta yi ta shiga mugun shock kafin kawai ta ga ta mik’e tsaye.
K’iri k’iri ta hau bori tace musu
“ba zata je ba suma kuma ta hanasu zuwa tace ai suma su Manubiyan jiya ba su zo mata gaisuwar Larai ba!”
Da mugun mamaki Yasirar ta bi ta da kallo har ta shige cikin bedroom d’inta ta banko k’ofar…
Tana shiga ta sak’ala key k’irjinta yana dukan uku uku,ta durk’ushe a nan bakin k’ofar…
kar dai maman manubiya ce ta rasu ba manubiya ba…Gidan babu wuta bata jona wayarta ba babu charji shiyasa bata samu ta yi confirming ba dama tun d’azu…inna lillahi wa inna ilaihirrajiun kenan yanzu duk wani effort da sacrifices d’inta sun tafi a banza kenan?
Kaii inaa ba zai yiu ba,inshaaAllah ma ba haka bane ba inshaaAllah Manubiya da mahaifiyarta tata ne suka mutu tare…amma kuma inda Manubiya ta rasu ai da Yasira zata gaya mata…..
Wani Irin bugawa k’irjinta ya shiga yi gashi zuwa yanzu dishi dishi sosai take gani ga wani irin juyawa da kanta yakeyi dan haka ta mik’e da kyar ta k’arasa kan gadonta ta kwanta ta lumshe Idanuwanta tana jin kamar ta saka hannu a cikin k’irjinta ta kwak’ulo zuciyarta ta jefar tsabar azabar da ta ke yi mata………
Bata da wani ragowar hope d’in da ya wuce tirsasawa zuciyarta’ta tsaya ta d’an jira zuwa anjima zata ji labarin mutuwar Manubiyan itama’.
Saboda she can’t even begin to imagine Manubiya ba zata mutu ba!effort da sacrifice d’inta sun tafi a banza!.


Tabbas Yasira ta tsorata kuma ta shiga al’ajabi da lamarin Mommy ko bayan shigar Mommyn d’aki har Yusra ta wuce d’aki ita tana nan a zaune ta ma kasa motsi kafin da kyar ta zaro waya ta Kira Manu ta yi mata gaisuwa tace “zasu zo inshaaAllah”
Daganan ta kashe wayar ta yi shiruuu…chan ta zaro wayar ta ta danna kiran Ya’isha!
Ta san Ya’isha tanada taurin kai amma zata gwada lallab’ata a samu ta hak’ura da aikin da Mommy ta turata yi kawai ta dawo,ba wai son Manubiya take yi ba amma Mommy ta wuce gona da iri tun kafin ta kai kanta ga halaka ya kamata a dawo da ita saiti,Wanne Irin bala’i ne har ka tashi mutum gari ya gari dan kawai ya je ya yo maka asiri ya dawo!har mai ya yi zafi haka…….
Layin Ya’isha yana shiga ga mamakinta kawai sai ta jiyo k’arar wayartata a d’akin da Ya’ishan ta kwana dan haka ta mik’e ta shige….ko da ta je d’akin ta duba ga wayarta har da charger da su AirPod d’inta da watch duk ba ta d’auki ko d’aya ba sannan kayanta ciff suka ba ta d’iba ba daga gani tun jiya ba ma ta tab’a ba…dan haka kawai ta juya ta fita ta je ta shiga buga d’akin Mommy…
ta fi mintuna ashirin a wajen har Yusra itama ta fito ta jona ta tukunna aka samu Mommy ta bud’e,yadda suka ganta dagaje dagaje sannan idanunta duk kwantsa sai da abun ya basu tsoro ya basu mamaki dan haka Yasira ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi amma dukda haka sai cewa ta yi”Mommy ki gaya mini tsakaninki da Allah Ina Ya’isha saboda na duba d’akinta Hatta wayarta ba ta d’auka ba!!”

Shiruu ta yi dan ita sai yanzu nema kwakwalwarta ta bata duk waennnan abubuwan…..da kyar ta nemo mafita tace musu”da k’aramar wayata ta tafi saboda hanya, kaya kuma ta d’auki dogayen rigguna biyu. Dan Allah Yasira ki bar ni in huta mana bakiga situation d’ina ba???
Ki huta kema ki zo ki je mini pharmacy ki siyo min maganin ciwon Ido saboda wannan d’ayan har na daina gani da shi sannan ki fita ki nemo min chargi ina buk’atar in yi waya da gaggawa….Yusra ke kuma ki d’aura girki…”
Tana gama fad’in haka ta juya ta rufo k’ofarta hankali a masifar tashe………

Sai azahar tukunna Yash ya zo…zuwa wannan lokacin kowa ya fara jin tausayin gwaggo Suwaiba saboda sun fahimci zafin abun ne ya sanyata yin hakan dan kwata kwata ta k’i bari a nad’e inna a yi mata sutura…..ta zama kamar wata tab’abb’iya.
Manu tana zaune a parlourn ita da su Siyama da su anty Umma suna kuka su mama kuma sunata lallab’a gwaggo Suwaiba Baba ma yana gefe shi da Ya Musbah in banda hawaye babu abunda suke yi sun ma kasa tsawatar mata!
Suna a haka Muhsin ya shigo yace wa Manubiya “ga Ya Yash a waje yace ta je…”
Manu tana mik’ewa Gwaggo Suwaiba tace mata “tace masa tana son ganinsa ya shigo”
Sannan ta kalli su Baba tace “dan Allah tana buk’atar magana da Yash shi kad’ai…….”

Sai da suka gama kukan su shi da Manu ya lallab’a ta da kyar tukunna ta iya gaya masa sak’on gwaggo Suwaiba ya d’an yi mamaki amma kawai sai ya bi bayan Manu ta yi masa rakiya zuwa cikin parlourn.

Manubiya ta so zama amma itama Gwaggo Suwaiba ta sallameta parlourn ya rage daga ita sai Yash sai Inna….

Sun jima sosai sun fi 1 hour dan
har mota Yash d’in ya fita ya shigo da ita kafin ya tafi ko sallama bai yiwa Manubiya ba!
Ta ji mamaki matuk’a dan tun d’azu dama da ya zo ta Lura da yanayin da yake a ciki na tashin hankali firgici tsoro da kuma rud’ani tun da yazo tana kallon idanunsa ta fahimci ya ci kuka ba na wasa ba,da farko ta yi tunanin rasuwar inna ce ta tab’asa haka amma yanzu yadda ya tafi kuma ya k’i d’aukar wayarta ya sanya ta fahimci tabbas wata matsalarce ta sake tasowa bayan waenda suke a ciki.
Bayan tafiyar Yashjub suna shiga suka tarar Gwaggo Suwaiba har ta shirya Inna an sakata a makara ma wanda hakan ya sanyasu sake rushewa da kuka ko zama ba suyi ba ya Musbah ya shigo yace Baba yace “su ake jira.”

Da kyar aka b’amb’are Muhsin da Manubiya daga jikin gawar Hakanan Ya Musbah shi da Ya Nafi’u suka d’auketa a cikin makarar aka je a ka yi mata sallah suka mik’ata gidanta na gaskiya…..



Ana tafiya kaita su Yahanasu sukazo dukkansu har Yasmeen Yadira da Hajiya Mama da su Daddy.
Hajiya mama ba su had’u da Mama ba saboda da wuri suka tafi tare da su Daddy ita da su Yasmeen,Yahanasu ce ta zauna.
Ita kuma Mama a lokacin ta koma gida suka d’an kimtsawa tukunna suka taho ita da Ammi.
Yahanasu tana zaune a d’akin da Manubiya ta ajjiyeta kawai ta ga Mama ta shigo wadda dama ita maman ta san tabbas yau kam za ta
had’u dasu amma fa dukda haka sai da ta kusan fad’uwa a lokacin da sukayi ido biyu ita da Yahanasun,Yahansu kanta ta kusan suma gashi lokacin babu kowa a d’akin sai ita
A hankali jiki ba lakka ta mik’e tsaye bakinta yana wani irin karkarwa tace”maa maa!”sai kuma ta tafi da gudu ta fad’a jikinta ta fashe da wani irin kuka…
Itama Maman kuka ta saka a nan wajen ta yarda tray d’in hannun nata ta rungumeta a cikin jikinta!


Ba abunda ya fi yiwa Yahansu dad’i kamar yanzu da ta san whereabout d’in mama shikenan za ta had’a Yash da mahaifiyarsa cikin sauk’i
nauyin da ya ke a kanta shekara da shekaru yanzu zai sauk’a.
Cikin sharar hawaye ta d’ago ta kalleta tace”Mama dama kin san su Manubiya?ya aka yi kuka had’u?”
Ta yi mata tambayar waensu hawayen suna sake zubowa…..

Hannu ta saka ta share mata hawayen nata kafin ta ja hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna…nan ta faiyyace mata duk wata alak’a da take tsakaninta da su Manubiya
Tana kuka tana hawaye sannan tana dariya at the same time tace” da ma kece mama da nake yawan jin sunanki a bakin Manu?
Alhamdulillah!!
Mama na ji matuk’ar dad’in ganinki bari Manu itama ta zo na san zata ji dad’in jin wannan labari kwarai!”
Ta fad’i hakan cikin sake rungumeta.

Da sauri Mama tace mata “A’a Yaha kar ki gaya mata komai!”
Cikin rashin fahimta tace”ko
me yasa Mama?”

A take wasu hawaye suka zubo mata cikin ruk’o hannun ta tace”Yahanasu a halin yanzu ba zan iya fuskantar Hajiya mama da sharrin tarin abun kunya da aka yi mini ba,sannan mahaifinku ya sanar mini muddin ya ganni ko da a kusa da ke ne to fa abunda zai aikata a gareni mummuna ne!!”
Cikin tarar numfashinta Yahanasu ta d’ago tace”Mama duk sharri ne ba shi ne ya fad’i waennan maganganunba!duk makircin su Momny ne!”
Da mamaki ya kalleta tace”su Mommy kuma?”

“Tabbas ita ta had’a Baki da mai makarantarmu a wannan lokacin sannan asalin abunda ya faru shima duk laifinta ne!
Kar ki hukunta Daddy ta hanyar cewa kar a gaya masa an ganki na tabbatar shima neman naki yake yi yanzu haka.
Cikin gyara zama da sake ruk’o hannunta ta d’aura da cewa”
Akwai abubuwa da yawa da nakeso in faiyyace miki but first yanzu bari in kirawo su Daddy su zo Allah kad’ai ya san kalar murnar da zasu yi idan suka ganki!”

Shiruu Mama tayi dan ba kad’an ba ta shiga shock da jin sunan Mommy a cikin lamarinta!!!Mommy Mommy dai??an ya kuwa?
Sai kuma ta kalli Yaha kamar mai nazari kafin cikin hanzari ta sa hannu ta karb’e wayar hannu Yaha ta kashe kiran….
Da mamaki Yahanasu ta kalleta kafin tace”Mama pls dan Allah ki bari in…..”
Cikin tarar numfashinta tace”Yahanasu ki yi mini alfarma guda d’aya a matsayina na mahaifiyarki kar ki gayawa kowa kin ganni,inaso ace Daddy ya nemo ni ya maidani cikin zuri’arsa da kansa kamar yadda ya yi mini yankan k’auna da kansa…shekaru kusan talatin Yahanasu amma ace har ke da kanki kin fahimci sharri aka yi mini ta ya zan yarda Daddy da kansa bai fahimci hakn ba sannan meyasa bai neme niba???
Ni dai kawai inaso ya kasance ya nemo ni
ya mayar da ni da kansa da hannunsa Akan ace kece kika mayarda ni ba tare da yarda da amincewarsaba kuma inajin tsoron had’uwa ta da shi ban san ya zata kasance ba kince abun da mai makarantaar ku ta fad’a sharrin su Mommy ne ko?
To na ji na yarda amma kuma wat if ya yi mini kamar yadda suka ce zai yi d’in?dan na san zai iya aikata hakan Yahansu mutumin da ya kashe ni zai iya aikata fiye da abunda suka k’aga suka fad’a suka ce ya ce zai yi.”

Ciki girgiza kai Yaha tace
“Na tabbata idan na yi masa bayani zai fahimta zai yarda.
Kumafa Mama shi a tunanin sa kin rasu ne muma a da duk hakan muka d’auka,ki bari a yi masa bayani”


“Yahanasu idan ace ya damu to ya kamata ace by now ya fahimci gaskiya kamar yadda kema kika fahimta”
Yahansu zata yi magana Mama ta katseta ta hanyar cewa”dan Allah kar ki yimin jayayya bana son musu daga gareki ki yi yadda nace hakan shine farin ciki na.
Na fi so ya fahimta da kansa ya nemoni da kansa,hakan shine kad’ai zai goge mini abunda ya faru
Sannan bamuda tabbacin zai karb’eni Yahansu idan aka yi rashin sa’a ya tozartani Ina riba?
Ba zan so a ci mini mutunci a b’atamin suna ba dan haka na rok’ek’i da girman Allah kar kiyi komai kar kice komai,alfarmar mutunci da daraja ta a idanunki ki bari mu yi addu’a ya yi yadda nakeso d’in ko na samu peace of mind da sauk’in radadin da nakeji a cikin zuciyata!”.

Da kyar Mama ta samu ta yi convincing Yahanasu ta hak’ura ba zata gayawa kowa ba har sai Daddy ya huce ya nemota da kansa ya fahimci komai…ba dan Yahansu ta so ba ta yarda da hakan amma InshaaAllah bazata yi k’asa a guiwa ba har sai ta nuna masa hanya shi kuma ya gane gaskiya ya nemi sanin inda take da kannasa kamar yadda Maman takeso.







Washegari Jidda suka zo ita da Al’ameen nan kuwa komai ya dawo wa su Manubiya sabo fil…..sun ci kuka kamar ransu zai fita Jidda da Siyama masu d’auke da juna biyu wata uku uku kam sai da aka dangana da kwantar da su a asibiti tsabar kuka da damuwa.
A ranar ne kuma Gwaggo Suwaiba ta tashi tafiya babu yadda basuyi da ita ba amma firr tace musu ita tafiya zata yi
Wanda hakan sam bai yiwa kowa dad’i ba dan kai tsaye hakan rashin kyautawa ne…hakanan su Ya Nafi’u suka kaisu tasha ita da Hadiza suka kama hanya gidan ya rage daga Manubiya sai su Jidda abun tausayi dan ma Anty Umma tana tare da su dan Siyama ba ta wani dad’e ba aka sallamota daga asibitin,Mama kuma ita take tare da Jidda a asibiti itakam sai da ta yi sati biyu a kwance dama cikin nata ya zo da laulayi sosai tun usulinsa.

Yahansu har asibitin take zuwa ta duba Jidda su tattauna da Mama amma har yau bata samu ta yi convincing maman ba,ganin fa bazata tab’a yarda ba ne ya sanya ta mayar da hankalinta ga tunanin ta yadda za ta bawa Daddy ko da clue ne a samu ya fara bincikenta dan maman ta sanyata ta yi mata alk’awarin ba zata tab’a cewa kowa komai ba.

Sosai mama ta ji dad’in ganin kamal a matsayin wanda Yahanasun zata aura dan shima ya je ya duba Jidda kuma ya je ya yi gaisuwa.

Sai da aka yi kwana ashirin da rasuwar Inna tukunna su Manubiya suka koma gidajensu anty Umma ma ta koma gida gidan ya rage daga mai sunan Baba sai Baba Muhsin da Ya Musbah dan Bararka tunda ta fita da gudu har yau ba’a ganta ba cigiya har a gidan radio mahaifiyarta ta bayar amma shiru…shi ya Nafi’u ma ya d’auka da ta ji labarin zata yiwa mutane hauka amma sai ta big’e da bada hak’urin abunda Barakar ta yi tace dan Allah a yafe mata a tayata addu’ar nasarar samun ganin ta……..
….

Bayan kwana goma..

Yau kwanakin Inna talatin da rasuwa su Manubiya kuma goma da komawar su gidajen mazajensu…Jidda ma a nan Al’Ameen ya barta ya tafi dan saura kwana sittin ya kammala abunda ya je yi kuma exams ne Masu zafi a gabansa shiyasa tace masa tana son zama a nan su Ammi ma suka ce ya barta a nan saboda jikin nata ya yi tsanani sosai….
Ya siya mata gida mai kyau a Na’ibawa ya zuba kaya ya yi komai amma dai a hannun Ammi ya barta for now saboda kusan kullum sai an k’ara mata ruwa..sosai kuwa Ammi da Mama suke kula da ita dan abunda suke yi mata ko Inna iyakacin abunda zata yi mata kenan.

Siyama ma ta koma gidanta lafiya k’alau itakam bata wannan fitinannen Laulayi kamar na Jiddah.

A b’angaren Manubiya kuwa gaba d’aya ta gagara gane kan Yash!!tun ranar da Inna ta rasu ya chanja gaba d’aya kuma ba wai ita kad’ai ba kowa yake yiwa hakan….haka kurum sai dai ya yi shiruu ya zauna ya tusa mutane a gaba babu um babu um’um ya yi ta kallon kowa amma iyaka idanuwansa kad’ai idan ka kalla tashi d’aya zaka fahimci yana cikin masifa da tashin hankali…
Hatta office ma da Najeeb ya zo zai yi masa handing over cewa ya yi ya cigaba kawai ba zai iyaba……..
Shima da so ya yi ya chanjawa Manubiya gida amma sai Hajiya mama tace”kawai ya zo Mansion d’in Daddy su zauna a side d’insa na da dan tabbas yanayinsa yana mugun bawa har su su Hajiya maman tsoro gashi an yi tambayar duniya yace musu”he’s fine!!!”


Mommy kuwa har yau bata cire raiba……Ya’isha dai ta tafi dahirr ta ma cire rai….….amma tsohon yace mata”ta kwantar da hankalinta indai hular Manu aka d’auko
akayi aikin da ita to fa ta zuba ido
Anytime labarin rasuwar Manu zai risketa!!watak’il inna itama ta saka hular shiyasa abun ya shafeta kuma shiyasa aka samu delay na mutuwar Manubiya amma tabbas tana hanya itama….Su Yasira kuwa zuwa yanzu sun dawo daga rakiyar Mommy…babu Ya’isha babu labarinta zuwa yanzu idan suka yi mata maganar Ya’ishan ma fad’a take rufe su dashi…dukda sun san itama tana cikin masifa amma sam wannan ba abun da za su yi shiru bane dan haka Yasira ta shirya akan zata je ta samu Daddy tace masa ba fa su ga Ya’isha ba kuma Mommy ko maganar ba ta so ayi!!!
Ta san ko da matsalar ganin da take fama da shi aka barta ya isheta(dan zuwa yanzu kwata kwata idonta na dama ba ya aiki na biyun shima ya tab’u sosai)amma fa ba zata iya cigaba da yin shiru ba wallahi,dan this is a serious case.


A lokacin da Yasira suke maganar za su je su samu Daddy ita da Yusra Mommyn tana jinsu…
Shiyasa hankalinta ya sake tashi matuk’a,dama masifar rashin gani da tsohon ya ke ta amshe kud’inta ana ta yin magani amma a banza ta isheta ga Manubiya da ranta har yanzu Yash ma haka…a halin da take ciki dai yanzu ta ajjiye komai a gefe a samu ta fara gani tarr tukunna sai a yi komai su kuma su Yasira ta san ta rufe musu Baki a kan case d’in Ya’isha to amma kuma gashi yanzu kwatsam! Suna shirin jik’a mata aiki,har fa su Yasmeen ta hana zuwa gidan duk dan kar a tambayi Ya’isha a waya kuwa da suka ji shiru tace musu bata da lafiya ne ita kanta sai yanzu ta san tanada matsala fa dan Bata san me zata ce game da Ya’isha ba a gaba dan ba zai yiu ta yita b’oye b’oye forever ba.



A b’angaren Abbakar shima tunda aka yi rasuwar kusan kullum sai ya je musu gaisuwa da daddare lokacin da ya tabbatar ba zai had’u da Yash ba!
Ita dai Manu gaisawa kawai suke yi daga haka ta wuce d’aki dan abu da Abbakar sam ba ta so…to yanzu kuma ya isheta a waya yanason taimakon ta,ta yi blocking d’insa amma a banza a rana sai ya kirata sau bakwai da different layuka ga messages,dan ma Allah ya taimaketa Yash bai tab’a gani ba saboda shima he’s
not himself

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login