Showing 75001 words to 78000 words out of 244445 words
mata sallama yana kallonta yana murmushi,a hankali ta mayar ta rufe idanunta ta d’an kauda kai gefe.Murmushi ya yi ya kama kunnensa kafin yace”sorry!”
Ganin ta k’i ta bud’e idanun nata ne ya sanya ya d’an rissina dai dai saitin kunneta ya shiga rad’a mata wasu kalamai da suka sanya ta ta fara k’ok’arin tashi a gigice amman kuma ta gagara tashin,ganin k’iri k’iri ta kasa tashin ne yasanya kawai ta fashe da kuka….Cikin rashin jin dad’i yace”Wasa fa nake yi miki…so kike hawayenki su k’afe a yau ne??”
Ya fad’i hakan yana mai taimaka mata ta zauna kafin a
hankali ya sakata a jikinsa ya shiga lallashinta har sai da ya ga ta yi shiru tukunna ya mik’e ya k’arasa gaban dressing mirrow ya d’auko abinci ya kawo.Kamar jiya yau ma shi ya bata a baki yana ci yana bata tana ci yana gaya mata cewa”likita za ta zo ta yi mata allura ta bata magani”
Tana gama cin abincin kuwa lokacin dai dai 8:00am ko gama saka kaya da shiryawa ba ta yi ba wayarsa ta hau k’ara dan haka ya fita ya sauk’a cikin mintunan da ba su gaza biyu ba ya dawo d’akin ya kama hannunta suka fita wajen Dr d’in…….sosai ta ji dad’in allura da maganin ga wani bacci mai d’an karen dad’i da yake ta faman fusgar ta.
Akwai abubuwan tafiyar su da zai karb’a sannan ya kamata ya je ya ga su Mommy dan
haka yace mata ta basa 30 minutes inshaaAllah zai je ya dawo yanzu…
Sai da ya rufe koina ya tabbatar bata buk’atar komai
tukunna ya fita bayan ya ga
bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita…..shi kad’ai sai faman murmushi yake ta zubawa….ya san dama zai iya yin komai akan Manubiya amman yanzu ya sake tabbatar da hakan!Mata rahama ne,shi a
lokacin da bai fara soyayya ba
mamaki yake idan ya ga wasu mazan suna nan nan da matan su da kuma mutanen da idan suka fara zina ba sa iya dainawa sai waenda Allah ya kubutar…sai yanzu ya fahimci bayan zazzafan so da k’auna ashe wannan rahamar ce dalili….
Yana wannan tunanin ya tsaya ya karb’i sak’on nasu daga nan ya wuce gida.
Ba kowa shiruu parlourn dama ba ya son hayaniya balle a rik’esa. Zai samu lokacin su Yassira amman ba yau ba dan a halin yanzu fuskar Manubiya kawai yake son gani
Allah Allah yake ya koma gidan
besides ba zai tab’a yarda ya yi ma kansa ruing wannan momment d’in na genuine happiness da yake a ciki ba ta hanyar tunkurar su Yasira….tbh
wallahi jikinsar har ya fara karkarwa ya san za su fafata
shi kansa bai yi expecting haka ba amman he can’t help it.
D’akin Mommy ya shiga ga mamakinsa ba ta nan dan
haka ya d’auki waya ya kirata….har lokacin suna d’akin Kausar ta samu wani bacci mai dad’i ya kwasheta
anan kan sofa wayarta ta fara ringing….Baba larai ta kalla bayan ta kalli screen d’in kafin tace “Yashjub!”
Da sauri Baba larai ta matso tace”Ki d’auka duk yadda na gaya miki ki yi dan Allah ki yi
k’ok’ari ki danne zuciyarki.
Sai da ta tsinke ya sake kira tukunna Mommy ta iya d’auka dakyar ahankali tace”Yashjub!”
Numfashi ya fesar kafin yace
“Na zo bakya nan”
“Ganinan zuwa”tace
daga haka ta kashe wayar ta rik’e a hannunta tana huci.
Ba k’aramar lecture Baba larai ta yi mata ba itada Yassira wadda karatun Baba larai ya shiga kunnenta ya samu mazauni a kanta,kafin ta mik’e ta nufi side d’in nata fuskarta a murtuke,sai da ta yi da gaske kafin ta samu fuskar nan ta d’an sake dan ba kad’an ba hankalinta ya ke a tashe ji take kamar ta yi hauka! abubuwa sun yi mata yawa jiya haka ta dinga zirya har asuba tana lek’e ko za da ga sauk’k’owar Ummi daga side d’in Daddy amma shiru babu Ummi babu alamarta kuma har bacci ya d’auketa lokacin 8:49 ba ta ji ta sauk’o ba shiyasa ta kuma shiga cikin tashin hankali tana mai jin kamar ta je ta barbard’a musu fetur ta kyasta ashana!tsabar rashin mutunci ko sallar asubah ba ta ga Daddyn ya fito yi ba…..
Ko da ta zo shiga side d’in nata ma sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta tura k’ofar ta shiga dan wallahi sam ba ta k’aunar ganin fuskar Yashjub!.
A parlournta ta samesa yana ta faman safa da marwa dan ya k’agu ta zo su gaisa ya biya ya gaida Daddy ya wuce.
Sai da gabanta ya yanke ya fad’i sakamokon fresh d’in da ta ga ya yi.Su na had’a ido yad’an daidai ta kansa kafin ya taka zuwa inda take ya d’an rissina yana
kallon k’asa yace”Mommy Ina kwana!”ya fad’i hakan yana sosa k’eya.
Murmushi ta yi kafin tace”Da ikon Allah yau kunyata Yashjub yake ji.Ina ita surukar tawa?
ya ba ku zo tare ba??”.
Yanzun ma sosa k’eya yayi kafin yace”Am..tana bacci
sai zuwa jibi InshaaAllah za mu zo tare” .
Dum!!!
Haka k’irjin Mommy ya buga,da kyar ta lalumo nutsuwa ta sakawa kanta
kafin ta yi yak’e cikin son fahimtar wani abun tace”Ai dama da gajiya!”
Cikin son b’oye sirrinsu da kuma kar ya bawa kansa kunya Yash d’in yace”Ni kaina kam gajiyar bikin nan tambaya ta take yi,balle ita da ta ke mace”
Ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Yashjub ya ji ya d’an kalleta.
Da sauri tace”Inata fama da Kausar ma shiyasa ban yi muku ko breakfast ba,ku yi
hak’uri!”
Tashi d’aya Mommy ta lura da yadda yanayin fuskarsa ta chanja daga jin an ambaci sunan Kausar a ranta ta ce”Tabbas akwai aiki jaa a gabanmu”
A b’abgaren Yashjub kam hakan take da sunan Kausar da Mommy ta kirawo ne ya b’ata masa rai matuk’a,ya san matsananciyar tsana ba ta da kyau a musulunci shiyasa yake so ya d’an rage tsanar Kausar a ransa amman sam ya gagara,cikin son kawar da ita a kansa yace”Ba komai Mommy.Bara in je in gaida Daddy sai na wuce,na barta ita kad’ai.”
“To”kawai ta samu damar cewa kafin ya fice fitt!.
Binsa kawai ta yi da kallo
Baki a sake ganin yadda
yake ta uban rawar k’afa ko zama fa bai iya yi su gaisa da kyau ba,”wanne irin abu ne haka?”ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba.
Baba larai ta ce mata ta kuncewa Manu jini sannan shima yanzu a yanayin maganarsa ta d’an fahimci babu abunda ya shiga tsakaninsu amman kalli yadda yake ta rawar k’afa wannan Allah ya rufa asiri duk ranar da ya san Manubiya a mace ai ta su ta k’are!ya zama dole su yi sauri su san na yi da Manubiya tun wuri ta kama gabanta dan tabbas idan har ta bari Yashjub ya santa a matsayin ta na y’a mace to abun zai yi musu dank’o kafin su iya fitar da ita a gidan.
Daga side d’in Mommy direct side d’in Daddy ya wuce ya gaida shi….sai da yayi da ya sanin zuwa kuwa saboda yadda Daddyn ya tusa shi a gaba da tsokana har da cewa ya yi fari overnight sai wani kyalli yakeyi….har hajiya mama wadda ya shiga ya tarar suna
video call ita ma sai da ta tofa albarkacin bakinta.Ganin Yashjub yana shirin shigewa cikin k’asa ne ya sa suka d’aga masa k’afa…Daddy Hajiya Mama da Ummi wadda ta shigo da breakfast ne suka saka sa a gaba suka sake yi masa nasiha sannan Daddy ya nuna masa muhimmanci y’an uwansa yace dan Allah kar ya yi fad’a da su saboda Matarsa kuma kar ya yi musu wani abunda bai dace ba a gabanta”Daddy ya yi haka ne saboda idan akwai abunda ba zai so gani shine rabuwar kan y’ay’ansa!kuma ya san abunda su Yassira suka yi ba su kyauta ba shiyasa yake so ya yi saurin yi wa tufkar hanci tun kafin abu ya fara tab’arb’arewa tun yanzu.
Jinjina kai Yashjub ya yi kafin yace”inshaaAllah Daddy zan kiyaye”
A ranshi yana lissafin maybe Daddy ma ya ji tab’argazar da su Yassira suka yi a gidan su Manu,Daddy yau da kansa ya rok’esa abu while he’s in a good mood kuma tunda har Daddy yace’saboda Manubiya’ya san yana yin wani abun to bak’in jini zai janyo mata a wajen Daddyn,shiyasa kawai ya saka a ransa zai bar maganar ta wuce inshaaAllah ba zai yi musu komai ba amman still zai yi wa Yassira warning!…..
Maganar Ummi ce ta katse masa tunani jin tana cewa”ga breakfast d’inku chan,da har na cewa driver ya yi maza ya shirya ya mik’a muku ashe ma kazo,in kun gama ka yi min magana sai mu je in nuna maka idan kuma ya riga ya shirya gwaggo ta basa ya wuce shikenan.”
Murmushi ya yi yace”Thankyou Ummi”
Tsaf Daddy ya lura Yashjub so yake ya tafi shiyasa ya tsaida Ummi da ta ke shirin fita ta basu guri ya had’ata da Yash d’in ya sallamesa suka fita shi da Ummi shi kuma suka ci gaba da video call d’insu shi da Hajiya mama.
Ko da ya biya d’akin Yahanasu ya ga kamar bata jin dad’i ya tambayeta “me ya faru?”ce masa ta yi “babu komai”dan ta san idan ya ji to yanzun case zai tashi a cikin gidan hankalin kowa sai ya tashi,ita kuma ba ta son ta yi masa ruining special days d’insa dan yadda ta gansa cike da annuri da annashuwa hakan ba k’aramin dad’i ya yi mata ba.
Da taimakon Ummi wadda ta shigo d’akin basa basket d’in abinci aka samu Yash ya yarda ‘ba komai, kawai gajiya ne ya saukar mata da zazzab’i’
Daga haka yayi musu sallama bayan ya karb’a basket d’in abinci ya wuce nndc quaters.
A tsaye ya sameta tana d’aura d’ankwali,ta chanza kaya zuwa wani red lace mai d’ankaren kyau shima d’inkin fitted gown
ya zauna a jikinta d’ass!!kamar
ka saceta ka gudu. K’arasowa ya yi ya ya tsaya a bayanta ya rungumota yana mai sauk’e ajiyar zuciya.
Tunda ta ji shigowarsa dama ta ji gabanta ya fad’i amman sai ta dake….cikin sunkuyar da kanta ta yi masa sannu da zuwa,bai iya amsata ba sai juyo da ita da yayi ya zuba mata ido ya shiga yi mata wannan kallon k’urillar nasa..
“Ya su Mommy??”
Ta yi masa tambayar cikin son kawo k’arshen kallon.
Ahankali ya ce
“Um..l-afiya s una gaida k e”
Sai kuma yace
“K inyi k yau s osai”
Ya yi maganar kamar Yaro mai koyon magana
“Thankyou”ta ce ta d’an kallesa tanaso ta tambayesa ko ba shi da lafiya ne ta ji
muryarsa a rarrabe kuma yana d’an shivering…bai ba ta damar tambayar tasa ba
sakamokon kissing d’inta da ya fara yi…sai da tafiya ta yi nisa tukunna Manubiya ta fahimci dalilin yanayin maganar tasa,ai kuwa tace ba zai yiu ba shi kuma ya ce ba ta Isa ba!.
Tou dai wannan karon su Manubiya har da cewa “Allah sai ya yi musu hisabi!”
Tayi kuka kamar ranta zai fita! jiya ta fi jin zafi amman wahala da azaba kuwa sai yanzu ne ta san menene meaning d’insu,ashe jiya bata ga komai ba Introduction ne akayi mata…..shi kansa sai da yayi mamakin yadda ya kasa
controlling kansa ganin komai ba a hannunsa yake ba ya sa ya ci gaba da godiya ga Allah ba tare da ya san lokacin da Allah zai ba sa ikon tsayawa ba……”
After 3 days…..MANNUBIYA
(Book 2)
Page 22
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
After 3 days
Ramar da Kausar ta yi a cikin kwana biyun nan sai da ya bawa kowa mamaki,har
duhu sai da ta yi gaba d’aya ta fita a haiyyacinta wanda hakan ne ya sake tasowa da Yassir tsumin zargin ta da ya yi a kwanakin baya.A kaff cikin sisters d’insa babu wadda bai tambaya “mai yake damun Kausar?”ba,amman duk suka b’oye masa,Mommy ce ma ta sake ba da goyon bayan a b’oye masa d’in dan ta san ba k’aramin aikin sa bane ya d’aga wa kowa hankali ya hautsina komai ba tare da sun samu yadda suke so ba.
Shi kam zuwa yanzu ya san tabbas akwai abunda ake b’oye masa….ya na zargin Kausar tana son Yash tunda sai da ya yi aure tukunna ta zama haka kuma ko a baya chan ma sai wata maganar aurensa ta taso tukunna take burkicewa,shiysa ya kullaci su Mommy yana mamakin ta yadda suka yi supporting Kausar ta yi betraying d’insa….tabbas ba zai barsu ba kuwa especially ma Kausar d’in wadda a kwana biyun nan ko wajenta ya je sai ta ke yi kamar ma irin takurata d’innan yakeyi.
Munirat kuwa idanunta sun rufe ba ta ji ba ta gani har side
d’in Yassir zuwa takeyi su
sha hira su sha soyayaya,hakan kuwa ba k’aramin dad’i yayiwa Yassir d’in ba dan Munirat ta sakar masa ragamar rayuwarta….kamar yadda ta yi zato kuwa tabbas ta taimaka wajen yaye masa tunani da muradin Jidda amman fa ko kad’an ba ta samu gurbi a cikin zuciyarsa ba dan tsantsar so da kishin Kausar ne cike taff a zuciyarsa…a halin yanzu yanzu bayan san ganin bayan Yashjub babu abunda ya fi sakawa a gaba kamar ya samu ya gano gaskiyar lamari ta fannin Kausar.
Sir Najeeb ma yana cikin damuwa dan kusan kullum sai ya kira Siyama amman sam ba ta d’auka jiya kam ya san saboda shi ne ma ta kashe wayartata gaba d’aya…zai ba ta space ta huta daga gajiyar biki sannan ta d’an yi tunani shima kuma ya samu ya rabu da Ya’isha cikin lumana kafin ya fara yi mata nacin da shi kansa ya san sai ya takurawa kansa.
Jidda kam itama tana cikin matsala gashi nata problem d’in ma bata isa ta yi sharing nasa da kowa ba dan kunya takeji..dukda ta ji Mama tana cewa Inna”jikin Al’ameen d’in Alhamdulillah ulcer da hawan jini ne yake damunsa but yanzu ya ji sauk’i anma sallamosa”amman hakan bai hanata shiga cikin matsananciyar damuwa ba,all she wants a halin yanzu shine to be with him ta samu ta ga ya jikinsa su shirya su yi aurensu….ta san babu wanda zai fahimceta shiyasa ta rik’e damuwarta iya ita d’aya take fama….har ramewa ta yi tashi d’aya ta yi zuru zuru.
A b’angaren Manubiya kuwa
Yashjub ya zame mata abun mamaki….tun tana fushi tana jin haushi har ta daina,dan ita gani takeyi ma kamar he’s possessed….shiysa ta zubawa sarautar Allah ido amman fa a cikin kwana ukun da suka wuce ta gane Allah d’aya ne! ga wahala ga azaba shi kuma Yashjub bai san maganar kauda kai ko kawaici a wanga harka ba….ita kam gaba d’aya komai ya fita kanta gashi sunk’i su yi bak’o
ko guda d’aya ballantana ta samu ta huta kullum sai ta kira su Jidda amma an hanasu zuwa har y’ar rama ta yi shi kuwa Yash sai kace wanda yayi watanni da yin auren dan ya yi k’iba abunsa ya yi haske sosai ya k’ara kyau.
Yau dai Allah ya d’aura Manubiya akan Inna ta yarda akan su Jidda su zo su kawo mata ragowar takardunta da aka manta ba a had’o da su ba.
Har da su ya Musbah za a zo amman Manubiya bata saniba…Ya Musbah da Baba har ma da Ya Nafi’u ne suka
harhad’a kud’i suka yi mata
gara kuma sunyi k’ok’ari sosai. Shine za su zo su kawowa a yau.
Tun safe taketa faman zumud’i dan ma Yash ya ce “kar ta damu ya riga ya yo order”ne da tuni ta shiga kitchen….bata ma riga ta fara shiga kitchen ba saboda ya ce “sai sun dawo daga honey moon tukunna sai ta fara girki”,Ummi ce take ta faman yi musu aike breakfast lunch har dinner.
Suna zaune ta ji k’arar doorbell dan haka ta mik’e da sauri ta nufi k’ofa,murmushi yayi ya bi ta da kallo yana mamakin zumud’in da takeyi ya san kuma har da murnar freedom d’in da zata d’an samu na wunin yau takeyi.
Tana bud’ewa ta ja ta tsaya ta yi turuss sakamokon ido biyu da sukayi da Yassira ita da muk’arrabanta a bayanta har da Kausar.
Kallo d’aya Kausar ta yiwa Manubiya ta d’auke kai da sauri sakamokon bugawa da ta ji k’irjin ta ya yi!tun ba ma da ta yi yi tunanin’yanzu fa a haka taketa yawo a gaban Yashjub kwalliyar ma saboda shi ta yi.’.
A b’angaren Manubiya kuwa ba wata kwalliya tayi ba sakamokon gajiya da ciwon jikin da take fama da shi..ita batama da energy d’in yin kwalliyar.Sanye take da red lace mai adon duwatsun silver d’inkin riga da skirt wanda ya d’an kamata ba laifi kuma ya fito da asalin surar jikinta,
babu komai a fuskarta sai d’an ragowar jan jambaki da kana gani kasan sid’e wa akayi,jewelries kuwa iyaka y’an kunne ne kawai a kunnenta sai agogo.
Kayan ba k’aramin karb’ar ta ya yi ba ya haskakata
sannan yanayin simple d’aurin da tayi ya sake fito da asalin kyawun fuskar ta,ga kuma kyallin amarci shiyasa ta sake fitowa ta yi wani irin azababben kyau….
Da kyar ta iya danne takaicin abunda sukayi mata ranar da aka je d’aukota dan tana ganinsu komai ya dawo mata sabo,a take ta shiga k’ok’arin yakice abun a cikin ranta…dan a ganinta fad’a da gaba da su bashi da amfani tunda su dolen ta ne itan ma kuma dolen su ce!sannan in dai har tana son Yash ya zama dole ta so su.
Ta ji zafi kwarai amman tunda shine na farko gara kawai ta manta ta yafe but zatayi k’ok’ari wajen ganin ba su maimaita cin kashin su a kanta a karo na biyu.
Murmushi ta yi a hankali da niyyar welcoming d’insu warmly ta ji Ya’isha tace
“Yassira ki bangaje ta mana ki wuce!”
Dariya Yusra ta yi kafin tace
‘’ki yi mata uzuri, kin san a gidan tsoho dogon soro ake antayawa…sannan kin san
babu k’ofa ba door bell
shiyasa take tunanin ya kamata ta barmu mu shige musu parlour kai tsaye ko kuwa?…tunda ba ta san ya ake shiga gida mara soro ba.”
Lumshe idanu kawai Manubiya ta yi tama kasa magana ta tsaya waje d’aya nan rike da k’ofar.
Tsaki Ya’isha ta yi kafin ta taho gadan gadan zata bangajeta ta shige daidai